← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 46

Sashe 31

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maheera ta durawa wata kawarta ashar yar burar...Walida har magana take fada min akan zata yi aure wai ta barmu da zaman kan layi kiji shegiya,tazo taga mijina wlh kamar bature,bari ku ganshi dan dai kawai na yarda da ku zan nuna muku shi,ta jawo wayarta ta nuna musu Sohail tace kalle shi,yan matan suka saki shewa gaskiya kin dace,Maheera har da wani gyara baki tace in fada muku badan yana Office ba da yanzu zance yazo ku gaisa,to a isar mana da gaisuwa cewar dayar kawar.

Ana zuwa ganin lefe haka Maheera take zakewa tana nunawa,wasu mata dangi sunzo Juwairiyya tana nuna musu Maheera cewa take baki bude musu akwatin takalman ba,a nuna musu na kayan baccin,suna daga kayan tana cewa wannan fa material ne Aunty Sa'a amma a haka kamar shadda,Mama tana jinta har ta gaji da halin Maheera rashin kunyar da take,idan kuwa Sohail ya kira waya ko su waye a gaban su zata ce Sweet ne miko min wayar ta tashi da gudu ta shige daki.

Mutanen suna tafiya Mama tace Maheera abinda kike yi ya isheni,a haka a ganki shuru shuru kamar kin shiryu kin nutsu amma sai rashin kunya kike yi,a kanki aka fara aure yau ni naji tsiya, ki taka a sannu wlh angon nan naki kin san irinsa amma ke ko a jikinki naga ma kunyar ma kin daina a gaban kowa nunawa kike murna kike yi zaki aure ki huta.

Maheera tace ba abinda zai faru sai Alkhairi Mama ki dinga addua fata na gari lamiri,Mama tace hmm kina dai ji yace sai ya jira dan uwansa babu abinda zai shiga tsakani in banda ba hankali yaushe za ayi haka,Maheera tace nifa zan iya rayuwata haka ba komai ba sai anyi komai ba dama ni ban san komai ba me zai dameni zan iya kare rayuwata a haka,dariya kawai Mama tayi tace baza ki gane bane bakya hangen nesa.
Maheera tace magana dai ta kare tunda aure ba fashi inshaallah kawai kiyi addua yafi,to shike nan Allah ya sa alkhairi.

Juwairiyya ce ta shugo gidan da wasu dinkunan tace Aunty yaushe za ayi lalle ne? Maheera tace sai ana gobe biki kar ya goge da wuri kafin a kaini ya goge,yaya gidan nawa kunje kun gano? Juwairiyya tace mun gano wlh ya hadu komai akwai munje mun kara gyara ko ina an shirya duk wani kayan kyale kyale ke baki gani ba,Maheera tace mashaallah,Mama tana ji tace nidai na shiga uku haka kika koma? So hauka ne Maheera?Maheera tace kowa fa da zamaninsa Umma,ni dama dan na samu miji na kara zama ta gari,Mama ta dora hannu a kai.

Ana gobe daurin aure Maheera ansha gyaran gashi anci lalle gaba daya ta canja tayi kyau sai kamshi take,fatarta in banda sheki ba abinda take yi,baki kullum a washe ana jin dadi za a auri Sohail.
Ranar kuma tayi yininta da kamu ya kayatar yayi kyau sosai anci an sha anyi liki iya mata amma.

Washe gari ranar daurin aure tun 4am Sohail ya farka kaya a goge amma ya wani jona dutsen guga ya sake goge musu kaya har Sahil,ga abokansu sunyi kara da yawa sun zo har mudassir me fada da matarsa shima ya shirya duk da shi a gari yake.
Su Adnan sabo da bakin ciki suka sallami me aiki Madam Oge suka ce taje gida sai bayan biki dan kar ma ta dafawa abokan da suka zo daga wasu wuraren abinci.

Suna kallo ma daga gidan Alhaji Saminu ake kawowa iri iri safe rana dare komai akwai kaci ka sha,ba a taba musu abinci ko daya ba.
Busy suka zama dan kar ma su shiga lamarin bikin kullum basa zama a gida.

Ranar daurin aure Ango ya riga kowa shiryawa suna ta tsokanarsa suna masa tsiya,Farar shadda suka saka shi da Sahil ba banbanci,da babbar riga da hula kamar a jikinsu a dinka,suma taci gyara a saka yar hula a goshi.
Turare ya fesa yafi kala nawa a jikinsa,Sahil yace Allah sarki Me Tallaja ana ta ci da rabonta.
Kawu Nafiu,da Kawu Tukur sai Daddy da abokansa mutum biyu rak sune suka zo a dangi.

Daddy ya kira Adnan a waya yace ya kamata suje,suna ta jin haushi suka shirya suka je haka,lokacin da suka je ma an rigada an daura auren 11:30am.

Ana daurawa Daddy ya tashi suka tafi yana cewa yana da meeting,Sohail ya kalli Sahil yace kaga bai tambayi ya aikin da nake ba,a ina nake yi,wanne iri ne ko a jikinsa,sannan matar ma ba ruwansa bai san wace ba,Sahil yace kyale shi ya tafi ba komai.

Abokai ne suka yi kara sosai duk abinda akeyi na biki a al'ada sunyi abinsu ba ruwansu,na nesa ne suka koma da wuri sai iya wanda suke gari su dama ba wasu abokan ne da su da yawa ba.
Amarya ta sha leshi me kyau pink and black,irin kyan da tayi ba a magana,sai da za ayi pics ango yace bazai yi ba,da kyar abokai suka sashi dole ya shiga aka musu da Amarya,sai cuno baki yake wai dole aka masa.

