← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 70

Sashe 34

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa sukayi suka nufi ciki Yana gaba tana gefensa jiki a sanyaye take tafiyar sbd yanayinsa duk ya Gama sanyayata ga wani irin damuwa daya shigeta ga faduwar gaban yanda zasuyi da ummen Amma koma menene tayi alqawarin jurewa sbd shi.

A palon farko dasuka shigo take qoqarin zama ya tsaya tareda juyowa ya kalleta yana girgiza Mata Kai tareda cewa''
Follow me.

Falonta na qurya suka nufa Wanda dagashi sai bedroom dinta Yana gaba tana bayansa.

Zaune take tana kallon wani Shirin girke girken larabawa da akeyi a mazzika taji shigowarsa tareda sallamarsa ta juyo fuskarta daukeda murmushin dake bayyanarda girman son datakewa Dan nata sai idanuwanta suka sauka akan wadda ke bayansa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauyawa zuwa bacin Rai da fushin ganinta ta tsuke fuska sosai tana dauke Kai daga bakin qofar.

Tsayawa Amatu tayi daga Inda take tana sauke Kai ganin irin kallon qyama da tsanar da ummen ke Yi Mata,
Qarasowa yayi gefen ummen
ya zauna Yana kallon fuskarta data canza yaji ransa yaqara jagulewa ya sauke wani irin numfashi Mara Dadi Yana dafa hannun ummen cikin kulawa da sanyin jiki tareda sautin daya sakasu kallonsa duk su duka biyun yace"
Umme Meyesa Zaki dauki halayyar daba naki ba
Shin Amatu tanada wani banbanci ne da sauran mutane da Kika zabi qyamarta ita kadai?

Umme Amatu matar dazan aurace sbd Ina sonta da dukkanin zuciyata
Shin umme kodan son datakewa dan naki bazaki qaunacetaba kodan hakan?

Girgiza Kai tayi tana danne 6acin ranta ta kallesa tace"
Khalil kadaina cewa tana sonka wannan bayan kudi duk duniya Babu yaren datake ganewa,
Wannan Babu wani buri a rayuwarsu Bayan samun kudi ta ko wane halin Yaya,
Kudine kawai agabanta ta yanda zata iya yin komai akan kudi ciki ina fada maka harda mutuncinta zata iya siyarwa akan kudi,
Wlh khalil kaima sbd kudinka take sonka da bakada kudi bazata taba sonkaba
Irin wannan matar kakeson nabari ka aura Khalil???

Dagowa yayi ya kalli Inda Amatun ke tsaye cikin wani irin yanayi na damuwa ya sauke ajiyar zuciya tareda cewa''
Zo AMATULLAH,
Zo Nan kusada umme.

Kallon ummen tayi taga ko kallon inda take Bata qaunar Yi sbd qiyayya ta tako ahankali tazo gefensa ta zauna ahankali Kan carpet din dake gurin tana sauke kai maganganun ummen na sake jujjuyawa cikin kanta.

Numfashi ya Kuma saukewa cikin wani irin yanayi na damuwarsa dake bayyane wadda tasa dukansu su biyun kallonsa yasake riqo hannun ummen cikin sanyin murya yace"
Ummen banfara son AMATULLAH ba Sai danasan asalin wacece ita,
Nafara sonta ne bayan nasan batada kowa aduniya,
Banfara sonta ba saidanasan a bola ta tashi acan tayi wayo ta koyi gwagwarmayar rayuwa,
Banfara tsananin sonta ba saidanasan irin wahalalliyar rayuwar datayi amatsayin almajiri Mara yanci Wanda ta rayu cikinsu amatsayin namiji bayan tana matsayin mace,
Amatu bakowa mace face yarinyarda wasu bayin Allah suka taimaka suka daukesu Bayan sungama wahalalliyar rayuwa acikin bola da mataccin gidaje da shagunan daba'a gamaba,
Babu Wanda yataba kallonsu da idon Rahama,
Babu Wanda yataba duba yanayin shekaru da jinsinta amatsayin mace ya taimakesu,
Sun kwana da yunwa suntashi da ita,
Sunyi sata dan suci suyi rayuwa,
Maza da yawa sunyi yunqurin lalata rayuwarsu da sunan taimakawa shin umme Wanda yake ciki irin wannan qaddarar Dan yayi sata dan yaci ya Hana kansa Zina illa ne dahar za'a gujesa??????

