← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 70

Sashe 24

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinta Salman din yayi tareda kallon Amatu da mamakinta yagama kashesa yana cewa"
Lallai Nima zanso ganin Wanda take dashi daya Bata wannan qwarin gwiwar me ban mamaki da burgewa
Ina buqatar saninsa Dan basa jinjinawa ta musamman.

Kallonsa Amatu tayi ganin Yana qarawa wutar masifar fetur tace"
Amatu itace tsayayyiyar kanta Bata buqatar tsayawar wani gurin nunawa kowa matsayinsa,
Ki zauna ki nanatawa tosashiyar qwaqwalwarki ni Amatu nariga Masha gabanki
Idan har akwai Amatu har abada Dr khalil zabeera bazai taba kallonki ba
Kai da kake Dan uwanta saika taimaka Mata gurin fahimtar hakan
Amatu ba tsarar yinki bace.

Tana Gama fadar hakan ta wuce Yana shafa cikinta Dan qara qular da Nuratun
Cikin mugun baqin ciki da takaici nuratu ta juya a zuciye tabar gurin tana fidda huci kamar zuciyarta zata tarwatse idanuwanta har wani cikowa da hawayen baqin ciki suke
Dama can Kuma halinta ce saurin fusata.

The great ORTHOPEDIC Dr Salman zabeera kuwa gabaki daya Amatu tagama basa mamaki lokaci daya da burgesa sbd sanin darajar kanta datayi takuma nuna batareda tsoro ba,
Koma wacece Amatu shi tagama burgesa shiyasa yakasa dauke Ido daga kanta harta bace.
##Mamuh#
ZAFAFA BIYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899[3/28, 11:48 AM] Zafafa: *_MQ 19_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata koma
a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https:/
/Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*
**********
Doguwar tafiya tayi har zuwa sashensu tana Jin tsananin azabar radadin da hannunta keyi ta daure ta iso tana rintse ido cikin uwar azaba ga zufa sai karyo Mata yake shiyasa tana isowa tun a Palo ta zube Kan kujera tana kallon hannun da harya Fara kumbura
Sanin anty zarah na dayar palon tareda baquwarta yasa ta sulala tayi dakinta ta kwanta Dan kada ta dagawa anty zarah din hankali saidai ita kadai tasan uwar azabar datake ciki shiyasama takira usi
Yana daga wayar sai alokacin taji hawaye sun ciko idanuwanta sai Kuma takasa mgn ta kashe wayar ta ajiye tana gani yanata Kira takasa dauka sbd karta daga Masa hankali kawai.

Duk yanda take tunanin zata iya riqe ciwon takasa sbd sosaine tasamu gocewar qashin hannun sai kumbura yakeyi har takai tafara kasa motsasa sbd tsamin daya dauko.

Har dare tana dakin Taki fitowa sai bayan magrib baquwar anty zarah ta tafi
Itama anty zaran dakinta ta nufa sai datayi sallar magrib da ishai tukuna ta fito palon saidai rashin ganin amatu a palon yasa ko zama batayiba ta nufi dakinta.

A kwance ta taddata Idanuwanta a rufe tanajin anty zarah din ta tashi zaune tana rintse ido alamar ciwo
Nan anty zarah din ta qarasa bakin gadon da sauri tana dafa Hannun me azabar Bata saniba
Wani irin zabura Amatu tayi cikin tsananin radadin dataji tana tana cewa''
Anty hannuna ya karye.

Da sauri anty zarah ta kalli hannun batasan lokacin data zaro ido ba ganin ya kumbure sul a rude tace"
Amatu meye wannan nake gani?

Garin Yaya hakan yasame ki??

Sai alokacin hawayenta suka gangaro tace"
Anty wannan me son Dr din ce ta tureni na Fadi a hannun.....

Mene??""anty zarah tafada da qarfi tana maida kallonta Kan cikin Amatun da har lokacin Bata cire cikonba tace"
Ta ture ki batada hankaline bataga Abinda ke jikinki bane ko so hauka ne Bari nakira Dr yanxun Nan yazo
Ita Kuma Nuratun I will deal with her later wannan ai ganganci ne.

