Sashe 10
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa yayi zai tafi ta ruko shi tace na sallameka ne? Ban gane ba sai ma kin sallame ni? Ke mace fa ni baza ta juya ni ba in fada miki gaskiya 'yar nan, Maheera tayi dariya tace to fa,har ya tafi ya dawo yace na fasa tafiya zo muyi game?
tace wacce iri ba kayan game a nan.
Wasan yar buya buya zamuyi,okay ka bari sai gobe idan naje test sai muzo muyi kaga ko Oga ya kama mu kawai korata zaiyi shike nan.
Sohail yace no ba a haka kuyi rabuwar mutunci basai munyi ba tunda baya so.
Okay tace kawai,kallo ya fara kare mata yace wai mene wannan a kirjin ku?
Sam Maheera bata gane ba,yace gashi nan tulu tulu ana gani.
Maheera fuskewa tayi duk da taji kunya tace shi kuka sha kuka girma,yace Allah sarki na Mama yana kabari yanzu ina tunosa ke ya akayi naki chakare chakare ita kuwa Umma Nadia nata kamar na tsohuwar saniya wacce yunwa ta kamata.
Maheer ta dinga dariya ba shiri tace Umman taku guda?
Sohail yace ke bafa ita ta haife mu ba Na Mama yana Kabari nata me kyau ne Daddy ma ya dinga ta yashe baki idan tana wajensa ya dinga ta dariyar dole hahahaha ranar girkin Mama,Allah ko ni sai na iya Auren Mamata.
Dariya ta sake kama Maheera tace ashe ta hadu dai?
Yace tab ke kin isa ma kice shekarunta 47, Mamanmu ta iya sa kaya ko wanne wanka kyau yake mata ga kamshi,gata da mutunci ke Mama fa duniya ce,akwai uwar data kai tamu ma,Maheera tace Mamata fa? Sohail ya bata rai yace ko uwarki bata kai Maman mu ba.
Da sauri Maheera ta kalle shi tace zagina kayi fa Sohail,yace to ba uwarki bace? Uwarki mana nace bata kai tawa ba,nifa in kika takura min zan iya miki dukan tsiya.
Maheera tace ni din?
Kwalla ce ta cika masa ido tab da ya tuno da Mama Asmau.
Maheera tace sorry mene abin kuka? Yace baza ki gane bane... baza ki gane ba ina ta so na baki labarin damuwa ta sai kice baza kiji ba labari na akwai jira kafin a saurara,tsaki ya ja ya fice yayi tafiyarsa .
Maheera ta tsaya kamar gunki tana mamaki.
Bata yi tunanin zata ganshi ba washe gari ba
Sai gashi da yamma ya sha farar shadda tana shining ba karamin kyau yayi ba ka rantse wani me kudin gaske ne,ga kyau,ita kanta Maheera tsayawa tayi tana ta faman kallonsa,hannu daya a aljihu ya shugo yace ya garin me shago? Tace lafiya lau tana murmushi.
Hannunta ya riko yace zo mu tafi.
hararsa tayi tace bazan je ba shine jiya kayi fushi?
Yace ni din? Yana nuna kansa da yatsa yace me nayi jiyan?
Au ka manta? Yace na manta kuma har ga Allah har ya manta ma,sai da ta tuna masa yace Oh ya share zancen kamar ba shi ba.
Mikewa tayi suka fito,zata rufe shagon ya karbe key din yana cewa kawo kamar namiji mace tana wahala haka Mama bata irin haka,ai ana taba ki kice wash zan mutu.....harda gwadawa! dariya Maheera ta fara yi ba shiri har ya gama rufe shagon yace muje
Juyawa tayi tana rataya handbag dinta,yace kawo handbag din na rike miki ki daina wahala zaki yi muscles kamar na maza ki bubbude.
Jakar ya karba ya rike a hannunsa suna tafiya suna hira,yayi hauka yayi hankali a haka har suka je gidan su.
Maheera kanta ya kusa bugawa ganin irin unguwar da suke da layin da suke balle uwa uba gidan nasu tamfatsetse na gani na nunawa sa'a,tace a nan kake zaune? duk bata kawo gidan uban Sahil da Sohail bane,tunaninta ma yaran riko ne ko 'yan uwa.
Sanda suka shiga Maheera tana ta kalle kalle ya kalleta yayi dariya yace kinga gida me kamala ko? Yana dariya yace ai kamilallen gida ne wannan ba ballagazin gida ba irin naku,nasan gidanku ballagazin gida ne.
Maheera tayi dariya tace kaima ai ba naku bane,bai ce mata komai ba,yace muje na nuna miki kitchen din,In kin gama girkin ki shirya a dining sai na kira su masu gidan su dandana.
Haka ya fisgi hannunta ya jata ko ina na gidan sai da ta dinga hakkin sosai yanda yake fisgarta sai hakki take da nishi, da sauri yana nuna mata ko ina har katafaren kitchen din katon gaske komai akwai ciki,ya nuna mata komai da kayan sarrafawa,kin gane? tace ae naga komai da nake bukata akwai,yace yawwa to fara girkin ni bari naje na gyara dakin Adnan da na Ibrahim kafin nan kin gama,ta furta ba damuwa,ya juya ya tafi.
Farfesu ta fara yi na naman rago sannan ta tsara fried rice lafiyayya taji hadi da su hantar rago da naman kaza,sannan ta hada couslow da lemo ingantacce ta shirya a Dining, har da potatoe ball tayi da kwai da nama a tsakiya.
