← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 70

Sashe 31

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Palo ta fito ta nufi kicin da kanta yau ta dafawa kanta indomie da dafaffen kwai guda biyu sai custard data hado Wanda yaji uwar Madara takoma dakinta acan tayi breakfast dinta tana gamawa ta fitoda kayan ta maida kicin Takoma daki ta sake kwantawa tana tunanin Dr da irin dibbin soyayya da qaunar daya Bata,
Ya juyawa iyayensa baya akanta alokacinda aka koresa ya amince zaibar komai da komai ciki hadda iyayensa da 'yan uwansa da rayuwar daya taso ciki duk sbd ita
To menene Dan itama ta danne zuciyarta ta tauyeta daga Abinda takeso ta bashi koba komai Al'amarin da zuciyarta ta dauko me girma ne sbd mijin anty zarah ta haramtawa kantashi Koda sonsa zai kasheta har abada su biyun Nan anty zarah da Dr bazata taba barin susan halinda zuciyarta ta Shiga akan mutuminda sukafi qauna da komai arayuwarsu.....

Kiran Salman ne yashigo wayarta cikin nutsuwa ta daga tana qoqarin kawar da damuwarta tace"
Likitan qashi na duk Nigeria""ta qarasa tana Yar dariya.

Shima 'yar dariyar yayi Yana gyara zama cikin motarsa yace"
Zakije mukai usi airport kokuwa na tafiyata?

Wuntsilowa tayi bakin gado tana janyo dankwalinta da gyalenta ta fito tana cewa''
Ai karma kamin haka idan ban takasa a matsayin 'yar uwarsa da bamu taba rabuwaba arayuwa sai yanzu to zan takasa amatsayin matar Dr khalil tunda bayanan Dan shine yafi kowa cancantar ganin wucewar usi Dan shine yakawo wannan murmushin akan fuskarsu na samun cikar buri su samu ilimi kamar sauran 'yaya.

Ganinta kawai yayi tana bude gaban motar ta shigo ta zauna tana kashe wayar tace"
Muje ko
Dariya tabasa ya girgiza Kai Yana cewa'
Amatun likita bokan turai.

Kallonsa tayi tana cewa''
Nidai muje tun kafin na huce da zafi zafina nafito Dan yiwa USI huduba.

Jan motar yayi suka fice suna Dan taba fira ahankali har suka Isa gida inda su kadai ake jira suzo dauki usin.,
Tunda tashigo gidan idanuwanta suka sauka Kan 'yan gidan kaf a tsaye cirko cirko tsakar gidan kowanne fuskarsa cikeda yanayin damuwar rabuwa da USI din ta juya ta kalli kawu dake zaune radionsa a kunne Amma yanayin fuskarsa yasa taji idanuwanta suna qoqarin cikowa da hawaye tana kallon iyami sai kawai ta qaraso da sauri Yana sake hawayenta ganin yanda Usin yake tsaye riqeda hannun iyami Yana Bata qwarin gwiwa.

Usman din ta kalla tana share hawayenta tasaki murmushi Dan cirewa kowa damuwa takai Masa duka a baya tana cewa"
Ki yanda kasa kowa cikin damuwar tafiyarka bayan duk hutawa zamuyi da rashin Jin ka musamman maman junior da anty salamatu ko???""tafada tana kallon maman junior da anty salamatun dake qarasowa da jakarsa data fito Masa da ita.

Murmushi maman junior tayi tana cewa''
Usi Allah yabaka sa'a kamaida hankali kayi karatu ko zaka tallafa Mana wata Rana idan lokacin cin amfanin karatun yazo sbd Kaine kasan wahala da gwagwarmayar rayuwa damukeyi anan gwamnati batamasan da ire irenmuba.

Maman junior kada ki damu daya bayan daya dukkaninmu sai usi yakaimu Hajj da umrah da albarkar wannan karatun dazaije Amma idan kuka tsaya Kuna Masa wannan fuskar ta marayu ta Yaya zaije da gwarin gwiwarsa ai kawai ki Masa tashin hankali da hayaniyar da kuka Saba shizaisa yaje Yana tuno kowa ayanda halayyarsa take....

Dariya dukkaninsu suka dauka Nan aka hau hayaniya ana Masa Allah ya kiyayaye shima sai hakan yasashi Jin Dadi ya saki fuska Yana amsa musu kowa ana Masa alqawarin Abinda za'ayi Masa idan akai kudi.

