Sashe 42
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baturiya tana kallon su ta gane su,sai washe baki take tana faman kallon su tana hawaye,tazo zata rungume Sohail ya matsa da sauri yace inaaaa... Maheera yau sai ta kwana tana kuka,da turanci tayi magana kasancewar bata jin hausa sai gaisuwa ta iya shima dan ta taba auren Daddy ne,tana ta musu turanci sai suce su basa jin turanci in ta iya hausa tayi in bata iya ba ta kama bakinta kawai,tana ta faman magana da turanci shuru,da kyar dai Sohail ya danyi turanci yace su basa jin turanci wacece ita ance babarsu ce,tace ae itace, Sohail yace ga kudi dai zamu baki kyauta ki koma amma karki kara cewa ke uwar mu ce,mu bamu da wata uwa,rokon su ta fara su yafe mata,Sahil yace wlh baza mu yafe ba,sai Allah ya tuhume ki a lahira,shuru tayi sai kuma ta fara tambaya Muslim? Muslim? Wai musulmai ne?
Sahil yace sallah biyar kullum harda Nafeela,kwana nan zamu tafi makka duk wani dan bakin ciki sai dai ya gani ya kyale,yaudararsu zata yi Baturiya tace itama tana son musulunci,Sohail yace a'a kar a shigo mana wlh in ta shigo yanzu taci banza Aljanna zata je, ta gama kare rayuwarta a club taci duniya da tsinke har ta tsufa yanzu ta shigo ta wuce Aljanna baza ta sabu ba,Sahil yace Jesus ma ai Annabi ne ko mu musulmai muna son Jesus kuyi zaman ku kawai,Hausa suke bata wani fahimta,haka ta shiga mota ta bisu suka nufi gida.
Suna zuwa gida suka ga wasu kartai su uku sun fito daga gidan nasu da gudu sun haye saman machine sun bar wajen kamar zasu tashi sama,a kofar gate Sohail yayi parking suka bar Halley a mota suka shiga gidan da gudu,Islaha ya samu tana jan kafafu a palo ta kasa tashi gaba daya tana uban kuka,Sahil yayi kanta da gudu yana tambaya lafiya? tace bazan iya tashi ba wlh sun cutar dani,Sahil ya girgizata yana tambaya me suka yi miki? Su waye,ban sansu ba nima idonta yana rufewa a wajen ta fadi luuuu ta sume.
Sohail shima part dinsa ya shiga ya iske Maheera ita lafiya normal bacci ma take bata san me akeyi ba.
Wajen Sahil ya fito da gudu lokacin Halley ta shigo ciki da akwatinta,Sohail yace ka dauke ta mu kaita asibiti,daukanta Sahil yayi suka nufi asibiti.
Halley harda shiga mota ta bisu,an manta da Maheera tana bacci ma,suna tafiya mutanen dai suka dawo gidan suka shiga part din Sohail,a firgice ta tashi taga kartai a kanta su uku suna shirin yi mata fyade,Maheera ta samu waya dake gefenta ta bugawa wanda ke kokarin cire wando,haukace musu tayi kawai suna kokawa sosai da su,wani a ciki ya kifa mata mari yafi biyar sai da fuskarta ta kumbura.
Su Sahil har sun danyi nisa a mota,Sahil yace sauke ni Sahil na koma gida Maheera tana can,Sohail birki yaci ya juya da motar ya sauke Sahil shi ya wuce asibitin,Sahil yana shiga ya samu ma sun fara cirewa Maheera kaya tana ta ihu.
Duka daya ya yiwa me shirin fyade ya zube kasa a sume,sauran suka ja wanda ya sume suna kokarin guduwa Sahil yayi kansu ya dinga lodar su kamar zaiyi kisan kai sai da yaga basa motsi,Maheera kayan jikinta ta gyara,tana hawaye, 'yan sanda ya kira,suka zo suka tafi dasu sannan ya zauna a gidan tare da Maheera yana jiran Sohail ya dawo ya dauke su,ba a dade ba ya dawo ya dauke su suka tafi asibitin gaba daya.
'Yan dabar da aka kama waya kawai aka yiwa yan sanda a daren aka sake su ko kwana basu yi a Police station ba sabo da suna da daurin gindi,Su Sahil basu san har an sake su ba ma sun tafi.
Sahil ko magana baya iyayi sabo da tsananin damuwar halin da yake ciki,tsoro yake ji kar ace fyade suka yiwa matarsa yanda suka yi yunkurin yiwa Maheera.
Free page 1&2 400
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
51-55
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM
Page naki ne
Baby Ak
MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA.
Asibitin suka koma ana ta kula da Islaha ana bata agaji,bata farfado ba sam har gari ya waye twins suna asibitin tare da Maheera,suna zaune sun tasa Islaha gaba,Maheera tace kuje masallaci kuyi Sallah,Sahil yace to sallar ma zan iya kuwa,addua zaka yi mata ai,Sohail yace muje,fitowa suka yi suka tafi Masallaci,Sallar nan ba a hayyaci Sahil yayi ba,Maheera a ciki tayi sallah tana zaune suka dawo asibitin,har 9am Sohail yaje ya musu take away na abinci ya kawo,babu wanda ya iya cin komai har me siyowar.
Sai can wurin 11am Islaha ta farfado idonta ta bude a hankali tana kallon su Maheera,Suka koma jikin gadon da sauri suna tambayarta ya jikin,Sahil yace wai me suka miki ne? Maheera ta kalle su tace da sauki idonta ya ciko da hawaye sannan tace Allura suka yi min a tafin kafafuna duka biyu bazan iya tafiya ba yanzu,Sahil yace Innalillahi wa Innailayhirrajun amma akan ace fyade suka miki gwara wannan,tana kuka tace to ai ba a san Allurar mece ba,watakil ta guba ce suka yi min mutuwa zanyi shike nan ta karo sautin kukan ta.
