← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 70

Sashe 64

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude baki tayi ta korowa umman bayanin komai zata Dora da wata maganar umman ta daga Mata hannu cikin takaicin ZARAn da cewa''
Zarah kinada matsala babba idan har Baki dawo hayyacinki ba,
Shi so da zaman aure duk ba hauka bane,
Ta Yaya Zaki maida kanki doluwar qarshe akan gudun zuciyar namiji,
Shin meye amfanin rayuwar aurenda babu fahimtar tunani ko Babu so ana zaman aure me Dadi idan kowa yasan mutunci da darajar kansa data abokin zamansa,
Matsalarki zarah itace kin kasa bawa kanki darajarda shima abokin zaman naki zai baki,
MAHMOUD ya zaune dake cikin girmamawa da mutuntawa tsawon shekaru masu tsayi batareda ya taba complain ko nuna muzantawa garekiba duk da kece Kika kasa kawo sauyi da shaquwa acikin auren naku sbd kece mace kinada hanyoyi da damarmaki da Zaki sauya MAHMOUD tun
kafin wata tashigo rayuwarku Amma Kika kasa yanzu abin yazo a biyu na farko koki yarda ko karki yarda MAHMOUD son mararsa AMATULLAH yake so me tsanani musamman tunda yanzu gatanan tana bude Masa hanyoyin sanin zamantakewar aure sannan akwai fadanda ko sunyi abunsu na tsakanin ma'aurata ba huruminkineba Shiga gashinan yanzu kin qare zuwa bikon kishiya Wanda idan dai baki koyi sanin darajar kankiba data Kama kanki akan Abinda Babu ruwanki har ruwan wanka kina Kan hanyar daukarwa kishiya Dan haka kada kiga laifin mijinki laifinkine
Da Zaki farka ki nuna Masa kinsan darajar kanki data aurenki da zamanki matarsa tsaf zakiga yazo yazauna daku anbawa kowacce haqqinta anzauna lafiya.

Bance kinyi baya ba sbd wannan halindakike ciki Allah na gani Kuma Yana sane wlh zakiga irin tanadin sakamon da Kika samu agaba Amma gskia zarah ki farka Babu Wanda zai qwaceki a cikin wannan yanayin sai kanki da kanki Zaki qwaci kanki ki tashi kije bikon naki dakika daure kanki da zakiyi Danni bana cikin wannan mutuwar zuciyar.

Mutuwa jikinta yayi ta miqe ta wanko fuskarta tadawo ta dauki keys ta fice batace qala ba ta shiga mota ta nufi gidansu Amatu.

Tana Isa tayi parking ta fito tana daidaita kanta da nutsuwarta ta nufi ciki ta Isa qofar Palo tashiga da sallama
Su iyami dake zaune palon duk suka juyo suna kallonta
Saiga Amatu ta fito daga kicin daukeda indomie data dafo tana ganinta itama ta tsaya cak tana kallonta.

Anty salamatu ce tayi saurin miqewa tana cewa''
Zarah kece da yamman Nan sannu da zuwa.

Iyami ma cewa take"
Qaraso ki zauna zarah kinji sannu da zuwa fitar yamma.

Murmushin qarfin hali tasaki tana q
arasowa ta zauna tana kallon Amatu dake kallonta tana Mata sannu da zuwa itama.

Murmushi tasaki tana cewa''
Amatu idonki kenan.

Indomin ta ajiye tana murmushi tace"
Anty zarah kedai karkice komai nakira wayarki Allah harso biyu bana samu.

Zobo anty salamatu takawo Mata suna qara gaisawa zarah tace"
Iyami wannan 'yar Taki zaneta zamu farayi sbd tashin jinta yanzu kiduba kiga yanda takasa aje fushin datakeyi damu shiyasa nazo da kaina nabata hkr tunda taqi sauraron mijinta to gani nazo Dan yau bazan fita gidan nanba saida ita.