Kawu da iyami dasu akeje har airport inda suka taru su duka da hayaniyarsu suka cikawa Salman motar da hayaniya sai suke qara burgesa musamman Amatun dake qoqarin Hana kowa shiga damuwar tafiyar Usin bayan ita Yana iya hango tsananin damuwa da fargabar rabuwa da Usin a idanuwanta tana daurewa ne kawai.

Suna Isa ko zama basuyiba aka Kira jirginsu Salman ya kallesa Yana basa sauran dukkanin bayanan da Dr yace yayi Masa tareda basa takardun komai Dana atm card na account din da aka bude Masa tareda wadataccin kudi aciki ya miqa Masa tareda Dan rungumesa Yana cewa''
Zaka ringa ganina akai akai inshallah har sai kagama sanin komai da komai just take care brother,
Kuma Ina fatar zaka saka mijin 'yar uwarka alfahari dakai wata Rana.

Kallonsa yayi ya kalla Amatu Yana qirqiro murmushin qwarin gwiwa yace"
Inshallah Dr khalil saiyayi murmushi ga wannan aikin alkhairin nasa.

Gyada Masa Kai tayi tana qoqarin maida hawayen dake subuce Mata
Suka rungume suna tana sakin hawayenta gaba daya suna zubowa ba tsayawa.

Cikin kunnenta yace"
Amatu Ina Miki fatar samun Abinda kikeso arayuwa Wanda zaisaki farin ciki,
Inaso Kuma kimin alqawarin Babu wani Abu dazai sauya matsayin Dr acikin rayuwarki kimin alqawarin da ke da kanki zaki kirani Dan sanar Dani aurenki da Dr Khalil idan lokacin yayi.

Rintse ido tayi hawayenta na sake gudu ta janye jikinta tana kallon qasa tace"
Usi zuciyata takamu da son wani Wanda ba Dr khalil ba so me girma Amma wlh shima son Dr khalil bai sauyaba a zuciya da rayuwata,
Ba laifina bane sbd bansan yaushe hakan yafaru ba,
Bansan ta Yaya zan kankare wannan son daga zuciyata ba Amma nasan ta yanda zan dannesa dannewar da har abada bazai tasoba bare wani yasan dashi zanbarshi cikin Raina har mutuwata,
Jan kuka tayi ahankali tana cigaba da cewa''
Usman ayau ni Amatu nayi maka alqawarin bazan taba auren kowaba sai Dr khalil,
Nayi alqawarin Dr bazai taba fuskantar sauyawa daga gareniba sbd shi kadai na zaba amatsayin mijina Inshallah...."wani siririn kuka taqarasa maganar dashi zuciyarta na wani irin nauyi.

Baiyi mgn ba ya juya gurinsu kawu yayi musu bankwana ya wuce Yana danne zuciyarsa dake Jin tsananin damuwa da tsoron Abinda Amatu ta fada,
Shin yayi Mata adalci satayin alqawarin auren Dr Bayan tafada Masa akwai Wanda zuciyarta ke tsananin so???

Baya tunanin baimata adalciba sbd a nasa gani da sanin Babu Wanda zata aura ya sota ya qaunaceta yabata farin ciki da kulawa fiyeda Dr khalil zabeera Dan haka koma waye zuciyarta keso farin cikinta da kulawar dazata samu daga Dr yafi matasu ahankali zata manta sonta zuciyarta ta koya son KHALIL din.

Ahanyarsu ta komawa Babu me mgn acikinsu kowa yayi shiru Yana tunani kamar basune suketa hayaniya ba a hanyar zuwa.

Su kawu tunanin rahuwarsu dasu Usin sukeyi sbd dukansu basa gabansu yanzu sai sukejin kamar rabuwa sukayi dasu gaba daya musamman iyami datakejinsu kamar itace ta haifesu gashi yanxu ta tashi Babu ko daya a gabanta.

Shikuma Dr Salman yasan irin ciwo da radadin datake ciki na zabar danne sonta tabi Abinda rayuwarta da 'yan uwanta keso.

