Sashe 6
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adnan suna mamaki yanda suka kulle kitchen amma suke ganin su Sahil kalau da su,takaici ya sa suka bude kitchen din ma,Sahil a zaune ya iske Adnan da Ibrahim a dining suna duba files na aikin su,yana inda inda yana magana da kyar yace Adnan...za...zan...tafi...unguwa..Ibrahim yaci magani yana masa wani irin kallo cikin hargagi yace ina zaka je? Sahil yace kawai duniya zan shiga zan nemi kudi nima....kafin ya rufe baki sun kece da wata mahaukaciyar dariya suna ta faman sheka dariya,ya tsaya yana kallon su har suka gama dariyar,Adnan ya kalle shi sama da kasa yace so a haka zaka nemi kudi? Dama kana da kwakwalwa? Ina kaga kwakwalwar neman kudi?...suka sake kecewa da dariya,dama zaka iya tunani haka? Cewar Ibrahim,dariya suka sake saki suna tafa hannu,Sahil gaba daya sai yaji gwiwoyinsa sunyi sanyi,sai yaji ya sare gaba daya,ya tsaya kamar gunki,idanuwansa suka cika taf da kwalla yanda suka sashi gaba suna ta dariya.
Adnan ne ya dakatar da Ibrahim ganin zai fara masifa,yace wait Ibrahim,kai Sahil kudin mota za a baka? Sahil da kyar ya iya magana yace ae,Adnan yace wow Sahil you get heart wooo,nan take ya zaro 20k yace gashi ya isheka kayi manage har ka samu dai ka samu aikin yi,idan wahala tasa ka gaji zaka iya dawowa Abuja ga gida baka da damuwa.
Ibrahim yace yanzu duniya zaka shiga kenan Sahil? Sai kuwa suka sake barkewa da dariya,Adnan yace dan Allah jeka dariya zata kashe ni,Sahil ya juya jiki ba karfi ya tafi.
Dakin su ya wuce direct yana shiga ciki ya fada saman bed yana kuka wiwi,Sohail ne ya shigo ya same shi a haka,Shima bai ji dalili ba ya kwanta a gefensa ya fashe da kuka har yafi Sahil dinma kuka,Sahil a hankali ya dago da kansa yana kallon Sohail,Sohail yana kuka yace kar mu daina muci gaba dan uwana,Sahil ya daga kai sama alamar suci gaba din,suka ci gaba da kukan su,sai da aka dade suna abu daya sannan Sahil ya furta kai na gaji ya goge hawayensa ya jawo akwatinsa ya hada komai nasa,Sohail yace yanzu tafiya zaka yi? Yace mene amfanin zama ni tafiya zanyi na shiga duniya,gwara naje koma mene zai same ni ya same ni,to muje na rakaka.
Tare suka fito da Sohail suka shiga mota har tasha Sahil yace Lagos zan tafi naje nayi ta kwana a kasan gada a haka idan abubuwa suka warware sai na maka waya ka taho kaima kaji ko,Sohail yace to ba damuwa,har tasha suka je amma Sahil baida kudin hawa mota me kyau dole ya shiga trailer wacce ake zuba yan cirani a ciki ruwa da iska ya kare a kansu a hanya cikin kudi kadan.
Kudi ya biya aka rubuta sunansa da komai,yazo hawa trailer ya kasa,Sohail ya tsuguna a kasa Sahil ya hau dokin wuyansa ya mike sannan Sahil ya kama motar ya hau ya fada ciki,yana fadawa ya fada kan wata yar budurwa,yarinyar kuka take yi ta ture shi gefe tace malam mene haka,sorry ya furta ya dago ya kalleta,gabansa ne fadi ya ganta kyakyawar gaske yar fulani da ita,Jakarsa ya dauka tare da gyara zamansa a gefen yarinyar ga kafadarsa ga tata,gashi motar wani kan wani ake hawa ba wani Space dole a haka ake zuwa.
