← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 46

Sashe 26

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an gama girki sunyi sallar magriba,Lalai ta zubo tuwo tana ci tace kaji miyar yan bariki,miya sai bariki,amma mutane ace dunkule baya zakin miya,bayan ma farin magin nan cuta yake sawa amma wasu a dinga gabza shi a miya,Lalai tana wulla loma tace ai ni sam bana cin farin maggi duk inda naje indai an sa farin maggi a miya sai na gane,kana ci zaka ji zaki har kai,yana wani bauri kamar ruwan teku.

Islaha tana jinta tana dariya a ranta tace ace dunkule biyu rak miya kamar zan mutu idan ina ci sabo da rashin dadi,ai gwara da na siyo farin maggi na a boye na ajiye su,kullum da anzo girki zan faki ido na zuba.
Lalai tana yin sallar Isha ta mike ta dauki mayafinta tace na tafi gidan Baffanki Shamsu,Islaha tace a dawo lafiya.

Lalai tana tafiya ta dinga bin gidajen yan uwa tana basu labarin Ibrahim da irin kudinsa da kuma yanda Islaha tace ita bata sonsa talaka take so kaninsa.
Baffa Shamsu yana ji yace haba karya take wane ita, ita din banza,me akayi aka yi Islaha,Lalai tace to yace kuma zaizo ya gaishe ku zaku sha kudi ku mike tsaye so take tayi mana asara,Shamsu yace ai baza mu barta haka ba da malamai zamu hada ta dole ta so shi ta aure shi,gaba daya ki lallabata kiji sunan waccen wanda take so din ki fada min zamu bi ta wata hanyar kawai sai dai taji ta tsane shi ta fada son wannan Ibrahim kika ce ko? Lalai tace kwarai kuwa shi yasa nace bari nazo wajen ku ni tafi karfi na,baku ga yanda take min ba kamar zata dake ni har girgiza take idan tana min masifa,Shamsu yace jeki karki sake tsokanarta karki nuna komai ki nuna zabinta shine namu muma da haka zamu yaudare ta.
Lalai tace yawwa shike nan ai yanzu lallabata zanyi,bari na koma sai ka jini ina jin sunansa zan dawo na sanar maka.

Bayan Lalai ta dawo ta samu Islaha ta kunna wayarta tana game a ciki,amma ta sata a flymode, ta zauna da fara'a tace ku dai idan kuna wannan abin bakwa jin sallama,Ai na amsa cewar Islaha,Lalai tace Islaha wato dai bakya son wannan Ibrahim din? Zaki mana asarar kudi,arziki yazo mana har gida,Islaha ta turo baki tace ni bana son zancensa,Lalai tace ai muma zabinki muke so tunda kinki yarda ya zamu yi baza mu yi miki dole ba,Shi wanda kike so din iceko na kirki ne? Islaha tace ae sosai,ya sunansa ne shi wai?

Islaha dariya tayi a ranta tace haba Lalai da wayona da hankalina ba a banza na zauna a birni ba kuma ina aiki da ilimina,ni zaki rainawa hankali wallahi nafi karfinku nafi karfin tunaninku,a fili kuma tace Sunansa Tijjani,Lalai tace ya mori suna Allah yasa ya gaji me sunansa shehu ibrahim Tijjani Inyasi,dariya Islaha tayi tace hmm shi dai sunansa ne haka ba wani gado.
Lalai tace to Allah ya nuna mana Allah ya kawo shi na ganshi waye wannan me sa'ar.

Islaha tace Lalai amma yanzu tunda zanyi auren ai zan daina daka da sissika? Lalai tace inji uban wa ko gomna zaki aura sai kinyi sai in kin bar gidan nan, kawai sai na dafa na baki kici a huce hauka ake a ci dake sannan aikin ma baza kiyi ba sai dai kici a kwance sannu Sa'ida sunan wata bishiya,kece shafaffiya da mai da za a nemo da wahala sannan ayi aikin wahalar duk a baki kici a kwance sabo da kece Gimbiya hakima ishashiya,gwana yar hutu,Islaha tace to naji ni ki kyale ni.

Washe gari da safe da Abdulrazaqu ya shigo sakamakon dakinsa a waje yake daban na bukka, Lalai ta ja Shi gefe tana fada masa yanda suka yi da Baffa shamsu ta inda za a bullowa Islaha, Islaha tana can tana aikinta na gyara zogale yau dambu zasu yi kuma.

Lalai yau ma da dare ta koma gidan Baffa Shamsu ta fada masa sunansa Tijjani,Baffa Shamsu yace zaici ubansa ko waye wannan Tijjanin da take so,ga Ibrahim ai yafi.
Ya mike yace muje gidan Malam Ishu da shi kadai na yarda a garin nan.
Tare da Lalai suka je har can,suka zubewa Malam Ishu bayani da abinda ya kawo su ayi musu,Malam Ishu ya buga kasar dake gabansa, Malam Ishu sai da ya buga sau uku yace gaskiya babu wani me suna Tijjani da take alaka da shi,karya ta muku,amma ba sai ta fadi sunansa ba ku kyaleta aikin ba wahala ma an raba su aikin me sauki ne,amma zaku yanka zakara kuma ita za a bawa ta ci indai ta ci naman to shike nan zata fada son Ibrahim ta gigice da gaggawa zata matsu a yi bikin,Sai shi wannan za a raba su wani rubutu zan baku ku tabbatar kun zuba mata a ruwa ta sha indai ta sha ko yaya ko ba tijjani ba ko uban waye ma a ranta sai ta daina kaunarsa kawai sai Ibrahim,kullum sai tayi kuka akan Ibrahim,da kanta zata nemo shi yazo ayi biki.