Ajiye su kawu sukayi suka nufi gida har lokacin Babu me Magana acikinsu Saida yayi parking qofar part dinsu anty zarah sai ga MD ZABEERA yafito Yana amsa waya fuskarsa sai sheqin kwarjini takeyi ya nufi motarsa ya bude ya shige drivernsa na ciki yaja sukabar gurin idanuwanta na binsa da kallo har motar ta bace Salman na lure da ita ya saki numfashi ahankali yace"
Duk zabin dazakiyi Amatu kisani ni Salman zabeera Ina bayanki dari bisa dari saidai bazanso ki zabi Abinda zai kawo damuwa da qunci cikin rayuwarkiba,
Soyayyar MD ZABEERA Babu Abinda zata baki sai damuwa sbd bazai baki soyayya da kulawar da kike nemaba infact baimasan kinayi ba Koda yasani Babu so agabansa sbd keda idonki Kinga hakurinda matarsa keyi akansa Wanda mu bazamu iya ganinki kina irin wannan rayuwarba so please AMATULLAH for our sake kadaki saka kanki cikin quncin dazaki sakamu muma.

Share hawayenta tayi tasaki murmushi me ciwo tace"
Dr Salman zabeera daga yanxu anan munrufe maganar MD ZABEERA sbd soyayyarsa ba Abu bane Dani Amatu zansamu,
Soyayyarsa wani bangarene me girma a zuciyata da bazan iya cirewa ba saidai Kuma illace ga mutane da dama Dan haka na zabi azabtuwa da ita ni kadai acikin Raina bazan Bari ta azabtarda masoyanaba dan haka daga yanxu Babu mgnar MD ZABEERA da AMATULLAH,
Zuwa yanzu nasan kagama sanin Abinda yake faruwa kasan banida aure da Dr Khalil dan haka idan har ka daukeni kamar Yar uwa wadda kake tsananin qauna to ka nesantani duk Abinda zai cigaba da zurafaf soyayyar MD ZABEERA ka tayani nitsawa da kutsawa cikin son KHALIL ZABEERA sbd na riga na yanke shi na zabarwa kaina.

Kallonta ya tsaya Yi zaiyi Magana tayi saurin girgiza Masa Kai tana share fuskarta da tissue din motar tana murmushi tace"
Zancen ya wuce Kuma ai"" dan sake batarda zancen ta Dora da fadin"
ni yanzuma so nakeyi kafara koyamin wannan turancin naka na turawa idan Dr yadawo so nakeyi nabasa mamaki.

Dariya yayi Yana jinjinawa gwarin gwiwarta na kawo dariya Kan fuskarta da boye abindake zuciyarta Wanda hakan na daya daga cikin Abinda yake burgesa gameda ita.

Fitowa sukayi suna fira sama sama suna dariya kamar Babu Abinda yafaru.

Anty zarah na ganinsu ta daga wayar hannunta tana cewa''
Cikinku fa daya zankira sbd Ina ganin bangantaba nasan Kaine kawai zaka fita da ita.

Ko zama beyiba suka gaisa da anty zarah din ya juya ya fice sbd mum dinsa daketa qwalo Masa Kira.

Fes ta sakewarta Takoma Amatun ta me rayuwarta cikin Raha da Jin Dadi,
Duk wani Abu ko inda tasan zata hadu da MD ZABEERA ta tosheta gaba daya data fahimci lokacin dawowarsa yayi take komawa daki takira Dr ko USI ko Salman suyita firarsu cikin nishadi.

Kulawa kuwa da qaunar da anty zarah take Mata sai ninkuwa sukeyi sbd yanzu kwata kwata ta daina cire cikon datakeyi sbd umarnin Dr khalil ne Dan shima yanzu so yakeyi daya dawo Susan dubarar Yi maganar cikin Nan yaqare su fuskanci reality itakuma anty zarah data qwallafawa cikin Rai har MD ZABEERA yiwa zancen takeyi idan tasamu fuska sai hakan yafara basa tunanin Dole daman Suma wata ran suyi sha'awar samun 'da ko 'ya.

Sannu ahankali sabo da shaquwarta da Dr Salman yayi qarfi Dan shima saitakejinsa kamar usi da baya kusa duk wani gurbi na 'dan uwa me kulawa ya cike matashi Dan dukkanin shawararta da sirrinta dashi takeyi ta yanda shima baya boye Mata komai sai suka zama tamkar wasu best friends kokuma Yan uwan dasukafi kusanci da kowa.
Chapter 31 · 0% Book details