Sohail ne daga kasa a tasha ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya mike tsaye ya daga masa hannu suna dariya,yace karka manta in kaje ka kirani, inshaallah bro,ka kula da kanka,Sahil ya daga masa kai,mutane suna ta hawa motar kamar kasa,Sahil mamaki ya kamashi,gaba daya ba space a motar,wani akan wani haka ake a ciki,ko shanu baza a saka haka ba,jikinsu har yayi futu futu da kura,ga wasu gaba daya wari suke yi,ya rasa inda zai saka kansa a motar.
Wari ya isheshi,budurwar dake gefensa ya kalla ta toshe hancinta itama an matse ta da kyar take shakar numfashi a haka motar bayan ta dame da mutane babu kalar yaren da babu a ciki ta tashi ta hau kwalta suka fara tafiya.
Budurwar ce ta kwala ihu wani ya danno kanta tace wayyo zai kashe ni...zan mutu.....tana jan numfashi da kyar, Sahil ne ya dagata tana daga zaune ya dawo da ita saman cinyarsa,tace kai malam dan iska sauke ni,haka kawai ka dorani bisa cinyarka,suka fara kokawa da Sahil yace dole ki zauna ai nan yafi Safe,kina safe waje za'a kashe ki a nan wlh a banza,kina yar yarinya har kin san iskanci ne dalla rufe mana baki ko na kwada miki mari,budurwar ta zaro ido,wanda suke kusa da su sai dariya da ihu,wani dattijon banza yace wallahi kun dace kuma sai ace ma kanwarka ce kuna kama,Sahil yace na fita kyau ai,Budurwar tace Allah karya ne inji wa ka fini kyau?
Jifa taji anyi da ita a motar,wanda ta fada kan mutane sai da taji rauni,sabo da bata san Sahil ba shi a tabin nasa zafi ne da shi,mutane suka sake hankadota,kuka ta saki taji wuya,da kyar ta samu ta dawo wajen zamanta,Sahil shi kanshi motar ta ishe shi ya rasa inda zai sa kansa,ya gaji da tsaiwa ya gaji da zama.
Tausayi ya bawa budurwar tana satar kallonsa duk ya gigice kamar kansa da motsi,ana haka ruwa ya tsuge da iska me karfi,jakarsa tayi sauri ta jawo ta saka masa a cikin katuwar ledar da ta taho da ita yanda ruwa bazai taba ta ba,Suna tafiya ruwa na zane su a hanyar lagos,sai da suka kwashe lokaci me tsawo ruwan ya tsaya,mura da zazzabi suka kama Sahil,sai rawar sanyi yake,budurwar ta kalle shi tace ka canja ko rigar jikinka ce,bata jira amsarsa ba ta zuge ta zaro riga me kauri ta bashi,ya karba da kyar ya cire rigar jikinsa matan dake motar suka zubawa surarsa Ido suna kallon cikar sura da zallar kyau na halittar Allah,rigar ya canja,ta karbi wacce ya cire ta ajiye a gefe,dake ita da ledoji tazo manya ana ruwa ta saka abinta,ruwa bai jikata ba sam.
Gyangyadi ya fara bai sani ba ya dora kansa a saman kafadar budurwar ,da sauri ta juyo ta kalle shi zata yi magana ya dagata sai taga bacci yake sai kawai ta hakura ta kyale shi,kowa ya zaci tare suke ma mata da miji ne,basu san kowa tafiyarsa daban ba,wata mace dattijuwa tace gaskiya kinyi dacen miji 'yar nan gashi kamar yaro shagwababbe da shi ba ruwanki,dariya ta kusa kwacewar budurwar sai dai ta fuske tace uhm kawai, suna tafiya duhu yayi ba sallah ba salati ga uban duhu suna tafiya a daji,Sahil baccinsa yake kawai shi,zamewa yayi a hankali cikin bacci ya dawo da kansa kirjin Budurwar,tana jinsa gashi ko bra babu a jikinta, fuskarsa ya dinga turawa cikin kirjinta kamar zai sha nonon uwarsa,duka ta dirka masa a bayansa ya farka a hankali ya bude idonsa,sai lokacin ya tuna fa a mota yake.
