Sashe 40
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Islaha ce ta fito daga daki Sahil yace a nan kika zauna kenan? Ina turmin dakan? Islaha ta nuna masa,yace kinyi kokari gaskiya tafiya suka yi ta raka su gidan Baffa Gali,ganin su Sohail yayi Imani akwai kudi da sauri ya kira maza uku a dangi yace suzo anzo musu da maganar aure,har ya manta da Ibrahim,Kawu Tukur yace Sohail da Sahil su basu waje su jira a waje,sabo da baza su bari ayi abin kirki ba,suna mikewa Matar Baffa Gali ta fito dauke da danta a hannu ta zaro nono ta gaban riga yaron yana dauke a hannunta bakinsa yana a nonon yana shan abinsa.
Sohail ya kalleta ta wuce bagazan bagazan ba wani tafiya ta nuna macece,tace sannunku ta wuce, Sohail yace kai jama'a zanje na gwada akan Maheera, kun ganta da Danta bata daina haihuwa ba ai na zaci tsohuwa ce,Kawu ne ya harare shi,Sahil yace wato dai na fahimci a garin nan nono bashi da daraja da kima abin banza ne,Baffa Gali yace kuma dai kwa fada nayi nayi ta gyara taki matan kauye sai hakuri.
Iska ce ta taso filfil Sohail yana boye dariyarsa yace iska tana ta fifita shi,wai matarka ce? Baffa Gali yace ae me dakina ce,Sohail yace tab sannu,kuma idan ta wuce kana jin ta birge ka a haka? Kawu ne ya kore su nace kuje waje zan neme ku.
Fita suka yi kofar gida Islaha tana ciki wajen matan Baffa Gali,wasu yan matan kauye ne suka fito su uku suna tafiya,sai kallon su Sahil suke yi,Sohail ya kalle su suka hada ido da sauri suka dauke idon su tare da karawa tafiyarsu sauri,Sohail yace kai kuzo nan,a tsorace suka karaso 'yan matan,pic din Maheera dake kan wayar sa ya nuna musu yace kunga wannan? Suka daga kai ae suna dariya suna jin kunya,yace Sunanta Maheera duk duniya ba irinta a yanzu,kun san record din data kafa? ta kafa tarihi babba,domin itace wacce ta aure ni,Dariya matan suka yi,sun zaci wani babban abu zai fada da ta kafa tarihi a kai,Sahil yace ba kwaila bace irinku kuma,matan suka ji kunya suka fece da gudu,suna cewa kinji kamshin su kuwa,rabewa suka yi suna lekensu ta bayan bishiya, baki Sohail ya tabe suka ci gaba da hirar su da Sahil.
Baffa Gali da wuri suka Amince suka ce su ko yaushe suka shirya ba matsala su saka ranar daurin aure,gani suke su Sohail wasu attajirai ne,sai da suka fito suka bawa su Sohail labari yace ku fada yaushe kuka shirya? Sahil yace yanzu ma a daura,Kai shashasha rana za a tsayar su sunce wata biyu,Sahil ido ya zaro yace zan iya mutuwa sauri nake wata daya kawai zan iya hakuri, a matse nake Kawu bana bacci,Kawu ya zaci irin sha'awar nan ce ta damu Sahil harda daukan abin da muhimmanci yace to Inshaallah bari a fada musu.
Ya koma ya sanar musu,suna ta jira a basu kudin aure da komai su hau kai su danne sai da aka kira Sohail aka fada masa har sadaki da komai suka ce million daya,Sohail yace komai da komai? Suka ce ae mu yaran mu tsada ne da su,ba ragi? Cewar Sohail,suka ce ba ragi,yace ku duba mana ko dubu hamsim ku kankare,ba kudi ne damu ba kyawun ne kawai,suka ba ragi daga haka, yace ba matsala ya za muyi zan tura mata a account.
wani dukul suka ji,Baffa Gali yace ai iyaye ake damkawa, Sohail yace akan na baku bacci ya gagare ku gwara ku bari a bata abinta, kuka karbi kudin nan baza ku ji da dadi ba da kanku zaku dawo da su, Baffa Gali ya zaci kara zasu kai su wajen yan sanda irin ai zasu je wajen malamai su rufe musu baki sunci banza,nan take suka ce ba matsala,Sohail yace akwai me account? Baffa Gali yace ina da shi,nan take ya bayar aka tura masa,sai washe baki suke banza ta fadi.
Sallama suka musu suka fito,Baffa Gali yace munci banza yau zanje wajen malam Idi a rufe musu baki babu wanda zai tambayi kudin,har Islaha baza ta taba bude baki tace ina kudin aurenta ba,dariya suka yi Gali yace ai ni ko aron gona na karba ta mutum to da kanka zaka zo ka siyar min da gonar, idan kuwa kudi na karba bashi to sai dai a lahira na biya suna ta dariya.
Kawu Nafiu ne bayan sun fito yace ni naga saurin yardar su babu ko bincike sam sam,basu san wa zasu bawa 'yar su ba sun yarda,wannan yarinya bata da gata wlh,ace ba bincike kawai sun karbi kudin aure har an sa rana, Sahil yace sun taimaki kansu da suka yarda badan haka ba duk sai sun kwana akan kayoyi yau.
Islaha tana fitowa Sahil yace Amarya kusa da su ta karasa tana murmushi,Sohail yace an tura musu kudin aurenki komai da komai million daya kudina yanzu saura kadan a accnt kin kara min arziki na dade ina tarawa.
Hawaye Islaha ta fara ta rike Sahil tana shagwaba Allah....Allah...ni...uhmmmm...ya za ayi ku basu kudin...baza fa su bani ba...Sahil yace wayyo Kawu dadi shagwaba,Kawu da sauri suka yi can gaba sunji abin na twins ba kunya.
