Sashe 25
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulrazaqu yaji haushi yace amma kai baka da ilimi sam kazo garinmu ka tare ni kana min tambaya sai ka dinga chaba min magana ko ance maka so shi a kyau yake? Duk ga ba munana nan ba sunfi auruwa sunfi samun mazaje na gari kuma kyawawan maza suke aura,sai kayi mamaki kace me ya gani a jikinta shi gashi kyakyawa,kuma kyakyawa mace kaga tana ta fadawa hannun mazaje munana,kaga mace hadaddiya mijinta ficika baza a siye shi ba,shi so da aure ai ba ruwansa da kyau malam ka gyara kalamanka,daka ganni bakin ba Allah ne yayi ni ba,a gidanku aka kirkireni? Ko kai farin ne gaka nan wankan tarwada kai a wankan tarwadar ma da alama kanti ka shiga ka dawo haka dama ai munji labari yan birni mayuka suke shafawa har mazan,mu kuwa mun tsaya yanda Allah yayi mu,ka ganni nan ko vaseline sai na shekara ban shafa ba,watarana ma mangyada nake shafawa da sanyi amma gani dakaukau dani aikin da nake baka isa kayi shi ba.
Ibrahim yayi dariya yace shi yasa ai gaka nan kamar an tonoka daga rami abokina maida wukar ka kira min Islaha idan tana nan,idan na sameta na maka alkawarin jari me tsoka ka fara kasuwanci zan maka gida me kyau a kauyen nan da babu kamarsa.
Abdulrazaqu yana jin haka yace da ina son Islaha nima amma na bar maka ita zan tsaya tsayin daka ko da tsiya sai ka aure ta ka kaddara ka sameta an gama.
Ibrahim yaji dadi yace na gode jeka zan bika a baya da mota,Ibrahim maimakon yace Abdulrazaqu ya shiga mota su tafi baya so ya shigar masa mota kar kamshin ta ya canja ya bata masa mota,a haka suka tafi shi yana daga cikin mota Abdulrazaqu yana tafiya a kafa har kofar gidan Lalai.
Ibrahim yana parking a gindin bishiya ya fito yace ai a nan gidan Islaha take? Abdulrazaqu yace ae a nan take,yace cab,Shigo ciki gidan tsohuwa ce ba wani abu ta riga ta tashi a aiki, shigo ko a wanne hali ka kalleta ba komai,Ibrahim yayi murmushi suka shiga kai tsaye gidan,Lalai tana jikin katangar kara tana leken mota a kofar gidanta riga daban zani daban.
Islaha tana zaune a gindin murhu tana ta faman iza wutar tuwo ta hada zufa idonta yayi ja sabo da hayaki.
Mamaki ya kamata ganin Ibrahim a tsakar gidan su yazo, Abdulrazaqu yace Islaha kinyi bako daga birni ai kin sanshi ko? Lalai tace sannu da zuwa maraba, ta fada daki ta dakko tabarma sabuwa ta shimfida masa a kasan bishiyar mangoro dake gidan,Ibrahim ya cire takalminsa me kyau ya zauna,tare da gaishe da Lalai,Islaha haushinsa taji da yazo amma bata nuna masa ba tunda gidansu yazo kuma dan ita yazo,mikewa tayi sanye cikin riga fitted gown ta atamfa green,komai ya fito chass,Ibrahim ya kare mata kallo irin na wayayyun yan birni kamar ba kallonta yake ba,karasowa tayi tace sannu da zuwa ina yini,kazo lafiya,ya hanya? Ta furta a jere.
ya amsa lfy Alhmdllh,shine kika taho ba sanarwa,murmushi tayi,yace ba sallama ba komai ko dan zaman tare ai kya yi mana sallama,Islaha tace ai wanda naje dominsa yasan na taho.
Kishi ne ya cika zuciyar Ibrahim yace ai shi bai damu dake ba,da ya damu dake ai da yazo,ko ya zo ne? Twins basa soyayya ba masu lafiya bane baza su iya inganta rayuwar kansu bama bare su inganta ta wani,gagararrun Aljanu ne da su, bakaken aljanu kuma masu gulma ma su suka hau kansu,da cutar aka haife su,kinga wanda aka haifa da cuta ai baya warkewa,tsoro ma muke ji kar nan gaba su fara duka ko su fara tsince tsince a bola.
Islaha tace Allah baya sa ba inshaallah zasu warke baza su taba zama hakan ba,kaima idan kun san farkon ku ai baku san karshen ku ba,Ibrahim yace Allah ne ya dora musu ba ni ba,mu bar wannan maganar muyi abinda ya kawo ni, Lalai ce ta fito da ruwa da abinci ta kawo har da hado fura ta kawo masa, Islaha tana kallon ikon Allah yanda Abdulrazaqu da Lalai suke wani nan nan da Ibrahim kamar zasu cinye shi.
Lalai ce ta kalli Islaha ta gasa mata harara tace ki zauna mana kuyi hira wajenki yazo kin wani tsaya masa kerere a ka,Islaha ta zauna tana jin haushi a ranta,Ibrahim ko ruwan su bai sha ba,bare yaci wani abu nasu ma.
Islaha ya kalla yace kina shan wahala a nan kizo mu koma gida dan Allah wannan garin bai dace da irinki ba,ke ba kalarsu bace,idan ma baza ki koma gidanmu ba muje zan kama miki hayar gida idan ma so kike zan siya miki gida naki na kanki sannan zan baki jari na bude miki wani abun na Business ki dinga yin abinki,idan ta kama har Dubai zan nuna miki yanda ake shugo da kaya ki dinga samun kudi,Islaha a ranta tace gwara a bani Sahil na kare a talauci na,a fili tace na gode ni nan yafi min idan kaga na bar nan to nayi aure.
