Sashe 41
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Islaha tunda taje ba wanda ya bata sisi a kudin aurenta,Lalai tsoro take ji bata iya cewa Islaha komai bata ma iya sata aiki sai dai idan tayi girki Islaha tana ci sai ta dinga gallawa Islaha harara,ko bi ta kanta Islaha bata yi sam.
Sahil yau ya kira Islaha yace yaya sun baki kudinki kuwa? Islaha tace sisi basu bani ba,Sahil yace to kyale su karki tambaya kinji,tace to dan Allah iyaye nane karka musu komai yace ba abinda zai faru ai.
A daren cikin dare Baffa Gali yana tsaka da bacci sai yaga an daga shi sama sai ya tabo rufin kwano sai a sake shi ya fado saman tarin wata kaya,kayoyi ne cako cako kamar Allura haka ake masa kawai,ihu yake da kururuwa mutane suka cika gidan cikin dare ba a ganin kowa ba a wanda ke ganin wasu kayoyi a wajen,sannan ba a ganin Baffa yana tashi sama amma Baffa Gali Ihu kawai yake da kururuwa a kwance,jikinsa duk yayi bula bula kamar an caccake Allura,yana zan bata kudinta wallahi ban cinye ba na tuba,yanda aka yiwa Baffa Gali shima haka sauran duk wanda suka ci kudin nan ba wanda ya kwana lafiya,Amma Abdulrazaqu shi yaci banza duk zagin da yayi ba abinda aka masa.
Da sassafe sai ga matar Baffa Gali da kudi a katuwar leda ta kawo gidan Lalai ta damkawa Islaha tace gashi nan ki irga kwandala idan babu kiyi magana dan Allah inji Baffanki Gali,yanzu suna asibiti duk an tafi dasu,anya Islaha ba Aljanu zaki aura ba?
Islaha tace me ya faru da su? Lalai ta fada saman gado ta kudundune tace kudin Aljanu a dakina ku fitar min da shi,na dade ina tunanin Islaha da Aljani take soyayya,wlh ni nasan me na gani sanda na kwana ina daka,Islaha tayi dariya ta more tace Lalai duk son kudinki ga dubu ashirin ko kifi kya ci,Lalai tana lullube tace Allah ya kiyaye, Islaha ta ja kudi ta boye kasan gadon Lalai,Lalai ta fice da gudu ta bar gidan,tun daga ranar Islaha kadai ke kwana a gidan, Lalai ta koma gidan dangi sabo da akwai kudin Aljanu a dakinta.
Yau Sahil yana Office wani Hakeem shima babban ma'aikaci ne yazo ya bashi key din sabuwar mota me tsadar gaske yace ta zuwa aiki ce dama suna bawa mutum mota yawanci.
Murna wajen su Sohail ba a magana.
Biki yana ta kankama kamar wasa nan ma Daddy sai Iv ya gani kawai an kuma saka masa marigayi,baiyi magana bama yasan halin su.
Ana gobe daurin aure Ibrahim da Adnan suka bar gari ma gaba daya suka wuce kasar waje sabo da kar ma suje.
Ango ma ba wata gayya da suka yi,mudassir yayi yayi suyi gayya suka ce sun gaji da biki ba a dade da yin na Sohail ba,ba a fi wata biyu da wani abu ba baza su wahalar da mutane ba,mutane yan tsirari ne suka je daurin auren,Islaha dai gyaran jiki sai ta dawo birni za ayi mata,tana can zaune gidan Lalai ita kadai kama mayya,kowa tsoronta yake ji zance ya watsu Aljani zata aura.
Ana gobe Maheera da Aunty Aisha suka tafi can ,suka samu Islaha ba abinda ya shafe ta a dangi duk an guje ta sabo da tsoron Aljanu,ita kadai ta hado cefanenta ta dora katuwar tukunya wai miyar biki zata yi,Maheera suka dinga dariya,Komai na girki ta tanadi abinta a cikin kudin auren ta iba,Aunty Aisha tace me zan gani haka? Dariya Islaha tayi tace to sunki zuwa gaba daya dangina sun gujeni,wallahi kowa naje har gida na fada musu gaba daya dangin uwa dana uba duk na fada musu har makwafta duk sunce baza su zo ba,gidan Baffa Gali har rokon su nayi mazan dai sunce za a daura aure da su a bisa laluri,Maheera suka shige dakin Lalai suna ta mamakin kalar kauyen da gidan da Islaha take,kayansu suka ajiye suka fito,Islaha har girki tayi musu suka ci abin su sannan suka fara girkinsu su uku rak,Maheera da Aunty Aisha masifar Tausayin Islaha suka ji wai ita kadai a gida,ga dangi ma ace an rasa me zuwa biki,Aunty Aisha tace Allah wadaran wannan dangi naku,baki mori yan uwa ba wlh,tace uhm.
Sai da suka yi nisa dare yayi suna ta aiki sannan matan su Baffa Gali suka zo,sai makwafta suma suka yi shahada suka shugo,ana yin sallar isha suka gudu.
Su uku suka yi miyar su ta taushe da tuwon shinkafa da safe sai farar shinkafa da miya an yanka cabbage daban,pure water aka siyo da yawa,kafin yan daurin aure su iso sun gama komai sunyi wanka,Idon Amarya duk ya tasa sabo da hayaki.
Sai 12 angwaye da su Daddy suka zo Daddy sai tsaki yake yana korafi,a rasa inda mutum zai nemi aure sai wannan kauyen.
