← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 46

Sashe 11

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida Maheera ta koma tana murna ta samu wacce suke kira da maman Rahmat a palo,maman Rahmat tace yau ya naga yarinya ta tana murna?
Maheera ta bata labarin samun sabon aikinta da salary dinta,ta bata labarin Sohail,Maman Rahmat tace Alhmdllh sai dai zanyi missing zaki barni na daina cin girki me dadi amma na tayaki murna Allah ya taimaka ya bada sa'a,a kula sosai a tsare mutunci,sai kiyi waya ki sanar da yan uwanki da Mamanki ko?
Maheera tace ae anjima da dare zan kira su,kema ki kira Oga fadlu ki sanar masa ya nemi wani ko wata,Maman Rahmat tace yanzu kuwa zan sanar masa inshaallah,Yaran Maman ma suna tayata murna" tashi tayi ta shige bedroom tana cewa thanks.

Washe gari da safe da wuri Maheera ta hada wasu kayanta a akwati me kyau ta tafi gidan su Sohail,har kofar gida me taxi ya sauke ta,knocking tayi dake Sohail ne ke bude gate basu da me gadi,shuru ba a bude ba sai da ta gaji ta turo karamar kofar ta jikin gate sai taga ta bude kawai ta shugo.
A compound ta hango Sohail yana zaune a kujera ya harde kafa daya kan daya yana ji ana knocking bai kula gate din ba,tana shugowa ya bude idonsa da yake a lumshe ya kalle ta kawai,ta karaso inda yake tace Hey,Hey shima yace sannan ya wani tafi dogon tunani sai da ya jima a haka tana tsaye tana kallonsa sannan yayi zumbur ya mike yace oh wai kece?

Akwatin ya fisge a hannunta yace idan an hanaki daukan heavy abu bakya jin magana kawo muje ciki,ta bishi tana murmushi suka shiga ciki ya nuna mata bedroom hadadde kamar dakin amarya yace ga room dinki,tace na gode Sohail,ya hade rai tare da furta ki daina min godiya ki godewa Allah,tace ai ina gode masa yace wannan ke ta shafa,kije ki ma matar gidan girki kafin 5pm suma su Adnan kiyi musu nasu,Maheera tace to ta mike ta wuce kitchen.

Tana tsaka da girkin Sohail ya shugo sanye da jallabiya wata fara dangalalliya duk kaurinsa a waje fari kal me dauke da kwantaccen gashi me kyau yace yana kallon Maheera ya aikin? Murmushi tayi tace Alhmdllh
Yana murmushi yana sosa gashinsa ya furta ko na tayaki?
tace a'a na gode,zai kara magana tace jeka kawai karka jawo min a koreni a aikin nan suce wani abu muke yi ka rufa min asiri,Okay....okay...ya furta yana kallonta ya juya ya fita ya barta tana aikinta, kamshin girkinta ya cika gidan,tana gamawa ta shirya dining Sohail yana can yana wanke mota.

Maheera sai da ta tambayi Zayna ko za a miki wani abu Hajiya? Zayna tace no sai anjima ki dora abincin Ogana, okay tace,taje kitchen ta kwashe ragowar a plate da Spoon ta fito har inda Sohail ke wanke mota,tace ga abincin naka,yace harda ni? tace ae mana,yace ki daina dafawa dani kar su gani suji haushina ke 'yar aikin su ce ba 'yar aikina ba,to yanzu dan kaci abinci sai ya zama matsala? Yace hmm kawai......Adnan ne ya shigo da motarsa wata benz me shegen tsada,a idonsa yaga Maheera tana mikawa Sohail abinci,mantuwa yayi ya dawo gidan shima.

