← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 46

Sashe 19

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Sohail Ya dau wanka kace shine me kamfanin yana kamshi ya fice da sauri yana gyara agogo,Adnan da Ibrahim suka bishi da kallo sun ganshi da takardu,Ko kulasu baiyi ba bai ma nuna ya gansu ba ya wuce,dariya suka yi Ibrahim yace ana asarar wanka a hanya,Adnan yace wallahi dariya suke bani.
Sohail kuwa sai da yaje aka masa iso ciki wajen Ogan,yana shiga yaga yar yarinyar Oga Saminu kyakyawa da ita tana wasa a Office din,shi ai ya samu abin so sai ya dauketa yana dariya yace taho muyi wasa,yana ta mata wasa,Saminu a duniya yana so yaga me son yaransa,ai sai yaji kaunar Sohail,Yace kaine wanda Maheera tace? Yace ae nine ya mika masa hannu suka gaisa,daya hannun kuma yana dauke da yar Saminu,yace kaine wanda zata aura kenan mashaallah kamar ba dan kasar ba,Sohail yayi dariya yace haka ma dan uwana yake baza ka gane mu ba,zama yayi ya nutsu yarinyar tana cinyarsa,Oga Saminu sai wani washe baki yake an dauki yarsa,yace sauketa muyi magana to,Sohail ya ajiyeta yace Maheera tace nayi kokari na nutsu shi yasa zan ajiye wannan yarinyar kuma yanda tace sai na dage sosai kamfaninka sai yaci gaba a duniya,Alhaji Saminu yace Alhmdllh na yaba da kwazonka wlh,ka kwanta min a rai kuma naci alwashin baka duk wata gudunmuwa,Sohail yace na gode.

Takardunsa ya duba ya kalli yanda duk A1 ne da shi,yace ga kokari kuma,Nan take ya kira wani yaronsa yace Idris ga wannan kaje da shi office dinka ka fara masa training ka koya masa komai yanda muke tafiyar da company din nan sannan ka nuna masa yanda zai dinga tsara aikin a computer da abinda zai dinga yi,yace Okay Sir a wanne fannin za a ajiye shi,ka fara nuna masa wannan matakin zan tura maka me zaka nuna masa idan ya iya nan da 3days zan dawo da shi Office dina nan ma sai naga kwazonsa to ni nasan matsayin da zan bashi,yace an gama Sir, ya ja Sohail suka tafi,inda aka ci sa'a aikin daga wanda za ayi a computer sai takardu,Sohail ga Aljanu kafin azo a koya masa waje ma ya iya,Idris mamaki ya kamashi yace wai ka taba aiki irin wannan ne? Sohail yace kai dai muci gaba kawai,Idris yaga abin mamaki yau,idan ya bashi aiki kafin wani dan lokaci ya gama aikin,Aikin Idris da sai yayi wata yana abu daya sai yaga Sohail cikin lokaci kadan wai ya gama shi,ya duba kuma babu gyara ko tangarda.

Suka dawo fannin takardu duk paper daya ko a cike take da rubutu kallo daya ya gama da ita ya jawo wata mamaki ya kama Idris,kallo daya ya karanta ya fadi komai da ake nufi,Aikin da aka ce sai 5pm za a gamawa Sohail 12pm an gama shi,Idris ya saci jiki ya tafi Office din Alhaji Saminu ya dinga bashi labarin abinda ya gani,Saminu yasan wani labarin nasu yaji dadi,a ransa yace in hakane wannan kamfani zai ci gaba aiki da me aljanu irin wannan akwai dadi,nan gaba in naga yanda abin yake babban matsayi zan bashi kai har manager zan bashi na duka kamfanunuwa na su koma hannunsa indai yana da amana.

Sohail aka dawo da shi Office din oga Saminu kawai ya bashi System ya dinga zuba aiki,Office Office aka dinga kai Sohail sai gama musu aiki yake kamar inji ko inji bazai haka ba,Oga murna kawai yake,kuma idan suna shawara yanda kamfani zaici gaba sai aji ya kawo shawara me amfani wacce tafi ta kowa,Yau Oga yinin farin ciki yayi a Office.

