← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 46

Sashe 8

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido ya zaro yana kallon Islaha wacce suka zauna a mota budurwa tsaleliya cikin damammun kaya, bum short ne a jikinta da guntuwar riga gaba daya ta kudundune jikinta sai kakkare jikinta take yi tana jin kunya wanda da kyar take tafiya da alama bata saba ba,ga duwawu kaya guda komai ya ji,a gigice ta fito ta fice da sauri bata iya kallon kowa ta tare taxi ta fada ciki suka tafi,Sahil yana tsaye yana mamaki

Ya furta wonder shall never end,so duk mata haka suke wannan wato mummunar dabiarta ce ashe amma a haka kamar ta kirki,tsaki ya ja yana mamaki yace ahhh amma na dorata a cinyata harda wani ita ba haka take ba,shi yasa ni fa dama can jinina bai hadu da mata ba,indai akace mata ne to ba ruwana da su,Allah yasa nidai bana jin sha'awa,mata suje da abin su gwara da Allah yayi ni haka Dagger din bata aiki thank God ya juya zai tafi kenan sai Khalisat yar uwar Islaha ta fito cikin tsaleliyar motarta fara kal"

Sahil ta kalla ta furta wow kaga wani handsome,harshenta ta zaro ta lashi labbanta tace wannan idan na mallake shi aurensa ma zanyi,zan iya cinye wannan danye wow,da gani dan me kudi ne ba karya,anya ma kuwa yasan hausa,Sahil kuwa waya yake da Sohail bai ma san me take yi ba sai ji yayi an masa horn,bai ko juyo ba sai da ya gama wayarsa ya juya zai tafi Khalisat ta sauke glass kasa tana murmushi,ba karya ta zuba kyau doguwar rigar silk material ce a jikinta kusan tsirara tsirara haka take komai ana gani,Tunaninta zata birge Sahil sai taga ko a jikinsa kamar namiji ya kalla.

Murmushin da tasan yana kara mata kyau tayi cikin yanga da salon lankwasa murya ta furta zan iya dropping naka? Sahil da sauri ya furta no,please ta sake cewa tana wani shagwaba, gashi yana ta tunanin ko aljanun nasa zasu fada masa wace ita amma shuru,haka Islaha ya kasa gane gaskiya wanda a aikin banza kawai sai dai suji an fada musu abu amma wannan karon shuru ba labari.

Motar ya bude a fusace ya shiga baya yace muje,tace gaba zaka dawo sai kace ka shiga taxi
Yace haka nake so idan baza ki iya ba sauke ni,shuru tayi ta ja motar ta hau titi tana tambaya ina zan saukeka? Kafin ta rufe baki yace kasan gada,baki ta bude tace wacce gadar? Ya furta inda mutane suke kwana, Khalisat tayi mamaki sannan

Tace wai baka da gidan zama? Ya furta ae neman kudi nazo cirani,Wani dadi taji itakam tayi tsuntuwa,tace no ai baka samu aikin ba ko? Yace yeah, Alright muje gidanmu zan baka daki ka zauna har na wani lokacin da Allah zai sa ka samu wajen zama? Ko godiya Sahil baiyi ba ya furta Okay da fatan dai ba karuwanci zanyi ba? Domin kudin karuwanci da za a biyani bazai dauke ni ba,yana wani fisfisga shi kadai yana muzurai,dariya khalisat tayi kawai itama kyakyawa ce mashaallah komai na birge maza tana da shi.

Gidansu me kyau ta nufa da Sahil ba wani shayi ko dar dar, suna zuwa tayi parking ya fito ya kalli gidan yace gidan ba laifi,Khalisat tana murmushin jin dadi,ciki suka shiga tare.

FREE PAGE

400 NE

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

'Yan Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?id=6687e323e3651b348bbd12f6

🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸

11-15

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Mrs Chief

MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL A JUYA BA,DUK WANDA YA DORA A CHANNEL SAI AN SAUKE.

Gidan nasu yana da kyau sosai Sahil har palo Khalisat ta shigar da shi wanda palon ya gaji da kyau da tsaruwa, murmushi tayi tace sit,zama yayi ta shiga kwalawa Mum kira tana cewa Aunty dake duk ta hanasu kiranta da Mama ko Mum kawai Aunty ce kar su kara cewa ita ta haife su,Aunty ce ta fito tare da Khairat,suka zubawa Sahil ido suna kallonsa,Aunty ta hadiyi yawu dama ace saurayinta ne,itama Khairat haka,Aunty tana yiwa Sahil kallon duniyanci tace wannan fa? Khalisat tace he is my friend zai dan zauna damu for a while kafin ya samu gidan zama,ai dakin nan a gyare yake? Aunty ta saki murmushi tace a ranta da alama akwai kudi a hannunsa.

A fili ta furta ba damuwa a gyare yake ai ki kaishi sai a kawo masa abinci da ruwa, yaje yayi wanka ya huta,Khalisat tana murna ta riko hannun Sahil tace lets go,hannunsa ya fisge tare da hade rai ya mike ya bita har bedroom lafiyayye me dauke da gado da sip da mudubi tare da toilet dakin yayi kyau,ac ta kunna masa tace kayi wanka bari naje nima zanyi wanka sai na sa yar aiki ta kawo maka abinci,Sahil dai yana kallonta da mamaki abinda suke masa ba tare da sun san shi waye ba.