Fitowa yayi a nutse cikin suits me tsada yana danna waya,yana zuwa inda suke tsaye ya dakawa Maheera tsawa sai da ta firgita,yace ke waye ya dafa abincin da kike bashi? jikinta ya hau mazari tace ni..ni...nice na dafawa Hajiyanka shine da ya ragu na bashi.
hannu Adnan ya sa ya fatalar da plate din a hannun Maheera,abincin ya watse a wajen a kasa ya furta look daga yau ke ba yar aikinsa bace,ni na daukeki aiki ni kadai zaki yiwa aiki tare da matata da kanina,idan ba haka ba zan koreki a aikin,idan yana son yaci abinci ga kitchen ya dafa da kansa.

Juyawa yayi ya kalli Sohail yace ka dakko abin shara ka share nan kayi clearing komai ya ja tsaki ya juya abinsa ya wuce ciki.
Maheera tace ikon Allah haka kake shan wahala? Murmushi Sohail yayi yace rayuwa kenan ya za ayi ko a jikinsa ma taga ya dakko abin shara ya share wajen tas ya tattara plate din ya maida kitchen.

Maheera tana ta kallonsa cike da tausayinsa,yace kina ta kallona zan dafawa kaina karki damu.
Jikinta a sanyaye ta koma ciki gaba daya tausayin Sohail ya kamata duk tunaninta dan aiki ne suka dauke shi a gidan.

Daddy Ali ne ya kira Adnan ya sanar masa cewar zaizo Abuja wani aiki zai kawo shi amma a ranar zai koma kano ba zama zaiyi ba,Sohai ma bai sani ba washe gari Zayna a kitchen ta samu Maheera tace ke Maheera kike ko wa? kiyi abinci lafiyayye da wuri before 2pm surikina zai shigo,Maheera tace Alright ma.
Ta fara girke girkenta Sohail ya sameta yace yau girki da wuri? Wai surukin Madam ne zaizo,Sohail baki ya tabe yace na sani ai,sun fada maka ne? Yace sai sun fada min ma,ko sunanki ai ji kika yi na fada miki to ko basu fada min ba na sani yana hanya yanzu ma.

Maheera bata karyata shi ba,kira Sohail yaji Ibrahim yana kwala masa kamar zai fasa gidan,Maheera tace jeka ana kiranka,fitowa yayi da sauri,Ibrahim yace kawo min glass of juice,Sohail ya koma ya kawo masa lemo glass cup,yana karba yace jeka dakina zaka ga wani note book green ka dakko min shi sauri.
Sohail ya wuce sama da sauri har hadadden dakin Ibrahim yana dubawa ya hango notebooks guda uku daya green,daya blue,daya grey color,Sohail ya dauki daya ya duba yace wanne ne green din a haka ya daga sama yana karewa ko wanne kallo,blue din ciki ya dauka yace yesss....wannan shine green ya fito ya kawo.

Ibrahim takaici ya kamashi yace wannan yayi kama da green? shine green din? Sohail yace idonka baya gani wannan ai shine green,wannan color din itace ta dace da green haba Yaya kalli ko idon naka computer ta fara kashe shi,uwarka ce computer din ai.
Sohail ya furta ai kuwa da mun huta sai muyi ta danna ta ba ruwanmu muyi game muyi kallo,computer uwar mu guda ai sai game kawai,tsaki Ibrahim ya ja cike da takaici ya fisge littafin ya tafi da kansa ya dakko abinsa.

Sohail ya bi littafin da kallo yace wannan ne green? blue fa ka dakko,Ibrahim yace Sohail dan Allah tafi ka bani waje just go....
Sohail ya nuna hanya yace na tafi kake nufi?
Ibrahim bakar magana ya fada yace a'a ka zauna nace,Sohail ya dawo palo ya zauna tare da harde kafafu yace na gode Yaya yana dagawa Ibrahim gira kamar dan iska,Ibrahim yace kai Sohail karuwa ka gani a nan a zaune? kana wani daga min gira kamar dan iska yaga karuwa.

