Sashe 22
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sahil sai dare ya tuna da waya ana kiran mutum a ciki,cikin dare ya dinga kiran Islaha ko dagawa bata yi ba,da ta gaji ma kashe wayar tayi gaba daya,Sahil kwana yayi yana gwada kira sai bacci barawo da asuba ya dauke shi.
Gaba daya gidan baya musu dadi sam Sahil ya rasa sukuni hakan sai ya damu Sohail shima ga Maheera tana jin haushin su duk Sohail ya damu kansa,tunda ta tafi ganin gida bata kira shi ba.
Wayar Sohail ce tayi kara ya duba,yana dubawa yaga Email ne aka turo sako,dubawa yayi sai ya ga an dauke shi aiki a kamfani personal assistant na matemakin manager aka bashi,ga Alert na kudi,sannan gobe yaje ya karbi motarsa da takardun gidansa
Sahil yana daki yanda yanzu yake zama baya so ma a kulashi,Sohail ne ya nuna masa,murna ya tayashi sosai,Ya fito ya turawa Maheera text ya sanar mata,tayi murmushi tace mashaallah.
Message ta turo masa congratulations! sai ka dage nan gaba ka zama manager din da kansa.
Karantawa yayi ya tura mata yaushe zaki dawo?
Reply ta masa da Jibi Inshaallah,ya furta Allah ya kaimu da baki kawai ya maida wayarsa Aljihu shi a dole ya bata amsa yace Allah ya kaimu,shuru taga ba reply nasa ta zubawa wayar Ido tana jira,shi kuwa ya riga ya fada da baki.
Maman su Maheera wacce take katuwa da ita me kiba kyakyawa ta kalli Maheera tayi murmushi tace Maheera wannan Sohail din da kike min zancensa ko da shi za ayi ne? Murmushi tayi,Mama tace wlh naji dadi da kika canja hali Maheera amma da kullum baki da aiki sai tsokana sai fada,Maheera tace hmm yanzu ai wannan aikin da nake samu ina yi kinga Mama dole nayi ladabin dole kar a samu matsala a kore ni,daga haka ban san sanda na canja hali ba gaba daya,yanzu ko kudi kika bani bazan yi abinda nayi da ba,nayi hankali, a baya ma ai da kuruciya.
Juwairiyya tace lallai Aunty Maheera Allah dai yasa kin daina kar kije ki samu miji kice zaki yi masa wannan mulkin kama karyar kice dole ke sai an miki yanda kike so,sai kin samu yanda kike so nasan hali,Ammar yace wlh kamar kin sani nima abinda nake so nace kenan,dariya suka yi Maheera ta mike ta bar dan karamin palon nasu dake gidan nasu gaba daya 2 bedrooms ne sai palo sai kitchen da toilet,daya bedroom din na Ammar daya Juwairiyya, Mama da Maheera,gidan daidai talaka.
Adnan ne ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya fito yana tafiya da kyar kasancewar baya cin abinci sosai sabo da tafiyar Islaha,yana kallo Amal ta tafi gidan mijinta ko magana,Zayna ko me zasu yi kanzil baya cewa.
Adnan yace ka wanke min motar? har ya gama maganar Sahil bai jin ma me yace ya tafi tunani,Hello....Adnan ya furta sannan a hankali ya dago kansa ya kalle shi,yace munce mun daina aiki muma aikin yi muke nema ku dauki ma'aikatan ku ya juya baya abinsa yana cewa ina cikin tunanina kawai ka dameni.
Adnan cike da masifa yace kaje ka wanke min mota tun wuri na fada maka,ko kulashi Sahil baiyi ba ya koma ya kwanta abinsa.
Ran Adnan ya baci sosai yau Daddy ya kira a waya ya daga bayan sun gaisa Adnan yace Daddy karar Twins na kawo maka yanzu kwata kwata sun raina mu baka isa kace suyi ba,babu abinda suke yi sai rashin mutunci,aikensu idan kayi zasu ce baza suyi ba direct,Daddy murmushi yayi yace to baka ganin ba kalau suke ba,Aljanun ne suka canja su,ai Daddy ba komai Aljanu zasu sasu suyi ba naga dai Aljanun sai lokaci lokaci suke zuwa kansu watarana ma sai ka rantse kalau suke,ko yanzu yanda suka koma kenan da lafiyar su.
Daddy yace aiki yayi min yawa Adnan na kusa zuwa garin akwai wani meeting da zamu yi da me gidana zanga me suke yi,Adnan yace shike nan,Na bawa Ibrahim kyautar gida shima ya kamata yayi aure,Adnan yaji dadi,cikin Daddy ya buga yace twins fa?
Daddy yace su nake tunani gaskiya babu wata mace da zata so twins a haka bare ma suyi aure,ai baza su iya rike aure ba sabo da rashin lafiyar su,Adnan yaji dadi yace gaskiya dai,sai da suka gama hirar kamfani suka kashe wayar.
Sohail yau an bashi sabuwar Motarsa da takardun gidansa sannan ga Alert na kudi masu nauyi,Murna tasa yau da wuri ya shiga motar ya dawo gida,Adnan yana shirin fita yaga mota baka kirar Marcedes baka me kyau sabuwa ta shugo gidan anyi parking.
Sohail ne ya fito daga ciki da takardunsa a hannu,Adnan ya saki baki yana kallonsa ina ya samo mota ne,yanda bai kulashi ba shima Sohail bai masa magana ba ya wuce ta gabansa ya shige ciki.