Dari biyar suka bashi sadaka a haka sai murna yake ya sha kudi,yace gobe Lalai ta dawo ya karanta manta yanda zata aikata aikin, Islaha bata san me suke yi ba,washe gari Lalai ta koma ya bata wani rubutu a leda yace shi zaki juye mata a ruwan sha idan zata sha ruwa ko yaya ki zuba indai ta sha an gama,ya dakko wata laya ya bata yace wannan idan kin yanka zakara an gyarashi kisa layar a cikinsa ki samu zare da allura ki dinke cikin zakaran tsab ki dafa shi yaji hadi,idan ya dahu sai ki farke dinkin ki cire layar ki haka rami a binne ta sai ki bata taci,ko ya taci shima an gama,kuma zaku iya ci kuma iya abin ita zai shafa,Lalai tace an gama tayi godiya ta tafi direct gidan Baffa Shamsu.

A can Baffa shamsu ya bada katon zakaransa tace a nan gidan zan dafa kawai na kai can sabo da a can zata iya ganina,Yace haka za ayi,Lalai da matar Baffa Shamsu suka gyara zakara aka wanke tas suka saka laya tare da sa zare da katuwar allura ta dinkin buhu suka dinke da kyar yanda dai layar baza ta fito ba suka lallaba suka yi farfesu me kyau lafiyayye,Lalai ta binne laya amma tunda Malam yace zasu iya cin naman duk sai da suka ci aka barwa Islaha wani dan kadan a kwano iya wanda zata ci,dama yace ko yaya indai taci shike nan dama dan ita aka yi ita kadai zai shafa.

Lalai da kwano tazo a rufe da bargajejen hakarkarin zakara a kwano,ta samu Islaha har ta gama dafa musu dankalin Hausa tayi yar miyar jajjage,Lalai tace har kin gama sannu,tace yawwa,daga gidan Baffanki nake Shamsu zakaransa ya kasa zai mutu aka yanka shi shine suka dafa naci nima a can kinga naki na taho miki da shi maza kici abinki.

Islaha karba tayi ta duba tunani yazo mata haka kawai zasu bata wani nama kuma har haka da girmansa,ga wani mutunci da Lalai take yi mata yanzu,Islaha a ranta tace nafi karfinku wlh,Lalai tace bari nayi wanka maza ki cinye a wanke kwanon zasu zo karba,Islaha ta washe dan karamin bakinta tana murmushi tace na gade bari yanzu zan cinye abina,kai amma na gode ashe dai Baffa Shamsu suna so na,Lalai ta cika baho da ruwa tana cewa ai hannunka bai rubewa ka yanke ya yar,Islaha tace bari na baje naci abina yau akwai harka,Lalai tasan dole ma sai Islaha taci gashi taga sai murna take yi,sai ta shige wankanta,Islaha tana ganin haka ta dauke naman ta jefa cikin bakar leda ta kulle ta boye a cikin jakar kayanta,dan romon kuma ta dan jagwalgwala har gefen kwano alamar anci har romon an sha,ta fito hannunta duk maiko da romon nama,Lalai ta fito a wanka sai murna take Islaha ta cinye nama,Islaha tace bani Sabulu,Lalai ta mika mata ta wanke hannunta tas,abincinta ma da zata ci ko da hannunta bata ci ba da cokali taci dankalin .

Ta fita zata kai kwano kitchen kiri kiri taga Lalai ta bude randarta ta daki da sauri ta juye wani bakin abu a randar kamar rubutu ta mayar da murfi ta rufe,bata san Islaha ta juyo zata shigo ta gani ba,fuskewa tayi kamar bata gani ba.

Tana zuwa Islaha ta sake fita tace na manta bari na dakko kofi na sha ruwa,ta dakko kofi tare da bude randa ta cika kofi da ruwa ta fice waje ta juya ta kai kofin bakinta kamar sha take tana zagawa ta watsa ruwan a jikin katangar karan ta dauraye kofin ta maida ta kife ta dawo,Lalai sai murna take an gama aiki sun samu nasara.

Islaha tsoron Lalai ta shiga yi tun daga ranar bata kara cin abin hannun Lalai ba,sannan ruwan gidan bata sha fita take ta sha a can inda suke ebowa,abinci ma indai ba ita ta dafa ba to kwana take da yunwa.

Bayan sati biyu ko nisa Ibrahim bai gani ba ganin baya samun wayarta ya sake dawowa,Islaha tana ji ance ance shine ta dauki buta tace bari nayi fitsari ta shige bayi taki fitowa,har ya shigo gidan suka gaji da jiranta taki fitowa,Lalai tun daga nan tasan aiki bai ci ba,haka ta raka Ibrahim gidan dangi gida gida ai kuwa sunga ruwan Naira duk ya siye su da kudi sun haukace sai shi.
Lalai yau ma dubu hamsim, Abdulrazaqu ma ya sha nasa kudin,yaran gari ma duk wanda yazo dubu daya dari biyar biyar haka ya dinga rabawa yaran garin,dattijai da matasan kauyen daga me 2k sai me 3k haka ya dinga rabo,duk inda ka zaga zancen Ibrahim me ruwan Nairori ake yi,har an sa masa suna me ruwan Nairori Na Islaha.
Chapter 26 · 0% Book details