Sashe 2
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan wasu 'yan shekaru har Sohail da Sahil suka girma suna magana suna gudu ko ina har suka kai matakin zuwa makaranta,ba karamin wahala Asmau take sha da Sohail ba sabo da barna da wasa tare da lalata waje kamar aljani haka yake, maimakon yana girma aga ya canja sai abin ma ya kara rikicewa inda ya fara dalalar da yawu,kullum cikin dalalar da yawu yake, wannan yasa Mahaifinsu ya fara kaishi neman magani wajen malamai amma ba a dace ba duk sun ce ba aljani bane mutum ne,gaba daya Sahil ya fishi girma shi Sohail sai sun girma tare sosai kawai sai a wayi gari aga ya dawo wani yaro shi kadai.
Yau ma haka ce ta kasance Asmau tana ta murna Sohail ya dawo kai daya da Sahil komansu kai daya,kawai yau da sassafe sai gani tayi Sohail ya dawo yaro tafiyar ma da kyar yake yi ,a haka suka hakura aka sasu a pre nursery, Sahil yana da basira da ganewa shi kuwa Sohail kullum sai bacci yake yi har a gama karatu yana bacci,amma da ance an tashi an kada kararrawa zai tashi a bacci bazai sake bacci ba.
Malaman dama an sanar musu haka suke kyale shi, tare ake kaisu school da su Adnan a dakko su,kudin makaranta ma Adnan ake bawa a hannunsa ace ya raba musu su yaran kasancewar shine Babba,Adnan idan ya tashi sai kawai ya bawa iya yan uwansa wanda suke uwa daya uba daya ya hana twins nasu,haka zasu je school suna kallo ana ta ciye ciye na kayan yara amma banda su sai dai su zauna a class,gashi shi Sahil baya wasa wani silent ne baya kula kowa,Sohail shine sarkin wasa amma bacci baya barinsa yayi wasan indai a makaranta ne.
Watarana 'yan biyu sun kara wayo suna primary 2 Sahil ya gaji ya samu Mama Asmau ya fada mata yace Mama Yaya Adnan bai taba bamu kudin school ba muna kallo ana siyen alawa mu bamu da kudi,Asmau tayi murmushi tace to kuyi hakuri kunji ta basu hakuri,tun daga ranar take musu abinci suna tafiya da shi sannan a jakar su ta zuba musu alawoyi da biscuits,amma Adnan yana ganewa sai ya dinga kwace jakar yana kwashewa ya bawa kannensa.
Abincin ma ya kwace ya zubar ya basu flasks dinsu haka,nan ma Sahil ya gaji ya fadawa Mama Asmau.
Ranta yayi mugun baci amma ta danne ta basu hakuri ta canja sai ta dinga bude tsakiyar littafinsu tana sa musu kudi a ciki na break a haka suka tsira suke samu suna siyen wani abin.
Gaba daya Adnan da Mahaifiyarsu Ummi Nadia sun sawa sauran yaran tsanar su Sahil basa kaunar su ko kadan shi kanshi Daddyn nasu Ali Sa'ad bai damu da su Sohail ba,ganin kamar ba mutane bane,ba ruwansa da su komai sai dai su Adnan.
Ana wannan har su Sahil suka isa aike sosai ana aiken su su siyo abu a kanti,duk sanda aka aiki Sohail to baza aga dai dai ba,yau Asmau ta fito zata aiki Sahil ta iske jikinsa yayi zafi yana zazzabi tace kai Sohail zo na aike ka,yaje ya karbi kudin,tace kayan miya zaka siyo min,me nace? Yace kayan miya,tace good boy tattasai tumatir da attaruhu na dari biyu saura naga ba dai dai ba sai na zaneka yau.
Har ya fita tana nanata masa kayan miya zaka siyo ya fita yana gudu,amma yana fita bakin gate yaci birki ya fara tafiyar sangaya kamar bazai tafi ba yana wasa da kudin,sai da ya kwashe 30mnt bai je ba,yazo kusa da masu kayan miyar sai ya hango anyi ruwan sama ya kwanta a tsakiyar titi,cikin ruwan yaje ya shige yana ta wanka,kowa in yazo da mota sai dai yayi dariya ya kauce da motar ya wuce a nan ma ya shafe 1hr yana facaka da ruwa wanda duk jar kasa ne jajir da ruwan,sai da ya gaji sannan ya fito ya tafi siyo abinda aka aike shi.
Ance ya siyo kayan miya amma sai ya tafi wajen me abarba da kankana yace a bani kayan marmari,ai kuwa aka yanka masa kankana da yawa a leda aka hada masa da abarba itama a yanke aka bashi ya juya ya nufi gida,a hakan ma a hanya sai da ya nemi bishiya ya kwanta a wajen ga ledar kankana a gefe sai da ya sha sanyinsa sannan ya tashi ya koma gida,lokacin Mama har ta gaji ma tayi shinkafa da wake abinta,sai gashi ya dawo jikinsa jajir da ruwan kasa ga ledar kankana ce da abarba a ciki,bakin ciki ya kama Mama,duk hakurinta sai da ta zane Sohail da tsinken tsintsiya,ranar kuwa kwana suka yi basu yi bacci ba yana ta kuka yaki dainawa kamar an kunna inji,har Alhaji Ali sai da yazo cikin dare yace Asmau ke da yaran naki ne? tace wlh nayi danasanin dukan Sohail wannan masifa har ina kai Allah ya shirya,Murmushi yayi haka suka kwana ba bacci,Sahil ne kawai yayi bacci sabo da yaro ne.
