← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 70

Sashe 30

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binsa anty zarah tayi da kallo harya haye stairs din zuwa samansa tana karantar yanayinsa
Idan nazarinta yabata daidai MD na wasu abubuwan dabata ganewa kwanakin Nan duk da dai dama can Bata ganewa MD Amma dai yanzu kamar tana nazartan wasu abubuwan nasa.

Bin bayan Amatu tayi tana kawar da tunanin komai tana zuwa dakinta ta sameta Dr khalil na qoqarin cigaba da sata nishadi itama tana qoqarin nuna Masa nishadantuwarta sbd kada ta sace Masa gwiwa.

Palo suka dawo da anty zarah tasata gaba akan saitaci abinci ga cake din datakeso koyaushe Wanda ake Mata duk Bayan kwana biyu Amma ta kasaci komai ko ruwa ta kasa Sha sbd kanta dake daure tamau har wani sarawa yake Mata takasa cire tunanin komai cikin ranta saima wani irin tunanin MD din dayake neman zauta kanta bangare daya ga tunanin Dr da koma me zaije yadawo shi tayiwa alqawarin kanta matuqar suna raye saidai tunanin MD dakuma yake sake rikitata.

Miqewa tayi ahankali tace"
Anty kaina Yana ciwo sosai zanje na kwanta kozai rage.

Kallonta anty zarah din tayi tace"
Dakin daure kinci abinci ko kadan ne Kinga pasta ce aka dafa Kuma me ruwa ruwa ce zuwa anjima kadan lalacewa zatayi kada yunwar dare ta tayar dake ki rasa abincin ci yau ko fruits Babu a gidan Nan baa siyoba gashi rabonki da abinci tun rana da Kika ciyo a can gidanku.

Girgiza Kai tayi tana Dan dafesa tace"
Wlh banajin cin abinci saidai zuwa da safe idan ya warware zanci harda biyan bashin na yanzun din.

Miqewa anty Zaran tayi itama tareda wucewa gaba tana cewa''
Shikenan Allah ya tashemu lafiya Kisha magani kafin ki kwanta Dan Allah.

Hanyar dakin MD ta nufa tana gyara zaman rigarta a jikinta Wanda yasa Amatun binta da kallo idanuwanta na qoqarin cikowa da hawayenda suka sata saurin dawowa hayyacinta tayi dakinta da sauri tareda fadawa Kan gadonta tana rintse ido.

Tunda ta kwanta takasa bacci tana kwance ta qurawa Dan qaramin hoton Dr khalil dinta Ido dake cikin qaramin frame gefen gadonta Wanda anty zarah ce ta kawo Mata.

Dr Dan Allah kayi gaggawar dawowa sbd Ina buqatar kayi saurin aureni na zamo mallakinka
Bazan iya jira cikin Nan yakai wata taraba kadawo kasan yanda zakayi dashi nidai aurenka kawai nakeso yanzu fiyeda komai tun kafin zuciyata tafi qarfina.

Har qarfe goma sha biyu da arbain batayi bacci ba gashi zuwa lokacin yunwa tafara hanata sukuni sbd jikinta harya Fara 'yar makarkata
Ta tashi zaune tana kallon agogo.

Saukowa Kan gadon tayi tareda mayarda qatuwar rigar sanyinta me kaiwa har gwiwa ta zura hula tareda sanyo slippers ta fito tana adduar Allah yasa abincin bai buga ba Dan wlh bazata iya kwana haka ba.

Tana fitowa ta nufi dining Kai tsaye daidai shima yafito daga dining din sbd abincin daya sauko ci Dan duk yinin ranar baici abinci ba sai Daren Kuma spoon biyu kawai yaci yatashi sbd Abinda yafaru gashi yanzu yasauko abincin ya buga.

Kallonsa tayi bayan itama ta bude abincin batasan lokacin datace wlh yunwa nakeji ni bazan iya kwana ahaka ba.

Palo yadawo Yana tunanin zancenta koba komai tunda tanada juna biyu ayanda sukace Dole tana buqatan abinci akai akai.

