← Book details Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 46

Sashe 28

Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sahil yayi dariya yace yawwa Maheera karki kyale shi wlh rainaki zaiyi ,to kai kana kallo me zaka ce ta harare ka fa,sai ka kyaleta? Sohail baya son fushin Maheera yace to naji ni na siya shike nan a bar zancen jira na maida ke gida,Maheera ta juya tana tafiya zata yi tafiyarta wani me mota yayi slow a kusa da ita ya sauke glass kasa yana binta a hankali yana mata magana,Sohail kamar walkiya sai ganinsa suka yi yazo wajen ya rike hannun Maheera suka ci gaba da tafiya a haka yana mata magana yace Sweet I love you,kallonsa tayi tasan jarabar kishinsa ne ya kawo shi,Me mota yana ta magana anki kulashi tafiya yayi kawai,yana tafiya Sohail yace dan iska kawai, ya tare mata taxi harda biyan kudin motar ya saka ta a mota,tana shiga ya leka ciki yace naji riga ni na siya ko ba ni bane nine shike nan magana ta wuce,murmushi tayi abinta tace bye.

Office ya wuce suka ci abinci harda wasu ma ma'aikatan,Sahil yace ka kira Daddy kace a tura a nemo auren Maheera kawai ka huta da wannan kaunar idan ka ajiyeta a gida ai ka huta,Sohail ne ya dauki wayarsa ya manta rabon da ya kira Daddy a duniya shima Daddy haka,yana kira Daddy ya daga yace wai Sohail yau ba jiran gaisuwa yace ya akayi sohail?

Sohail yace Daddy kiranka nayi ayi min aure kawai,Daddy yayi dariya ya furta to kana da budurwar ne? Sohail yace ae ina da abata kuma ta yarda su suka ce ma na tura sabo da haka aje ko kuma na kai masallaci al'ummar Annabi su daura wallahi idan baka yarda ba sai nace ni maraya ne bani da uba kawai a daura min,Daddy yayi mamaki yace to ku wanne aiki zaku iya bare ta kai ga aure Sohail waye zai yarda ya baku yarsa sannan ita budurwar amma marar galibu ce ko?

Sohail yace lallai wato mu ba mutane bane? Daddy yace ba haka bane ai gaskiya ce sabo da lalurarku,to a hakan na samu kuma ko ka yarda ko baka yarda za a daura aure,Daddy yace gaskiya ban yarda bada yawu na ba, bada sa hannuna ba a zalunci yar mutane.

Sohail yace ni da amincewa ta da yawu na harda hawayena na kara ciki, ba yawu ba harda gumin jikina da yake tsatsafowa wlh sai dai kaji an daura ni dama bance kasa yawunka ba,idan zaka zubar ka zuba a shara a aurena kar a samun yawu ya kashe wayarsa.
Daddy yace Allah ya sawwake to a haka a bawa mutum aure da ya za a rike mace a haka nima ana min magana gatsal.

Sohail kuwa yana kashe waya ya sanar da Sahil abinda Daddy yace,Sohail yace gobe weekend ai mun san Jigawa din har garin su kawu Nafiu muje mu fada musu a bamu ko mutum biyu ne nima na sha babbar riga da hula muje a nemo maka auren inda hali a daura ma daga baya a kai amarya ko ya kace? Sohail yace ai dama kaine waliyi na karka sake wani ya karbar min aure dangi marasa mutunci ba wanda yake ta tamu duk rabu da su ana zuwa naka nine wakilin ango suje su karata da furfurar su.

Washe gari kuwa Flight Sahil ya biya suka ware jigawa,daga can suka shiga mota taxi har garin danginsu,gidan Kawu Nafiu suka dira,Kawu Nafiu yana zaure ya gansu katsam,yace yau yan biyu ne a gidana?

Sohail ko zama basu yi ba yace badan Allah muka zo ba,ba zuwa gaisheka muka yi ba,dama ai kaima baku damu da mu ba cewa kuke bamu da lafiya,Sahil yace dole ce tasa muka zo.
Kawu Nafiu inda sabo sun saba jin shirmen twins,yace to ku shigo muje ciki,Sohail yace a'a barmu a nan dakin matarka kamar mashekarin Jaki, wata baban bola da ita,tana yi mana wani gani gani ita su Adnan take so baza mu je ba.

Kawu Nafiu yasan matarsa kazama ce ta gaske kuwa dakinta sai me dauriya,yace to ku zauna,zama suka yi a gefen tabarma,yace meke tafe daku? Aure Sahil ya furta kafin ya rufe baki sun bada amsa,kana da budurwar ne? Ae duk muna da ita amma tawa tayi zuciya yanzu an rasa inda take ko jiya Allah sai da nayi kuka ko Sohail bai sani ba,Kawu ina jin jiki soyayya nake tana ta bani wahala kalleni duk na tsiyace na bushe na kekashe,dan Allah kawu kuyi min addua kafin zuciyata ta buga,Sunanta Islaha,kawu Ko kai ka ganta sai ka so ta sai munyi takara da kai,amma kana gani zan kasa ka na aure ta.

Kawu dariya ya dinga yi yace Allah Sahil? Sahil an sosa masa inda yake masa kaikayi yace yarinya ce kai Kawu gangariya, great girl,ta Sohail kuwa kasan Dawisu? Kawu yace ae yace to Dawisu ce,sabo da haka ayi gaggawar aurar da Sohail tasa tana hannu yanzu.
Sohail ya fara karin bayani yace yar mutunci ce kawu ko kai sai ta baka tarbiyya,kawu zaiyi magana Sohail yace dakata kawu karka ga kana da furfura kaima fa kuskure kanayi tunda ko kai baka damu da mu ba,kana nuna mana banbanci sannan matanka biyu zaluntar daya kake yi,Abu sabo da tana da hakuri shine kake zaluntarta amma Zulai marar mutunci amma kafi tsoronta badan Allah bama yi mata abu kake yi,kaga Maheera ta baza tayi haka ba.

