← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 46

Sashe 14

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sohail wayar ya kashe ya nufi bedroom din Adnan yayi knocking Adnan sai da ya gama yangarsa ya bude kofa sanye cikin gajeren wando,yana ganin Sohail ya bata rai,Sohail yace dama dan Allah kudi za a turawa Sahil zai dawo gida,Adnan ya kece da dariya ba shiri ya dinga dariyar mugunta harda shakewa yace yaji wuya,ina neman kudin? shi a dole me zuciya,ai ba abinda zai samu dama na fada muku ku hakura da rayuwa ku zauna ku dinga bautar mu kunki ji,baku da gata amma ku kunki yarda shi a dole zaiyi kudi to sai yayi kudin mu gani idan yana da kwakwalwar tara kudi.

Sohail yace arziki dai na Allah ne,Adnan yace au nasiha zaka min? Kai ka isa kayi min fada kana talaka? Me yasa baka yiwa kanka fadan ba ka zama me kudi,kayi tunani me kyau akanka ka zama me kudi in ka isa,amma ina me kudi ai kuwa nine nake da hankali da tunani,talaka ai bashi da hankali tunda ya kasa yin hankalin yin kudi.

Sohail yana jinsa yace hmm bani kudin na tura masa to,Adnan yace sai nan da 2weeks,bashi da kudin abinci fa Yaya dan Allah ka bani na tura masa dan Allah.....Adnan yace wlh na rantse sai nan da 2weeks kuma ko ka kira Daddy bazai bayarba sabo da komai naku yana hannunmu an dawo da rikon ku hannun mu.
Sohail juyawa yayi ya tafi kawai ya wuce bedroom dinsa yana rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya zame ya zauna a kasa hawaye ya fara zubarwa sosai yana kuka,ya daga hannaye sama yana rokon Allah yace Allah kaga halin da muke ciki Allah ka fitar damu Allah ka bani kudin da zan turawa Sahil,ya zauna yana addua yana kuka,ya dade a haka ya wanke fuskarsa sanna ya fito.
Maheera ya gani tana Gyara kujeru ta kalle shi taga alamar kuka yayi.

Murmushin karfin hali yayi ya zauna kawai ya zuba tagumi,Maheera zama tayi a kujera daya suna Facing juna tace Sohail lafiya? Me suka yi maka? Sohail ya kwashe labari ya fadawa Maheera yace kuma Sahil yana can ya kwana baici komai ba a kango yake kwana,Maheera tace to kwantar da hankalinka jiya Zayna ta bani dubu talatin tace na siyi kayan sawa ta gaji da ganina cikin tsumma wai kyankyamina take yi a haka,Sohail yace a hakan kika yi kalar kyankyami? Maheera ta daga masa kai tare da furta haka tace.

Aljihun doguwar rigarta ta duba tace gashi sai nayi mata karya nace tela bai dinka min kayan ba,dama dubu talatin a zamanin nan wanne kaya zata siya min na kirki kuma a garin Abuja sai dai atamfa karama da gwanjo. Sohail ya karbi kudin yace na gode Maheera,tace to ba gashi Allah ya rufa asiri ba ai dai ko a trailer ya dawo kamar yanda ya tafi.

Murmushi yayi sai yanzu hankalin Sohail ya kwanta ya fice da sauri ya nemi POS ya turawa Sahil kudin,ya kira shi a waya ya sanar masa,Sahil ya mike yana murna cikinsa ba komai ya fito daga kangon zai nemi me POS ya cire kudin,yana fitowa Islaha tana zuwa wajen a kafa tana ta dube dube tana nemansa,ido biyu suka yi ta ganshi ya rame sosai yayi busu busu da siminti ,Murnar ganinsa tayi tace ina ka shiga dan Allah Sahil yau nafi kwana shida ina nemanka

Sahil ya kalle ta yace ina nan wajen ai yanzu ma fita zanyi kika zo ina zan samu me POS? Kudi zan cire na siyo abinci,Islaha tace zo mu tafi,bayan ya cire kudin suka wuce wajen cin abinci, a nan suka zauna yace ke me zaki ci? Islaha zuciyar Sahil na birgeta yanda yake kula da mace,tace a koshe nake,ai daga gida nake fa,yace to lemo fa? tace zan sha to ta dauki nasa ta sha,yana cin abincin yana kallonta yace kika sa min baki a lemo na bazan sha ba,sai kace kazama ta dauke tace to siyi wani bari na shanye wannan din,lemonsa ya kwace yasa aka kawo mata wani.

Wani matashi ne ya zauna in banda kallon Islaha ba abinda yake,Sahil ya kalli matashin yace kai dauke idonka,Saurayin yace ai da gani budurwa ce baka da ikon hanani kallonta,Sahil ya kalli Islaha a fusace yace ke kika bashi dama ya kalle ki?
Islaha tace ni kaga nace ya kalle ni.
Idan kin san na iskanci kike nema kiyi magana tunda sana'arki ce,Islaha tana zaune ta share zancen tace nifa da zan samu wani aikin a wani gidan barin gidan Aunty zanyi.

Sahil ya kalleta kawai ya gama cin abincinsa ya mike tare da furta nifa Abuja zan koma gidanmu na fasa neman kudin bazan iya ba,Islaha tace da wuri haka dan Allah karka tafi,.
Ke da Sohail aka haifo ni bada ke ba.
A ina gidan naku yake a Abuja? Address ya fada mata,tace number waya please wlh kana da hankali kai nutsatse ne,dariya Sahil yayi yace tab ni din? dan baki san yanda ake cewa bani da hankali bane,ai har mahaukata ake fada mana,amma ai ni na sani me hankali ne,ya bata number wayarsa daga wajen ya mata sallama ya wuce Tasha a kafa yake tafiya.