Bayan su Sahil sun gama primary school abin mamaki ba abinda Sohail ya iya amma a jarabawa shine yake zuwa na farko komai sai ya cinye tas sai dai Sahil yazo shi na biyu duk kokarinsa,tun ana mamaki ma har andaina.
A haka suka shiga secondary school lokacin Adnan yana university a England can aka kaishi,Ibrahim ma yana shirye shiryen Tafiya can,Amal kuma Alhaji Ali yace mace ce kawai tayi karatunta a Nigeria ita da kasar waje sai da yawo.
Nadia Amaryar Ali idan taga Sohail kawai sai ta dinga sheka masa dariya haka kawai,har baya so ma ya ganta yaron ganin yana dalalar da yawu da girmansa dan secondary guda amma yana haka,gasu Iya kallonka baka taba hango muninsu sai dai Sohail rikida yake yau sai a wayi gari aga yayi dan duhu ko aga ya koma kamar bature sak ko watarana kawai aga ya dawo wani yaro sosai.
Sai da suka shiga ss1 yau suna aji malamai sun gaji da baccin Sohail gashi sai ya dinga cinye jarabawa sai suka daina daga masa kafa da anzo ana koyar da su kullum sai an masa tambaya an tashe shi komai baccin da yake amma ana masa tambaya sai yace shi ai bai dade da shiga school din ba jiya jiya aka kawo shi.
Yau ma wani malami ya gaji yana zuwa ya tashi Sohail ya mike tsaye yana murza ido,yace what is a Noun? Sohail yace ai sabon zuwa ne ni jiya aka kawo ni,malamin ya fara masifa yace tun pre nursery kuke a makarantar nan kace jiya aka kawo ka? yace ae ni wlh jiya aka kawo ni ya kwabe fuska zaiyi kuka,dole aka kyale shi.
A cikin class din kuma farin jini ne da su Sahil sabo da kyawun su ana mugun kaunar su duk makarantar, akwai wata yarinya Zayna a class din ba wanda take so ita sai Sohail a duniya,har tissue take zuwa da ita kullum ta gogewa Sohail yawun bakinsa watarana idan yana dalala,Sahil kuwa bashi da sakin fuska ma gani yake yafi uban kowa a duniya duk da yana da kyawawan dabiu haka Allah yayi shi sai ka rantse girman kaine da shi.
Ana haka a ss1 Sohail ya tsiro da wani abu duk macen da ta fara irgen dangi ko jinin Haila sai kawai aji a bakinsa ya tona asiri ya fada da karfi a class din sai kowa ya sani, budurwarsa Zayna ita ba abinda ta fara na nuna alamun balaga a tare da ita sai gashin hammata,yau tana zuwa aji kowa yayi shuru ana jiran shigowar malam tazo ta zauna a kusa da kawarta,Sohail ne yayi magana da karfi kuma da Zayna Isma'il ta fara gashin hammataaaaaa.....aji aka barke da dariya ana kallon Zayna,kunya ta lullube Zayna ta fada kasan sit ta buya,Sahil yana jinsu ko magana baiyi ba.
Malam ne ya shigo nan take Sohail ya fara baccinsa abinsa har aka tashi yana bacci,sannan Sahil ya tashe shi suka wuce driver yazo daukan su,Amal yayar su tana motar tana wani daure fuska suka shiga ciki driver ya ja suka tafi,Amal ta samu Sohail ta talla masa mari haka kawai tace shegu yan iska kunki fitowa da wuri muna ta jiran ku,Sahil kuwa ransa ya baci ba zato ya saukewa Amal mari a fuska,kumatu ta dafe tace Sahil ni ka mara? Yace an mare ki so what? Who do you think you are? ko yaushe sai dai ku zage mu ku dake mu,me muka yi muku,idan kin yiwa Sohail ya kyale ki ni bazan kyale ki ba,Sohail yana kallon su yace ku chasu arna ku chasu,shi da ake tare masa amma ko a jikinsa.
Suna Isa gida Amal ta fito ta samu saurayinta na university dinsu yazo wajenta shima dan gidan me kudi ne,suna fita wajensa ta wuce,Sohail yana zuwa zai wuce su yace saurayin Aunty Amal ai Auntyn m Jinin haila take yi yau ya wuce abinsa,Amal ranta ya baci kuma da gaske Sohail yake tace wlh idan na dawo ciki sai na lahira ya fika jin dadi,ciki suka wuce aka barta nan saurayin yana murmushi ya zaci lafiyayye ne Sohail yace ashe kina off,ya aka yi yaro ya gani,kwana nawa kike yi? Amal duk taji kunya ta share zancen.
Ai kuwa tana gama sallamar bako part din Mama Asmau ta nufa a fusace,Mama ta kalleta suna palo tare da yaranta tana biya musu karatun Qur'ani gobe suna da hadda,lafiya ke Amal ko sallama babu? Zuwa nayi naci uban yaran naki ta furta da tsiwa tana fisgo Sohail,Mama ta janye Sohail tace wlh kina taba min yaro saina kwashe ki da mari tunda baki da kunya.
Ae bani da ita ai bake kika haife su ba juya ....karaf a kunnen Alhaji Ali Daddy me shirin shigowa yana jin haka ya karaso ya cafke Amal babu bata lokaci ya hau jibgarta sai da ya mata lilis babu wanda ya kwace ta,yace idan uwarki ce zaki fada mata haka? Matata ita ba uwar ku bace? Amal tana kuka tana bada hakuri, da kyar ya hakura ya kyaleta ta fice da gudu kuwa.
Matarsa Asmau ya bawa hakuri,tayi murmushi tace ba komai fa Allah dai ya shirye su,duk Adnan ne ya koya musu.