← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 46

Sashe 18

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Twins ma yau haka suka sha wanka suka fita neman aiki basu samo ba,wasa wasa sai da suka kwashe sati kullum suna garari da takardu amma ba labari,hakan yasa suka ce sun hakura baza su samu komai a duniya ba suka daina fita ma gaba daya kullum suna gida tare da su Maheera.

Zayna ce ta aiki Maheera kasuwa ta siyo abinda babu na kitchen,tana hanyar tafiya a kafa,sanye take cikin t-shirts brown da wando ta saka hijab daidai gwiwa tana tafiya a nutse,Wani mutum ne shi ba tsoho ba kuma baza a kirashi da yaro ba yayi parking da motarsa cikin sauri ya bude motar ya fito da kansa waje yana ta faman tari yana shidewa yana jan numfashi da kyar, yana ta daga hannu alamar a taimake shi,kasa ya fado daga cikin motar,Maheera ta lura da hakan da sauri ta karasa inda yake tana tambaya lafiya? Da me zan taimake shi,gaban motarsa yake nuna mata da yatsa,ta duba da sauri ta ga Inhaler wacce masu Athsma suke amfani da ita,da sauri ta sa masa a baki,a hankali ya fara dawowa hayyacinsa har ya gama dawowa dai dai.

Kallon Maheera yayi yace na gode kin taimakeni idan ba damuwa dan Allah ki bani number dinki za mu gaisa,ba musu ta bashi number dinta ta kara gaba,yana ta roko ta tsaya ya rage mata hanya amma taki yarda.

Bayan ta koma gida da kwana uku ta manta ma anyi wannan sai ga kiran mutumin,dagawa tayi ganin bakuwar number gaishe da shi tayi ya amsa sannan yace sunana Alhaji Saminu wanda kika taimaka lokacin da Asthma dina ta tashi,tace oh ya gida ya aiki,yace lafiya Alhmdllh,ina sake godiya fa Maheera,tace ba komai wlh ya wuce ai,yace ni sunana Alhaji Saminu Shehu kamar yanda na fada miki,nine me kamfanin J&S nigeria,ina da branch a lagos da Rivers sai kuma nan Abuja,Banyi niyyar sanar dake ba amma da kika ganni fitowa nayi daga gida zan je wajen abokina,Maheera tace mashaallah.
Ci gaba yayi da magana dalilin da yasa na miki magana naji dadi kin taimakeni,so ina da matata da yarana uku,ina so a matsayina da kika ji ki fada min abinda kike so ni kuma inshaallah zan miki.

Maheera taji dadi tace wlh bana bukatar komai na gode amma akwai saurayina da dan uwansa mun dade muna neman aiki kuma an kusa bikinmu Sir amma basu samu aikin ba,'yan biyu ne kuma dan Allah ka taimaka ka bawa ko mutum daya ne aikinyi,amma a takaice idan ba dama zamu iya haduwa na baka labarin su ko zaka tausaya,Jamilu yace ba damuwa bari na baki address din Office dina,ta dinga godiya tana murna.

Suna gama waya ya tura mata address yace tazo yanzu yana Office dinsa ma.
Shiryawa tayi a gurguje cikin fitted gown ta leshi blackblue ta yafa mayafi me kyau ta saka takalmi kalar mayafin da jaka ta fice da sauri,A palo ta samu Sohail,Sahil da Islaha suna kallo,tace zanje unguwa yanzu zan dawo,Sohail ya kalleta yace kuma sai da kika yi kwalliya kice kawai party zaki je,party da safe 11am fa,to baza ki fita ba,Maheera tace hmm mamata zan turawa kudi,karya kike Sohail ya bata amsa,Sahil yace yanzu suka yi waya da wani Saminu,Sohail yace Saminuuuuuu....Maheera juyawa tayi kawai zata tafi abinta Sohail yace in kika fita kin gama yawo na fada miki.

Maheera kofa ta bude tayi ficewarta,Sohail yace za ayi jaraba....yau a gidan nan,Sahil ya fara dariya yana kallonsa yace wai ko sonta kake ne? Sohail yace so? na so wannan? Maheera ce fa ita zan so kawata ce fa? Ka kyaleta taje to,yace ai yau wannan fadan da jarabar duniya sai an yita a gidan nan,Islaha tana ta dariya tace wlh da nice kai Sohail auren Maheera zanyi.
Sohail ya nuna kansa ni na aure ta inyi me da ita? tsaki ya ja ya kalli Sahil yace kai ko haushi ma baka ji ba kana kallo ta fita,Sahil yace to ina zan iya da ita.
Sohail yana ta jira ko aljanu zasu haska masa inda taje shuru ba labari,takaici ya kama shi, Islaha sai jinsa tayi yana cewa ba wani bayani? Kamar wani boka,yana cewa ba rahoto? Mene ne rahoto a kanta? a bani bayani shuru bai ji komai ba.
Sahil ya tambaya yace kai fa? An baka bayani? Sahil yace shuru ba labari.
Sohail mikewa yayi tsaye sanye cikin jallabiyya yana sintiri a palo ya kasa zama.

