Sashe 9
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Adnan nayi sabuwar kawa me kirki,Adnan ransa ya baci nan take da kyar ya danne yace wace?
Wata ce sunanta Maheera kyakyawa ce sosai.
A ina take? A gaban layin nan take,Adnan yace lallai ya kamata na ganta mu gaisa
Sohail yace ba damuwa zan rakaka Sahil ma ya santa shima kawarsa ce mu kasan mace daya muke bukata,Adnan yayi dariya yace gaskiya ne mazaje yan biyu masu mace daya,Sohail yace ae mun sasanta kanmu ni da Sahil ko mace ta rungume shi nima sai tayi min nawa,Adnan yace nifa? Sohail yace direct yace a'a banda kai wlh ka kula mana mata sai gawarka.
Adnan ya jinjina kai yace matata zata zo anjima kayi girki me dadi,ba damuwa na kusa gamawa ma cewar Sohail"
Adnan yana takama ya juya ya haura sama abinsa.
Zuwa yamma Zayna ta sauka a jirgi,Adnan da kansa yaje ya dakko ta,tayi kiba ta kara kyau ga wanka yabi jiki,Sohail yana shirya dining ya gansu Adnan ya rungumo kugunta sun shigo,Sohail ya kura mata ido yaga Zayna ce,mamaki ya kamashi da alama itace matar Adnan din.
Nunawa tayi bata san ma Sohail ba,juyawa tayi ta kalli Adnan tace Baby wannan fa na tuna ashe fa kaninka ne,Sohail ko a jikinsa yayi murmushi yace yaya dama ita ka aura?
Adnan kiss ya mannawa Zayna a kumatu yace ita ce,Sohail yace sannu Aunty ya juya ya wuce part dinsa cike da mamaki,wai Adnan ya auri budurwar su shi da Sahil,baki ya tabe yace suji dadinsu ni ina ruwana da Allah zai sa ma ni kuka yazo min ai kwana zanyi ina yi naji dadin jikina,ai kuka wani Exercise ne daban,kuka duniya ne,dama shi Sohail haka kawai ma in kan ya motsa kuka yake shi kadai haka kawai.
Bayan Zayna ta huta dining suka zauna,Ibrahim,adnan da Zayna suna kwasar girkin Sohail suna hira abin su,Sohail ne ya fito ya wuce su da sauri,Zayna ta masa banzan kallo ta ja tsaki,bai ma san tana yi ba tuni yayi gaba,yana tafiya da uban sauri kamar zai tashi sama,wasu a layin sun sanshi sosai suna mutunci,sai magana suke masa amma sai dai ya daga musu hannu,ka rantse wani mummunan abu ne ya faru,bai tsaya ba sai da yaje shagon Maheera har ciki sannan yaci birki,ta dora kanta a table tana danna waya ya daki botiki da karfi ta tashi a firgice,dariya yayi yace nine,tace Oh Sohail ko sallama,kujera ya ja ya zauna yana so ya bata labari,yace bari na baki labari kinga ni gidanmu....gidanmu ..uhmmmm....katseshi tayi tace dan Allah ka kyale ni da surutun nan bana ganewa damuwa ta min yawa ka rabu dani,yace abu zan fada miki,tace no...ni kyaleni bazan ji ba kai labari ma kafin ka bawa mutum sai ya tsaya wahalar saurare.
Shuru yayi,wasu suka shugo siyayya ya mike ya fara basu amma duk ya rage kudin abin dari biyar sai yace ku bada dari biyu an muku ragi dole mu kawo canji a kasar nan mu da araha zamu siyar,Maheera ta mike da sauri ta fisge ledar kayan tace ke kudinki ba haka ba ta lissafa kudin da kanta,matar tace me shago ya mana kyauta ki hana yar bakin ciki,Maheera tace ba shagon sa bane malama ta karbi kudinta ta basu kaya suka fice suna Allah wadai da Maheera me kudi yayi kyauta ta hana.
Sohail ya kalli Maheera yana murmushi ya ja hancinta yace to bani alawa,kara maheera ta saki ta bige masa hannu tana shagwaba tace da zafi fa,Alawar ta ebo tace yau biyar zan baka ta mika masa ya zuba a aljihu tare da bare daya ya sa a bakinsa yace na gode na tafi gida.
Sunansa ta kira tace "Sohail"
Amsawa yayi ya dawo ya zauna tace ina cikin damuwa yau,na rasa wanda zan fadawa naga munfi kusa da kai, sai ya nutsu kuwa yace ae ina jinki tell me.
Tace mamana tana da lalura tana Sule ja a gida ina da kanne biyu mace da namiji nice nake kula da karatunsu,Mamana ciwon sugar ne da ita ina shan wahala ta kashe kudin magani,gashi aikin nan da na samu oga ya sani a shago baya biyana akan lokaci gashi babu abin kirki a salary din,ga kula da kaina ga yan gidanmu,ubanmu tun muna yara ya rasu,yanzu aiki nake nema wanda ya dan fi wannan ko wanke wanke da shara ne indai yafi wannan albashi zanyi,Sohail ya nutsu yanzu.
Ya dafa kafadarta yace akan wannan kike damuwa? Ki kwantar da hankalinki indai aiki ne zaki samu,zan nemo miki,kinyi karatu? Tace na fara university amma kasan bani da kudi dole na hakura yanzu ni kannena nake biyawa kudin makaranta,Sohail yace to za a samu wani karki damu kinji ke da kike da Allah,wannan ba matsala bace ki kwanta kiyi bacci in ta kama ma kina shan giya ki sha abarki aiki zaki samu Inshaallah.