Sohail,Ango da abokai suna motar su sai nishadin su suke yi,Ango yace yau Islaha shike nan sai abinda nace da ita kuma,Sohail yace uhmm zaka gane kurenka ne.
Sai 2pm aka daura bayan an idar da Sallah,ana daurawa Sahil ya mike yace ku tashi abinda ya kawo mu ya kare an gama,Daddy ne ya ja babbar rigarsa wai yayi shuru,Sohail yace yau ba ruwanka Ango lukwi cikin bargon ku,Baffa Nafiu ya harare su,Mutanen kauyen sai sallallami suke angwaye yan iska ne.
Amarya Islaha ta zuba kyau duk da haka sabo da a cikin na lefe Maheera ta dakko mata leshi dankarere milk and brown tayi kyau sosai,kayan lefen dama suna gida Abuja,Sai da aka daura sannan Lalai tazo,ita da gidanta amma ka rantse bakuwa ce,suka bata abinci tace o.o.o aci dadi lafiya Allah sanya Alkhairi,Maheera tace haba Lalai,fafur taki ci,tace wlh bazan ci ba cikin dare a yaga min bakina biyu ba ruwana,sauran yan garin almajirai da maza ne kawai suka iya cin abincin bikin Islaha duk anki ci kowa tsoro yake ji.
Dan gidan Baffa Gali ya karbo shinkafa da miya zai shiga da ita Baffa Gali ya dawo daga wajen daurin aure ya gani yace kar ka soma shigar min da ita gida,kana gani har yanzu ban warke ba karfin hali kawai nake yi duk jikina a soke yake,fitar min da masifa daga gida ya kori yaron da abincin.
Sahil shi ya yarda anyi pics sai kallonsu ake yi har abincin sunci abinsu,Daddy tuni sunyi gaba sun bar kauyen,sai Mudassir,Sohail da Sahil,ga motar tayi musu kadan tunda zasu taho da Amarya.
Aunty Aisha ce kadai a gaban mota,Muddassir driver,Sahil da Amarya a baya,Sohail da Maheera suma a baya motar ta matse su,Sahil yace Amarya ta dawo cinya zamu fi samun Space,Islaha tace a'a zamu je a haka,Sahil yace zanyi fushi mala'iku su tsine miki tun daga taraba har Abuja,tashi tayi ta zauna a cinyarsa da kyar yace yawwa Tallaja.
Mayafinta ya gyara mata suka tafi,Lalai ta leko taga mota ta tafi ta furta jaraba sun tafi ta koma gidanta ta duba kasan gadon taga sun kwashe komai tace yafi sauki.
Sahil yace ayi sauri Allah ya kaimu lafiya yau akwai kara'i,Maheera tana kallon Sahil sai zumudi yake shi da Alama yasan kan gari,tausayin kanta taji,Sahil kana kallonsa har ya canja yanayi shi idonsa ma ya canja zallar sha'awa ce kawai a ciki,Islaha sai zare ido take yi a cinyarsa,cikin dare sosai suka dawo,Aunty Aisha suka fara ajiyewa a gidanta sannan Muddassir ya tsaya nan ma ya musu siyayyar kayan makulashe har da nasa da zai kai gida,da na Sohail ga kuma na Ango daban,har gida ya sauke su ya musu sai da safe suna ta masa godiya suka wuce ciki.
Maheera tace wash na gaji,Sohai ya dauketa cak yana murmushi suka wuce part dinsu.
Ango yana rike da Amarya a part dinsu suka wuce bedroom,Islaha tace ina dakina? Yace yau fa ke ake jira malama dama a fara soyayya,Islaha taji tsoro tace da gajiyar hanyar? Sahil yace to mene a ciki a kwanta tare a tashi,Islaha tayi dariya ta zaci wani abu zasu yi babba sai taji ma wai kwanciya,yace ke Taskira zan gani yau,ni ba abinda zan miki gani kawai zanyi,gani dai ba ci ba,murmushi tayi ta shiga toilet.
Tana shiga Sahil yaga kiran Daddy,a hakan ma Daddy yafi kiran Sahil sabo da gani yake yafi hankali,Sahil ya daga yace da dare haka sai kace anyi mutuwa? Daddy yace Mahaifiyar ku ce tazo Nageria tana Airport yanzu haka a nan Abuja kuje ku dakko ta gidanku,ta dade tana fada min zata zo ni na manta ma,Sahil yace Mahaifiya? Ashe zata daskare a airport kuwa ina angon zanje dakko ta na santa ne ni,Daddy yace ba fa wasa nake ba,uwa uwa ce kun sani Allah zai tuhume ku idan har kuka wulakantata,kuje tana airport zaku ganta baturiya ce wata bushashiya me dogon wuya,Sahil yace bushashiya me dogon wuya?Daddy yace ae,yace to zamu je,ya kashe wayar,Islaha tana fitowa a wanka ya fada mata yace ance wata bushashiya me dogon wuya, tace to kuje mana tana boye dariyarta,ya kira Sohail ya bashi labari Sohail yace Bushashiya me dogon wuya muje mu ga zahiri,Maheera ya sanarwa.
Motar Sahil suka shiga suka tafi,suna ta nanata bushashiya me dogon wuya,har suka je suna dube dube a wajen,Sohail yace Bushashiya me dogon wuya tana ina,can ya hango wata batura kuwa dattijuwa karmashashiya ga wuya zololo,Sohail ya kalli Sahil zasu yi dariya,Har inda take suka je,Sahil ya fara dariya yace Allah ya so mu bamu yo kama da ke ba.