← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 46

Sashe 1

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?id=6683ec1256566fe605af16a3

🪸MUMMUNAR DABI'A🪸

1-5

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
UMMEETAH MUHAMMAD

BISMILLAH

ALLAH YA KAWO MU FANS, ALLAH YASA MU FARA LAFIYA MU GAMA DA RAI DA LAFIYA.

INA KAUNAR KU MASOYANA INA KUMA GAISHE KU.

JAN KUNNE GA MASU AUDIO,DUK WANDA YA JUYA MIN LITTAFI YA KOMA AUDIO SAI YA SAUKE SHI DAGA CHANNEL DINSA.

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Labari
England

Baturiya ce kyakyawar gaske ajin karshe ta zauna tare da zuba uban tagumi tana hawaye da kuka,yara ne maza guda biyu da alama 'yan biyu ne, kyawawan gaske kana ganin su kaga ruwa biyu,hasken su bai kai na turawa ba kuma ya wuce ace na yan Africa ne,haka gashinsu ma da komai nasu gaba daya,zaune suke suna wasa.

Wayarta ce tayi kara" ai da sauri ta daga cikin harshen turancinta tace kazo kasar? wanda ta kira ya tattabar mata cewar nazo yanzu zaki gani,murna tayi tace mutum ya huta da wannan masifa ko na kaisu gidan marayu,yara sun hanani sakewa,ko club bana zuwa dama ni a club ya tsince ni muka yi aure,yazo ya sake ni ya tafi da yaransa Nigeria bazan iya ba.
Tana zaune taji Door bell,da gudu ta mike ta bude kofar ranta a bace,wani matashi ne kyakyawa shima wankan tarwada me suffar kamala da alama musulmi ne,Sunansa ta kira Ali ga yaranka na gaji ka sake ni irin sakin ku na musulmi,bazan iya ba,wannan yaran na gaji da su,ka dinga kawo su hutu,Ali dama ya gaji da wulakancin da baturiyar take masa tunda ta haihu yake fama,nan take ya sake ta, divorce paper ta mika masa yayi signing nan take itama tayi,ya duka gaban yaransa 'yan biyu ya dauke su daya a hannun hagu daya a na dama ya fice daga gidan.

Waye Ali

Ali dan asalin kauyen Jigawa ne wani gari na fulani,maraya ya taso wanda shi kadai iyayensa suka haifa a hannun kakansa namiji ya taso ya girma kafin Allah ya masa rasuwa shima sai yan uwa na kauye,Ali cikin ikon Allah Cirani ya taho birnin kano ya fara kasa lemo a faranti yana bi makarantu makarantu na yara.

A haka ya samu ya shiga University kasancewar ya gama karatun secondary gashi da ilimin muhammadiyya, cikin ikon Allah ya kammala degree dinsa,yana gama bautar kasa wani abokinsa dan gidan gwamna ya bashi babban aiki a mininstry,daga nan Ali ya auri matarsa ta farko uwar gida Asmau, tunda ya auri Asmau bata taba haihuwa ba,sunje asibiti iri iri ance a ita ne baza ta taba haihuwa ba,sabo da wannan dalili ya kara aure ya auri matarsa ta biyu Nadia, shekarar Nadia daya ta haifo Danta namiji kato kyakyawa da shi,yaci suna Adnan,Asmau ba ruwanta ita ta fawwalawa Allah murna take, mutuniyar arziki ce,ita kuwa Nadia tunda ta haihu sai bakaken magana,bayan ta yaye Adnan ta sake haifo Danta Ibrahim sai yarta mace Amal, tun daga sannan kuma bata sake haihuwa ba itama har aka kwashe shekaru uku.

Ali kuwa Business ya fara gwadawa yana hadawa da aikinsa na gomnati,kamar wasa sai ga Ali ya zama hamshakin me arziki har ta kai bazai iya aikin gomnati ba kawai ya bar aikin,bashi wannan kasa bashi waccen,ya koma hadaddiyar GRA a cikin garin Kano.

Ya mallaki kadarori na gasken gaske,har gidajen mai ne da shi state state,Ali Sa'ad ya shahara wanda duk Nigeria an sanshi,yayi fice sam har iyalan nasa basu fiye zama a Nigeria ba sai dai suzo da yawo, ganin yaransa sun dan fara tasawa sun isa a sasu a secondary school sai suka dawo Nigeria garin kano gaba daya.
Yayin da shi kuma yake fita kasashe a inda yaje club yawon bude idonsa ya hango halley baturiya ce usul kuma ba musulma ba,suka fara soyayya cikin kankanin lokaci aka daura musu aure,shekara daya Halley ta haifo masa yan biyunsa kyawawan gaske suka ci suna Sohail da Sahil.

