← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 46

Sashe 15

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabuwar kawace nima na yo mana ita Allah ta hadu tafi wannan ma Maheera din,Sohail yace kai anya kuwa zata kai wannan? Ta kai wannan hankali? Sahil yace tab Islaha dai bata da hankali ita can na tsinceta tana duniyanci,yarinyar nan ta dinga nuna min barikanci,ni Sahil zata yiwa bariki Allah ya kamata ai,Yanzu ma da zan taho harda kuka,Sohail yace ubanta ne kai to da zata yi kuka,ga Maheeran mu.

Maheera tana jinsu tana ta dariya tace ayi maka hugging dinka ko? Sohail yace ance sai gobe ba yanzu ba,muje dan uwa kyaleta tayi aikinta,ka daina kulata sosai sabo da kar a koreta a aiki,Sahil yayi dariya dan shi bai gane nufin Sohail ba yace to ni dama ai ban fiye magana ba.

Fitowa suka yi Islaha anya ta kai wannan kuwa Sohail ya sake tambaya dan abin ya tsaya masa ance zata fi Maheera,Sahil yace sai ka ganta kawai za dai suyi kai daya da wannan din sai dai kamar Islaha din ta fita cola shape,Sohail yace ji karya kai yunwar lagos ta kashe ma ido.

Sahil yace fatar Islaha zam flour suluf suluf,Sohail yace uhm ita wannan din ance maka garin masara ce fatarta? Libis take itama,Sahil yayi dariya yace naga rayuwa a kira Maheera na bata labarin Lagos,Sohail yace ni yafi cancanta ka bawa domin nine jininka,fafur Sohail yaki yarda.

Zuwa dare Maheera ta fito kallo palo ta samu sai Sahil da Sohail kawai,Sohail ya ganta cikin kayan bacci doguwar riga har kasa me dogon hannu,yace me kika fito yi? Tace kallo mana,Koma daki kiyi baccinki,ba a so mace ta dinga kaiwa tsakiyar dare har 10 ta wuce tana kallon aikin banza shedanu zasu shigeta koma ciki.

Maheera tace kallon bazan yi ba haba Sohail fuska ya bata ya kalleta ransa a bace juyawa tayi ba shiri ta koma ciki,Sahil yace mace sai da muzurai ka birge ni.
gobe zamu je ka rakani muyi sabon aski cewar Sahil"
Sohail yana kallo yasan askin Sahil ya lalace amma sai yace ai askin ka fes yake bro,ba sai kayi ba,ni ya kamata nayi sabo kalli nawa fa duk ya lalace kai kuwa fess kake kana taba gashinka zai lalace.

Sahil yace baka isa ba sai naje ya zaka barni na dawo kazami,bakin ciki zaka fara min? Sohail yace Allah ya kiyaye ni nayi maka bakin ciki Sahil im sorry muje taren.

Washe gari suka yo askin su iri daya gashi yaji gyara,Sohail Allah Allah yake kar Maheera taga Sahil,sai kuwa suka sameta a palo tace kaiiii mashaallah kunyi kyau yan biyu na rasa wa yafi kyau ma,Sahil ya harareta dan me zaki yabe ni ke mama ce? Maheera baki ta bude tace daga abin arziki? Sahil yace ae bana so a yabe ni,Sohail yace yawwa a kyale mu yana hararar Maheera suka wuce.

Maheera tace uhm ai kan yana kubucewa dole sai anyi hakuri da ku,Sai da suka yi wanka Sahil ya kwanta bacci Sohail ya fito wajen Maheera tana kitchen tana musu girki,yace kika ce kin rasa wanda yafi wani kyau a cikinmu? Maheera ta manta ma ta fada,tace ai kamar ku daya amma kace baka da kamarsa zaka iya bar masa ni ma,Sohail yace ae zan iya mana ance miki damuwa nayi dake ko sonki nake?
Maheera tayi shuru ya ja tsaki ya fice.

Sai bayan Sahil ya tafi da kwana daya Aunty ganin ba kowa a gidan ta kori Islaha tace tafi kisan inda dare ya miki,kije duk inda zaki a duniya na gaji da ke tunda baki da wani amfani a rayuwa,sabo da bakin hali anyi anyi a hadaki da mazan arziki kinki,ashe abinda kika yiwa Alhaji Umaru kenan? Na tura ki har hotel ki tayashi kwana ashe da maganin bacci kika tafi kika zuba masa a lemo sai da yayi sati bai farfado ba yana bacci,kin kusa kashe bawan Allah,sai yau ya kirani a waya ya fada min sai da aka kwantar da shi a asibiti.

Islaha tace to kawai ni sai naje yayi iskanci dani ni kuwa na zuba masa maganin bacci a lemo ya sheka bacci,nayi kwanciya ta na sha bacci na da safe na fito.
Aunty tace kinwa kanki hada kayanki ki kara gaba,Islaha ta dauki jakarta tace a bude taskira lafiya,watarana mazan zasu daina yayin ku duk tsafinku,Aunty da gudu ta bi Islaha har Islaha ta fice da gudu daga gidan.

Tasha ta wuce ta shiga motar Abuja da kudin asusunta da ta tara sunfi dubu hamsim,dake karamar mota ce zuwa dare sun sauka bayan sallar Isha,Direct gidan da Sahil ya bata address ta nufa ruwan sama ake tsulawa kamar da bakin kwarya haka me mota ya sauketa ta fito,tuni ta jike sharkaf sai rawar sanyi take,tanaturo karamar kofar gate din taji ta bude ai kuwa ta fado gidan.

