← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 70

Sashe 51

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umme tasan ayi hakan shiyasa ma batai yunqurin rarrashinta ba sbd tana buqatan kukan ko taji sanyin Abinda akai matan Dan kuwa da tsananin ciwo da kunya Mara iyaka tareda nauyi a aura maka mijin Wanda ya yarda dakai tareda baka qauna Mara iyaka,
Duk su dukan Kam sai hkr Amma zarah ce tafi kowa cancantar ban hkr sbd kishiya ba Dadi musamman irin wannan ta bazata Kuma da wadda baka taba kawowaba
Gashi Amatu mace ce daba kowane namiji zaisamu ya iya Bari ba sbd ita kanta shaida ce tagani akan Khalil dinta tanadai fatar Allah yabasu rayuwa me albarka acikin wannan zaman nasu.

Ganin kukan yaqi qarewa gashi lokaci yaja tafiya tayi nisa yasa umme dafa kanta cikin kulawa da taushin murya tace,
Amatu wannan kukan dakikeyi Babu sauki ko mafitar dazai kawo Miki acikin wannan alamarin,
Aure dai anriga andaura Kuma banajin akwai abindazai warware hakan Dan haka amatsayina na tamkar uwa agareki Ina baki shawara da umarnin ki daina wannan kukan da duk wata masifa ki aje gefe neman lafiyar danki mukazo ki maida hankali mu dage muga munsamu Abinda mukazo nema,
Ki aje komai muyi Abinda yakawo mu idan yaso Bayan munyi nasara idan ankoma gida sai ayi maganar auren kinji.

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya me qarfi akai akai sbd qarfin kukan datasha Wanda har lokacin zuciyarta Bata daina Mata zafi da ciwo ba tunanin anty zarah da halin datake ciki da irin kallon datake Mata sun kasa barinta sukuni saidai kamar yanda ummen tace su maida hankali Kan Abinda yakawosu neman lafiyar Muhammad khalil idan sun koma za'a yi Yanda za'a yi a warware auren kokuma tun anan zatasan yanda zatayi ya sawwaqe Mata tun anan suna komawa gida kowa yakama hanyarsa.

Share hawayenta tayi ahankali tareda dago idanuwanta dasukai jajir suka kumbura sbd tsananin kuka ta kalli anty salamatu taga bataga Muhammad din a hannunta ba ta bude maki cikeda mamaki zatai magana antyn ta rigata da cewa''
Yana gurin MAHMOUD.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda mayarda kanta ta jinginar tana rufe idanuwanta tana tuno zancensa na cewa zai rabata da Muhammad take taji kamar tsoro yanason kamata saidai Kuma ita ba anty zarah bace batajin tsoronsa tafison daganan har qasar sin tabisa akan 'danta duk inda yakaisa.

Bacci ne ya Dan dauketa sbd ciwon Kai me tsanani daya saukar Mata sbd kukan datasha har jikinta sai daya dauki zafi Wanda da wuya idan ba zazzabi bane ya damqeta ga tashin hankali,ga kuka,ga pressure,ga fargaba da tsoro duk sun hadu sun dabaibayeta Dole zazzabi ya damqeta me qarfi kuwa.

Koda jirginsu ya sauka saidai anty salamatu ta riqota suka fito sbd jiri jiri take gani.,
Basusan Yaya akaiba sai ganin wata white jaguar XK120 tayi parking gabansu yanayin motar kawai yasa umme gane MAHMOUD din ne sbd kusan duk Wanda yayi Masa farin sani yasan irin motocin dayake hawa ko a Nigeria ko aqasashen waje.

Zagayawa tayi tabude gaban motar tacewa salamatu" Zo sakata anan salamatu.

Qwacewa tafara qoqarin yi Jin ance zata shiga gaban motar umme ta kalleta ba Wasa a fuskanta tace"
Salamatu zoki shiga mutafi tunda ita Bata tashi tafiyarba.

Jin kamar ran ummen yafara baci yasa ta shiga gaban motar ahankali tareda rufewa tana jinginar da kanta tana kallo gefe zuciyarta na sake cunkushewa.