Shima Dole Yana buqatan abinci bazai iya kwana a hakan ba ya juya zuwa dakinsa ita Kuma tayi kicin ta hau dube dube Babu Abincin ci ta dauko ruwa Tasha taji cikinta na neman qullewa ta fito tana riqe cikin daidai ya sauko sanyeda riga da wando masu Dan kauri kamar na sanyi hannuwansa daukeda mukullan mota da wayarsa batareda ya kalli fuskartaba kamar bada ita yake maganarba yace"
Muje.

Tsayawa tayi binsa da kallo harya fice kafin tabi bayansa da sauri.
##mamuh#
ZAFAFA BIYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[4/2, 11:30 AM] Zafafa: *_MQ 24_*
Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai sanyin AC da qamshin turarensa daya Gama Kama motar dama can yake ratsata Yana Bata wani sabon yanayi cikin zuciyarta Wanda yasata fadawa tunani.,
Tuqinsa yakeyi cikin nutsuwa shima Yana jiyo siririn sahirtaccen qamshin jkinta na Shiga hancinsa ahankali Wanda kusan shima yasashi Shiga tunanin banbanta yanayin qamshinta Dana zarah.,
Istigfari yayi saurin Yi cikin ransa Yana Dan tsuke fuska tareda 'dan qarawa motar gudu.

Ganin sun kamo hanyar blue fox yasata saurin kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace"
Rabin ran Anty Dan Allah muje blue fox akwai abinci me kyau da dadi acan.......

Wani irin kallo ya juyo ya aika Mata Jin sunan data kirasa dashi Wanda yasashi qurawa cikin Idanuwanta Ido Yana son sake tabbatarda Abinda takirasa dashi
_Rabin ran anty_
yanda tafada sunan batareda kulawar komaiba yasashi yimata wannan kallon itama Jin idanuwansa akanta yasata kasa juyowa ta qurawa waje Ido Yana damqe hannunwanta dake rawa zuciyarta na harbawa.

Jin shiru yasata Dan dagowa tareda juyowa ahankali ta kallesa hankalinsa na Kan hanya saita qurawa fuskarsa da fararen hannuwansa dake tuqin motar cikin nutsuwa da qwarewa,
Kan fuskarsa ta tsayarda kallonta tana yaba kyawu da tsarin fuskarda ubangiji yayi Masa me daukeda da tarin kwarjini da Kamala,
Dogon hancinsa ta kalla zuwa manyan idanuwansa batasan lokacinda ta lumshe ido ba hawaye na gangarowa daga cikinsu batareda ta gogesuba cikin ranta tace"
Meyasa zuciyata ta zabi wahalar da rayuwata data Dr ta hanyar son Dan uwa mafi soyuwa agaresa?

Dukkanin kyawu da Abinda MD yakedashi Dr khalil dinta nadasu harma yafi MD din kyawawan halaye masu sanyaya Rai hasalima kusan kamanninsu daya sbd duk mahaifinsu Modibbo suka dauko har Khalil dinta ma yagi MD din hasken fata saidai MD ya nuna Masa gogewa da hutu irin na Boko da yawan qasashe suka hudasa sai kalar fatar mahaifiyarsa daya dauko me sheqi.

A harabar blue fox din yayi parking tareda Dan juyowa ya kalli gefenta tayi saurin share hawayenta tana bude motar ta fito tana washe baki cikin tsananin farin ciki ta juyo daidai ya zagayo tace"
Yau duk abindake restaurant dinnan saina cire kwadayinsa na tsawon aikin danayi anan din.

Bai kalletaba yayi gaba ta biyosa tana sake bayyanar da murnarta ta zuwa gurin.

VIP direct suka nufa inda tuni aka hau sintirin attending dinsu ga mamakinta kusan Rabin ma'aikatan gurin an sauyasu Nan ta bada odar abinci kusan kala hudu da tarkacen su fruit salad harda ice cream da furar blue fox din me shegiyar Madara da Laban yoghurts.

