← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 46

Sashe 13

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa yamma Khalisat tace Sahil ya shirya su fita,Islaha ta fito lokacin ido ta kyafta masa tana makale kafada wai yace yaki bazai je ba,Sahil ya kalli Khalisat yace ni bazan je ba Islaha tace kar naje,baki Islaha ta rufe tare da sauri tace ba ruwana ni nace kar kaje? Sahil yace ido ta kyafta min tana min nuni nace wai bazan je ba.
Khalisat tace to Allah ya kamaki,Islaha ta wuce bedroom dinta da sauri,Sahil kuwa tashi yayi yace ke Khalisat kike ko wa kilishi bazan je ba,ni ba sahoramin namiji bane da zan bi mace ta fita dani yawo,ai idan ban fita da mace ba to kuwa mace bata isa ta fita da dan uwan Sohail ba,duk gidan nan baku isa ba ko uwar ku ce bazan je ba.

Haka kawai kun kawo ni gida an ajiye ni neman kudi fa nazo ba zan zauna gidan yan iska ba,Babarku ma jiya sai da tayi kawalci,ta hada kawarta da wani me kudi ya biyata kudi kuma anyi.
Itama Khairat dazu dazu ta gama waya zata samu wani a hotel senator ne kuma arnene sunansa Michiel,bazan iya ba,ga yayarku can Shema'u a gidan ta ajiye yaro matashi tana kashe masa kudi yana biya mata bukata ina zaku kai wannan zunubin?
Dakinsa ya wuce sai gashi dauke da jakarsa yana zarewa Khalisat ido yace akan ki fita dani wani yawon shakatawa gwara na bar muku gidanku ni dama bance a kawo ni ba,indai sai an kaini yawon shakatawa ne gwara na bar gidan.
Abincinku kuma kuyi kudinsa na biya ku mutanen banza,ni dan iska ne ance muku?.

Khairat da Aunty ne suka fito jin Hayaniya Sahil ya nuna su da yatsa yace duk iskancinku sai kun kyale min abu dita bata iya hasala komai,mata kun sani a gaba sai lashe lashen harshe kuke yi,bazan iya ba kuje ku zuba min magani a lemo na a rabani da mazantaka ta.

Aunty tace kai ka iya bakinka wlh gidanmu kazo,butulu an taimakeka kazo kana mana wulakanci,Sahil yana ji yace ni nace a taimake ni? Kuma badan Allah tayi ba,Baba ki iya bakinki.
Khalisat ta zaro ido tace uwar tamu? Uwar taku kuwa wata ta kirki ce,Islaha ce ta fito ta tsaya a gefen Sahil tace kuma ai ba fin wasu matan kuka yi ba asiri kuke yiwa maza ana baku kudi amma ai baku fi kowacce mace ba.

Sahil yace kuma Taskirar ma duk Infection ne a ciki,gasu nan kullum a shan magani,matukar baku tuba ba baza ku warke ba,ai dama Khairat watanta Uku bata yi period ba ai Sanyi ne da ita,inji uban wa? Aunty ta furta amma kai Aljan ne idan ba Aljan ba a gidan uban wa ka sani.
Sahil yace ai mijinki sai kunyi sharia da shi a Lahira dama kina da aure kina bin maza bai sani ba,Aunty ta zaro ido nan take ta fara hada zufa,tana kame kame,Sahil yace kuma Yaseer ba dan mijinki bane Sale me maganin yan bori shine ya miki ciki,Aunty ta shiga tsoro tace amma kai aikoka aka yi kaci zarafin mu fita ka bar mana gida.

Sahil yayi tafiyarsa ya bar gidan,Islaha suka kama suka rufe ta da duka ta musu rashin kunya sai da suka mata lilis sannan suka kyaleta yashe a kasa tana kuka,Aunty daki ta shiga ta fara watso kayan Islaha dama kadan suke jira,tana masifa tace dauki ki bar mana gida kusan inda dare ya miki,Islaha ta mike da kyar ta tattara kayanta tana cewa dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh bazan kara ba.

Aunty tana masifa tace wlh sai kin bar gidan nan dama kin ishe mu,Yaseer ne ya shigo ya iske abinda ke faruwa yana gidan yayar su Shemau,shine ke tukata a motarta duk wani iskanci da zata je Yaseer kaninta shi ke kaita sannan kullum suna tare a gidanta ko hotel,kudi take kashe masa sabo da yanda komai shi take aike, shine kamar yaronta kuma kaninta uwa daya uba daya.

Yaseer yace ke Aunty ki kyaleta 'yar gidan yar uwarki guda jini daya,wa take da shi bayan ke? Aunty tace tana da su tunda ta iya yi min rashin kunya ta bar min gida na gaji,taje ta bi bako Sahil ya bata uwar da zai bata,Islaha ta mike tana dingishi ta zuge jakarta me dauke da tsumman kayanta zata fita"
Yaseer ya rike ta tare da furta dan Allah kuyi hakuri Aunty, Aunty da kyar ta hakura ta kyale Islaha tace ta zauna badan halinta ba.

Sahil kuwa machine ya tare ya hau abinsa yace kaini Banana Island ko Lekki,Me machine yace ai nan yankin bama shiga da machine wani wajen amma zan kaika kusa da Banana sai na ajiyeka ka shiga mota,Alright muje.

Me machine dai wuta yake kawai a titi ta wajen wata katuwar gada suka zo wucewa mutane 'yan cirani gasu nan fululu,Sahil yace sauke ni a nan ga gidanmu,Me machine yayi dariya ya tsaya yace nan ne gidan ku? Kace Banana Island ko Lekki,
Na fasa zuwa can to ko zaka min dole ne? Sahil ya furta ransa a bace.
Me machine yace ni a wa! bani kudi na kawai,Sahil ya bashi kudinsa ya wuce shi kuma ya nufi kasan gada.