Yana cikin tafiya a titi wata mota me bala'in tsada ta gaske ta fara wala wala a titi kamar zata yi hatsari Allah yasa ya ganganre kasa a hankali yayi parking a gaban Sahil.
Wani dattijo ne fari da alama bahaushe ne sabo da yana ta waya da hausa sannan kayan jikinsa shadda ce me tsadar gaske,agogonsa da takalmi duk masu tsada ne sosai,gaban motar ya bude yana tunanin kiran me gyara sai Sahil ya tambaye shi yace Baba gyara motar ta samu ne? Yayi murmushi ya kalli Sahil sannan ya furta yaro kana gani karambani yasa nayi tuki da kaina amma bana driving sabo da ido na baya gani sosai ma.

Sahil yace bude motar na duba maka to,Dattijon yace thank you ya bude gaban mota yace ka iya gyara ne? Sahil yace a'a zan gwada dai ko zan samu sa'a,Dattijon yace to Alhmdllh gwada mu gani gaba daya taki tashi ma mutuwa take a hanya.
Sahil yayi tabe tabensa ya gama yace shiga ka kunna mu gani,Dattijon ya shiga ya kunna ta tashi normal,yaji dadi yace ta dawo dai dai amma da har wani kuka take yi,Sahil yace ta warke ai baza ta kara yin komai ba,amma ka dinga kiran Engineer suna mata service akan lokaci.

Dattijon yace na gode ya zaro kudi da yawa yan dubu dubu ya mikawa Sahil,Sahil yace ka barshi akan dan wannan sai ka bani kudi bana bukata,Dattijon dai yayi ta godiya yace sunana Alhaji Isah Danjuma,Sahil yayi murmushi kawai ya juya zai tafi,Dattijon Alhaji Isa yace zo na rage maka hanya mana ina zaka je?

Sahil yace aini bako ne ma zan koma gida da kaina,Alhaji Isa yace ko kana cikin masu zuwa cirani? Sahil yace kamar ka sani.
Okay Okay da alamarka kayi karatu?
Na dai fara University aka cire mu sabo da bamu da kokari bama ganewa mu dakikai ne.
Dariya Alhaji Isa yayi yace kana da kokari mana gashi ka gyara min mota ai kasan me kake yi tabbas,karka damu muje gidana ni ka kwanta min a rai zan taimaka maka karka yi rayuwar da wasu suke zuwa suna zubar mana da mutunci hausawa.

Sahil cewa yayi na gode Alhaji a wajen Allah nake nema,Alhaji Isa yace ka taba ganin anyi ruwan kudi a duniya duk adduar ka? Sahil yace idan Allah yaga dama fa ni yayi min ruwan kudin? Ni Inshaallah Allahruwan kudi za ayi min daga sama!
Alhaji yace ba a ja da ikon Allah amma duk da haka na gode,Sahil ya juya yayi tafiyarsa yana cewa haka kawai ka cuce ni za ayi min ruwan kudi.

Tasha ya wuce ya shiga wata trailer din zuwa Abuja,rana tsaka sai ganin Sahil suka yi ya dawo a rame yayi duhu yayi futu futu,Adnan da Ibrahim suna palo suka dinga sheka dariya harda buga kafa,Zayna ce ta sakko itama daga sama ta hau dariya tace masu zuciyar neman kudi.

Sohail ne ya fito tare da janye Sahil suka wuce bedroom dinsu,Sohail yace duk ka rame sai da na fada maka karka tafi,ya fita yaje kitchen ya kawowa Sahil girki,Sahil ya zauna yaci ya koshi yace Alhmdllh Allah ka raba mu da cirani.
Sohail yayi dariya,Sahil ya shiga toilet ya dinga wanka sai da ya dade yana abu daya haka ma brush duk da yana yi kullum amma na yau na musamman ne.
Yana fitowa sai gashi fes da shi ya canja kaya masu kyau,jakarsa kuwa gaba daya kayan ciki ya zuba a washing machine ya sake wanke su,jakar ma ya wanke ta du ya shanya sannan yayi sallar Azahar.

Sohail yace tashi muje kaga Baby Maheera kawar mu,kwanaki ta rungume ni sai ta maka kaima dama nace sai ta dauki Alkawari.
Sahil yace Good hakan yayi muje,fitowa suka yi gidan ba kowa da Alama mutanen gidan sun fita,a kitchen suka iske Maheera cikin riga da skert yan kanti,Maheera tace barka da zuwa Sahil tana murmushi,Sohail yana gefe,tace ya hanya? barka da dawowa,kaci abinci kuwa? Ta tambaya tana murmushin birgewa,Sohail kawai sai yaji ai bai kamata ace Sahil ta yiwa haka ba,amma sabo da kar Sahil yaji haushi sai ya wayance yace kin fiye dariya da yawa da murmushi,saukinta ma Sahil kika yiwa amma wannan surutun da kike ba birgewa a ciki,kin fini son dan uwa nane da zaki zauna kina surutu? Ki tsaya a matsayinki,abinci dai yaci na kula da abina karki kawo mana iyayi kice ke zaki kula da shi.

Maheera tace kuka ce ni kawar ku ce duka na ma tuna da alkwarin Hugging da muka ajiye yau ga Sahil yazo shima ayi masa,Sohail yace ba yau ba sai ya huta ya gaji yanzu,Sahil yace da Islaha ce ma tayi mana nata zai fi dadi,Sohail yace wace Islaha?
Chapter 14 · 0% Book details