← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 70

Sashe 9

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau hakanan ta tashi da annashuwarta shiyasa batayi lattiba kamar yanda tasaba ta Isa blue fox din tana zuwa ta sauya cikin kayan aikinta suka hau aiki,
Customers biyu yau ta tsamewa kudi a jaka Kuma dukkansu Babu Wanda ya lura bare yagane harsuka tafi ta qirge kudinta tsaf kusan dubu goma sha biyu ta maida jaka tana cewa'
Saura dubu talatin da daya su cika kudin jarabawar usi ya Allah kabani ikon hadasu kan lokac......

Bata qarasaba wasu manyan hamshaqan Mata guda biyu suka shigo gurin tareda wata kyakkyawar budurwa tana biye dasu,
Kallo 'daya tayi musu tasaki baki tana cewa' Masha Allah da ganin wainnan hajiyoyin da hutu ya bayyana ataredasu.

Cikin gaggawa madam bell ta rude jiki na rawa take musu sannu da zuwa kamar zata kwanta su zauna akanta tsabar rawar jikin tarbonsu.

Cikin girmamawa aka wuce can qurya dasu spa room dinsu madam bell nacewa"
Welcome ma,
Welcome ma I've arranged komai da Kika bugo zakuzo kuyi in no time za'a kammala.

Suna shiga suka zauna tareda ajiye manyan jakunkunansu
Haj Maryam dake waya har lokacin ta ajiye Tata akan kujerar bakin qofar shigowa tareda tsayawa jikin window tana sake bude muryarta gurin yiwa 'danta Salman fadan karya dawo yanxu sbd wani banzan nadin sarautar MAHMOUD dinda basuma wani San juna ba sbd ita din qanwace ga Modibbo ta Dade a gida sakamakon mijinta daya rasu shekaru goma kenan yabarta da manyan 'yaya biyu rak da nuratu da Salman din.

Umme kawai aka farayiwa gyaran sbd sanin idan haj Maryam tafara waya saita share awanni tanayi itakuma nuratu dama gyaran Kai ne zaayi Mata so tanacan guri daban.

Cikin nutsuwa anny keyiwa umme gyaran itakuma tana dudduba wayarta ahaka harsuka gama qafa daya
Amah dake tsaye tana jiran haj Maryam tagama ita zatayiwa taja boyayyan tsoki yafi so ashirin harta gaji da tsayuwar ta Dan zauna gefe kan kujerar aikinsu kamar ance ta kalla saikuwa idanuwanta suka sauka kan jakar dake Kai wasu sabbin bunch na dubu dubu na leqota batasan sanda ta saki siriyar dariyar farin cikiba a boye tana sauke numfashin farin ciki tace"
Sa'a sa'a wlh saina fanshe zaman jirana danayi akan jakarki.

Fakaitan haj Maryam din tayi taga har lokacin waya takeyi tabada baya ta dawo da kallonta kan umme datayi nisa a taba wayarta ta 'dan matsa tana
zirara hannunta ahankali sai akan kudin ta janyosu batareda tsoroba ta cusa cikin robar hannunta ta kayan aiki saita miqe tareda ficewa.

Wani tsalle ta daka tareda kallon kudin tana washe baki tace'
Hummm.

Cikin Jakarta tasaka kudin tareda kaiwa ta boye cikin kayanta kafin tadawo sparoom din tana wani basarwa annashuwa na fita a fuskarta Takoma tana zaman jiranta tana cewa'"
Ko darema kikai kina waya zanjiraki Dan nagama cire kudin zaman jirana.

Anny nagama yiwa umme ta miqe ta ficewarta.

Sai bayan fitar anny tagama wayar tazo ta zauna amah din tafara yimata har aka gama tas ta ficewarta.

Tsabar zumudin kudin kasa Bari tayi atashi taje gurin madam nema alfarmar tafiya gida da wuri sbd uxuri ana Bata dama ko kayanta Bata sauyaba ta tattaro su ta fito zuwa gida tana tafe tana lissafi cikin ranta fal farin ciki.