Tana gama shiryawa a dining ta zauna a palo tana kallon tv,sai taji karar takalmi me tsini ana sakkowa daga sama ,Kamshi na mamaki ya mamaye palon.
Zayna ce take sakkowa ta sha wata material gown ready made abinta golden ta tsula kyau,kana gani kasan taji hutu da kudi ba karya,Maheera tsabar tsananin kyawunta yasa duk inda mace takai bata isa ta fita ba sai dai daiku tunda a duniya baka rasa wanda ya fika dole ne wannan.
Zayna wani kallo ta bi Maheera da shi sama da kasa ta ganta sanye cikin material silk black me adon flower pink sai dan mayafi siriri data dora a kanta,takalminta normal dai na talaka me dan kyau gashi nan dai,sai dai kyawun Maheera ya tsoratata amma ganin mijinta yana da class kuma sannan yana sonta gashi ma shi sai me kudi yake kulawa sai kawai ta fuske a ranta tasan itama me kyauce komai da namiji ke nema wajen mace tana da shi.
Maheera mikewa tayi tsaye da sauri tace good day Ma,Zayna ta wuce Dining kawai ta zauna ba tare da ta wani amsawar kirki ba,Ibrahim ne ya fito yayi arba da Maheera ya bita da uban kallo ya dauke kai ya wuce Dining ya zauna,shima tace Good day Sir, har tana risinawa,hannu kawai ya daga mata,Adnan ne ya fito shima yana zuba kamshi ya hade cikin kana nan kaya masu tsada blue, ko kallo Maheera bata isheshi ba ya zauna a Dining,sai ga Sohail shima ya fito sanye cikin gajeren wando da riga singlet da bocket da mopper a ciki ya hada uban zufa.
Hannunsa ya goge da karamin towel ya karaso wajen Maheera yana murmushi yace kiyi serving nasu cikin rada yayi maganar.
Maheera ta karasa da sauri tana cewa kuyi hakuri" nan take ta fara serving nasu har ta gama,suka ga girki sharr tun a ido ga kamshi.
Ibrahim ne ya riko hannun Maheera zata juya yace zo ki canja min Spoon 'yar kauye.
Tsoro Maheera taji akan idon Sohail aka yi,daga haka Sohail kawai idonsa ya canja ya nufi Ibrahim gadan gadan ya sa baki a saitin keyarsa ta baya ya gartsa masa cizo sai da wajen ya fashe,Ibrahim ya saki kara da ihu ya mike zasu yi kokawa da Sohail!
Adnan yayi sauri ya rike Ibrahim yasan yana hada jiki da Sohail sai buzunsa karfinsu ba na mutane bane,yace kyale shi kai zaka biyewa mahaukaci,abin kullum karfi yake fa sun fara duka da cizo nan gaba sai tsince tsince a bola suna bin yara da gudu.
Zayna ta tabe baki tace yo ni da suka ce zasu aure ni su biyu ma.
Sohail yace in Allah ya yarda baza ki haihu ba,mahaifarki ta mutu a haka zaki gama aurenki,Adnan yace ameen da sauri kayi addua me kyau dama ni bana son haihuwa, Zayna kamar zata yi kuka tace da Sohail mahaukaci karya kake,Maheera tana ta kallo ta gaji ta janye Sohail tace relax mana ta jashi suka koma gefe suka zauna,Sohail yace da Sahil ne ya rikeki da sauki bazan damu ba ai wannan ba yi bane,kawai a rike mutum idan kika masa ciki fa,Maheera ta danne dariyarta,tace au ba ma shine zai min cikin ba nice zan masa? Ina ka taba ganin namiji ya haihu?
Sohail yace ke wancen kwarto ne tsaf zai iya haihuwa,tayi murmushi kawai tana boye dariyarta.
Kallonta yayi yace ki dinga rufe wannan chakare din naki ni bana son ganinsa duk sai gani ake ta yi Mama fa Hijab take sawa idan zata fita ba a ganin nata,badan ma mama ce ba ai sai nace miki bata da Chakare din nan.
Amma ke kowa sai gani akeyi haba Allah za a daina ce miki Classy girl me shago kawai yafi dacewa dake,Maheera ta rufe bakinta sabo da dariya.
Can gefe kuma su Zayna sai kwasar girki suke yi me shegen dadi suna ta ci,Adnan cikin santi ya kira Maheera da hannu,ta karasa a nutse yace aikinki yayi kyau na daukeki aiki,zan dinga biyanki dubu dari,tana murna tayi ta godiya abinta yace gobe ki dawo nan da zama ki fara aikinki,ga Sohail nan zai nuna miki room dinki,tace na gode Sir na gode ta juya ta fice.
Ibrahim sai duri yake ko kala bai ce ba,itama Zayna haka.
Maheera ta fice daga gidan tana ta murna,Sohail ya biyo bayanta yace dama na fada miki zaki samu baki yarda dani ba gashi kuma,tace na yarda ai yanzu na gode sosai Sohail,yace ki daina gode min ni,muje to ka rakani,yace a'a na gaji ni bacci zanyi,tace to bye,ya juya abinsa ya tafi itama ta wuce gidan da take kwana gidan wata kawar Maman su,matar tana auren me rufin asiri a Abuja,itace ma ta samowa Maheera aiki ganin halin da suke ciki a suleja ta kawota gidanta Abuja ta samo mata aiki,matar yaranta uku yare ce kuma na Igala,tana da kirki ga tausayi.