Dariya Maheera tayi sosai da sosai,tace na gode to,aljihunsa ya duba ya ciro 4k yace suke nan gareni ragowar kudine da naje kasuwa siyo nama ungo ya mika mata,ta saki baki tana kallonsa yace karbi kyauta na baki kawarmu ce ke,
ta karba tana ta godiya kamar yasan bata da ko sisi sannan idan kana wajen wani a zaune dole ka dinga yiwa kanka wani abin, tace Sohail na gode,ya sake duba aljihunsa ya ciro naira ashirin yace ah sorry ungo wannan ma hada da ita.
Ta karba tana dariya tace na gode.
wajen shagon taga ya leka ya dawo da leda baka a hannunsa ya ajiye mata a table.
Mene kuma? Ta tambaya
Yace duba ki gani yana tsotsar alawa me tsinke,dubawa tayi taga naman kaza soyayye da yawa a ledar zai kai kaji biyu,ta zaro ido tace amma tun dazu baka bani ba kuma me yasa ka ajiye a waje jikin kofa?
Yace ai bana so ki gani surprise zan miki kuma na manta badan kin tuna min ba da tuni na tafi na barshi a wajen,tace kai ka soya? Yace ae,na gode sosai,yace bani daya a ciki naci karki ce na saka miki wani abu"
Maheera harararsa take tace ai nawa ne bazan baka ba,Murmushi ya fice fit ko sallama bai mata ba.
Tayi dariya kawai ta fara cin naman.
Yana komawa gida ya iske Zayna tana masifa a palo tace da Adnan ni gaskiya a kawo min mace yar aiki wacce zata dinga yi min girki da wanki da sauran hidima ta,shi Sohail ya muku naku,ni bazan iya cin girkin namiji ba,Adnan yana rawar jiki yace za a nemo yar aikin tunda haka kike bukata,Sohail yana ji yace yaya akwai wata ta iya girki sosai indai za a biyata albashi me kyau a kawo ta.
Zayna tace karka kawo mana mahaukaciya irinka fa,Sohail yaji zafin maganar amma bai ko nuna ba yace ta iya fa, ina fada muku zan kawo ta nan ta fara yi muku na gwaji,idan kuka gwadata in yayi shike nan,Adnan yace ba damuwa tunda haka kace a kawo ta gobe tayi muji,yace an gama.
Zuwa yamma likis Sohail ya koma shagon da Maheera take da sauri, Maheera tana zaune tana shan lemo da da naman da ya kawo mata, Sohail ya fado ciki yana sosa sumarsa wacce taji aski irin na kwallayen shegun gari,gashinsu kamar na mata daurewa suke da ribbon amma sun kwashe gefe da gefe an rubuta sunansu a gefe daya an saka Sohail daya barin Sahil,shima Sahil yaka yayi,Daddy yayi yayi su gyara sunki amma ba karamin kyau ya musu ba sai dai a al'adar mu ta malam bahaushe za ace ba tarbiyya.
Maheera ta kalle shi tace Sohail ya ka dawo?
Yana murmushi yace albishirinki
Goro ta furta tana kallonsa"
Yace kin samu aiki amma sai dai ba irin na classy girls bane irinku,girki ne zaki dinga yi,matar Yaya tace baza taci girkin namiji ba,shine nace akwai wata zata yi,kin san nawa zasu biyaki duk wata? Maheera tace nawa?
Yace dubu dari,idan kina aiki me kyau zasu iya kara miki ma.
Zumbur Maheera ta mike tana tsalle da murna kamar yarinya,tace wannan fa dubu ashirin yake bani duk wata!
Yes zanyi zanyi ba matsala,wayyo dadi Alhmdllh Allah na gode maka,tana murna tace Alhmdllh.
Gaskiya Sohail kai mutumin kirki ne na gode.
Sohail yace na fada miki ai ko kina shan giya ki sha abarki kiyi bacci aiki zaki samu,gobe zamu je zaki musu abinci da yamma zasu yi miki test in kinci shike nan an dauke ki,kuma nasan ma kin iya girki!
Na iya girki sosai Inshaallah zanyi kokari zan dage Sohail.
Sohail ya furta aha Sahil yace a gaida ki,kin san da za a haifo mu a tare muka fito duniya ba wanda ya riga wani zuwa,Maheera ta iya bi da Sohail ta kalle shi tana dariya tace Allah? Aradu ya furta yana daukan alawa
Dariya ta sake saki tace amma yau naji dadi come ba zato Sohail yaji anyi hugging nasa,ido ya zaro da sauri ya janye jikinsa tare da ja baya yace mene haka? Sahil fa baya nan,to wlh shima sai kin masa na rantse.
Ido Maheera ta zaro tana murmushi tace Sahil din? Sohail yace ke ba a wasa damu na fada miki sai kin masa shima ya hade rai,Maheera tace to never mind zan masa shima amma ai kaine abokina Sohail ka gane?
Ni bazan gane ba kawai malama zamu yi fada,Sorry to zan masa shike nan?
You promise? ya sake tambaya,tace yeah,yatsa ya mika mata yace mu kulla,ta kawo nata suka kulla ta furta shima sai an yiwa Sahil? yace kamar da kasa.