Sai dai an samu matsala bayan sun shekara sun fara tasawa sai aka gano daya a ciki wato Sohail ba lafiyayye bane daya ne lafiyayye,daya kamar dan ruwa haka yake abubuwansa,gasu bulbul da su kuma kusan kansu daya Sahil yafi tsayi da kadan amma banda wannan basu da banbanci,ba kowa ke gane su ba ma.
Daya daga cikin Dabi'un Sohail kuwa shine idan aka bashi abinci baya ci sosai sai wasa,sannan sai anga ya girma shima kansu daya da Sahil sai kawai a wayi gari aga ya rage girma ya sake komawa yaro,ana sake tashi washe gari sai aga ya dawo ya zama kai daya da Sahil,har suka fara cin abinci da kansu,idan aka zuba musu shi Sohail sai ya dinga wasa da nashi ya juye a kasa yana wasa a haka sai ya zana zero 0 da abincin nasa.

Idan kuma ruwa zai sha sai ya samu wuri me rami ko dan kurmi sai ya juye nasa a ciki ya kafa baki ya fara sha,wannan Dabi'ar ta Sohail yasa baturiya Halley ta gaji ta bawa uban su yaransa baza ita iya ba ita kam.

Bayan sati biyu da yaransa Ali ya sauka a Nigeria Kano driver da escort suka dakko shi motocin da suke take masa baya sunfi biyar har zuwa katafaren gidansa dage wata sabuwar GRA,yaransa suna hannunsa su biyu har part din uwar gidansa Asmau ya taka,cikin shigarta ta alfarma ta sha material me tsadar gaske ta harde kafa daya kan daya tana kallon film,murmushi tayi ganin mijinta ya shigo ta mike tare da karbar yaran su biyu tace yarana sun iso,murmushi Ali Sa'ad ya saki ganin Asmau bata da matsala ko da yace zai karbo yaransa daga wajen baturiya ya bar mata tayi na'am har da murna kamar ita haife su sai zumudi take itama tayi yara har yan biyu.

Wata Allah ya bata bata so sun ishe ta ga wata tana murna an bata kyauta wanda ba ita haife su ba,Sohail ne yake ta faman rikida yana wani haske yana duhu kuma,Asmau ta kalle shi sosai tace kai wannan sai kace Nepa ana wal-duf,Ali yace wlh nifa wannan yaron ina tunanin daya dan ruwa ne,Asmau tace haba dai inshaallah ba haka bane,tace bari naje na kula da yarana kaje ka huta yau Amarya ke da kai ni nayi yara,Murmushi Ali yayi yafi so ace kwanan Asmau ne yafi zumudi sabo da Asmau ta musamman ce.

Juyawa yayi ya nufi part dinsa,Asmau kuwa tuni ta wuce bedroom dinta da yaranta 'yan biyu.
A ciki ta shirya abinta ta musu wanka dake sun san da zuwan su komai an tanada har kayan wasa, cikin fararen kaya ta shirya su tsaf abinta sannan ta kawo madarar yara ta hada ta fara basu suna sha,Sahil normal yake shan nasa amma Sohail hannu ya sa ya fisge tasa da karfi,Hajiya Asmau taji kamar babba mutum ne ya kwace sabo da yanda taji karfi sosai an fisga,kallon Sohail tayi tace sai kace Daddy dinku ne ya kwace abu irin wannan karfi haka,tana mamaki a ranta, sai taga yaki sha sam yana ta kalle kallen wurare a palon.

Rarrafe yayi ya wuce yaga babu wani waje me rami ko kwurmi a hankali ya dafa jikin kujera ya mike yana tafiya da kyar ya fice daga palon yana fitowa ya hango wani dan kwari inda akwai flower a wajen a nan ya juye madararsa ya kafa baki yana sha,Haj Asmau tana binsa a baya tana kallo,abin ya fara bata tsoro kuma.

Abinda ya kara girgizata shine bayan wasu kwanaki katsam ta nemi Sohail ta rasa,hankalinta ya tashi matuka ta shiga kitchen tana shiga ta iske shi a cikin bowl din gasarar koko da ta tace yana ta wankansa a ciki,duk inda yaga laima ko danshi sai ya tafi ciki ya zauna.

Kishiyarta Nadia ita kanta tsoron Sohail take gasu kyakyawan gaske,Yaranta sune manya Adnan ya kusa gama Jss3 shi kuma Ibrahim yana Jss 1,Amal tana primary 4.
Gaba daya Adnan bakin hali ne da shi shine wanda gaba daya ya tsani Sahil da Sohail,ko kulasu baya yi sannan ya hana 'yan uwansa su kula su ko da wasa,itama Nadia amaryar Ali haushin yaran yan biyu take ji sabo da ta gama sakankancewa itace kadai zata ci gado idan mijinsu ya mutu tunda Asmau bata haihuwa,ji take kamar ta kashe yaran ta huta sabo da tsana,duk da haka wani dadi take ji da Allah yasa daya dan ruwa ne ba lafiyayye bane,ita gani take yi Dan ruwa ne ma Sohail,shi yasa bata kallonsa a mutum sam,idan ta kalle shi ma sai dai ta dinga tuntsira masa dariya haka kawai.
Chapter 1 · 0% Book details