Muryarta yaji me dadin saurare tace ka tasar min a jikina, tashi yayi a hankali yace ruwa....dariya ya bata tace lallai ma wannan wai sai kace yaro mutum da gemu kato da shi amma ni ina karama yake min haka, sai ka bari ai aje inda za a tsaya sai ka siya ka sha,wai kamar ba namiji ba kai,shuru ya mata yana zaune a gefenta ya sake komawa baccinsa.
Motar su ce ta lalace a dajin kowa tsoron hanyar yake,ana ta salati masu addua suna yi amma Sahil shi baccinsa yake ma,sun dade a wajen kafin ta tashi suci gaba da tafiya,sai cikin dare suka samu aka tsaya a garin yarabawa tasha suka firfito kowa ya tafi neman abinda zai ci da masu sallah,budurwar ce kadai ta kasa fitowa kafarta daya waje daya a ciki,Sahil yayi dariya sannan yasa hannu ya dakkota kamar ya dauki tsinke ya direta a kasa.
Kunya ta kamata ta diririce, Masallaci ya nema yaje yayi sallolinsa itama haka sannan yana fitowa ya siyi Apples,ya siyi ayaba,ya siyo naman kaza,sai ya siyo yogurt da lemo ga ruwa da wuri ya dawo cikin motar sabo da kar a fara turereniya,Ita kuwa budurwa bata da ko sisi na siyen komai kawai motar ta koma sabo da itama bata so a dinga ture ture da ita wajen shiga,shi kadai ta samu a ciki ya hau saman jakarsa ya zauna.
Kallonta yayi yace ya baki siyo komai ba? murmushi tayi tare da zama tace banda kudi ni,yace tab rayuwa sai da cin abinci,ki dinga cin abin kanki,shi yasa bakya ci gaba kullum jiya i yau gaki nan tsiya tsiya sai son kudin tsiya, kici a jikinki baza kici ba sai shegen asusunki a boye,Ido budurwar ta zaro duk abinda ya fada gaskiya ne,bata kashe kudi,indai abu ne wai tasa kudi ta siya sabo da ta ci to baza ta siya ba kuwa sai dai ta tara kudin a asusunta.
Abinda ya siyo ya mika mata gaba daya yace gashi ki cinye,baki ta bude tace kai fa? Yace kici kawai in kin rage ni na ci,tace no ai baza ayi haka ba to muci tare, a hasale yace kici dalla ko na kwashe na zubar,mamaki ya kamata,ita wannan wanne iri ne,haka ta fara ci duk abinda take sai da taci da yawa tace na koshi alhalin bata koshi ba.
Yace baki koshi ba kici karya kike,"hmm" kawai tace taci gaba da cin abinta sannan tace ya sunanka wai? Yace "Sahil",tace ni kuwa...katseta yayi yace sunanki Islaha,baki ta bude tace a ranta ko ba mutum bane wai,amsa taji ya bata yace mutum ne mana.
Tsoro taji yace ki daina tsoro mutum ne,ido ta zaro ta kasa cewa komai,yace zan iya fada miki asalinki gaba daya da tarihinki tsaf, tace to fada min naji.
Asalinki ku ba hausawa bane wani yare ne ku can yankin Taraba State wanda kamar fulani kuke da shanunku da komai amma ku ba fulani bane kuma,iyayenki yan Taraba ne,Babanki mahaifi sunansa Sule mamanki sunanta Halisa ana kiranta Nany,kuma ke kadai suka haifa sannan sun rasu, a hannun kanwar Mamanki kika taso a taraba,karshe itama mijinta ya rasu ta fara tuwo tuwo,daga nan ita da yaranta data haifa mata su uku namiji daya gaba daya da yaran nata karuwanci suke yi.