Sohail ya sake kashewa Ibrahim ido yace ai mu idan iskanci zamu yi karyar karuwa ta kama kafar mu,dariya Ibrahim yayi ba shiri,yace gaskiya haukarku shahararriya ce, Sohail yana jinsa yace Yaya Ibrahim jiya Allah kaje kayi iskanci da wata mace sunanta Bilkisu,mamaki ya kusa kashe Ibrahim,yace a gidan uwarka?
Sohail yayi murmushi yace Allah kayi Sex da wata kuma shine na farkonka ta rinjayeka,ka cuci kanka tunda kakai wannan shekarun baka taba yin iskanci ba sai jiya,duk shekarun da ka kwashe kana hakuri sun tashi a banza fa.

Ibrahim ya hade rai yana muzurai yace kai karka min sharri zanci ubanka,in nayi ma ina ruwanka? Ku aljanun naku ma munafukai ne,Sohail yace shike nan dama tambayarka zanyi...Adnan ne ya shigo palon,Sohail yace Yaya Jiya Ibrahim yayi zina,dubu dari ya bawa karuwar,budurwarsa ce ta kaishi ta baro.

Adnan ko a jikinsa yace to ina ruwanka munafuki yayi din rayuwarsa ce bazai huta ba,idan ku baku da lafiya shi kalau yake,mu da lafiyar mu,Sohail yace ba a dai kuri da lafiya,mu ko zazzabi ai bama yi sam.
Tashi yayi ya bar wajen nasu,Suka ci gaba da hirarsu shi da dan uwansa.

Ali ne ya karaso da escort dinsa motocinsa da securities dinsa,Sohail ne ya karasa jikin motar Daddy dinsu ya bude masa kofa,Alhaji Ali ya fito ya sha farar shadda,kana gani kasan akwai kudi,Sohail yace Daddy ina kwana barka da zuwa,Daddy yayi dan murmushi bai ma amsa gaisuwar ba kawai tambaya yayi ina Adnan? Sohail yace Adnan kafi kowa? Daddy yace wanne sunane haka sabon nick name ya samu? Sohail yabi Daddy suna tafiya yace to ai kai kace kafi sonsa kaga ai yafi kowa ka sa masa kafi su kawai.

Shuru Daddy yayi suka shiga ciki,Sohail sama ya haura yana kwalawa Adnan kira Yaya ka fisu kazo ga ubanku yazo,da Adnan yazo Sohail ya kara furta ka fisu kaje ubanku ya zo,kai fa banda kai? Adnan ya tambaya.
Sohail yace to gashi nan wa ya sani uban mu ne ko ba shi bane Allah ne ya sani,Adnan ya ja tsaki ya wuce abinsa.

Zama suka yi suka gaisa da Daddy suka fara hirar aiki da harkokin kamfani da yanda kudade suke shigowa,Zayna tana cikinsu a zaune suna ta hira abinsu,Sohail kuwa yana dakinsa sai da ya gaji ya fito ya wuce kitchen ya samu Maheera tana fitar musu da abinci,tayata yayi suka shirya abincin a dining,Daddy Ali yana kallo ko a jikinsa sai ma murmushi da yayi yace Sohail akwai aiki wai ina Sahil? Sohail yace yana Lagos,Ali bai ma san dansa ya tafi Lagos ba,Ali yace amma baku fada min ba?
Wanda kafi so din naka basu fada maka ba?
Ali ba kunya yace wallahi basu fada min ba, Kai Adnan me yasa banji labari ba?

Adnan yace wata harka ta samun kudi Sahil ya samu wacce zai tsaya da kafafunsa,aiki ne me tsoka kuma shi yasa muka amince ya tafi,duk wani kudi da komai mun bashi yana can ya fara aikinsa ba matsala yana samun kudi,Daddy ba bincike yace to ai hakan yayi amma Sahil zai iya tsinana wani abu kuwa a duniya? Kar ya zubar min da mutunci ina so zan fito takarar gomna next year, Adnan yace to wa ya sani ne zanje na bincike shi naji.
Daddy yace kayi gaggawar hakan bana son abinda zai taba min siyasa ta.
Chapter 11 · 0% Book details