Kallonta Amatu tayi cikeda mamaki tace"
Anty zarah.

Tsit antyn tayi sbd tsawon lokaci sai yau takirata anty zarah complete.

Juyowa tayi ta kalleta zuciyarta na rauni da damuwar datake ciki Amma tana daurewa kada ta gasa ta bude baki zatayi mgn sukaji sallamarsa dukkaninsu suka juya.

Iyami na ganinsa gaisawa kawai sukayi ta miqe ta bar gurin hakama anty salamatu.

Kallonsa zarah tayi harya qaraso gabanta baice komaiba ya kamata hannunta ya miqar da ita yace"
Let's go.

Kallonsa tayi da idanuwanta dake son cikowa ya sakar Mata murmushin dake nuna banhaqurinsa Yana girgiza Mata Kai yace"
Ita tariga ta taho gidansu ke dakike taredani bazan Bari ki barni ba,
Bazaki bawa kowa hkr ba sbd selfishness ba.

Wani irin sanyin Dadine yake kwaranya cikin zuciyarta haryana bayyanuwa Kan fuskarta tasaki wani yalwataccen murmushi tana girgiza Kai tace tunda nazo zankoma da ita idan har da akwai mutunci da ganin girma a tsakaninmu.

Gyaran muryar kawu sukaji daga bayansu suka juya Banda Amatu da abun duniya ke neman shawa Kai.

Palonsa suka nufa aka zazzauna Nan ya rufe Ido duk su dukan yayi musu fada tareda sanarwa da kowa laifinsa Kuma ya buga rantsuwar yau Amatun a gidanta zata kwana da daddare iyami da salamatu zasu kawota.

Godiyar da MAHMOUD din yaringa yiwa kawun yasa su iyami Jin wani iri sbd zarah din.

Bayan tafiyarsu Amatu Tasha kuka harta gaji iyami ta kalleta tana cewa''
Amatu kiji tsoron Allah kobaki zauna da mijinki lfy Dan Allah ba Kya zauna dashi lafiya kodan baiwar Allan Nan tasamu nutsuwa gidan aurenta,
Karki manta shifa aure hkr ne cikinsa kusan gabaki daya,
Bakiyi rayuwar zaman aureba da Khalil ya rasu sai yanxune zakiyi rayuwa Kuma wlh duk Kika dagawa MAHMOUD hankali har hakan yasa aka Shiga haqqin zarah Allah bazai barki ba,
Matar Nan koba komai wlh duk Wanda yasameta abokiyar zama ya huta a rayuwa sbd matardake danne kishin Mijinta Dan kawai a zauna lfy ai itace abarso da tattali Banda shi so yake wani dabam,
Dan haka Amatu Dan Allah ki dauke Ido ki koyi hakuri Kuma ki zauna da Matarnan tsakani da Allah kamar yanda kuke ada ni wlh tausayi take bani Kuma Ina tsananin ganin girmanta.

Itadai Amatun Banda hawaye Babu Abinda takeyi sbd hukuncin da kawu ya yanke akanta ta wani bangaren Kuma yanzunema zasu Fara tsara zaman auren dakuma kishin tunda yanxune za'a hadesu araba musu kwanan aure da komaima.

Daki Takoma anty salamatu na hada Mata sauran kayan Sha da iyamin ke hada Mata kullum tun ranarda aka Fara maganar tarewarta.

Har dare Basu Gama Shiri ba sai Bayan ishai tayi wanka ta shirya cikin wata farar lafaya da wani lace me taushi aka bita da turaruka masu sanyin qamshi suka fito bayan kawu yaqara tashi nasihar.

Andi ne dakansa ya aiko drivern dayazo daukarsu suka nufo zabeera inda ake jiran isowarsu.
##Mamuh#*_MQ 48_*
*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*
Ina ma
abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al
adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau
ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nau
uka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....

Ba Mu tsaya anan ba
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata...

Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l
Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.
*******
*********
Suna Isa zabeera Kai tsaye motar data daukota sashen Andi aka nufa dasu sbd har Modibbo da umme na can dashi kansa MAHMOUD din Wanda ranar yakoma MD ZABEERA dinsa sak miskilanci da izzarsa sun motsa ko wayoyinsa duk akashe ma suke Abu daya kawai yakeji atare dashi shine nutsuwar zuciya data ruhi harma data gangar jikinsa Wanda yagama tabbarwa da kansa cewa tabbas Amatu tarigada tazama wani babban bangare an zuciya,jiki da rayuwarsa tunda haryakejin wannan nutsuwar me sanyin Dadi tattare da dawowarta garesa.

Suna shigowa akansa idonta yafara sauka ta dauke Kai Yana sunkuyarwa ta zauna daga qasa gefen umme dake kallonta fuskarta na bayyanarda farin ciki da murmushi.

Da MAHMOUD din Andi yafara nasiha akan haqqoqan Mata dake Kan mijinta dakuma ire iren halayen .ata da Dole namiji saiyayi hkr dasu sbd rauninta dakuma rashin zurfin tunani
da Rashi haquri irin na wasu matan kafin yadawo Kan Amatu da nasihar zama da miji da girman haqqoqinsa akanta da girmansa dayafi na kowa akanta yanzu yaqara da nasihar adalci tsakanin mataye biyu dakuma haqurin zama da abokin zama Dana rayuwa kafin daganan Andi yayiwa Amatun kyautar aure ta sabuwar mota fil sak irinta zarah datake hawa banbancin kalane kawai dayace Tata Ash ce ta zarah farace.

Godiya sosai sukayi suka fito umme na riqeda hannun ta saka Mata wani acikin hannun dayake rufe cikin qaramar kwalbar roba suna shiga mota tace"
Shanye kiban roba.

Kallon ummen tayi tana sake kallon abun ta Dan 6ata fuska zatai mgn tace"
Bansan Jin komai hanzarta kishanye kiban.

Marairaice fuska tayi tana kallon abun.

Anty salamatu dake sit din gaba ta juyo ta kwace kwalbar ta bude tareda Dora Mata abaki tana cewa''
Dallah shanye da abin dadine da yanzu kinfara maganar qari to wannan dadinsa saikin fi kowa.....

Rufe Mata baki Amatun tayi da sauri tana zaro Ido kunyar umme kamar ta nitse ta saci kallonta tace"
Haba anty salamatu nidai karki fara zancenki Dan Allah.

Itama anty salamatu kunya taji sbd mantawa tayi da umme da iyami dasuke taredasu sbd sun Saba zantukansu na banza dasu maman junior shiyasa.

Shanyewa tayi ta miqawa umme kwalbar daidai isowarsu qofar part dinta motar har qofar palonta ta faka suka fito umme na riqeda hannunta tana fada maganganu qasa qasa na rikita miji wainda sukafi qarfin duk rawar Kan Amatun kunya kamar ta qwace hannunta ta zura da gudu Amma ummen ba ruwanta fada Mata takeyi har suka shiga suka zauna palon tana sake zayyano Mata zantuka masu qarfi wainda wasune suka samu damar shiga kanta wasu kuwa nauyinsu yasa suna kasa shigewa Kan nata.

Turaruka ummen ta fitar cikin jakar hannunta ta fesawa Amatun ko Ina jikin masu wani irin sanyin qamshi dagaji tasan bazasu wuce ouds ba masu tsananin tsada take qamshinta ya qaru tana fitarda wani qamshi me ni'imtaccen sanyin dadi suka Fara qoqarin tafiya anty salamatu tace"
Zarah ko lafiya Naga banganta ba na dauka ma zamu sameta anan gashi har zamu tafi.

Umme tace'
Eh Kam gashi dai Nima duk yau banganta ba Nima nai zatan zamu sameta anan din tana jiran isowarmu.
Chapter 64 · 0% Book details