Ai me sauki ne sai na turo manya a nemar min aurenki,Islaha tace ban shirya aure ba yanzu ni soyayya ma gaba daya bata gabana,murmushi Ibrahim yayi yace a ransa a hankali zaki shigo hannu ne yarinya,a fili kuma yace ba komai zan jiraki ni,ya dan dade yana hira tana amsawa sama sama sannan yace Alhmdllh tunda na san inda kike yanzu hankalina ya kwanta zan tafi,tace a yau zaka koma Abuja? Yace a cikin gari zan kwana a hotel gobe sai na wuce,tace yafi dai,mikewa yayi zai tafi tace ka gaida gida.
Lalai ta tsomo baki au baza ki raka shi ba? Mayafinta ta yafa tabi shi suka fita,Ibrahim sai dadi yake ji shi gani yake ma ya samu Islaha an gama,50k ya ajiyewa Lalai sabo da ya siyeta da kudi, Abdulrazaqu ma haka ya bashi 20k,sai murna suke yi,Ibrahim yace idan na dawo za a rakani gidajen yan uwan Islaha na gaishe su,Lalai ta yashe baki tace Allah ya kaimu dan nan kaji,an gode Allah ya tabbatar da alkhairi gashi kayi dace dama bata da saurayi bata kula kowa a sadaka zaka sameta,Ibrahim yace na sani ai ya wuce abinsa.
Suna zuwa jikin mota ya bude motarsa ya dakko ruwan roba ya balle ya sha abinsa,wato bazai sha na gidan ba,Islaha tace shine mu kaki shan ruwanmu ka dakko naka ai ba so bane wannan,Ya kalleta yace Typoid masifa ce sabo da ina son budurwa kawai sai na cuci kaina Typoid ta kamani ko na sha tsutsa a cikina ta hayayyafa ta cika min ciki, Typoid bata jin maga ni.
wato mu ta kashe mu kenan?cewar Islaha,Ibrahim yace ku ai kun saba ta saba da jininku ta sanku,baki ta tabe ya shiga mota sannan ya sauke glass ya miko 50k itama yace gashi kya samu ki dinga siyen wani abin,Islaha tace ina da kudi na ance maka bana ci ina koshi ne..
Nasan kina koshi mana amma garau garau gashi nan naga kin kara cikowa ma,Karki wa kanki ki karba karki koma gida kina cizon yatsa,Islaha taki karba fafur tace ina so na fada maka karka dawo wajena ni dai da Sahil nake soyayya sabo da haka bazan kula yaya na kula kani ba.
Ya kalleta cike da kishi yace Sahil baya sonki ki daina batawa kanki lokaci bai san ma kina yi ba harkarsa yake ya manta da ke ma,Islaha tace na ji duk da haka,kai fa bai ma dace ko da wasa ka kulani ba sabo da kaninka tunda tare ka ganmu,Ibrahim yace idan kika ga na hakura to kice an daura miki aure,Ba ruwana da wani Sahil kanina ne yazo muyi takara wanda ya samu shike nan ba abinda ya dameni,Islaha ta gaji tace to ka gaida gida na gode ta juya ta shige gida ko sisinsa bata karba ba.
Islaha tana komawa gida Lalai ta fara masifa tace ina lekenku kina fada masa magana,har ya baki kika karba to ubanwa kike so yaro kyakyawa da shi ga kudi dan birni,Islaha tace to ni bana sonsa kaninsa nake so karki dameni,Lalai tace to kuwa matukar baza kiso wannan ba sai dai ki bar min gida wlh,yaro dan mutunci ga kyauta,Islaha tace ae naji zan tafi bazan taba sonsa ba wlh ni bana sonsa,sabo da ya baku kudi ni zaku cuceni.
Lalai ta fara ruwan bala'i kizo gidana in ciyar dake amma nace kiyi abu kice a'a ai kuwa baki isa ba kici ki sha kice zaki rainani,Islaha tace iya na aikin wahala ta naci kyauta kika bani ba aiki nayi ba sannan aka bani,tuwon da rogo sai dambu ko danwake shine ake ta min gori sabo da ni bazan baki abin duniya ba,nidai na fada miki bana sonsa gwara na bar gidan kuma da bana gidan ai da baku samu kudin ba,zan iya danne ki na kwace kudin nayi tafiya ta gwara ki kyale ni kaka Lalai,ni talaka na nake so kaninsa,ba wanda yake bani ci da sha a dangi babu wanda zai fada min naji kaf garin nan,bani da mafadi sai a bari ace an dauki nauyina sannan sai a fada min naji,kullum in yini ina aiki a bani dan tuwo shike nan a dameni ace za a bani Umarni a haka zanbi umarnin? Ba a dauke ni a matsayin 'ya ba,ko Baffa Ghali dukkansu basu isa dani ba,daurin aure kuma ko a masallaci al'ummar annabi zasu daura min.
Lalai tace zaki ci ubanki da ni kike zance,duk wannan abin da kike yi kyaleki ake yi,ai dai a gabana kike to kamar kin so Ibrahima,Wallahi bazan aure shi ba cewar Islaha,shuru Lalai tayi mata suka ci gaba da aikin girki,Lalai ta kawo maggi dunkule biyu rak wai shi za a sa a miya ya isa,ga miyar da yawa,Islaha ta mike ta dakko farin maginta data siyo a boye ta faki idon Lalai ta watsa a miya sannan ta kara dunkulen biyu a ciki,haka take yiwa Lalai kullum,sai aji miya zakwai zakwai Lalai ta zaci tsabar gogewa ce da girki irin na yan birni yasa Idan Islaha tayi miya zaki kamar kar miya ta kare,sai Abdulrazaqu ma yace a dinga bawa Islaha miya tana yi gaskiya tafi dadi.