Bayan ta fita yace karfa ko yan mafia ne ban sani ba,no..no..kaina yafi karfinsu baza su iya dani ba,Allah bazai basu iko a kaina ba,wani tunanin ya sake ya furta kaiiii....karfa naji na bace kar a siyar da kaina,su din banza nafi karfinsu yace sannan ya shiga toilet abinsa,wanka yayi ya fito ya saka kayansa kanana riga da wando,Navy color ya sha uban kyau sosai, gefen rigarsa ma da yar laimar ruwan jiya da ya zane shi.

Knocking yaji anyi,yace come in,a hankali aka turo kofar tare da shugowa dauke da sallama a bakinta,Sai yaji kamar yasan muryar,Islaha ce ta shugo dauke da tire a hannunta na abinci da ruwa,sanye take da Hijab har kasa tana wani dari dari,a hankali ta dago kanta suka yi ido biyu,yace you.....yana nunata da yatsa,kanta ta sadda kasa fuskarta dauke da murmushi ta dago a hankali

Fuska taga ya daure kamar bai taba saninta ba a duniya,mamaki ya kamata matuka,ransa a bace yana mata wani mugun kallo yace kalle ki kamar ta kirki a haka,munafukar banza,ido ta zaro tana kallonsa,yace ban san me ke damunku ba matan wannan zamanin masu fuska biyu,a fili kuna nuna ku na Allah ne a badini ashe kuna da wata mummunar Dabia da ba san da ita ba,daga yau karki nuna kin sanni a duniya,kuma duk wani abu nawa karki sake kice zaki taba,avoid me duk inda kika ganni karki sake ki kulani kuma karki taba min abu,abincinki dauki ki kara gaba bana bukata.

Islaha tsoro da mamaki ya kamata,ita tasan bata masa komai ba ita,a tsorace ta juya! Ya ja mata wani wawan tsaki tare da furta stupid,yana uban huci ya kwanta a saman bed din,tuni Islaha ta fita ta bar masa dakin tana mamaki me ta masa sannan me ya kawo shi gidansu a ina yasan Khalisat,jajayen lips dinta ta turo gaba tace koma mene zan gani wlh Allah yasa ace dan iska ne me neman mata wallahi sai ya hadu da rashin mutunci na sai na fito da sabuwar bad character dina a gidan Nan,kowa sai yasan Islaha bata da mutunci,kowa sai yasan ni ba a gaban uwata na taso ba,kuma sai an san ni yar tuwo tuwo ce ta raini ni,badai suna bada gabansu ba maza suna ishiriniya abinsu,mace kawai ki bada jiki namiji ya dinga ishiriniya a kanki zan gani ta ja kwafa.

Khalisat ce ta shigo dakin Sahil cikin wata gown guntuwa maroon wacce da kadan ta rufe duwawunta,Sahil dai kamar yaga namiji again,tace ya an kawo maka abincin? Yana kakkafe idanuwa yana masifa kamar ubanta yace wata banzar yarinya ce ta kawo bana so ta sake kawo min abinci,Khalisat tace Islaha ce yar kauye,ai wannan yarinyar dabba ce gaba daya,Sahil nan take yace a'a fa Allah ya gani dai mutum ce,Khalisat zata sake magana yace ba ruwana da ita ni kawai kiyi shuru,sam baya so a zageta,Khalisat tace yar iskar yarinya.....kafin ta rufe baki ya fara waka dan kar ma yaji yana kida da bakinsa gijib... gijijib...tsayawa Khalisat tayi tana jinsa tana dariya wakar tasa ta hausa ce yake yin abarsa,Juyawa tayi tace bari na kawo maka abincin da kaina ta fice.

Dauke da abincinsa ta dawo a plate jullof rice ce ta sha hadi da naman kaza ga ruwa da lemo,zama yayi ya fara ci Khalisat ta zauna a gefensa tare da dafa kafadarsa,ya zame a hankali yana cewa hannunki nauyi,kasar da aka halicce ki da ita wajen nauyi aka ebo,,kyale shi tayi tare da furta sorry tana lasar labba,yace ko ci zaki yi ne? da sauri ta furta a'a,sai bayan ya koshi sannan ta mike ya gabatar da sallolin da ake binsa har ya idar,Khalisat tana zaune a gefen bed din tana jiransa,juyowa yayi ya kalleta tare da furta zanyi bacci,Khalisat ba kunya tace zan iya taya ka kwanciya? idanuwa ya zaro sai da ta tsorata tun kafin yayi magana a fusace ya mike ya jawo jakarsa yace ki tayani kwanciya a wanne dalili raping dina zaki yi? Mikewa tayi tana bashi hakuri I'm sorry kwanta akan yar wannan maganar zaka tafi? Kayi hakuri kwanta abinka,ta fice da sauri sannan ya kwanta abinsa.

Sohail....Adnan ya kwalawa kira....Sohail...ji wannan banzan yaron ina kiransa,Sohail ne ya fito daga kitchen da sauri,fada Adnan ya hau yi yace sabo da hauka kana ji ina kiranka,Sohail kansa ya nuna yace oh dama kirana kake yi? Uwarka nake yi cewar Adnan.
Sohail yace ai ta mutu Maman,
Ba wannan ba ai ba ita ta haife ku ba,uwarku arniya ita nake nufi, Sohail yana tsaye sanye da jean black da riga arsh color yace kai ka santa ma ashe?
Dama muna da uwa? Kuna da ita arniya ba Adnan ya bashi amsa.
Arniya ce? Taji dadinta ba ruwanta da kishirwar azumi,ta tsula tsiyarta kawai ba komai.
Adnan ido ya zaro yace uwar taku? Sohail yace kai mu bamu da uwa.
Chapter 8 · 0% Book details