← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 46

Sashe 45

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni gwara kana talaka kullum muna tare,sanda kafin ka samu aiki ko kafin a kara ma girma kullum muna tare kana nuna min kauna amma yanzu komai babu ni an rabani da masoyina,kuka take bilhaki tana tirje tirje,Sohail sai faman rirrike ta yake tana fisgewa kamar me aljanu,ki tsaya na miki bayani,bazan ji ba babu abinda zaka ce dani....bakinsa taji cikin nata shuru tayi ta fara tayashi,daukanta yayi yana dariya tace da haka kake yi ai da an zauna lafiya,amma baza kayi ba sai aikin kudi, saman bed ya kwantar da ita ya fara lalube ta,Maheera bata sake korafi ba,duk da dai baiyi wani nisa ba ita hakan ya gamsar da ita taji dadi,Islaha sai gani tayi ta fito tana nishadi.
Kwanan Sohail biyu rak yace Baby kinji zanje Morocco amma bazan dade ba sati daya kawai dan Allah karki fushi,Maheera tace ohhhh ....nidai ta danyi guntun tsaki tace shike nan ya zanyi za a rabani da mijina,dariya yayi yace babu me rabamu muna tare,tace to shike nan..
Haka Sohail ya tafi daga can sai jinsa tayi sun tafi wata kasar nan ma bai dawo ba ya wuce China,bayan sun dawo kwanansa daya tal da sasaafe suka tafi Lagos,har tsoro yake ji yace da Maheera zaiyi tafiya,shi kansa yasan baya kyautawa amma ba yanda zaiyi,tun tana magana har ta daina sai dai kawai tunani da damuwa da ta taru tayi mata yawa.
A baya tana dan ganinsa taji dadi amma yanzu ganin Sohail ma aiki ne.

Tana ta hakuri sai da ta kwashe wata uku a haka baya zama,gwara ma a baya kullum ko ba komai suna tare,Islaha dinma Sahil din ba wani zama yake ba amma gwara ita,abinda ke damunta rashin lafiyarta ta kafafu sannan itama wani romance ma basa yin komai yanzu ta aiki suke yi kawai.
Yar gidan Alhaji Umaru Amatullah kullum sai ta kira Sahil kamar mayya baya dagawa,haka ta dinga masa text,baya bari Islaha ta gani yake gogewa.
Ga Alhaji Umaru ya dame shi ya fito ya auri Amatullah Sahil yaki yarda,ganin haka Alhaji Umaru ya zage ya sanarwa Daddy.
Daddy farin ciki ma yake yau kamar Alhaji Umaru ace yana so ya hada zuria da shi ai shi sai godiya da murna,jiki na rawa yace InshaAllah ko Sahil baya so sai ya aure ta,Sahil yana can su suna ta shirin yi masa aure bai sani ba.

Yau Sohail ya dawo yana gida,duk da haka Maheera ba wanda ya kaita murna,yanda suka saba soyayyar su haka suka yi bata ma nuna fushin ba tunda ta ganshi kusa da ita,washe gari da sassafe ya shirya zai fita meeting,kofa ta tare tace wlh ba inda zaka je yau na gaji,kullum aiki jiya ka dawo ina murna yau zamu zauna tare ka tashi da sassafe kace zaka je wani meeting,Sohail yace kiyi hakuri Maheera lokaci ne komai da kike gani duk don wa nake aikin nan? indai dan ni kake yi yau baza ka fita ba, Lallashinta yayi taki yarda,lallashin duniya taki yarda har ransa ya baci yace matsa to zan wuce tace wlh yau sai ka zaba ko aiki ko ni,harara ya balla mata yace matsa min a hanya,tace na fada sai ka zaba yau ko aiki ko ni fa ato ta furta tana jijjiga,Sohail ya ture ta yace na zabi aikin yafi ya furta cikin fushi,baki ta rufe da hannaye biyu tace kace aiki ya fini,juyawa tayi tayi reverse ta dawo baya ta sake youturn,ta fadi a kasa ta dinga kururuwar kuka shike nan an rabani da mijina ya samo wata yar kasar waje....taci kuka kamar ranta zai fita,ta fito part din Islaha tana hawaye tace yau wai Sohail ya zabi aikinsa over me,akaina gwara aiki yafi masa,Islaha tace babu lafiya zama bai ganmu ba,mun shiga uku gwara ke da kafafunki,Ai kuwa ba shakka wata ya samu wacce ta fiki wlh karki yarda.