2pm nayi sai ga Maheera dauke da Flask na abinci lafiyayye ta shiryo shi ta kawowa Sohail,bata shiga Building din ba daga bakin gate ta tsaya ta kirashi a waya.

Fitowa yayi ya wani soke biro a bayan kunnensa shi ga ma'aikaci,Maheera tayi tayi dariya ta more,yana zuwa yace sabo da na soke biro a bayan kunne kike min dariya,me kika zo yi? Abinci na kawo maka,murmushi yayi tare da shafa gefen fuskarta yace na gode wai so na kike ne? Maheera tace a'a kawai kaunarka nake,Kauna? Ni bana son Kauna kawai so nake so ya furta yana turo jajayan lips dinsa,ni zan tafi ko ka ci abincin ka bani na koma da shi gida,Haba ki sha wahala ki kawo kuma na cinye na kuma baki ki tafi dashi ai idan nayi haka na zama Adnan marar Imani,kije zan taho da su,please karka manta,bazan manta ba Hajjaju kin kusa zama Hajiya,a makka za a daura mana aure,Dariya Maheera tayi tace hmm,yace Allah da gaske nake da ni da Sahil da Islaha dake zamu tafi a daura mana,Sahil ne waliyyi na,ki fada a gidanku,Maheera tace ba ruwana sai kace aljanu ne zasu daura,yace to shike nan,ina siyan mota zaki ganni na daukeki munje gidanku naga danginki,ranar Mamanki ta shiga uku ta lalace da kudi,kudi dai kudi dai,ke har wani kudin zan bata nace ungo wannan ki zubar da su me rabo ya tsinta,Maheera tana ta dariya.

Flask din ya ajiye ya matsa jikinta sosai kamar zasu manne da juna,rungumeta yayi yace na gode,jikinta ta kwace ta karfi ta matsa baya tace ana kallon mu fa,kuma ni ba matarka bace,Sohail yace ke da a kauye kika girma ba a san me zakiyi ba mene haka? Dariya tayi ba shiri wai Sohail ke fadar haka,juyawa tayi ta fara tafiya zuwa yayi ya dauketa cak ya tafi da ita a haka tana cewa ka sauke ni wai mene haka iskanci ne fa wannan,Sai da yayi nisa ya sauketa yace na rage miki hanya,karki ta wahala,murmushi ta saki ta juyo tare da tsura masa kyawawan idanuwanta,juyawa yayi yace bye ya koma ciki da sauri.

Abincin da ta kai masa sai da yaje Office din Oga Saminu ya bashi yace ko zaici yace na gode na fita lunch yanzu, wajen Idris yaje yace suci tare,tare suka ci abincin na Maheera,Idris sai santi yake.

Sai 4pm suka tashi,Oga Saminu yace Sohail muje na saukeka a gida naji ma unguwar mu daya ashe,ya sake furta Sohail tabbas babu tantama zan baka aiki sannan nan gaba ma zan canja maka matsayi inshaallah indai muna raye,Sohail yayi ta godiya suka fito,Driver ne ya bude musu mota suka shiga katuwar motar Saminu ta gani ta nunawa sa'a suka wuce gida.

Suna tafiya Sohail yace gaskiya Sir baka nuna kai me kudi ne,magana ta gaskiya ka dinga cin kudinka,a yanda kake da kudi ya kamata a dinga ganinka da securities da motoci na binka ko uku ne,sannan sutura ma gaskiya ka godewa Allah ka dinga saka me tsada,kalle ni fa bani da sana'a siya mana akeyi amma takalmi na kadai sai ya siyi yadin jikinka,Alhaji Saminu yayi dariya yace kullum fadan da mukeyi da matata kenan wallahi,ita dole sai na canja ni kuma haka nake ban damu ba,Gaskiya ka canja ai shine godiyar Allah din aga banbanci,Alhaji Saminu yayi dariya yace amma a haka ake ce muku baku da hankali gashi muna magana ta nutsuwa,Sohail yace to da aka daukeni aikin za a bani mota wai?