Shiru dukkaninsu Babu me Magana har suka isa wani kyakkyawan building din dake jerin wasu Athens self-contained flats.

Parking yayi acikin qatuwar harabar kafin suka firfito shine yafara wucewa gaba kansa na juyawa sbd baisan ta Yaya zai zauna da mutane acikin gidansa ba Sam baya iya zama da mutane musamman ana inda yake sakewa yayi rayuwarsa gashi harda umme.

Forth floor ne nashi Dan haka suna fitowa lift din forth floor da sunansa baro Baro dake rubuce akan qofar shiga sukaci karo *_MD ZABEERA_*
da security password yabude qofar yafara shiga tareda kunna fuse na wutar gidan take komai ya kawo haske anty salamatu ta bude Ido da baki tana kallon aljannar duniya tashigo tana kallon sama idanuwanta kaman zasu fado,
Haduwarsu da familyn ZABEERA yasa idonsu suka Dan bude da ganin rayuwar masu kudi da Kuma ganin daular masu kudi Amma anan Kam taga Abinda duk kyau da tsari tareda dukiyar zabeera Bata gani acan ba.

Umme ma data Saba da yawon qasashe Saida Nan din ha burgeta sosai ta yaba saidai flat din 2 bedrooms ne bayan master bedroom dake Dan daga gefe saman qananun stairs Wanda aka zagaye da glass door.

Sauran 2 bedrooms din Kuma sune suke kallon juna daga gefen hanyar dining can umme tace su nufa sbd ganin can ne masaukinsu danshi tuni yayi hanyar master bedroom dinsa yashige qofar glass din kafin ya nufi qofar asalin bedroom din.

Umme ce tashiga dayan bedroom din Amatu da salamatu suka Shiga daya bayan salamatu ta kwantar da Muhammad toilet tafada da sauri sbd fitsarin datake ji tun acikin jirgi Amma tsoro ya hanata ko motsawa bare tayi Magana.

Amatu kuwa bakin gado ya zauna tareda rafka tagumi tana dafe kanta dake tsananin Mata ciwo ga tunanin duniya daya kasa barinta.

Dayake dare ne Babu Wanda yadamu da wani abinci salloli kawai sukai bayan wanka suka kwanta.

Dadin AC da qamshi me sanyaya zuciya tareda gajiyar dake taredasu yasasu samun bacci me Dadi da nutsuwa.

Qarfe takwas na safe qarar doorbell yasasu fitowa kowanne a shirye sbd zuwa asibiti.

Breakfast ne umme tayi odar daga wani restaurant data bincika online Dan haka Babu Bata lokaci sukaci Wanda suka iyaci Amatu da salamatu suda Basu taba fita waje ba.

Bayan sungama anty salamatu batareda kowa ya sataba ta tashi tahau gyaran koina tana gamawa me gidan na fitowa sanye cikin qananan Kaya hannunsa daukeda key din mota da wayarsa sai zuba qamshinsa yakeyi ba kowa a palon sai anty salamatun Dan haka suna gaisawa yace ta sanarwa Amatu Yana mota tafito da Muhammad.

Yana ficewa tayi daki ta tararda ita zaune tana hawaye bayan Gama wayarta dasu kawu da iyami da wayar umme da layinta na qasar sungama qara Mata zafi da maganganunsu akan auren.

Kallonta tayi ta fada Mata saqon MAHMOUD din ko kallon anty salamatun bataiba ta miqe ta dauki Muhammad ta fice zuciyarta a cunkushe.

Suna barin gidan umme takira yayarta Prof zainab zabeera tace a aiko driver yazo ya dauketa bazata zauna a gidanba sbd irin wannan auren na Amatu da MAHMOUD suna buqatan abarsu su kadai Dan asamu su fahimci juna su bawa auren dama sbd so take kafin sukoma komai ya daidaita tsakaninsu duk da ita sati biyu zatayi Takoma tabarsu anan din.

Anty salamatu dataga ummen zata tafi duk sai taji wani iri za'a barta ita kadai tsakiyar amaren duk da umme ta jaddada mata akan ta bada himma matuqa gurin taimakawa komai yatafi daidai tsakaninsu.