Maheera ta zauna ta zuba tagumi irin tunanin mata marar kai shi suka dinga yi,Maheera bata ce komai ba ta tashi ta lallaba ta koma part dinta ta saka hijab har kasa ta nufi Office din Alhaji Saminu.
Sohail yana can a wani hotel suna meeting kamar sun samu lafiya yanzu haka suke komai na aikin sun goge.

Maheera taci sa'a yana Office ta shiga har ciki ta fadi a kasa ta zauna zaman dirshan,Alhaji Saminu yace lafiya kuwa Maheera? Tana kuka tace mijina ya daina so na ka rabani da mijina dan girman Allah indai har dan ni ka bashi aiki ka sallame shi ni kawai burina ka sallami mijina a aiki yafi min komai,indai har sabo da ni ka bashi aiki ka kore shi kawai, mijina ya daina kaunata kun rabani da mijina,na shiga uku na jawa kaina,Alhaji Saminu yace dakata kiji...ni bazan ji wata maganarka ba kawai ka kori mijina daga aiki.
Alhaji Saminu yace mijinki yana aikinsa lafiya yana samun kudi muna jin dadin aikinsa bai yi mana komai ba amma haka kawai ba laifin komai mu kore shi daga aiki,ae ai dan ni kace ka bashi aiki to ka sallame shi.
Alhaji Saminu ya buga ya buga duk wani kokari na ya fahimtar da Maheera amma taki ita kawai a kori Sohail gwara suyi soyayya ya kula da ita,yace bashi da kudi da me zai kula dake? kowa burinsa ya samu aikin yi ya dogara da kansa yanzu kina matarsa sabo da soyayya kawai kice a kore shi bai mana laifin komai ba,Maheera tace ai dai sabo da ni kace ka bashi aiki to bana so a sallame shi kawai mijina ya dawo gareni ya kula da ni.
Mamakin mata ya kashe Aljaji Saminu yace shike nan kije kiyi tunani,ni ba wani tunani da zanyi na gama kawai ka kore shi,yace shike nan jeki ba damuwa zanyi yanda kika ce tunda dan ke nayi amma wlh duk abinda ya biyo baya karki dawo min,tace naji ni a dawo min da mijina.

Bayan kwana biyu Sohail suna kwance da Maheera suna kallo a Bedroom ya dora hannunsa a kirjinta yana shafawa kawai yaji karar message,yana dubawa wai an sallame shi daga aiki aka tura masa,Alhaji Saminu ya kira a waya cikin gigita ya tambaya nan take yace laifin me nayi aka kore ni? Yace ba laifin komai kawai kamfani bazai ci gaba da aiki da kai ba,Sohail ya kashe waya ya nunawa Maheera yace kinga wai kawai an turo min letter duk kokarin da na yiwa kamfanin nan,na bada rayuwata da lokacina da komai kawai ace an koreni,idan ma kora ce akan nayi laifi ai bazan damu ba amma ace banyi laifin komai ba,Maheera gaba daya sai jikinta yayi sanyi ganin yanda Sohail ya damu ya sulale a hankali ya zauna a kasa ya dora hannaye a kai yana hawaye,tace Baby kayi hakuri Allah zai baka wani,tashi yayi yana layi kamar dan giya ya koma palo ya fada saman kujera ya kwanta kawai,Fitowa tayi yace bana bukatar wani a kusa dani dan Allah ki tafi,duk da haka zama tayi tana lallashinsa amma ina.
Sahil bai sani bama sai washe gari da Maheera taga Sohail yaki ci yaki sha sannan ko bacci baiyi ba haka ya kwana idonsa biyu taje ta fadawa Sahil an kori Sohail a aiki ne,shi kansa Sahil tambaya yake me yayi? tace sunce ba komai.
Da sauri ya taho wajen Sohail ya samu ya kulle kansa a daki kawai baya bukatar ganin kowa ma,Suka yi suka yi ya bude kofar yaki budewa sam,sai da kyar da Maheera tace zata tafi gidansu sannan ya bude kofar,Sahil ya shiga ciki ya zauna yana ta lallashinsa yana masa Nasiha akan kaddara.