Su mudassir sune suka tattara kayan ango suka kai gidan Amarya,ango yace kafata kafar Sahil yazo mu tafi, 3 bedrooms ne da dakinsa,Sahil yace zan dawo ai daga baya,Sohail yaki yarda dole aka kai kayan Sahil can dakinsa idan ba haka ba amarya baza taga ango ba.

Mudassir ne yace da Sahil yayi wayo kar ya kwana a gidan ya barsu sai nan da satikai sai ya koma,Sahil yace to kamar ya gane suka koya masa yanda zai fice da dare ya dawo gidan su Adnan ya dinga kwana,yace to.

Zuwa yamma Maheera dangin su maza suka kirata suka mata nasiha sosai akan zaman aure,Mama ma tayi nata nasihar tace na sanki da son kai Maheera nasan hali karki je ki nuna son kanki,Maheera tace Allah bazan yi ba na gane gaskiya,to shike nan Allah yasa,bayan sun gama Nasiha akace ta shirya za a kaita angwaye zasu zo daukan Amarya.

Sai lokacin kuma ta fara kuka,dariya ma ta basu,angon kansa tun biki saura kwana uku basa waya sai a daurin aure suka hadu,wanka tayi ta canja kaya cikin wani material dark blue ta sha kyau sosai kamar wata yar India,kayanta da lefe komai an tattara an kai can gidanta,Maheera ta kira kanwarta gefe tace an kai min wannan takardun nawa gidana iceko bazan zo ganin gida da wuri ba sai nayi kiba na canja, Juwairiyya tace ke kama Aunty wannan son da kike masa yafi nasa ai,tace daga na fadi gaskiya sai tayi shuru.
Juwairiyya sune a kan gaba kanwar Amarya,tuni sun shige mota,Motar Alhaji Saminu itace za a sa amarya ciki.
Bayan Amarya ta shirya dattijai suka fito da ita kanta a lullube aka sata a mota,motoci sun kai goma aka tafi kai Amarya Alhaji Saminu ya bada wasu motocin da driver guda hudu,komai anyi cikin aminci da rufin asiri.

Bayan an kai Amarya gidanta kowa sai yabawa yake ana ta yi mata murna,Aunty Aisha itace tayi ruwa tayi tsaki komai sai da aka aiwatar na Al'ada,Amarya aka bari daga ita sai wata kawarta guda daya Mardiyya,itama bata dade ba saurayinta yazo ya dauketa ya maidata gida aka bar Amarya ita kadai a saman makeken bed ya sha gyara.

Shima bangaren ango abokan duk sun tafi saura Mudassir kawai,shine ya siyo kaji da kayan makulashe,yace to ango taso mu tafi, Sahil yace yanzu kaimu za ayi shike nan gida kuma,Mudassir yayi dariya,Sohail yace Shike nan kuma har abada bazan dawo nan da zama ba rayuwa kenan,yau Allah yayi tashin mu,Mudassir yace dan Allah muje ku dai Allah ya shirye ku, haka suka tafi gidan Amarya harda Sahil.

Amarya tana jin mota tace Alhmdllh dama tsoro nake ji,tace oh ina tare da Aljani da kansa mene abin tsoro kuma,Sohail ne a gaba yana shiga yace ni ba sai an nuna min gidana ba,ni da gidana ace dole sai an rakani ai nasan dakin ku kyakeni,Sahil ga room dinka Mudassir a gaida iyali,ya karbi ledojin ya mikawa Sahil nasa yace karbi, Mudassir ya dinga dariya yace butulci zaka min? dariya yayi yace to kaine da naci ai, Mudassir yace to sai da safe,mun gode sosai cewar Sahil ya raka Mudassir har mota, Mudassir yace shiga mota mu tafi na saukeka a gidan su Adnan yanda muka tsara,Sahil yace tab ga gidanmu mun dawo kace na koma bazan koma ba, soyayya fa zaka hana su yi,Sahil yace ba abinda za ayi sai an jira ni,Mudassir ya buga ya buga yaki yarda,haka ya tafi ya kulle musu gidan ya wuce room dinsa,wanka yayi yaci kayan dadinsa yana kallon film a dakinsa har yayi bacci.

Ango kuwa Amarya na zaune ya shiga da sallama,murmushi tayi ta cikin mayafi,hannu yasa ya fyalle mayafin yace mene haka kin sanni na sanki ki zauna kina boye fuska.
Har ya juya zai shiga toilet ya fasa ya dawo ya leka fuskarta yace naga kamar kinyi kuka,Maheera tace uhm rabuwa da gida wasa ne,nan ba wani gidan kika dawo ba? murmushi tayi me kyau zata yi fari yace dakata karki fara na gaji.

Dariya tayi tana kallo ya bude kayansa ya dakko wasu kayan baccinsa ruwan zuma sababbi,ya dauki man shafawarsa da turare da komai ya shige toilet,Maheera tayi murmushi tace idan ka shirya a gabana menene to,kofa ya rufe amma bai sa key ba,sai da yayi wankansa da brush ya dade yana faman shiryawa sai da ya shafa mai yayi komai har gashinsa ya gyara yana shafa turaren kaya Maheera ta gaji ta bude toilet din,da sauri ya juyo yace Allah ya fiki na shirya to,dariya tayi tace to me kake yi haka ne? Kin takura min daga aurenki kin dameni fa.

Kayi Alwala? yace yanzu zanyi ya juya baya,da tsokana Maheera ta rungume shi,Laaaaaa ya furta kamar an masa wani abu ya tsaya a haka kanta ta kwantar a bayansa tare da furta wayyo ni duniya dadi,Ido ya zaro waje yace ke Maheera uwaki ni na hadu da yar duniya wlh dama Sahil yace zaki karya alkawari,hannu yasa ya banbareta daga jikinsa da masifa yace ki daina bana so ni.
Chapter 31 · 0% Book details