Bayan tafiyar ummen wanka tayi itama ta kwanta bacci bayan ta rufe dakinta.

A asibiti duk wasu formalities sun cike anyi komai an kwantarda Muhammad din yabiya komai da komai anan zasubarshi saidai su riqa zuwa dubasa shine qaidar asibitin, basubaro asibitin ba sai maraice inda yunwar cikinta ta isheta gashi asibitin da nisa sosai.

Ahanyarsu ta dawowa Babu me mgn saishi dayake amsa waya akai akai tanaji hadda anty zarah yayi waya.

Wanine ya damesa yanason ganinsa akan project dinsa na Nan Athens daya tsaya sbd wata babbar matsala Dole ya juya Kan motarsa ya nufi private joint dake cikin babban hotel din Athens din Yana daukar baqin mirror goggles dinsa ya sanya daidai lokacinda suka shigo gurin Wanda matakan tsaronsa da securities dinsa sukai yawa sbd girmansa da haduwarsa ga mutane sai abubuwan gabansu sukeyi.

Shine yafara fitowa Bayan yayi parking kafin yagama fitowa security ya bude Mata motar itama bataso fitaba sbd bataga dalilin zuwa da itaba Amma tsoron gurin da yanayin yanda gurin yake yasata fitowa ta tsaya gefensa yagama waya kafin suka nufi cikin gurin Yana sake amsa wata wayar.
##Mamuh#*_MQ 39_*
Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka tanada domin VIPs itadai komai na gurin bai burgeta ba ko dogon kallo bai ishetaba sbd damuwar dasuke Wanda sukazo gurin tare,
Sam ta rasa walwalar rayuwarta tun jiyan data samu sanin shine mijin da aka daura mata aure dashi.

Da sauri Jan baturen yataso Yana Masa sannu da zuwa tareda miqa Masa hannu sukai shaking Yana kallon fuskar Amatu dake daure ba alamar fara'a ko wata walwala ya maida kallonsa Kan MD din Yana sake washe baki zaiyi Magana MD din ya katsesa a gajarce Yana zama yace"
My wife.

Da sauri Mr Jeremy yasake kallonta Yana sake sakin fuska da murmushi yace"
Nice to meet you Mrs ZABEERA.

Kallonsa tayi ta Dan daga gira daya kadan alamar amsawa ta zauna nesa dasu tana kallon gurin ba cikin dadin raiba sukuma suka zauna tareda fiddo laptop ya kunna yafara nunawa MD din aikin dayakeson nuna Masa.

Sauraron Mr Jeremy yakeyi Yana Kuma fahimtar Abinda yake Masa bayani daidai hankalin nasa ya rabu Kashi biyu ne,
Waiter""ya furta ahankali cikin nutsuwa daidai lokacinda wani Waiter ya nufo VIP din.

Yes sir""Waiter din yafada cikin Yar rusunawa.

Amatu ya nunawa waiter din Yana cewa abata menu ta zaba Abinda take buqata.

Koda aka miqa Mata menu girgiza Kai kawai tayi batareda ta juyo ta kalli gefensu ba.

As you wish"yafada Yana dauke hankalinsa gabaki daya daga kanta ya maida Kan aikin gabansu.

Awa daya,awa biyu har uku taga aikin bana qarewa bane ga uwar yunwa kamar zata illatata ta waiwayo ta kallesa akaro na kusan hudu Amma ko inda take baya kallo kamar ma ya manta da ita gabaki daya..

Cikowa idanuwanta sukai kamar zatayi kuka sbd baqin ciki da takaicin yimasa magana takeji Amma haka ta miqe jiki a mace ta nufesu tana sassauta damuwarta sbd kada takaici yasa ta zuzzuduma Masa zagi ayi Mara kyau.

Jin mutum tsaye akansu yasa Mr Jeremy dagowa Yana ganinta ya washe baki Yana bata hakurin riqe Mata Miji da yayi itadai ko kallo bai ishetaba ba MAHMOUD din take kallo Wanda ko motsawa baiyiba bare ya juyo ya nuna yasan da mutum agurin
A hasale tace"
Ka maidani gida sbd Banga amfanin zamana anan dinba.
Chapter 51 · 0% Book details