Dr najin Abinda yafaru hankalinsa ya tashi gashi wani mahimmin meeting sukeyi sbd gobe shida wasu manyan likitocin asibitinsu zasuyi tafiya zuwa china gurin wani program na sati biyu.

Tunda zarah takirasa tafada Masa hankalinsa ya rabu biyu
Meeting din kawai suke Amma Rabin hankalinsa na gidan sanyi daya dayakeji aransa shine SALMAN yananan yadawo kwararren likitan qashi ne yasan basa buqatar zuwa koina.

Sai guraren 8:40 suka fito gashi Kuma yanada wani Wanda yayiwa alqawarin ganinsa idan yafito hakanan yakoma office dinsa
Koda ya Isa office din mutumin na kiransa Nan suka Fara mgnar dazasuyi ahankali yanayi Yana shafa qirjinsa da numfashinsa ke Dan sauyawa tun safe yakejin hakan Kuma yasan alamace ta ciwonsa zai iya tashi ko wane lokaci Amma meeting din yasa baisamu damar amfani da inhaler gashi idan yataso duka Dole saidai oxygen Wanda duk lokacinda aka saka Masa oxygen rayuwarsa tana cikin mugun hadari ne sbd oxygen din nabawa lungs dinsa matsala sbd dama can basuda qarfi lungs din tun haihuwarsa shiyasa shida likitocinsa sunriga sunkai qarshe akan karya taba Bari ciwonsa natashi gaba daya harya tafi qarfin inhaler ta riqesa.

Qoqarin Kama numfashinsa dake son qwace Masa yakeyi Yana dagawa mutumin Kai sbd Magana tafara son gabatarda ya dago daqyar ya kallesa Yana dannewa yace Masa yaje zai nemesa idan yadawo daga tafiya zasuyi Magana.

Mutumin na fita ya dafe qirjinsa cikin tsananin azabar rashin fitar numfashi idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa sunfito sosai
Hannunsa na rawa ya jawo drawer office din nasa ya Fara laluba baiji inhaler dinsa ba,
Firfito da duka kayan ciki yayi Yana watsowa cikin sauri da tsananin azabar dayake ciki baiganta ba gashi yafara loosing control din kansa sbd idanuwansa sun Fara gani dishi dishi
Da sauri ya miqe ya dauki wayarsa da keys din motarsa ya fito Yana riqeda kurkinsa ya nufi motarsa ya fada Yana tayarwa yafito asibiti saidai abin yaci qarfinsa gaba daya zuwa lokacin sbd numfashinsa daya dawo gaba daya bakinsa tuni motar tafara qwace Masa.

Daga government house yafito daga wani guntun meeting dayayi da deputy governor akan investing dasuke sonyi a sabon ZABEERA LTD dinsa dake Bangkok,
Shida malam Umar ne a motar shike tukasa
Gaba daya hankalinsa nakan wayarsa dayake duba tarin misscalls din da akaita Masa Wanda duk yawanci daga mutanen hurdarsa ne sai sauran daga family wainda yasan dukansu bazai wuce buqatar kudi daga garesaba Wanda Sam shi ko mamakinsu baida lokacin tsayawa yayi
Misscal din zarah guda hudu ne ya kalla numbernta dayayi saving da ZB wato zarah zabeera,
Sam Bata gajiya da Kira ita duk da tasan bako yaushe yake dagawa Amma Sam taqi sabawa da hakan
Wasu mutanen suke aikata Abinda zai 6ata ransu,
Abinda tasani ya koya a rayuwarsa shine kayi rayuwa akan mizanin dazai baka nutsuwa da ease
Baya tunanin har abada zai iya jefawa ko Kai kansa ga Abinda zai baqanta ransa ya Bata Masa Rai yayi iya qunci da baqin cikin dazaiyi tun Yanada quciya Dan haka wannan babin na damuwa akan alamarinda wani zaisaka ya Dade da wucewa agurinsa
MD ga wannan kamar motar Dr khalil ce Kuma kamar dai ba lafiya ba Dan.....

