Sashe 39
Mumnunar Dabia Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sohail girgizata yayi yace mene haka kwaya kika sha ne? Tana uban kuka ya zaunar da ita yace dan Allah mene haka ne? Kinki fahimtata,bawan Allah ya bani aiki ya min abin arziki sai ki zage shi kamar bakya so na,ki kwantar da hankalinki babu wacce zan so ba wacce zan kula in kika ga na kula wata sai kaddara idan Allah yayi zan kara aure,Maheera kasa ta zamo wayyo na shiga uku a hanya zaka hadu da wata garin jarabar yawon aiki shike nan kishiya zaka min,ashe har kana tunanin kara aure ban sani ba.
Sohail tagumi ya zuba wajen lallashi ya bata komai,gani tayi duk ransa ya baci ya shiga damuwa,sakkowa tayi kuma tace to kaje na hakura dan Allah karka kula wata ka dinga bani kulawa ko a waya waccen lokacin bana samun jin muryarka,Murmushi yayi yana kallonta yace to kiyi hakuri zan gyara Inshaallah ki daina wannan borin haka duk kin birkice kalli yanda kika hada gumi,duk a kaina kike wannan? To ba sonka bane ya jawo nifa zan iya mutuwa a kanka,Sohail yayi dariya yace baza ki mutu bama inshaallah sai nayi kudi munji dadi mun haifo yara kin aurar da yara suma yaran sun haihu wanda aka haifa ma sun haihu,Maheera taji dadi ta rungume shi tace wayyooo duniya ta....dariya yayi yace Baby...hannu ta yarfe tana jin kunya tace kana fada sai naji kamar na sume ,kana fasa min kai,yace to abincina, fita tayi taje ta kawo masa,Yace gobe zamuje kauyen su Islaha kafin na tafi Dubai,Yana ambatar tafiya Maheera ta zuba tagumi,kin san ina sonki ba wata wacce zan kula,tace to ai ni caring din please ni a kulani,yace to yana murmushi,abincin ma a baki take bashi,yana mamaki a duniya shi kuwa da me zai biya Maheera,bashi da kudi ga halin da yake ciki amma take masa mahaukacin so haka.
A ranar Sahil waya kawai yayiwa su Kawu Nafiu yace suzo za a kai kudin aurensa,Ba ko musu suka ce muna tafe gobe,Sahil Address ya tura musu yace mu hadu a kauyen zan tura muku kudin mota kar ku bata mana lokaci sannan idan kunne yaji jiki ya tsira,su Kawu Nafiu da sauri suka ce ba damuwa.
Daddy ya kira,ya sanar masa yace to fa muma kuma Allah yayi zamu daure mu ja daya ciki,Daddy yace ban gane ba ku ja daya wanne lokaci kuma? Yace aure nima zanyi,Daddy ya ja tsaki yace a gidan ubanwa zaka saka ta a wannen gidan karami na Sohail? Arna ne ku daki uku da palo kawai, Sahil yace sanda kayi auren fari naga a gidan haya ka zauna daki ashirin da uku a gida daya,kowa daki daya daya,Mama Asmau babu layin toilet da bata sha ba.
Daddy yace kaje kayi ba ruwana,Sahil ya furta dama kawai fada maka nayi ba wai wani abu ba,to kaje Allah ya taimaka,Sahil yace Ameen matar sunanta Islaha yar duma duma ce ma,ko kai ka ganta sai ka karar da dukiyarka a kanta,Daddy yace ni ina ni ina yarinya ma da har zan karar da dukiyata a kanta,idan ma kana so baza ka samu ba dai cewar Sahil,Kwafa Daddy ya ja,yace to me kake jira ka kashe wayar mana,da kudina to a ciki cewar Sahil,"Daddy"yace na'am da masifa ya amsa,Sahil yace akwai wata Hajiya Kulu me tuwo tuwo a tasha ta dace da kai wlh da zaka aure ta da ka huce takaici,Daddy wayarsa ya kashe yana masifa me tuwo tuwo lallai yaran nan sun rainani kamata da arzikina wanda a yanzu zan iya auren irin matan su hudu ma yara yan mata,amma yazo ya fada min wata Kulu me tuwo tuwo da kuwa nayi asara.
Washe gari Sohail da Sahil suka tafi Taraba a motar haya,Islaha tana gefen Sahil minti kadan ya kalleta ko motsi tayi sai yace mene ne? Me kike so? Itama Islaha duk ta haukace irin Maheera soyayya ta gigitata,ga Maheera sai ziga Islaha take akan ta auri Sahil tayi sauri.
a can suka samu su Kawu Nafiu,an gansu a motar haya ba wanda ya kula su a gindin bishiya suka zauna,suma su Twins ba a motar gida suka je ba ga Islaha anje da ita.
Gidan Lalai ta musu jagora suka tsaya a waje Islaha ta shiga da Sallama,a tsakar gida ta iske Lalai kwance saman tabarma hannayenta biyu a ruruce amma sunyi sauki ta shanya su iska na fifita su.
Tana ganin Islaha tsoron Islaha ya kama Lalai,tace Islaha...ta mike da kyar tace sannu da zuwa Islaha,Islaha tayi mamaki tace me ya same ki Lalai? tace mutanen boye ne labari sai an zauna,Islaha tace da baki nake fa.
Lalai tana daga zaune da daura kirjinta zanin ma ya warware ya dawo cikinta nono rabebe ana gani kamar takalmi yaraf a kwance,Islaha ta manta da nonon Lalai a waje ta kira baki tace ku shigo,Lalai ba hannun da zata gyara zaninta,Sahil ne ya shugo.