Umme wallahi tallahi ina tsananin son AMATULLAH da dukkanin zuciyata bansan ta Yaya zanyi Miki bayani ki qaunaci Amatu ba,
Na shirya auren AMATULLAH na zamo gatanta itada zuriarta Wanda Babu wani Abu dazai sauya niyata akan hakan,
Shin umme kintaba zaunawa kinyi tunanin irin tarin Lada da farin cikin dazaki samu aduk lokacinda Kika kawo murmushi da farin ciki a rayuwar marayu?

Umme tarin ladace me yawa wadda zata iya gyara Miki ko wanke kurakurenki Kuma yabaki nutsuwar zuciya da ruhi....

Zuwa lokacin Amatu kuka takeyi sosai sbd Bata taba sanin khalil yasan asalinta ba daduk halinda suka Shiga arayuwa Kuma ahakan yake sonta tabbas yagama bawa rayuwarta girgizar data sauya zuciyarta akansa gabaki daya.

Umme ma hawaye takeyi sosai tsananin so da qaunar danta na ratsata...

Ahankali ya zamo qasa ya durqusa gabanta tareda riqo hannuwanta idanuwansa dasukai laushi na kallonta a karye yace"
Umme ayau gani na durqusa a gabanki Ina roqonki daki ajiye dukkanin wani burin rayuwa ko komawa Allah kodan samun nustuwar zuciya,
Umme Ina roqonki da ki qaunaci Amatu ki da zuciya daya sbd bazan iya ganinku acikin halinda kuke cikiba,
Umme......

Bata Bari ya qarasa ba tayi saurin dagosa tana rungumesa hawayenta na qara tsiyayowa tace"
Nayi maka alqawari Khalil wlh Babu wani al'amarin duniya dazan sake Bari na 6ata akansa,
Idan dai Amatu ce Kuma wlh na amince maka bazan qara qintaba idan har na tabbatarda har zuciyarta itama take sonka....

Rungumeta yayi da sauri Yana cewa''
Thank you ya umme.

Share Mata hawayenta yafarayi tareda juyowa ya kalli Amatu dake kuka sosai ahankali tanajin Sam Bata cancanci soyayyar khalil ba,
Zuciyarta batayi Mata adalci ba son wani 'da namiji a zuciyarta Wanda ba khalil ba...

Ahankali yakamo hannunta ya dawo da ita gefen umme dake kallonta cikin wani irin sabon yanayi ya zaunar da ita ahankali yace"
Amatu ga amanar ummi na ki kular min da ita amatsayinki na matar 'danta.

Dago jajayen idanuwanta tayi ta kallesa kafin ta kalli ummen ta daga Kai ahankali takasa cewa komai sai binsa takeyi da Ido zuciyarta na karban zazzafan baqon yanayi akansa Wanda ta tabbatarda sone me zafi.

Murmushi umme tasaki ahankali tareda kallon Amatun tana nuna Mata gefenta tace"
Kimin alqawarin zaki so shi fiyeda yanda yake sonki??

Murmushinsa me nutsuwa ya saki Yana kawar da zancen da cewa"
Umme wannan son Kaine zakice ta Soni fiyeda yanda nake sonta sbd bazata iya Sona yanda nake sontaba nawa me girma ne.

Murmushi sukayi Banda Amatu dake Jin wani babban al'amari me girma atareda ita hakanan taji gabaki daya nutsuwarta na barinta.

Haj maryam da Nuratu dasuka jima Bakin qofar palon suna jin dukkanin Abinda yafaru baqin ciki me girma yarufe zukatansu da idanuwansu musamman nuratu data gama zaucewa a fusace ta juya tana qoqarin sakin ihun baqin ciki da zuciyarta dake neman tarwatsewa da gudu Haj maryam tabi bayanta tana cewa''
Yau tunda Kika juyamin baya Aisha akan danki kowa ya shirya tashin hankalin dazai biyo daren Nan Dan wlh yau sai takardun asalin Amatu sun kwana a hannun Modibbo da Andi.
##mamuh#
[4/7, 2:51 PM] Zafafa: *_MQ 27_*
Ko gabanta Bata gani ta qarasa sashensu tana qoqarin dafe qirjinta dake mugun zafi da radadi kamar zai tarwatse
Tana shiga palonsu ta zube qasa Kan gwiwowinta tareda fashewa da wani irin kuka me tsanani da zafin Rai,
Da sauri momynta ta qaraso ciki tana rikota tana Kiran sunanta cikin nata ciwon ran me tsanani da tausayin 'yarta tana sake kamota tace"
Nuratu please kada kiyi irin wannan kukan wlh karyamin zuciya zakiyi bazan iya ganinki cikin irin wannan halin ba Dan Allah kidaina kuka zamu samu mafita,
Bazan taba Bari Khalil ya auri wadda bake ba musamman wannan barauniyar karuwar yarinyar Dana Gama alwashin bazata taba aurensaba kodan yanda ya fifita sonta akanki.