Bai qarasa yayi saurin over taking motar Dr din sbd wani junction dazata nufa ta buga.

MD din ne da kansa yafito ya nufi motar Yana budewa idanuwan Khalil din na qoqarin rufewa da zafin nama ya fizgosa daga cikin motar tareda taimakon malam Umar suka kamasa zuwa motarsa da kansa ya qara sanyin AC din motar tareda fitowa cikin sauri ya zagaya ya bude gaba cikin sauri yabude can qarqashin sit din driver saigashi yaciro inhaler da sauri ya zagayo ya dago Kan Khalil din Yana shaqa Masa Amma Ina Sam ko Shiga batayi sbd numfashinsa ya tsaya gaba daya.

Kasa mgana yayi yafito idanuwansa na sauya ya karbi mukulli hannun malam Umar ya zagaya ya figi motar cikin mugun speed din dayasa Mutanen gurin watsewa da sauri sbd gudun tsautsayi shikuma Mal Umar yashiga motar Dr din yaja yabi bayansu.

Zabeera ya nufa Kai tsaye
Securities suna hango motarsa da yanayin da yake tahowar cikin speed yasasu saurin wangale Masa makeken gate din da mutum uku ne ke iya rufesa
Yana isowa yashige gate din Yana qara gudun motarsa yabi bangaren dama inda tacan gefen hanyar zuwa part din Khalil din yake.

Yanayin parking bakin part dinsa yafito ya nufi wata qatuwar flower vase dake bakin qofar shiga palonsa inda anan yasan Khalil din na aje keys dinsa.

Ya a budewa da bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye sbd yasan inda allurar take
Tun daga cikin dakin ya hadota yadawo motar Yana shiga ya daga hannun Khalil din ya soka Masa tareda dannata da sauri ruwan suka shige jikinsa take yayi wani irin yunquri tareda Jan numfashi me qarfi da qara kafin jikinsa yakoma yasaki.

Sai alokacin MAHMOUD ya sauke ajiyar zuciya Yana 'dan dafe goshinsa tareda lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya kala.,
A duniya idan akwai mutum daya dazai iya sadaukarwa Koda rayuwarsace to shine Khalil,
Khalil ne kawai weakness dinsa a duniyar Nan sbd shikadai ne yake shiga tashin hankali akansa aduk lokacinda yaga ciwonsa yatashi sbd hakan na razana jarumtarsa Dan Khalil shine mutum na qarshe dayake baya iya tunanin ma rasawa,
A rayuwarsa he has only two dear ones,
Na farko mahaifiyarsa da har yanzu take cikin qasan ransa daya kasa cire kewarta,
Sai na biyun shine khlail,Wanda bayada wani Dan uwa dayake gani amatsayin jininsa kamarsa.

Tsananin mataki da kulawar daya daukarwa ciwon Khalil din yasa dukkanin motocinsa da office dinsa yanada ajiyayyar inhaler dayake ajewa sbd Khalil din Dan Koda ta kwana irin haka.

Ahankali yaji an dafa hannunsa
Saida yaqara rinste idanuwansa yasaki qaramin numfashi kafin yabudesu akan hannunsa da khalil din ya dafa a wahalce.

Kallon fuskarsa Khalil yayi tareda sakin wani wahalallen numfashi ganin duk duniya idanba ubangiji daya halacci MAHMOUD din ba Babu me iya gane kowane yanayi na MAHMOUD da Abinda yake ciki sbd fuskarsa Bata taba nunawa,farin ciki ko akasin hakan.

Kallonsa yayi da jajirtaccin idanuwansa cikin nutsuwa yace"
Koma me kake tunanin kanayi zaifi idan kadawo kanka,
You know this is stupidity right??
Chapter 24 · 0% Book details