← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 70

Sashe 8

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin kamar MAHMOUD din yayi musu nisa sosai Wanda yanzu suke alfahari dashi amatsayin Dan zabeera sbd mutunci da girma tareda qimarda yake sake kawowa zuriar sai suka yanke shawarar nemar Masa auren 'yar qanin Modibbon Wanda yake kan kujerar zabeera ayanxu ZARAH,
Zarah ta auri MD ZABEERA cikeda alfahari da auren sbd samun miji yanxu kamarsa dibbin nasara ce arayuwa,
Tana tsananin qaunarsa saidai sanin yafi karfinta yasa ko a mafarki Bata tunanin aurensa saigashi Allah yayi shidin mijintane Wanda taqara haukacewa a tsananin qaunarsa,
Baya musu arayuwarsa sbd baisaba doguwar mgn ba ko ta fannin business dinsa ko deals dinsa Abune nayi ko bari bayasan dogon Bata lokaci shiyasa baibi wani dogon sawa Kai ciwon kaiba ya amince musamman da akayi saa zarah mace ce me tsananin nutsuwa da hkr ga biyayya da fahimtar Abu Sam Bata cusa kanta gurinsa tunda akayi auren
Rayuwa suke ta mutunta juna da kiyaye gudun shiga haqqi.,
Shi mutum ne marason damuwa da hayaniyar mutane akusa dashi shiyasa idan har yananan ko volume din tv bata sawa sosai sbd karta damesa,
Bata taba yin wani abu Dan damuwarsa ko sakasa ciwon Kai ba shiyasa yake respecting nutsuwarta musamman dayake dama baya shaawar mace arayuwarsa saidai sbd girman Modibbo da Andi dakuma qimarta yasa yake qoqarin bawa auren nasa haqqin.

Yau amatu Bata fita aikiba Saida tagama hutawarta a gida kafin tayi Shirin aikin ta fito tareda usi Dan dama kullum tare suke zuwa aikin
Suna Isa tun a harabar gurin suka fahimci da masu kudi a gurin saidai rashin saar dasukayi gefen VIP saloon dinsu sukaga motocin Wanda sunsan Babu rabonsu yau acikin aljihun masu wainnan motacin masu kama da tarwadar ruwa sbd sheqi.

Direct gefen restaurant suka nufa usi na cewa"
Juyawa zanyi amah zanje gurin insfector Garba naji uban me zaimin dayake nema na tun Daren jiya.

Tana shigewa tace' idanma ni yakeson katayasa lallashi kafada Masa duk yabari nayi Ido biyu dashi Aina sace Masa shegen cikinsa me kama da tayar motar Mai.

Juyawa yayi Yana cewa' nizan Fara nuna Masa kalar rashin mutuncina kawuma nacan Yana jiran ganinsa.
#mamuh#
______________________
KUNA BU
ATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES
IN BOOKS
IN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon hazi
an marubanku
an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da sa
o ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai bu
atar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntu
ar wa
an nan Numbers 0903
5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks
in kana bu
ata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sau
i.

Idan kuma wasu adadin pages kake bu
ata koda
aya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sau
in gaske
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sau
______________________
#MIN QALB
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/11, 6:12 PM] Zafafa: *_MIN QALB 7_*
_mamuhgee_
Kai tsaye change room dinsu ta nufa ta sauya kayanta zuwa na aiki ta fito tana gyara zaman qaramin Rolling dinta a wuya tana Dan yamutsa fuska tace,
Ni wannan aikinma harya Fara isata sbd wannan kayan aikin kullum mutum atakure bazan iyaba aje aikin zanyi na huta kafin daga baya zanda usi yasamomin wani yanzu dai kafin na ajiye zansamu kudinda zasu riqemu kafin asamo wani.

Tana isa reception dinsu manager
dinsu na isowa
Shigowarsa kenan Yana waya yayi Mata hannu cewar ta tsaya yagama wayar
Wani harara tabisa dashi tana dauke Kai sbd manager dinnan nasu tafara gano take takensa akanta bazai shiga hankalinsaba sai ranar data sanfe duk wani arzikin dake aljihonsa,
'daga Masa qafa takeyi sbd kudaden datake sanfewa na restaurant Dan kullum saita diba son ranta take tafiya gida Bari tayi yaringa ji da 'daya Amma yakasa Kama kansa,
Kullum sai ayi rikici gun lissafin yanda kudi ke ba'ta Amma ankasa ganewa har so biyu ana sauya cashiers din aje kudin Amma 'yanda kasan 6era ne me satar ko clue bata bari bare amayi zargin mutum ne me satar.

Kallon qeyar kansa tayi tana sakin murmushin qeta tace"
Manager tashi aiki zakayi kwanan Nan...

Maganarsa ta kwasheta ta 'dago tana kallonsa tana 6oye murmushin gayyar datakeyi tace"
Barka da zuwa manager,
Kazo lafiya?

Washe haqora yayi Yana gyara zaman medical glass dinsa cikin son nuna shi wani ne yace"
Yawwa lfy klau amah
Dama sbd matsalolin damuke fuskanta na 6acewar kudi a bangaren restaurant namu yasa na yanke shawarar maidaki gefen saloon sbd zamu dauki mummanan mataki akan maakatan restaurant din banason asaki acikin Abinda baima shafekiba,
Dukkaninsu maganinsu zamuyi saisun fitar Mana da 6arawon cikinsu.

Kallon Wawa taqare Masa kafin tayi fuskar marayu taredayin qasa da Kai cikin nuna maraicinta tace"
Nagode da hakan Dan ni ko yanda alamarin kudi dake gudana agurin banma saniba,
Banmasan meke faruwa a gunba da azo adauki alhakina abatamin suna kawuna ransa ya baci ciwonsama na hawan jini zai iya tashi idan yaji hadda ni acikin wainda zaa tuhuma da sata Kai Allah dai ya tsareni ya rabamu kalmar sunan satama batada Dadi.