Kawu Nafiu,yace ayi sauri a aurar da Sahil wlh sai yayiwa yar mutane ciki bashi da kunya, Kawu Tukur yace yanzu watakil da kake gani Matar Sohail watakil ciki ne da ita,kasan irin yan shashashun yaran nan wlh sunfi kowa shegen sha'awa da son mata,Kawu Nafiu yace baka gani ba nonon tsohuwa ma kalla suke.
Sahil yana wani Lallashin Islaha tace ya za ayi ku basu kudi kun san baza fa su bani baaaaa.....ta karasa da kukan shagwaba,Sohail yayi dariya yace ka fara shiga Masifa Sahil,ina nan ina fama da Maheera zaka gane aure ba hutu a cikinsa.
A haka suka koma gidan Lalai,Baffa Gali har da sawa a biyo su da fura da nono har gidan Lalai,ga abinci rogo dafaffe da kuli,Lalai tana jikin bishiya inda suka barta zani ya sake sutalewa ya koma kasan ciki,Sahil dariya ta kamashi yace muna ta zuwa a sa'a,Kawu kalli suka sake sakin Dariya,Sahil ya juyo ya kalli Sohail yace yayi malafa da shi.
Lalai tana kallon su aka kawo musu rogo da fura taga Ibrahim ma ko ruwan su bai sha ba bare yaci abincin su,Sahil ne ya bude kwanon ya dauki sandar rogo fari tasss da shi ya dafu sosai,Sohail yace kawu ga takwarar mu kawu rogo wlh,Kawu yace takwara kuma waye me suna rogo anan? Sohail yace kawu ta wandonka ko basa kama irin tamu ce dukkanmu maza suna kama data wando,Kawu ya dauki kwanon rogo daya yace muje Tukur muje daga waje wannan yaran sai su kunya ta mu.
Sohail sunci iya rogon kawai,suna ta satar kallon Lalai,tace amma a nan zaku bar Islaha har lokacin aure,Sahil yace ae da jakarta ta taho ma ai,tana nan sai an daura sai na tafi da abata,Lalai tace hmmm kai ko kunya babu? Sahil yace ba gwara ni ba iya a baki ne ba zani na saki ba kirji waje, shuru ta masa sai da suka yi sallar la'asar suka tafi,a cikin gari zasu kwana sun kama hotel,Sohail ya kira Maheera yana kwance a room dinsa yace sai gobe fa muna hotel,tace tsoro nake ji fa,ba kowa kuma baka fada min ba sai yanzu dare yayi bare na kira Juwairiyya tazo mu kwana tare,Ko na tafi gidan Aunty Aisha tunda dare baiyi ba yanzu nayi sallar Isha? Da kyar ya amince ta shirya ta tafi gidan Alhaji Saminu.
Aunty Aisha tace sannu amarya yau ina da babbar bakuwa,Maheera tayi murmushi,dakin da zata kwana ta kaita tace to abinci fa? Maheera tace Alhmdllh naci kafin na fito,duk da haka sai da Aunty Aisha ta kawo mata.
Har part din Alhaji Saminu ta rakata suka gaisa sannan suka dawo dakin suna ta hira,Aunty Aisha sai labarin magungunan mata take yiwa Maheera,Maheera bata ma sansu ba,tace wai ke bakya amfani da ko wanne ne? Maheera tace uhm ina Amarya Aunty Aisha,ni duk wannan shaye shayen ba yi nake ba tukun tunda ba abinda muka yi har yau.
Ban gane ba? Maheera tace ko romance bamu taba yi ba to da alama ma bai san me ake yi ba,Aunty Aisha ta rike baki tace duk uban soyayyar nan? Sannu Maheera Allah ya miki Albarka da wata ce wlh da yanzu anji kansu,kuma wai suna karatun Qur'ani da adduoi kuwa? Aljanu basa son me nacin karatun Qur'ani suna barin jikin mutum,Maheera tace kullum sai sunyi wallahi ko da dare ko da safe,Azkhar ma baya wuce su sabo da wacce ta rike su ta dora su a hanya.
Aunty Aisha tace kina addua kema? Maheera tace sosai kullum cikinta nake Aunty.
To ya kina nuna masa yanda abin yake? Nayi nayi yaki fahimta jikinsa ma bai so na gani ba sutura,Aunty Aisha ta jinjina kai tace to fa,ikon Allah mu dage da musu addua inshaallah zasu dawo dai dai cewar Maheera.
Washe gari da wuri ya kira Maheera yace ta koma gida,haka ta koma ta gyara gidan tayi girki sabo da suna hanya.
Bayan sati biyu Maheera,Islaha da Aunty Aisha su suke shirin biki abinsu amma Sahil yace ba abinda za ayi kawai aure za a daura su taho da Amarya,yanda aka hadawa Maheera lefe haka aka hadawa Islaha.
Alhaji Umaru ne ya kira Sahil yace ya fara zuwa Office za a nuna masa aikinsa zai fara,sai murna yake,bayan kwana biyu ya fara zuwa katafaren Office dinsa,kansa wajen da Sahil yake aiki abin kallo ne.
Alhaji Umaru ne ya bawa Sahil gida katafaren gaske part biyu sama da kasa ko wanne part,yace gudunmuwar aure ce su koma ciki shi da Sohail kowa da part dinsa,amma komai iri daya ne a ciki abinda ke wannan part din shine a can,sai ka rantse ma a daya kake ba babanci har komai na kitchen da furniture.
Kayan abinci an zuba,gidan ya sha fulawoyi da interlock ga wurin parking daban na motoci,Sohail gidan da suke ciki sai dai a bawa wasu haya.