Maheera kuwa har katafaren building din Saminu ta nufa,har tanfatsetsen Office dinsa aka kaishi wanda ya gaji da tsaruwa,kujera ya nuna mata yace Zauna bismillah,Zama tayi a nutse sannan suka gaisa,yace I'm busy bani labari a gurguje ina da meeting,Maheera ta kalli Saminu sanye yake cikin wani yadi wanda bai da wani tsada in ka ganshi sai ka rantse da Allah ba shine me kudi haka ba,sam kudin babu kama a jikinsa.
Labarin su Sohail ta bashi a takaice,yace amma na tausaya musu wannan wanne irin azzaluman dangi ne amma laifin iyayen ne da uwarsu da uban sune masu laifi babba.
Bamu neman ma'aikata yanzu babu wajen daukan yan aiki sam amma zan iya daukan mutum daya a ciki,zan sa a koya masa aiki,idan naga kwazonsa zan bashi babban matsayi sannan sai ya koma karatu in ya gama sai ya kawo min takardunsa,kije ki tuntube su" su zabi daya a ciki sai na bashi aiki,amma nayi ne sabo da ke, jin kince shi zaki aura,Maheera tace na gode tana ta godiya suka yi sallama ta fito.
Tana zuwa gida Sohail kawai ta samu a palo ransa a bace yana ta zirga zirga tasan hali,da kuka ta shugo tare da dingishi da kafa,rudewa yayi ganin ta dawo da kuka sai ya manta da fadan da zaiyi,ya karaso da sauri ya riketa yana tambayarta menene? Lafiya?

Maheera tace faduwa nayi mota ce ta taho kamar zata kade ni garin gudu na fadi,Sohail yace sannu to muje asibiti? tace no ina jin sauki,yace okay to tana dingishi sai ya dauketa cak,taso tayi dariya,sai ta fuske ya kaita har dakinsu,Islaha tana kwance a gefen bed yace matsa ke,Islaha ta matsa can baya ya kwantar da Maheera sannan ya cire mata takalman kafarta ya adana su har jakar a inda take ajiyewa ya sa mata,mayafin ya cire mata a hankali ya ajiye gefe ya kalli Islaha yace Jinya zanyi ki sauka kwanciya zanyi,Ba shiri Maheera ta mike zaune tace naji sauki wlh dama kadan ne,Sohail yace idan kinga banyi jinyar nan ba to na mutu,Islaha tana ta dariya ganin yanda Maheera take ta zare idanu.

Sohail Saman bed din ya haura ta mike zata gudu ya jawota ta fado kansa,tace dan Allah ka bari ba kyau,yace duk masu jinya haka suke da raki, Islaha kawo min ruwan zafi a bowl,Maheera tace na shiga uku dan Allah Sohail na yafe ka kyaleni,tsaki yaja tana rike gam gam a jikinsa,sai da Islaha ta kawo ruwan a bowl da towel karami tana ta yiwa Maheera dariya,Sohail duk ya shaketa a jikinsa,kokawa suka shiga yi shi Ita,hakan sai ya masa dadi kamar wasa suke yi,ba shiri tace iya kafa ne gata ka gasata ta miko masa kafar,sai haki suke faman yi,kafarta me kyau fara ya jawo tare da dorata a cinyarsa ya matse towel din yana dannawa a kafarta,ruwan yayi zafi fa Sohail ka rage zan kone,ko kulata baiyi ba sai da ya gama gashinsa sannan ya mike ya fita.

Islaha tana dakin bayan ya fita Maheera tace to dariyar me kike kuma? Islaha tace wlh duk ya taba miki duwawu da kirji kamar ya kama namiji,Maheera tace ina ji ai,dadi kika ji kenan? dariya tayi tace uwar dadi naji,ki zauna na baki labari amma to be sincere jikinsa wlh dadi kamar kar a daina ta furta tare da rufe fuskarta da tafin hannayen ta, Islaha tayi dariya tace yau kwana zakiyi kina tunaninsa kenan? Hmm kawai tace.

Zama tayi Sannan Maheera ta bata labarin Alhaji Saminu da haduwar su da kuma yau abinda yace,Islaha sai murna tace Alhmdllh,yanzu su biyun zaki samu kiwa bayani daya sai ya barwa daya.

Zuwa dare ganin su Adnan suna palo sai Maheera ta kirasu a sirrince suka koma garden har Islaha,Zama suka yi Maheera ta basu labarin komai akan aikin,Farin ciki ya kama Sohail da Sahil suna ta murna,Sohail yace na barwa Sahil yaje yayi aikin,Sahil yace a'a kai zaka yi ni na fika zafin nema.
Suna haka Islaha tace ga takarda mun rubuta daya yes daya no wanda ya dauke yes shine zaiyi aikin wanda ya dauki no sai yayi hakuri sai nan gaba rabonsa in ya zo,Takarda ta watsa guda biyu a nanade,Sohail ya zaba Sohail ma ya dauka ko wanne ya bude,Sohail shine ya dauki Yes Sahil kuma no? Sahil yayi dariya yace Allah yayi zabinsa.
Maheera tace to sai ka tattara iya takardun da kake dasu gobe kaje ka same shi a Office,ga address zan baka,Sohail yace na gode taho Islaha na rungume ki,Islaha da wasa ta tafi kamar gaske,Sahil ya riketa yace ba kyau fa babu aure,Maheera har ta sandare a zaune sai taga Islaha tana mata dariya a sace.

Sohail a wajen suna hira amma shi ya dauki tsinke sai faman zana zero 0 yake,Maheera tace dan Allah karka je ka zana musu Zero a takardu ka kula sosai kayi aiki me kyau,Sahil yace ai mun sha wahala kafin a samu Inshaallah zaiyi kokari ko? Sohail yace Allah ne masani yaci gaba da zana Zero,Sun dade kafin su koma ciki.
Chapter 18 · 0% Book details