Kallo daya yayiwa Lalai sai ya koma bayan kawu Nafiu yana ta kyalkyala dariya,Sohail bai sani ba ya wuce gaba shima yayi arba da nonon Lalai,baya ya dawo bayan Kawu Tukur yana ta dariya,yace Allah ya so ni na Matata chakare chakare ne,Sahil handkerchief yasa a bakinsa ya cusa a ciki wai dan kar sauti ya fito.
Sohail yace mudai ba ruwanmu su Kawu Nafiu nake ji dai dai suce kar su kyasa,Kawu Nafiu sai yanzu ya gane abinda suke yi,da sauri yace Allah ya kiyaye ko ni na wuce ajin wannan me zan kalata a jikinta,bare kuma ni cewar Kawu Tukur.
Lalai ko a jikinta dake mutanen kauye ne,suka zauna a sabuwar tabarma,Sohail da Sahil sun kasa boye dariyarsu sai dariya suke suna kallon juna,Lalai ce tace Islaha miko musu ruwa mana,Sahil ya kalli Kawu Nafiu ya toshe bakinsa da hannu yace kaiiii....yana dariya,a sace kawu Nafiu ya tsawatar musu ya dinga musu signa,Sohail ne ya gaji da gani yace Islaha mu bamu saba ba azo a suturta nonon Iya.
kai ubanka kawu Nafiu ya zungure shi yana zaginsa kasa kasa.
Sahil yace Iya Lalai taci daka rannan,ai nine nan....ya karasa da dariya...dama nace sai ta kwana tana daka,Lalai ido ta zaro,Sohail yace yes yin mune,shuru tayi dan bata san kan abin ba.
Kawu Nafiu ne ya katse zancen suka gaisa da Lalai Islaha tana daura mata zani Sahil yace Allah wannan kadai ya isheka comedy...Sohail yace sai ka kwana kana kallon abinka kai ta dariya wallahi, wai Nonon Lalai suke nufi,Islaha ita kanta dariya taci karfinta ga dariyar nonon Lalai ga na su Sohail.
Abdulrazaqu ne ya shigo yace wa nake gani kamar Islaha yau sai na tattaka ki a gidan nan,shine kika mana asarar kudi sabo da ke yar iska ce yanzu kin lallabo kin dawo a ciyar dake,shegiya tambadaddiya ke kam kinyi asara,yar tsiya a haka zaki kare,ace yaro me kudi kamar Ibrahim,to ki sani har yau muna kan bakanmu Ibrahim zaki aura me ruwan nairori,shi muke so shine zabin mu.
Lalai kuwa sanda take daka ita tasan me ta ji me ta gani,sai faman cewa Abdulrazaqu take kai kayi shuru dan ubanka amma sai faman masifa yake ko bakin ma bai kula da su ba,tun a waje yaji mutane na labari Islaha tazo shine ya taho da masifarsa.
Free page 1&2 400 ne
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
46-50
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM
Page naki ne
MARYAM T BALIYA
MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA.
Sohail zaiyi magana Kawu Nafiu ya hanashi da sauri yace fadan yan uwa ne ba ruwanku da shi,neman aure muka zo ku bari dan Allah muyi lafiya,shuru suka yi.
Lalai ce tayi magana tace marabanku lale marhabin sannunku da zuwa,Islaha baki muka yi ne daga Amurka? ko kuwa daga ina an bar ni a duhu?
Su Kawu Nafiu ne suka gaishe ta sannan ya mata bayanin abinda ke tafe da su,yace kuma Alhmdllh yaro da yarinya munga sun daidaita kansu shine muka zo a hada mu da iyayenta maza domin shi neman aure da maza ake yinsa ba mata ba,Sohail yace kwarai kuwa yafi inganci ma,Islaha dai ta shige daki taki fitowa wai ita kunya,amma ta rabe a jikin bango tana jin me ake cewa.
Abdulrazaqu yana tsaye kerere da rigarsa ta gona dukun dukun ya furta mu baza mu bawa kowa ba sai Ibrahim mun rigada mun masa Alkawari shi zamu bawa,Islaha ta Ibrahim ce,Kawu Nafiu yace to ai mun ji labarin zuwan Ibrahim, abinda yayi Ibrahim shi yayi Sahil gasu kannensa ne uban su daya,kuma dama Islaha budurwar Sahil ce tun farko Ibrahim neman fada ne ya kawo shi.
Abdulrazaqu ya dora hannaye a kai yace yanzu na tabbatar 'yan uba masifa ne shi yasa na godewa Allah da Lalai kadai Mahaifi na ya aura har ya koma ga Allah kuma ni kadai ta haifa,Sohail ne yace kai lallai living thing ne babba yanzu kai kadai ta haifa dama duk kaine ka dawo mata da nono haka sai kace inji ne a bakin ka sai kace ta haifi yara ashirin,Kawu ne ya bigi Sohail,Sahil yace dama tun tana budurwa bata yi farin jini ba babanka ne kadai yaje zance shima sai da kyar abokai suna ziga shi lokacin tana tallan Alkaki.
Lalai tace wlh tunda nake ba kowa yasan zamanin da nayi tallan alkaki ba amma kai aljani ne wlh wannan ba mutane bane ku tashi ku tafi wajen Iyayenta maza,bazan iya ba dama tunda naga kyawunku haka naji a jikina ba mutane bane,Kawu Nafiu ne ya wayance yace tsokana suka yi abin ne yazo a daidai ba haka suke nufi ba, Lalai ta dan saurara a tsorace tace ina jinku,Kawu Nafiu yace kawai a raka mu wajen mazan.
Abdulrazaqu yace bazan je ba ita da take son auren ta taje ta kaiku ya juya tare da ficewa.