Sake washe baki yayi ganin kamar yayi Abinda ya burgeta taji Dadi ya sake gyara tsayuwa Yana katse Kiran dake shigowa wayarsa yace"
Ai dama shiyasa naga yakamata a sauyaki saga gun sbd kada sunanki ya baci gashima Kinga Ashe kawunmu zai iya samun damuwa.

Tana qaqalo murmushi tace'
Eh dama gashi Muna fama dashi yau ciwo gobe lafiya ko tashi zaune baya iyayi" yaqarasa fada tana soke kanta kasa.

Subhanallah Ashe dai alamarin sosai ne to Allah ya sawwaqa inshallah yau ko gobe idan nabar office zanje nadubasa.

Zakasan me ake nufi da asalin sunan sata idan kaje duba kawo ka laluba kaji usi ya sanfeka tass""tafada qasa qasa tana Masa kallon sakarai....

Me kikace????

Eh cewa nayi akaini inda aka sauyamin din manager.

Yawwa muje'' yafada yanayin gaba tana binsa abaya tana sake 6ata fuska sbd Sam ita Bata wani son wani canje canje ita dake Shirin barin aikin ake Mata wani yaje Jaye Amma dai bangaren saloon din idan taga yamata zata zata Dan jima Amma yanzu babbar damuwar shine kafin ta 'dan gama gane Nan bangaren harta Fara samun damar sanfesu za'a dauki lokaci qila gashi komai nasu yayi qasa na abinci iyami kasuwancinta na Saida garin 'dan wake baya tafiya da albashinta suka dogara yanzu sai Abinda tasamo ko usi yasamo.....

Katsewa tunaninta yayi daidai lokacinda suka iso bakin qofar saloon din dake cikin blue fox din sbd wasu manyan hamshaqan Mata data hango ta cikin glass,
Sake 'daga wuyanta tayi tana 'dan leqawa tasake hango wasu 'yan Mata daga dayan gefen take tasaki ranta tana cewa"
Yauma ranar sa'atace kenan
Nakusa zamowa shiyasa Allah yasa aka daukeni daga Inda mutane basa ajiye jakarsu Amma anan dole mutum ya ajiye jakarsa tunda aiki zaa Masa,
Numfashi ta aje tana cewa"
Inshallah usi nakusa samun kudin karatunka Dan Banda buri yanzu dayafi kayi karatu sbd Kaine namiji qarfinmu zaifi qarewa akan naka kawuma ga manyanci na rufarmasa.

Tana cikin tunanin taji muryar manager na cewa"
Shikenan amah kuje ga shugabarku Nan zata baki Abinda zaki ringa yi
Sai akula please amah.

Gyada Masa Kai kawai tayi sbd tuni hankalinta yayi ciki a matse takeda tashiga ai madam bell na cewa tazo sushiga tayi gaba
Tana tura qofar glass din wani sanyin qamsh ya dameta ta lumshe ido tana qurewa gurin kallo daga sama taji madam bell na cewa"
Oya amah kije gurin anny gatacan tana sawa wata Rolex ki riqe Mata tana sawa idan kungama saikizo kiyi kallon yanda zan gyarawa waincan baqin namu qafafu.

To tace tana ajiye Jakarta a inda aka nuna Mata cikin haushi ta nufi anny din ta karbi robar Rolex din a karkace ta riqe tareda dauke Kai sbd yanda daga zuwanta ko Dan mutuntawar Nan Babu adai nuna maka Kai ba kowa bane face 'dan aiki.

Yini tayi aiki ranar sbd kowane aiki madam bell sata takeyi ayi da ita sbd ta iya gabaki daya Bata zaunaba tundatashiga gashi aranar taga asalin
ire iren Mata masu kudi wainda suke cikin kudi,
Matane sai masu arziki da wainda suka fito gidan arzikin sune kawai ke shige da fice agurin wasu na fita wasu na shiga shiyasa gabaki daya taji yanxu zatayi kudi wato ma a restaurant bataga komaiba sbd can iyajacinsu Kai abinci su dawo.

Sai yamma sosai Takoma gida a matuqar gajiye dan haka tana dawowa ta tarar ana fada hadda dambe da anty salamatu da maman basiru gasu maman junior a gefe anata qara zugawa kawu dai na zaune a shimfidarsa yaqi ko kallonsu bare ya matsa jira yake wani shegen ya fado Masa ya dauko musu motar yansanda ayi me kankat.

Kota kansu batabi ba ta wucewarta daki tana cewa'"
Allah yasa ayiwa maman basiru dukan sakwara muga qarshen qaryarta.

Washe gari ma da wuri sukaje aikin bayan ta biya cafe din kusada layinsu tabada cikon kudin scratch card din usi dazai zana waec Wanda shi baima sani ba.

Koda ta Isa gun aikin yauma Babu sauqi aiki tayi sosai ha lokacin tashi,
Kwanaki kadan tayi a saloon din ta iya aikinsu ba laifi Dan dama daurewa takeyi tana aiki sbd samun sanin Yaya kan gurin yake kafin tafaracin ubansu da halinta musamman madam bell databi ta addebeta da aiki sai janta ajiki takeyi tana yabonta ita kuwa sai sake musu kwantan 6auna takeyi Amma dai abokan aikinta sunfara sanin halinta sbd ba sauqi a tsakaninsu qaniyarsu takeci har mamakinta sukeyi yanda madam ke yabonta sbd batasan waye amah din ba.
Chapter 8 · 0% Book details