Tsananta kukanta yayi tana girgiza Kai tana cewa''
Momy wlh inoson Khalil fiyeda yanda 'dan Adam zai iya lissafawa,
Zuciyata zafi takeyi sosai bazan iya kallonsa ya auri wata ba,
Gwara na mutu danaga wannan ranar.....

Da sauri momyn ta rufe Mata baki tana girgiza Mata Kai cikin tashin hankali tace"
Dan Allah Nuratu kidawo hayyacinki ki daina wainnan maganganun
Zan zamo Mana mafitarda zamu Kori Amatun daga rayuwarmu gaba daya da duk ahalin zabeera ma bama Khalil kadai ba.....

Dagowa nuratu tayi da idanuwanta dasukai jajir suna tsiyayo hawaye tana qoqarin fahimtar zancen momyn ta zabura da sauri tana tunowa da takardun data karbo hannun manager na kaf asalin Amatun harma da qarin rayuwar karuwanci datasa aka qara Mata akai,
Dakinta ta nufa kamar mahaukaciya ta nufi inda handbags dinta suke tahau wargazasu tana neman jakar da tasaka envelope cikin hauka,
Ganin yanda take wargaza Kaya yasa momyn saurin qarasowa tana sake riqota saigashi ta zaqulo jakar
Jikinta har rawa yakeyi ta bude ta dauko envelope din gaba cewa''
Momy yau Babu Abinda zai Hanani wulaqanta wulaqantacciyar rayuwarta,
Saina sakata kuka ninkin Wanda ta sakani tun zuwanta zabeera,
Ayau zata San asalin irin girman soyayyar Dana kewa Khalil.

Juyawa tayi ta fice tana share hawayenta dasuke sake bulbulowa cikin tsananin zafi da baqin cikin da zuciyarta ke ciki
Da gudu momy tabi bayanta tana Kiran sunanta sbd ayanda take yanzu ba acikin hayyacintaba komai lalacewa zaiyi Bata haka zasu tona asirin Amatun ba so takeyi harda umme ta fito cikin zancen....

A firgice ta biyo bayan Nuratun tana Kiran sunanta Amma tuni nuratun ta hada da gudu gudu tana sake sakin sabon kuka ta nufi sashen Andi inda tasan Modibbo nacan taredashi a daidai lokacin.

Ganin takasa cimma Nuratun data nufi hanyar sashen Andi yasa hankalinta mummunan tashi tuni ta firgice sbd wlh tasan Kwana zasuyi aciki Suma sbd zancen ba qaramin tashin hankali da masifu zai janyo ba,,,
Salman dake qoqarin parking yaga wucewar Nuratu da gudu gudu kamar tana kuka Yana qoqarin kashe motar ya fito saiga momynsu cikin sauri itama tanabin bayan Nuratun hankalinta amatuqar tashe daga ganinsu yasan ba lafiya ba bare ganin sunkama hanyar sashen Andi koma meyene to ya girmama dan duk Abinda yasa aka wuce Modibbo aka nufi Andi to da matsala babba.

Kashe motar yayi da sauri ya fito yana qoqarin bin bayansu saiga Dr khalil ya fito daga sashen ummen tareda Amatu da ummen zasu mayarda Amatu
Da sauri Khalil ya taresa ganin Yana Shirin gudu yace"
Lafiya likitan qashi???

Kallon hanyar Sashen Andin yayi cikin sauri sauri yace"
Inaga akwai matsala ne Naga Nuratu da momy sun nufi sashen Andi kowannensu Babu nutsuwa atare dashi Nuratu ma kamar kuka takeyi...

Juyowa yayi ya kalli khalil din cikin fargaba yace"
Ina Jin tsoron Abinda zaisa suje gurin anty musamman Nuratu nasan halinta da tsananin fushi da rashin tunani Wanda kowa yasan yawancin fushinta akan Abinda ya shafeka ne
Akwai Abinda yafaru yanzu a tsakaninku ne????
Chapter 34 · 0% Book details