← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 46

Sashe 33

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta kwana uku a gidan Hajiya kulu tace Islaha kawai ki zauna a wajena ki dinga tayani siyar da abinci a wajen saida abinci na mana nan gaba idan an samu aiki me kyau sai na kaiki can, Islaha tace ba damuwa,daga ranar Islaha bata sake kuka ba, idan suka shirya abinci a gida sai a zuba a manyan kuloli su jera a cikin kurar ruwa su tura zuwa layin da Hajiya kulu ke siyar da abinci,wata rumfarta ce da katon tabir da benchi sun kai hudu na zaman samari masu siyen abinci,Tebir din kuma a samansa suke jera kulolin.

Islaha kurar ta turo sanye take cikin riga da skert na atamfa tana tura kura sai ga Khalisat,Khairat,Aunty da Shema'u sai Yaseer shine ke tuka su a motar Shema'u,da sauri Aunty tace tsaya tsaya ga Islaha can tana tura kura ta koma tuwo tuwo.

Aunty duk da ita ta kori Islaha bata ji dadin ganinta a haka ba yar yayarta ce ta jini,a gaban Islaha yayi parking,Yaseer yace Aunty baki kyauta ba wlh banji dadi ba bai kamata ba,Khalisat tace shegiya gwara haka gwara da aka koreta bata da kunya,na samo saurayina kyakyawa ta rabani da shi.

Aunty ce ta bude mota ta fito tana bulbula kamshi ta sha kitson Attach,Islaha tana ganin itace ta dauke kai,Murmushi Aunty tayi tace kin iya rashin kunya baki da abinda kika taka a kasa yanzu ina amfanin wannan rayuwar? kizo mu koma gida kici gaba da zama amma sai in zaki canja hali kibi umarni na,Islaha tace Allah ya kiyaye ni ba asararriya bace.

Gwara nayi wannan sana'ar ta fimin na bawa maza kaina,Aunty tace kije jiki magayi ta shiga mota tace Yaseer muje naga alama bata ji jiki ba,Yaseer yace ke Aunty...ja mota muje ko naci uwarka wlh,motar ya ja suka bar Islaha a tsaye,kurarta ta tura tana hawaye har ta kai abincin rumfa.

Maza da yawa sunzo siya su suka dora mata abincin a saman tebir sannan ta fara zuba musu tana karbar kudinta,wani matashi yace ki sa naman kato fa ke,Islaha ta kalle shi kawai ta zuba masa a robar take away, ya karba yace kudin sai na dawo,tace hey.... don't Dear me miko min kudina bana son wasa ta bata rai,ba shiri ya mika mata kudinta ta karba ta saka a jaka ta bashi canjinsa,sai daga baya Hajiya kulu tazo.

Amarya ce taci gayu cikin sabuwar atamfa doguwar riga ta mata mugun kyau,dauri taci ture kaga tsiya baya ta gyara gashinta har baya ta sa ribbon kalar atamfar dark green,tana kamshi Sohail ya kalleta yana murmushi,Murmushin tayi masa itama,kinyi kyau yace,tace na gode kaje kayi kaima,yace nayi da asuba sai anjima,tace oh na tuna,yace ae bana karya dan a so ni,tace nima haka,yace aka sani ko na amarci kike yi,Maheera fuska ta bata ta juya,hannunta ya ruko yace hijab din fa,tace sai kace na sa kana nan kaya kullum kace sai na saka Hijab ina gidan mijina,Sahil fa yana nan,to a haka wacce shiga nayi ta rashin dacewa kowa zai iya ganina a haka haba Sohail wannan wanne irin kishi ne, Sohail yace namijin kishi ne dani.

Juyawa tayi zata fice yace dan Allah to sa mayafi please Baby,dariya tayi ita zai wa wayo har da Baby,zuwa tayi ta dauki mayafi kalar kayan ta yafa tace Allah idan kace Baby sai naji ko nayi fushi gaba daya na huce,yace Baby wuya a waje da gashin da dai Hijab dinne,harararsa tayi yace to jeki na hakura muje ya mike yabi bayanta sai kakkareta yake.

Sahil yana palo shi karinsa yake suka fito suka iske shi yana cin abincin,Maheera tace ina kwana Sahil? Kallo daya yayi mata yace lafiya lau Amarya ta Ango,Sohail hannu ya mika masa suka gaisa yace nazo da safe kana bacci,Sahil yace zo kaji,Sohail ya duka ya mika masa kunne yace iceko ba aci amanata ba? A jira Islaha fa,Sohail shima da rada yace banyi komai ba,sai faman kus kus suke,Maheera ta wuce Dining ta zauna tayi serving kanta tayi serving Sohail ta hada masa tea da komai sannan tace Sweet yunwa nake ji.

Sohail zama yayi a dining yace har kin zuba min komai? tace ae yace Allah ya miki Albarka,bari na baki a baki,Maheera tace a ranta abu kamar hawa da sauka ayi daidai a dawo a kauce, chips din ya tsikaro da fork spoon ya sa mata a baki Maheera ta tauna jin dadi yau tafi kowa a duniya jin da takewa kanta,sai murmushin jin dadi take Sohail yana bata a baki tana ci yana ci shima, Sahil yana can daga palo yana cewa a dai tsaya iya nan.

Sohail yace karka damu yana sa tissue yana gogewa Maheera baki,Maheera dadi ya kashe ta tace haiiiiii Sweet tana wani sosa cinya kamar wacce Aljanu suka shigeta

Sahil ya kalleta dariya ta bashi ma ya dauke kansa yace sabo da anga bani da ita shine ake cusa min takaici,dariya Sohail yayi ya yace zata dawo ne kaima kaji ka daina damuwa,ni da zaka yarda ma da na aikeka,Sahil yace Ina? yace kaje ka gaida babar Maheera kafin nazo kace na gode da aka bani ita,Maheera harda rufe fuska sabo da farin ciki,Sahil yace bazan je ba gidan Aunty Aisha zanje tace naje wai za a kawo garar Maheera zan taho da su nan,Sohail yace har wata gara za a kawo ni na yafe kar a kashe min zuciya a barni nayi cefane na.