Table dinsu kusan kasa daukan abubuwan yayi sai kawai yayi odar
noodles with veggies salad da power drink yafara ci cikin nutsuwa Yana kallonta tana cin abincin cikin tsananin Jin Dadi Dan harwani lumshe ido takeyi tana cika bakinta da Naman kazar chicken rings dataji carrot da spices.

Yana kallo ta Gama yagalgala kazar ta janye gefe ta jawo shawarma tafara ci itama ta ajiye ta janyo soyayyan dankalin dayaji egg source
Furarta ta janyo ta kurba ta lumshe ido tana cewa''
Wayyo Dadi" kafin ta aje tacigaba da cin noodles Kuma.

Jingina yayi da Bayan kujera Yana zuba Mata iduwansa masu karya kuzarinta tareda dukkanin nutsuwarsa Yana kallonta kamar ya baby a gabansa.

Saida tayiwa komai ci rabi aje rabi kafin ta qoshi ta dauki ice cream dinta ta bude ta diba tana hadiye yawun matsuwa taji sanyinsa ya sauka a bakinta taji anrike ice cream din
Da sauri ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna ahankali ya girgiza Mata cikin qaram
in sauti yace"
This is not good for your health......

Kasa motsi tayi ta harya zare ice cream din daga hannunta ya ajiye idanuwansu na cikin na juna Saida waiter din dake tsaye yayi gyaran murya da qarfi Yana sake miqawa MD din bill dinsu.

Fuskewa yayi Yana Dan tamke fuskarsa ya juyo ya Ciro ATM card dinsa ya miqawa waiter din batareda ya karba bill dinba.

Bayan andawo Masa da atm din anyi clearing bill dinsu suka fito suka Shiga mota sukabar gurin.

A mota shiru tayi tana sauraron karatun Qur'an din dayasa a motar Yana fita ahankali saitaji tana sake samun nutsuwa da yanayin da suke ciki na kasancewa da juna ahaka.

Koda suka dawo zabeera har bacci yafara daukarta cikin motar shiyasa da yayi parking sai bai tayarda itaba hakama bai kashe motarba sbd AC ya zauna ya fiddo wayarsa Yana duba saqon dayaji shigowarsa sunacin abinci.

Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta zuba akansa tana lumshe ido ahankali ta furta"
Tabbas Ina cikin tsananin son MAHMOUD ZABEERA Kuma so me qarfi Wanda nakejin kamar ruhina zai rabu da gangar jikina idan nayi nesa dashi,
Lumshe ido takuma Yi tareda budesu akansa cikin sauti me taushi dazai iya jinta tace"
Nagode.

A natse ya juyo ya kalleta da nasa idanuwan dasuka nuna sunfara Jin bacci taji zuciyarta na qara narkewa da sonshi tayi saurin dawowa hayyacinta tareda tashi zaune tabude motar da sauri ta fice hartana hadawa da Dan gudu tayi ciki.

Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta fada Kan gadon tana sakin hawayen dataketa riqewa tace"
Amatu kidawo hankalinki Mana,
Kidawo Amatunki da kowa yasani,
Amatun Dr khalil matar Dr khalil,
Babu kowa a zuciyarki sai Dr khalil sbd shine Wanda zuciya da ruhinki keson aure.

Ta jima ahaka kafin ta miqe tafada toilet ta wanko fuskarta tayi fitsari tazo ta kwanta tareda lullubewa tana qudurtawa ranta gobe zata amayarwa Salman abindake zuciyarta kafin ta rufe zuciyar gaba daya ta mallakawa Dr khalil dinta Wanda idan har tana Raye Inshallah batada miji sai Dr khalil.

Washe gari tunda wuri ta tashi yau da kanta ita tafara Kiran Dr
Meeting zasu shiga Amma ganin kiranta Saida ya tsaya ya dauka yaji lafiyarta kafin yace idan yafito zaikirata.

Wankanta tayi ta shirya cikin riga da skirt na atampa kalar blue tayi Mata kyau sosai ta yafo gyalen akanta sbd Bata dauro dankwalin kayanba.
Chapter 30 · 0% Book details