Wayarta ta fiddo tareda lalubo numbern usi taji switch off taja tsaki tana cewa'"
Dama nasani tun ahekaranjiya na lura ka Saida wayarka sbd kudin daka bawa iyatu na garinta da jarin ya karye
Karka damu kaida kawu duk saimun siya waya yau yaqarasa fada tana sakin murmushi itakadai a hanya.

Ganin napep yaqi samuwa yasa tadan Fara takawa tana tafiya a gefen hanya
Tayi nisa sosai wata qatuwar baqar mota Tasha gabanta tayi saurin matsawa tana qoqarin zubawa ko waye zagi.

Parking motar tayi aikuwa itama cikin tsananin masifa ta matso taga uban waye yake neman kassarata adaidai gabar datake ganin tayi kudi.

Cak ta tsaya lokacinda Glass din motar ya zuge tayi Ido hudu da matarda tabaro blue fox dinsu.

'dan hadiye fushinta tayi tareda 'dauke Kai zata tafiyarta tana damqe jakar kudinta.

Kudin dakika dauka nabiyoki karba ko"""""kamar daga sama taji saikar zancen ta tsaya cak tareda rintse ido tana damqe Jakarta tace'"aiko wlh banyarda Naga samu Naga Rashi bazan bayarda kudin nanba kome zaayi.

'dan qaqalo sakin fuska tayi tareda juyowa tace'"
Hajiya Dani kike???

Murmushin takaici umme tayi tareda cewa shigo muyi mgn idan bakyason Tarawa kanki abin kunya anan gurin.

Murmushi tayi tareda Dan matsowa jikin motar tayi qasa da murya tace"
Haj aini bana gudun abin kunya sbd acikinsa nake
Banda kowa Dan haka Babu Wanda zanjawa abin kunyar yi mganarki hajiya.

Kallonta umme tayi cikin tsananin qyama da mamakinta amatsayin mace ta yamutsa fuska tace"
Kudin dakika dauka nakeson kidawo dasu kokuma na miqaki hannun Yan sanda su rufeki har sai anmanta da sunanki.

Dariya amatu tasaki tareda dafe bakinta tace'
Haj canza dai Amma amatu Bata tsoron 'yansanda ataqaice Babu station dinda basusan niba.

Qarara mamakin umme ya fito tana sake kallon amatu din qyamarta na sake shigarta Dan tuni taji yarinyar ta sake fita ranta Sam Bata ko qaunar magana da ita Amma tun yanda ta lura tana kallon jakar
haj Maryam cikin kwadaituwa da yanda ta dauki kudin cikin tsananin kwadaituwa dasu da yanda take kallon kudin ta fahimci soyayyarta da kudi ba 'yar kadan bace shiyasa taqi tonata Kuma ta mayarwa da haj Maryam kudin ta biyota sbd ganin qila itadin zata iya aikinsu.
#mamuh#
_____________________
KUNA BU
ATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES
IN BOOKS
IN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon hazi
an marubanku
an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da sa
o ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai bu
atar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntu
ar wa
an nan Numbers 0903
5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks
in kana bu
ata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi.