Kawu yasan hali Allah yasa ba a gaban matan suka fada ba,Sabo da haka tana so na ina sonta iyayenta sunce a tura dangi kuma da uba ake ado dole aga dangin ubana shi yasa ma nazo amma badan haka ba wlh baza muzo ba,to me zamu zo muyi maka,Kawu yace to mahaifinku ya yarda? Ko bai yarda ba sai kunje cewar Sahil,da kudinmu muna da aikin yi yanzu da gida da mota zamu iya,ko gidanka sai mun rike ku ba tare da mun girgiza ba,kullum kuma sai anci nama ba ma garau garau ba,amma karka sa rai bafa rike ku zamuyi ba sisi baza ku samu ba kuje Adnan su baku.

Kawu yace to ni yanzu naje mahiufinku bai yarda ba,Sohail yace kayi masa magana ai yana jin maganarka wlh kawu idan baka je sai an kwana ana zuba ma bulala yau kaji na fada maka sati za ayi kullum da dare sai an zaneka gwara ma kaje kawai ka lallaba shi kuma kuna zuwa ni bana son wannan kudin kaza kudin kaza kawai ayi balance na komai a fada min.

Kawu yace wai da gaske kudin kuka yi ne? Sahil yace zancen kake so Kawu ka tambayi dangin Maheera idan kaje sai da suka lalace da kudinmu,tun a waje suke ci,Sohail yace Kanwar Maheera yarinyar nan Juwairiyya har ta fara gurun wuya sabo da yanzu komai suna da shi ba tunanin an dora da rana ana tunanin na dare,Kawu dariya yayi yace kun kyauta,Sahil yace zamu baka kudin mota kai da Kawu Tukur kaje ka samu Daddy kwandala ba mu ce a taimaka mana ba,kawai aje a nema mana,kuma nine wakilin ango.

Kawu yace to madalla za aje gobe Inshaallah nasan yana gida,idan ma baku je ba jikinku zai fada muku cewar Sohail,ya zaro damin kudin a aljihu ya balle wrapper guda yace gashi,sabo da Allah dai sauran ka kashe kuma kayi adalci a gidanka kar ka sake da kudinmu ka siyawa Zulai tsire ka kyale Abu da tuwo,Kawu hannu na rawa ya karba yace na gode za aje inshaallah za a daura ma.

Mikewa suka yi suka ce ka kira su Abu mu gaisa a nan mu baza mu shiga ba,Ya mike yaga kudi harda sauri ya shiga ya kira su Abu suka fito tare da Zulai,Zulai tace au wai dama kune shine baza ku shiga ba?
Sahil yace wa zai shiga kuna ta kazanta a gida sai kace bola,ko ruwanku baza mu sha ba kuji gaskiya, babu ga amarya ba ga uwar gida ba me tashin wani kuna zaluntar Kawu wlh ku gyara halinku Ina yininku Sahil ya furta ko yawu bai hadiya ba kamar uban su.

Zulai tasan hali suka rufawa kansu asiri suka yi shuru suka amsa gaisuwa,Sahil ya basu 5k ko wacce yace gashi nan a samu a dinga gyara daki,suka amsa suna godiya,Sohail hannu a cikin aljihu yace in mun dawo kawo muku amarya Allah yasa muzo baku canja ba sai dai kuga wannan jeren samirar na dakin ku suna ruftowa kasa sai anyi daga daga da su,Zulai ta zaro ido dan tun suna yara ta taba dukan Sohail kwana tayi bata yi bacci ba ana tsikara mata allurai a jiki.

Mu zamu je wajen Kawu Tukur,suka musu sallama suka tafi.
Kawu yana tsakar gidansa yana cin abinci a saman tabarma suka shiga kai tsaye gidan,gidane shima kamar na Kawu Nafiu shima na bulon siminti komai a sumulmule, zama suka yi a gefensa shi gidansa da tsafta me tsafta ne.

Suka ce Kawu ina yini yace lafiya lau yan biyu kune? Ae mune cewar Sohail,meke tafe...aure mun yiwa Kawu Nafiu bayani kawai zakuyi maganar da shi,sannan kaima ga kudin mota suka bashi shima,yaga kudi ya rude,yace zanje naji me ake ciki yanzu Inshaallah,Sahil yace ba maganar kin aiwatarwa idan ba haka ba zai fada maka wlh an tanadi bulalai kawai kuje,suka zauna shima suka kora masa warning,ko ba da sanin Daddy ba kuje kawai da uwar kudinmu,Kawu yace InshaAllah za ayi ma ai haka ake so.
Ina matar taka? Yace wanka take yanzu zata fito,Sahil yace to bari mu jira ta, gashi 5k zamu bata baza mu baka ba sai ka rage mata ko ka hanata.
Matar ce ta fito tace Sohail wai kune? Sohail yace mune ke kam kin huta bakya kazanta gashi ya mika mata ta karba tace an gode to bamu gaisa ba,mun gaji tunda muka zo muke gaishe gaishe kai tashi mu tafi cewar Sohail suka barta babu gaisuwa suka yi tafiyarsu,sai lallonsu ake yi a garin ana cewa turawa ne suka zo.
Me taxi yana jiransu suka shiga suka koma airport suka bi jirgi abinsu.

Suna komawa ya kira Maheera ya fada mata yace ta fada za azo gobe wajen manyanta,Maheera tayi mamaki sai murna take yi bata taba zaton da gaske zai iya hakan ba,sabo da abin nasu sai sunyi gaba suyi baya basu da tabbas sam.
Chapter 28 · 0% Book details