Mata da maza ne a wajen ga karuwai nan iri iri wasu a nan suke badalar su idan Allah ya taimaki mace ta tara kudi ko ta hadu da me kudi sai ta kama gida a wata unguwar ta koma shike nan taci gaba ita.

Sai faman kallon Sahil suke yi,ga maza nan wasu duk sun bar kayansu a wajen sun tafi neman kudi,Sahil ya tsaya yana ta kallon wajen in banda kazanta da wari babu komai a wajen,kamar zaiyi amai ga kudaje na dole wanda kazanta ta kawo su ta dole.

Sahil gajiya yayi da tsaiwa ya tsallaka gefen wasu flowers yayi fitsari,ashe ba a fitsari a wajen sai gani yayi 'yan sanda sun zo sun kama shi,daya a ciki da rashin mutunci yazo yana kiransa da Aboki zai mari Sahil hannun dan sanda baras ya balle ihu ya saki ya tsuguna a wajen,Sauran su tunaninsu kuskure ne yasa Oga ya karye,suka fincike jakar Sahil a jikinsa,duk yana kallon su bai ce kala ba,cikin yan sandan su biyar daya a ciki ya rataya jakar a kafadarsa ya cakumi kugun Sahil yace muje Office suna masifa ya jawo Ogansu ya karye,Sahil ya kalle su yace ku jani ku kaini Office din,Suka fisgo Sahil amma suka ji gam gam kamar sun taba jikin katanga,sai da suka hadu su hudu ko zasu iya daukan Sahil amma gam gam a tsaye,kuma yana motsa jikinsa yana komai amma sun kasa,tsorata suka yi,wanda ya rataya jakar Sahil ya fara kokarin cire jakar zai bashi abarsa amma jaka taki ciruwa.

Yayi yayi ya cire jakar ya kasa,sauran suka tayashi amma taki ciruwa,Sahil suka dawo suna roka Oga please....hannu Sahil ya daga musu yace na yafe muku kuje kawai,wanda jaka taki ciruwa a kafadarsa ya kwabe fuska zaiyi kuka yace Sir....Sir....please....yana nunawa Sahil jakar ya fara sheshekar kuka,Sahil ya barsu a cikin rana ya juya zai tafi ai binsa suka yi da gudu,me jaka yana faman tiri tiri da ita ya rike Sahil tare da durkusawa a kasa yana bashi hakuri yana rokonsa, wanda ya karye kuwa yana yashe a kasa rike da hannunsa yana ta ihu da danasani.

Sahil hannu yasa ya janye jakarsa a kafadar dan sanda sai gashi dansanda ya mike yana murna suna godewa Sahil,Sahil yayi tafiyarsa ya barsu.
A haka ya dinga garari a gari idan ya gaji ya samu waje ko jikin bishiya ya zauna ya huta,ga ruwan sama ko yaushe sai dai ya nemi wajen fakewa.

Bashi da inda zai kwana gashi ruwa zai iya tsinkewa komai dare,tafiya ya dinga yi har ya samu sabon gini kango ne an rufa shi kofa da window ba a sa ba,ciki ya shiga ya ajiye jakarsa a nan sai da ya huta sosai sannan ya samu ya fita ya nemi abinci ya siya ya dawo ya zauna ya cinye abinsa ya sha ruwa pure water,a nan ya kwanta bacci ya kwashe shi wurin duk yashi da siminti.

Islaha ce kwance tana ta tunani ko Ina zai je oho,mikewa tayi tana kwance ta zuba tagumi a hankali ta mike ta dauki wasu kudi ta saka rigar ruwanta a saman doguwar rigar atamfarta wata maroon ta fito.

Tana ta duba Sahil unguwa unguwa bata ganshi ba,ta nufi kasan gada inda marasa galibu suke tafiya taje ta duba ko ina babu shi,ta sake hawa machine tayi ciki ta kangon da Sahil ke kwance ta wajen ta wuce haka ta gaji da nemansa ta koma gida cikin dare.

Washe gari ma da wuri ta tashi ta gama ayyukanta ta sake fita nemansa duk inda tasan yan cirani na zama sai da taje bata ga Sahil ba,har sai da ta kwashe 5days kullum sai ta fita nemansa,shi kuma yana cikin kangon sai dai ya fito ya siyi abinci ya koma.

Kudinsa ya kare bashi da ko sisi babu kudin siyen abinci,Sahil sai da ya kwana ya yini bai ci komai ba ruwa ma a wani pampo ya samu ya sha,zama yayi a cikin kangon yace gwara na koma gida kawai wannan ciranin bazai yuwu ba babu riba a cikinsa,gwara na kira Sahil ya turo min kudi na koma naci gaba da bauta bazan iya ba.

Please call me ya yiwa Sohail nan take Sohail ya kira shi,yace ya lagos din ko ta samu ne? Sahil yace Allah ya tsinewa lagos wlh gwara arewa mutum yana cikin mutunci da sutura,ni dawowa zanyi gida ka nemo kudin mota ka turo min,Sohail yace da wuri haka? Yace ai gwara ka dawo gashi me shago ta zama kawar mu,Sahil yace nemo kudi ka turo min jira nake yau na kwana na yini ba uwar da naci kaje ka roki Adnan a bani kudi dan Allah yunwa zata kashe ni.
Chapter 13 · 0% Book details