Sahil yace wlh sai mun karba in ba haka ba ta shiga uku da gorin dangin miji,na dinga gori kenan na dinga ce mata yar rashin gara,gwara ma a karba,Maheera tace sai ku kashe mutum da dariya jeka dan Allah,Sahil ya karbi key ya fita.

Yana fita Maheera ta mike tsaye Sohail yace zauna ke wai bakya zama kawai sai kin hau min jikina,Maheera tace to wai ba mijina bane ni shike nan bazan ci abincin ba ma ta juya zata tafi,da sauri ya riketa yace to zauna kadan amma karki dade ya gyara mata cinya,Maheera ta zauna ita kanta ba sabawa tayi ba kawai so take ta canja shi ya gane me akeyi.

Sahil yana fita yaga motocin Daddy sunzo kofar gidan,Sahil yayi mamaki,parking suka yi driver ya bude masa kofa ya fito,Sahil yace Daddy kaine kazo gidan nan? Daddy yace ae nine zuwa nayi naga zahiri,Sahil ya juya yace to muje suka shugo har palo,Maheera tana saman cinyar Sohail a zaune suna cin abinci sai dariya suke yi,Sallama suka ji kawai.

Daddy ya zaro ido ganin gida mashaallah,Maheera da sauri ta mike tsaye tana gyara mayafinta,Sohail yace Daddy? Alhaji Ali ya kalli gidan yace uhm ashe kuwa da gaske kuke yi shi yasa na kawo muku ziyarar bazata.

Maheera ta mike taje palon tace sannu da zuwa Daddy,zauna Daddy,Daddy yaso ganeta yace kece yar aikin su Adnan ce ai,tace ae nice,zama yayi yana mamaki yace Allah me iko kamarki kika amince lallai kowa baya rasa masoyi,ina ganin ai ko kamar su Adnan a yanda Allah ya tsaraki ko kamar su Adnan sai sun kai ruwa rana sai kuma gashi to Allah me iko.
Maheera dai durkusawa tayi har kasa ta gaida shi ya amsa yana ta faman furta Allah me iko.
Sahil yace kar dai ka kyasa Daddy ba kyau,shi yasa aka ce ka samu wata yar bazawara ka aura ka dinga mai da yawu amma kaki,an rasa me keka yi,idan baza ka iya ba mu yan mata kawo kansu suke wajen mu ka bamu zabi muyi maka hanya da dai dai kai,kunya Maheera da Daddy suka ji amma su twins ko a jikin su.

Sohail yace Daddy ina kwana da sassafe sai ka taho gidan Amarya,ai ba a zuwa gidan yara da sassafe,Sahil yace ina kwana Daddy ya amsa duk sai da suka rusuna sannan suka gaishe shi.
Maheera ta dinga kawo abinci tana dire masa,su farfesu ya zaci ma ita ta girka,ta shiga kitchen ta kawo lemuka da ruwa tace Daddy ga abinci dan Allah ko kadan kaci.

Daddy ya cika da mamaki sabo da saka ido sai da yaci ya tabbatar yaji ya girkin yake,yaji dadi,Sohail yace ba ita tayi bama nata yafi wannan dadi na gidan Aunty ne wannan,ai wannan ka taba cin girkinta kaji wlh ko kakar mu Iya me Koko bata kaita iya girki ba,Daddy har sinasir ta iya,Daddy yace zaka ci uwarka Sohail ni kake fadawa ko Iya me koko bata iya ba,uwar tawa mahaifiya, Sohail yace to yan zamani sai yan zamani ai,Sahil yace wannan Special ce ba irin su Zayna bace me hanci kamar tulu.

Maheera tana durkushe a kasa,Sahil yace tashi ai kin nemi Taskirar zaman ya isa haka,Daddy yayi shuru yana jinsu yayi murmushi,Sohail yace nidai ko kowa bai yaba ba tunda ni na yaba ina son abata shike nan.
To ku zauna cewar Daddy,zama suka yi yace shi aure da kuke gani Ibada ne,Sohail yace a'a mu ba sai an mana nasiha ba mun sani,da can ba a damu damu ba sai da aka ga munyi abinmu,ko gudun muwa ba a bamu ba,a barmu idan ma duka ne mu nadawa matan namu,kudin mu ne,Daddy yace ai shike nan ya mike zai tafi Maheera tace Daddy ka gaida gida.

Yace Madalla Madalla ya fita ya tafi Sahil ya bishi yana cewa da ka tsaya an kawo garar ko kwano uku ka dauki shinkafar ba komai wlh mu har abada mahaifin mu ne kai.
Daddy ya rufe motar yana dariya ya sauke glass Sohail yace gara ai ana bawa gidan iyaye nasu Daddy ka tsaya ka tafi da ta gida duk da cewar gwauro ne kai.

Daddy son gulmarsa tasa yace Sohail yanzu kai wai hankalinka ya kwanta ko kai ga ango? Sohail yace ya hankali na bazai kwanta ba da mace fa na kwana jiya,kai kuwa yaushe rabo,ni wlh na daina jin haushi ma in kayi mana wani abun Daddy na gano dalili babu mace.
Daddy ya bawa driver Umarni ya ja mota ya tafi sai dariya yake ta yaran nasa yanda suke wanke shi tas.
Chapter 33 · 0% Book details