Alhaji Saminu yace za a baka mota me tsada ta gaske sannan za a baka gida a estate me kyau,Sohail sai murna yace dama mun iya mota tun muna yara kawai dan kara gogewa zamuyi, mashaallah cewar Alhaji Saminu,ya sauke Sohail a bakin gate dinsu ya wuce gida, Sohail ma ya shiga gida dauke da takardu a hannunsa da aka ce ya karanta a gida ya cike su.

Yana shugowa ya samu Adnan da Ibrahim a zaune a palo suna ta aiki a System sun saka Sahil Mopping yana ta mopping haka kawai akan Zayna tace su Islaha ne suka yi Mopping shine suka ce wallahi sai ya sake yin sabo.

Sohail yana shugowa ya karbe Mopper din yayi jifa da ita yace muje dan Allah,Adnan ya zaro ido yace Sohail nine na sashi da tsawa yayi maganar, Sohail tsawar yayi shima kamar wani zaki yace bazai yi ba na hanashi,ai mun fada muku mun daina aiki a gidan nan aikin kudi muke nema sabo da haka baza muyi ba muma aikin da zai amfane mu muke nema,Ibrahim yace a tunaninku zaku samu aiki a haka? Sohail yace zauna ka sa wasa sai na zana muku Zero wallahi,Sifili ba saina zana muku shi ya furta tare da jan hannun Sahil suka haura sama,Suna shiga daki Sahil yace ya aikin?

Alhmdllh suka zauna a bakin gado ya bashi labarin aikin,Sahil ya dinga murna yace har mota za a baka da gida? Sohail yace me tsada ma ina fada maka amma muyi shuru kar mu fada su, Maheera kawai zamu fadawa ko Daddy bazai ji ba sai dai a ganmu da abinmu,Sahil yace mun faso gari muma,ai kana aikin nan ina ta kallonka,Sohail yayi dariya domin yawanci ana nuna musu aljanun,shege ai na ganka har Oga sai da ya baka kujerarsa ka hau kayi masa aiki,tafawa suka yi kamar abokai,yace bari nayi wanka nazo,kaga takardun da zan cike,duba ka karanta ka cike min,Sahil ma kallo daya kamar Aljani ya dauki biro duk yayi sai kace yasan kan aikin kuma daidai yayi shima.

Islaha ce ta shiga bedroom ta samu Maheera tana bacci tace ki tashi sweetynki ya dawo daga Office,ido ta bude kadan tace bana son iskanci waye Sweetyna yayi ta dawowa mana,abinci ne ai yasan inda yake ko kije ki kai masa,baya ta juya tare da komawa baccinta.

Sahil yana fitowa yaga Amal tazo gidan itama yau ta kawowa yan uwanta ziyara,ta sha Shadda fara,Zayna ya shiga kira Yaya ta palo.....Yaya ta Palo....Zayna...ki fito kinyi bakuwa kanwar miji tazo azo a nemi shiga,kin san dangin miji masifa ne dole sai ana yin shishigi da neman taskirar zama wai bazai ce gindin zama ba.

Amal tana wani kallon up and down tana tabe baki tace wace kuma Yaya ta palo? Sahil yace Zayna ce, to mece idan ba Yaya ta palo ba matar da mate dinmu ce,sa'ar mu ce fa duk mace akace shekarun mu daya da ita ai ta zama Yaya ta palo kuma.

Amal tace lallai Ibrahim kun bari yaran nan suna shanawa shi yasa suka raina kowa,wallahi da ina nan azabar da zasu sha sai sun kwammace ba a haifo su ba yan iska mahaukata marasa kwakwalwa,ba ilimi ba komai sai jahilci da hauka.
Chapter 19 · 0% Book details