Idan kuma wasu adadin pages kake bu
ata koda
aya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sau
in gaske
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sau
______________________
#MIN QALB
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/13, 5:49 PM] Zafafa: *_MIN QALB 8_*
_mamuhgee_
Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa hannunwanta dasuka Saba dauka da zuwa stations takeyi mamakinta na qara girmama musamman shekarun amatun datake ganin bazasu haura ashirin da uku ba,
Gyara zamanta tayi cikin motar tana 6oye mamakinta tareda 'dan kallon amatun datake qara damqe jakarta sbd kudin dake ciki alamar bakin Rai take da kudin ta saki wani guntun murmushi tana nazari wani abu kafin ta kalli fuskar amatun tana cewa'"
Ta yaro Mai takeyi Bata qarko
Idan har kinawa kudi wannan son ta tabbas zan baki kudinda kaf zuriarku bazaku iya qirgasuba,
Sake kallon amtun tayi tareda sakar Mata murmushi kafin yace"
Amatu idan da zaki bude idonki ki kalli Abinda nake qoqarin yi zaki fahimci Abinda nafada bashi nake nufiba sbd danaso kamaki da yanzu kin jima da sauya kammani a cell and banyi Miki Kama da wadda kike tunanin zaki fadawa bakya tsoron yansanda,
Amatu akwai rayuwa me kyau danake Miki fatan samu Wanda zaki manta da yanda ake sata,
Zaki samu rayuwarda ko a mafarki bakiyaba tunaninta,
Zaki samu duk wani Jin Dadi da kudinda saikin rabawa 6arayi 'yan uwanki ta yanda Suma bazasu qara tuna sunan sataba.

Wata siririyar dariya amatu tayi tareda sakin jakarta datayiwa riqon Gam Gam tana gyarawa jakar zama a kafadarta tareda gyara tsayuwarta tace"
Hajiya mama Allah ne kawai zai iya cike gurbin kwadayin samu kudi danake dashi Dan gurbin me mugun zurfi ne cikesa ba qaramin aiki bane
Kiyi hkr da wannan kudin Dana dauka tunda dai kinsan ba komai bane acikin arzikin da kike dashi to Allah ki barmin kawai sbd Nima dai bazan iya bayarwar ba.

Bude jaka umme tayi tareda ciro wasu bunches din guda biyu ta miqa Mata tana cewa'"
Ungo ki hada Dana hannunki ki hau abin hawa gobe zandawo spa dinku muyi mgn.

Tana gama fadar haka tace'"
Hafiz muje.

Jan motar yayi suka bar gurin da speed me qarfi suka barta da baki a bude tana kallon kudin hannuwanta da qafafunta na rawa sbd wannan ne karo na farko data taba ganin kudi a fili haka irin Wainnan Kuma ma a hannunta da sauri ta turasu jaka tareda fadawa ckin napep dinda ya tsaya gabanta Yana tambayar Ina zuwa malama?

Tunda tashiga napep din take share zufan dayaqi tsaya Mata gaba 'daya kanta ya shiga lissafi Bata taba tunanin kudi irin wannan zasu rudataba duk tsananin samu kudinta dubu talatin ne zuwa qasa albashinta ma duka duka dubu goma sha uku be duk wata saina mutane idan ta sanfo Amma yau itace keda kudi dubu 'dari uku a hannunta amatsayin nata bama na sata ba""wayyo Allah" tafada tana dafe gashi.

Kasa wucewa gida tayi direct ta kalla me a daidaita din tace yabiya da ita ta bakin Luna inda tasan usi na can.

A daidaita din na tsayawa bakin Luna ko fitowa batayiba ta hango bakin gurin cike an taru Kuma daga gani rigima akeyi babba sbd har mitar 'yan sanda ta iso gurin.

Da sauri ta fito tana cewa me napep din" Ina zuwa
Ta qarasa gurin da sauri sbd hango usi da ake kokuwar sakawa cikin motar Yan sanda Yana cijewa su Kuma sai dukanda sukeyi.

Tana isa ta qwacesa da qarfi tareda shiga gabansa tana karesa tace'"
Lafiya meyake faruwa??

Cikin sa'a Allah yasa insfector falalu ne a shugaban tafiyar Wanda tunda dadewa yayi sonta Amma ganin batamasan meye rayuwa ba batada mahimmanci agareta yasa ya qayaleta Dan dole Amma Allah yagani yaso aurenta.

Kallonta yayi Yana cewa'"
Amatu kibari idan munje can office zamuyi magana saiki San Abinda yayi.
Chapter 9 · 0% Book details