Maheera kuwa ganin yanda Sohail ya canja duk ya fada lokaci guda sai kuka take,kwanciyar hankali da soyayya da take tunanin zata samu sai ma dagulewa da abin yayi.
Yar soyayyar da take rainawa yanzu babu ta kare aikin Sohail ya kwanta shi kadai yayi tunani yayi hawaye,sannan babu bacci ya daina bacci amma duk da haka yana sauraron Maheeransa bai san itace ta sa a kore shi ba.

Bayan sati biyu Rashin bacci da yake yi da kuma baya cin abinci yasa Maheera kullum cikin kuka da dana sani take,gashi tsoro take ji ta fadi gaskiya,tana ta rokonsa tana kuka dan Allah Sweet ka tashi kaci abinci so kake ka kashe kanka akan aiki,Please tana lallaba shi,ganin itace haka ya mike zai je Dining a nan wajen ya zube a sume,tayi kansa da gudu tana kuka,ruwa ta ebo da gudu ta yayyafa masa ya farfado,ta sake tafiya da gudu ta kira Sahil dawowarsa kenan daga Office yazo suka wuce da shi asibiti.

Bayan gwaje gwaje likita yace hawan jini ne ya kamashi ga rashin cin abinci da damuwa ta masa yawa,Maheera ta tsure gaba daya.
Kwanan su daya a asibiti yaji sauki aka sallame su,baya kula kowa ko magana sai dole yake yi kamar ba Sohail ba lokaci guda ya canja.

Suna komawa gida washe gari da sassafe Maheera ta saci jiki ta fice daga gidan ta tafi Office din Alhaji Saminu,da kuka ta shiga Office din tana ka taimaka min rabin raina zai mutu ya barni,bani da kwanciyar hankali,nidai dan Allah a dawo masa da aikinsa idan ma a kasar wajen zai zauna ya zauna na hakura zan jira haka wallahi ina son mijjna ba sai yayi min soyayyar ba na hakura da soyayyar,mijina ya daina bacci ya daina cin abinci magana ta gagara,bazan iya rayuwa ba nafi so na ganshi cikin farin ciki.
Dan Allah ka tausaya masa a bashi aikinsa,jarabar mummunan halina ya jawo min ina son mijina wlh,Alhaji Saminu ne ya dakatar da ita fuskarsa a daure,yace kinga Kamfani ba wajen wasa bane,taimakonku nayi kuma nayi abinda zan iya,Kina tunanin samun aiki a kasar nan sauki ne,na bashi aiki yana aikinsa normal kamfani na jin dadinsa shima yana jin dadin kamfani ya samu experience ya goge kince a sallame shi bai yiwa kowa komai ba,ku mata baku da hankali kawai aiki kuke yi da ka sabo da rashin hankali kizo kice a sallami mijinki daga aiki akan soyayya,nayi abinda zan iya,tashi ki bar min Office,Maheera ta durkusa a gaban Alhaji Saminu tana rokonsa tana kuka kamar ranta zai fita amma ya koreta gaba daya ransa a bace.
Chapter 45 · 0% Book details