A ranta tace gaskiya batan kai nayi ta ya Sahil zai kasance a irin wannan gida,duk da cewar komai kalarsa ta me kudi ce amma yanda taga yana fama da talauci ta ya za ace nan ne gidan,har kofa ta nufa tayi knocking ruwa na zaneta,Sahil ne a palo shi kadai yayi zugum ya zuba tagumi kasancewar yau yaci uban aikin da Ibrahim ya sa shi me wahala duka motocin su sai da ya wanke,ya share compound ko ina,ya gyara fulawowin da suke gidan ko ina har garden.

Tashi yayi cike da gajiya ya bude kofar, tsayawa yayi kamar gawa sabo da tsoro,idanuwansa ya murza sosai ya bude ya ga dai ita ce,kumatunsa ya buga yace ba ita bace Sahil dawo hayyacinka,ya ga dai tana nan,hannu ya mika a hankali tare da rike hannunta a tsorace yaji dai mutum ce,yace ah'ah lafiya?
Nice fa Islaha ai Aunty ce ta kore ni shine na taho nan.

Kuma ki rasa wajen wanda zaki taho sai wajena,Kizo ayi miki ciki ko wata matsala ta faru ace nine,Islaha tana rawar sanyi tace dan Allah ai da mace a gidan,Sahil matsawa yayi daga kofar yace wuce ciki,ta shige da sauri ya kulle kofar, Ibrahim ne ya fito ya bi Islaha da kallo yana gadara,yace ke me ya kawo ki nan? Sahil yace na santa kawata ce hanya ta biyo da ita zata tafi soon.

Sabo da mugunta Ibrahim a ransa yace Allah yasa kayi mata ciki tunda baku da hankali masifa ta afka muku a ja ku can a kulle a prison kowa ya huta da jaraba Allah yasa,Mamaki ya tsaya yi ina suke samo yan mata haka ne full option shi kuwa duk baya samu duk kudinsa da motar da yake hawa,a fili ya kalli Sahil yace kuke nan kawo mata gida wannan tazo wannan tazo bakwa gajiya da zinace zinace ne sabo da Allah yayi muku kyau sai ku dinga lalata yaran mutane an muku fada kunki ji,kuje duniya ce zata yi muku karatu da kanta,wai dan ya bata Sahil a gaban Islaha.

Zayna ce ta fito cikin kana nan kaya riga da wando 3qtr farare ta sha kyau sun mata kyau amma ba ruwanta da kannen miji na kallon surar ta haka take fitowa cikinsu suna kallo,

Tana zuwa ta kalli Islaha,ran Zayna ya kara baci tace a ranta a barni naji da wannan yar aikin Maheera ita kadai ga wata an kara kawo ta na rasa wacce tafi kyau ma a cikinsu.

Zayna a fili tace wannan fa? Sahil yace sabuwar yar aiki ce aka kawo miki zata dinga miki wanki da guga,Zayna tace kuma me yasa ake kawo min mata irin wannan munana,Maheera da kyar na karbe ta ga wata me kiba a duwawu duk sai jika mana palo take da ruwan jikinta dan Allah jata can kuje ta furta tana yatsina.

Islaha kuwa Ibrahim da Zayna ta gasawa harara suna kallonta tabi Sahil suka tafi,dakin Maheera ya kaita,ya samu Maheera tana linke kayanta yace ga bakuwa anyi wata ce sabuwar yar aiki me wankin Zayna,Murmushi Maheera tayi tace to bismillah amma kinci dukan ruwa shugo.

Islaha ta shugo jakarta a cikin leda yanda ruwa bazai sameta ba,Maheera tace ga toilet shiga kiyi wanka,room din yaji gyara yana ta kamshi ta shige toilet tana cewa na gode,Wanka tayi sannan ta gabatar da Sallah Maheera ta kawo mata lafiyayyen abinci,taci ta koshi,Maheera ta kalleta tace ya sunanki ne? "Islaha" sunana, mashaallah sunana Maheera ni,Nice to meet you,nice to meet you too.

Kwanciya suka yi a bed dinsu suna hira sama sama cikin kankanin lokaci suka saba,Sahil kuwa a bedroom ya samu Sohail yace Islaha fa tazo,ban gane ba? Yace wannan kawar tawa bata gari ba,ni wlh bana so tazo ba ta gari bace,Sohail yace ba komai muyi musaya na baka ta garin Maheera ka bani wannan zan ji da ita ni zan sa ta dawo ta gari,Sahil yace to sai dai haka muyi musaya kawai ni da Maheera kai da Islaha,Sohail yace congratulations ka samu ta gari.

Washe gari Islaha ce ta taya Maheera suka yi girkin tare,Islaha tace muje mu gyara gidan,Maheera tace karki fara ma idan ba so kike masu gidan su ci mutuncinmu su kore mu ba,su Sahil ne suke yi aikinsu ne kuma baka isa ka taya su ba,Islaha tace ni na isa,naga alama tsoro su kike ji.

Sohail ne ya fito Islaha ma bata banbance su ba tace Sahil ina kwana? Sohail yace ba shi bane,Sahil ne ya fito ta shiga kallon su shima tace ina kwana Sahil yace ni yanzu ba naki bane munyi musaya nida dan uwana,Islaha zata yi magana Maheera ta dan taba ta alamar ta amince,Nan take tace to.
Chapter 15 · 0% Book details