Sahil ya samu yana kallo a palo,yace wai Sahil baza kayi hakuri ba akan yarinya ta tafi fa, please kaci gaba da rayuwarka,kaga Allah ban zanci zan iya komai a duniya ba duba da yanda a makaranta gaba daya bani da kokari ba abinda na sani sai dai a jarabawa,amma yanzu kuma komai sai naga kamar ba yi nake yi ba da kaina kamar yi min akeyi,ta ya zan san wannan uban turancin Sohail,amma sai naga na karanta sai naga na iya computer,amma a school bamu iya komai ba muyi ta jin kunya,ni dai mamaki nake yi da nake iya aikin nan sai mu kasa abu watarana kuma mu iya shi,turanci fa ka duba watarana sai muji munyi watarana sai mu kasa ko sentence daya.
Sahil yace rayuwa ce kawai ni ta Islaha nake yi,na gaji kada Allah yasa ta dawo tayi ta tafiya na gaji da halin yarinyar nan,bata da kunya dama badan haka ba daga yar magana sai ta tafi cikin dare ita ga me zuciya,tana dagula min lisaafi.
Sohail ya nuna masa key din mota da takardun gida ya nuna masa Alert yace to wahala ta kare gobe zan fara aiki.
Sahil wannan murnar tasa ya share zancen Islaha sunyi kudi yanzu.
Sohai ya furta Yanzu Oga yace Business na kayan da suke shigowa da shi za a koya min sosai nafi dacewa da wajen sabo da ko wanda bai boko ba zai iya wannan bangaren na shige da ficen kaya ta kamfanin yace shine daidai ni,tunda na fada masa watarana zata iya kwabewa na kasa karanta komai ko computer din ma ta gagareni,shine yace to wannan bangaren shine daidai ni ko ba boko zan iya.
Bari a nunawa Maheera Sahil yace kai baka da hankali ka nuna mata gida da mota amma kudi ba a nunawa mace samu baka ji maza suna fada ba,Sohail yace ahhh gaskiya a nuna mata na farko shike nan ai,ita ta iya bata yi kyashi ba ta samo aikin sai mune zamu ce baza mu nuna mata ba"
kai nuna mata karka ishe ni,ko ni yanzu baka so na irin Maheera,komai ita komai ita cewar Sahil.
Dariya Sohail yayi yace nima na rasa dalili ba a son raina ba ban san ina yi ba,abin yana damuna ka tayani da addua,Sahil ya furta Allah ya yaye maka to.
Sohail Maheera ya samu a kitchen lokacin ta dawo daga gida tana girki a hankali ya tsaya a bayanta,kamshinsa ta ji ta juyo da sauri,dariya yayi yace kin fiye tsoro,matsawa tayi daga yanda suke tsaye gaf da juna,Maheera ta kalle shi tace any Good news naga kana wani murna kai kadai,wayarsa Samsung ya mika mata yace gashi ki kalla,Maheera ta duba ta gani ta rufe baki da tafin hannu tana murna,Key din mota ya karkada mata a saitin fuska,ta karba ta gani tace wow,sai takardun gida, Alhmdllh gaskiya na muku murna sosai Allah sanya Alkhairi.
Yace to aikinki ya kare kuma ki shirya ki koma gida,Maheera tace a'a ni ka kyale min aikina gwara na dogara da kaina,au ke bada Allah kika dogara bama da kanki kika dogara? Karki shirka dai.
dariya tayi tace wai kudin nake nufi, badai albashi ne ba ni zan dinga biyanki abinda suke baki,maganin Mama da sauran matsala ta kannenki duk zan dinga yi.
Maheera tace idan ka daina yi fa? ku maza wani dorar da alkawari kuke yi wannan ba yuwuwa zaiyi ba, haushi Sohail yaji yace kice kawai karya nake yafi miki,wanne irin abu ne haka ana fada miki bakya ji,kinfi so ki zauna kiyi ta girki,Maheera tace gida kake so na koma? Na barku kuci gaba da wani abin ba daidai ba nasan me zaku aikata gaba.
Da ke kika raine mu ba haka kika tsince mu ba Allah ne yake tafiyar da komai,Kice dole sai kin samu a hanya,ke zaki shiryar damu? badan muna ganin mutuncinki ba 'yar tatsitsiya dake har ke zaki ce kato kamata nayi abu nayi,Kalle ki fa kalle ni baki wuce na goyaki na zagaye Abuja da ke ba gaba daya ko hutawa bazanyi ba.
Maheera dariya take tace Sohail ni kwana biyu naga kamar hankali kuke yi sai kuyi ta magana ta normal mutane,kallonta yayi kawai tare da shafa gemunsa yace girma ne yazo kalli fa gemuna ya furta yana shafa gemunsa.
Sahil ne ya shigo ya kalli farfesun da Maheera tayi yace mota ta dawo min da hankali na yanzu yunwa nake ji,nama daya ya dauka ya cinye ya karbi key din motar yaje ya shiga ya tafi dani shima wanda da akwai karambani Sun iya mama Asmau ke hanasu hawa sabo da matsalar kwakwalwarsu.
Maheera suna ta hira da Sohail basu saba rike kudi ba sabo da ba a basu kudi sam,yace yanzu ya za ayi da kudin nan ne? Sun isheni a accnt dina ni na rasa abin siya,Maheera tace ance maka kashewa zaka yi lokaci guda? Matsalar data dame ku zakuyi,Sohail ya lula tunani yace matsala mu bamu da wata matsala muna ci muna koshi muna da sutura to mene za muyi?
Kuje kuyi tunani mana matsalar taku,Sohail yace yawwa kika ce muna bukatar aiki mu samu kudi muyi aure mu haifi yara ko? Maheera tace ae mana to ai a fara ta kansa,dariya tayi tace kuma daga samun kudin sai auren kana da budurwar ne?