Maheera hawayen tausayi ya zubo mata tace baza ki mutu ba inshaallah ba ita suka miki ba,babban likitan ne ya shugo yana suka fada masa halin da ake ciki,yace ku tsaya akwai test din da za ayi za san wacce allura ce,nan take yasa aka maida Islaha wani bangaren daban,test suka yi mata na gaggawa,sai bayan an duba likitan ya kira su Sohail yace, to gaskiya zan fada muku Allurar da suka mata baza ta sake iya amfani da kafafunta ba a duniya,kafafunta baza su iya amfanuwa su motsa ba itace Allurar da suka yi mata,babu kuma wani waje da zaku je su iya maganin abin ko da kuwa za ace kasar waje ce.
Sahil yace ai ba kune Allah ba zata taka watarana inshaallah ni bazan yarda da maganarku ba,Allah yana nan zai mana maganin abin,likita yace ina muku fatan hakan,yanzu a jikinta kalau take lafiya,komai na jikinta zaiyi aiki kafafu ne kawai sai ku siya mata wheelchair aci gaba da ganin likita kafin aga me Allah zaiyi.
Sahil jiki a sanyaye suka fito Maheera kadai suka fadawa,a ranar suka canjawa Islaha asibiti wanda yafi wannan tsada,washe gari suma suka yi iya binciken su abinda waccen likitan yace suma shi suka fada,komai sai dai Maheera ke yiwa Islaha Sahil yana tayata duk da cewa ma Allah yasa tana amfani da dukkan sassan jikinta,kafafu ne kawai suke da matsala. har sai da suka zage asibiti sun kai bakwai duk abu daya suke fada.
Islaha sai da ta matsa sannan suka fada mata me ake ciki,taci kuka da kyar aka lallasheta,Sahil yace nifa akan suyi miki fyade gwara wannan din yafi min,Islaha tace gwara fyaden daga ya wuce ai shike nan amma wannan bazan fa yi tafiya ba na zama gurguwa ina ji ina gani,Sahil ya kalleta yace haka aka ce miki to zaki yi tafiya inshaallah,Aunty Aisha da Alhaji Saminu sai sintiri suke yi a hanya,Daddy sun fada masa amma ko zuwa baiyi ba sai waya kawai,su Adnan sun dawo daga tafiya sunji labari amma ko leke ba a gansu ba,har suka gama yawon jinyar su suka koma da Islaha gida a Wheelchair Sohail yace InshaAllah nan gaba har kasar waje za a kaita a gani,Maheera ce ta gyara kujerar Sahil ya dora Islaha a kai suka shiga cikin gidan.
Islaha ta shiga damuwa matuka,abinta tafi karfi yafi karfinsa,hawaye ne ya gangaro mata ganin Sahil yayi wankansa ya fito ita kuwa sai dai a kaita a zaunar da ita,kallonta yayi yana murmushi yace ke komai kuka sai kace baki san kaddara ba ki godewa Allah kina amfani da hannunwanki da komai kafafune fa kawai,yanzu in na kaiki toilet komai zaki iya yiwa kanki ai da sauki,a gabanta ya tsuguna tana goge hawayenta tace ina Amarya yanzu idan ka gaji dani fa a haka wata zaka auro,tunaninki kenan? Ni da kika aure ni a marar lafiya fa? A haka fa kuka ganmu kuka iya auren mu baku ji komai ba kuka ce kun ji kun gani sai nine akan lalura ta faru kuma ba ke kika dorawa kanki ba kawai sai na juya miki baya,ki daina fadar haka please.
su Sohail ma sun manta da Baturiya tunda ta bisu asibiti ina tayi oho basu ko tuna ba.
Toilet ya kaita da kansa tayi wanka da brush,ya taimaka mata ta daura Alwala sannan ya fito da ita har yau bai san ya jikin Islaha yake ba baya kallonta ba sutura,Maheera ce ke mata komai yau ma sai da ta gama ta daura towel yaje ya tayata alawala ya fito da ita.
Sallah tayi a zaune ta sha magunguna sai ga Maheera ta kawo abinci a katon tire,Sahil yace ya zakiyi Maheera hutu bai ganki ba sannu Allah ya biyaki,murmushi tayi tace wai ina Mummy baturiya ne kunce tazo ina take? Sahil sai yanzu ya tuna ma yace ni tun ranar ma ban ganta ba,ina tayi ne? Basu san ita tun a daren ta nemi hotel tayi tafiyarta ba,taga sam basa ma kulata sun manta wajen su tazo.
Sahil yace ai tana da wayo koma ina tayi zata fito ba yarinya bace.
Maheera tace Allah ya kyauta muku to,Sahil yace Ameen jeki to kinga ni nan Amarya ce,Islaha ta saki kuka tace ni ka daina ce min Amarya haka ake amarya a nakashe,Maheera ta fita tana dariya,mai ya dakko yace yau zan fara aikina,ni baza ka shafa min ba zan iya abina,harararta yayi da wasa ya cire towel din juyawa tayi da sauri ya kifa kansa a saman bed yace bazan iya gani ba,na jawa kaina nayi zaton shege ne ni ashe ba haka bane,dariya ya bawa Islaha tace tab a haka ake mazajen? Ai da mata basu yi aure ba,miko min rigata da nayi sallah na maida jikina,Idonsa a rufe ya miko mata ta saka sannan ya bude idonsa yace kai yau naga abinda yafi karfina,abincin ya jawo ya zuba musu ya dauketa tare da dorata saman bed ya zauna a gefe suka ci abincin nasu tare.