← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 70

Sashe 59

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Bayan duhun magriba suka kammala Amatu ce ta jera abincin a dining kafin itama ta nufi bedroom dinta tayi sallah Bata sake wani wanka ba sbd ba wani jigatar dasukai a aikin tabari sai idan zata kwanta tayi wani.

Baidawoba sai dare sosai shiyasa Basu wani jirasa ba sukaci abincin su tana waya da USI harta bashi anty ZARAn suka gaisa Yana qara yimata godiya akan yanda ta fahimci auren Amatun da MAHMOUD tace Masa ba komai dai Amma har yanzu tunda akai auren haryanxu takasa zama tayi tunanin irin daukar dazatayiwa Amatun Wanda take ganin kamar ba yanzu ne lokacin dazata zauna yin wannan tunanin ba Kuma tana riqon Allah dakuma fatar kada tasamu wannan lokacin har abada sbd tana zama shaidan ne zai zauna shawarar da ita.

Tashi tayi ta shigewarta bayan tayiwa Amatun Saida safe itama Amatun miqewa tayi tattara dining din tasake jera Masa nashi abincin tana gamawa Yana shigowa a gajiya Dan haka Kai tsaye daki yanufa Yana cewa takai Masa abincin can wanka zai shiga.

Kadan ta dibar Masa tareda fruits data San yanason sha yawanci da daddare takai Masa tareda ruwa power drink dinsa
Tana zaune yagama ci ta kwashe kayan ta fita dasu ta sake gyarawa tareda fesa Masa peach blossom airfresh ta qara Masa sanyin AC kafin tashiga wanka anan dakin nasa qarshema shirt dinsa Fara tasanya wadda Tai mata yawa ta kwana da ita.

Washe gari tanada zuwa makaranta daqyar ta tashi ta shirya ko aikin abinci bata iya yiba hakanan suka fita bataci komaiba driving dinma cemasa tayi bazata iyaba very weak take jinta shiyasa yakaita da kansa Bayan yakaita wani private restaurant din dayafi so taci abinci kafin ya jiyeta makarantar yadawo gida.

Kamra Wasa da zazzabi ta yini ko makarantar da qyar ta lallabo tadawo gida tashige ko abinci Bata fito ci ba tace ta qoshi sbd kada abin yayi Mata yawa Dan tasan yau anty zarah ce zata Kwana gunsa.

Annushuwar da zarah take ciki bayason Bata Mata ita Dan haka bai nemi Amatun ba yadai Yi Mata text takuma yimasa reply.

Kwanan zarah biyu Amatu ta karbi girkin ta ringa Jin wani iri kamar bazata iya wannan rotating din ba shima daya lura da ita gudun tashin hankalinta da rigimarta yasa yaqi nuna yagane tana cikin damuwa.

Sannu ahankali yafara sabawa da canjen kwanan har tsawon wata daya ana haka saiga anty zarah tafara rashin lafiyar ciwon baya da zazzabin dare ga Amatu Kuma Kai yadauki zafi exams sukeyi Bata cika zamaba shima MAHMOUD din bai cika zamaba ga ciwo kadan kadan Yana cin anty zarah din basuda masaniya.

Ranar wata talata tadawo daga makaranta ta tararda anty zarah Bata Nan sai Bata damuba harsai dataga dare yayi sosai Bata dawoba takira wayarta Bata daga ba harso uku sai hankalinta ya tashi takira MAHMOUD din Yana dauka ko gaisuwa bata tsaya Masa ba tace"
Dady anty zarah fa Bata gida inata kiranta wayan ba'a dauka..

Numfashi ya sauke Kai tsaye yace"
Tana taredani muna Santorini batada lafiya.

Santorini?" Tafada cikeda mamaki tana qarawa da cewa''
Yaushe kadawo ne dahar kuka tafi yau din?

I came back because you're too careless ta Yaya Kuna tareda mutum Yana fama da rashin lafiya haka sosai Amma kice baki sani ba this is unbelievable...

Tayaya zangane tunda Bata fadaminba Kuma kullum ni lafiya nake ganinta Kuma karka manta ni makaranta nake zuwa tayaya kake....

Kashe wayar yayi Yana cewa''
Idan nagama Abinda yakawoni I will call you back.

Wayar tabi da kallo zuciyarta natafarfasa dama kwanakin kullum zuciyarta a kusa take batasan dalilina,
Take tadauki mugun zafi tana cewa ni zai datsewa waya cikin wulaqantawa sbd nace bansan ciwon anty zarah dinba??

To uban kowa da kowama tace Bata saniba ayi Abinda za'ayi din.
##mamuh#
Manage please.
##Mamuh#*_MQ 44_*
_INA MA
ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA?

WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA?

TO KU MATSO KUSA...

DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI..

DAYA NE TAMKAR DA DUBU..

YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._
_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021.

AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._
_WANDA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYA_ _*NIMCY LOVE*_ _TA RUBUTA._
Zaku iya payment dinku na wannan daddan labarin na *UNCLE NE* ta wannan numbrn dake rubuce
08119237616
******
Zama tayi a palon zuciyarta na wani irin tiririn takaici da baqin cikinsu su dukan sbd itama anty zarah din taga damane su hadu su Bata laifin daba nata ba Dan me daga abin arziki zai cillo Mata maganganunsa bacin Rai?

Miqewa tayi ta nufi kicin ta dauko ruwan sanyi Tasha ko zataji saukin zafin zuciyar Amma a banza qarshe tsoki taja tabar kicin din Takoma dakinta tayi kwanciyarta.

Da safe sanyawa gidan key tayi takuma qi ajiyewa a inda suke ajiye keys na gidan Dan idan waninsu ya dawo ta sakasu jaka ta tafiyarta makaranta tana ganin kiransa taqi dauka.

Bayan zuwanta makaranta da kusan awa shida Yayi Mata kusan Kira fiyeda biyar Taki dauka ganin hakan tasan zasu iya zuwa makarantar nemanta Dan haka tayiwa annah Magana ta tafiyarta tabar cikin makarantar.

Duk yanda sukaso ganinta su karbi keys na gidan taqi Bari Dan blocking dinsa ma tayi a qarshe anty zarah ma Kira daya tayi Mata Bata Bari tai Mata na biyu ba ta sanyata blacklist tana cewa''
Kun Manta waye Amatu idan shi baisaniba aike matarsa kinsan waye Amatu halina Babu inda yaje boye abuna nayi.

Sai dare tadawo gidan ga mamakinta sai Bata tarar dasuba a gidan suna jiran isowarta ta bude tashigewarta ta rufe dayake taciyo abincinta sai kawai tashige tayi wankanta ta kwanta sai bacci.

Washe gari ma haka ta tafi da keys ta wuni a school taqi dawowa da wuri sai dare Kuma still ma dai Babu ko inuwarsu.

Al'amari na Wasa Wasa saigashi ta share sati guda cur babusu Babu labarinsu Kuma ko awaya Basu taba maganaba duk inda zuciyarta takai ga girma ta 6aci Dan kuwa iya qonuwa ranta ya qonu wato ko ohon Mata tunda ta rufewa shida matarsa gida ko ohon Mata sunyi tafiyarsu sun bar Mata gidan ita ciwon idan yazo kanta tadade Bata mutu ba kenan.

Exams suka kammala ta daina fita gabaki daya abun duniya yazo ya sanyata gaba Babu Abinda ke sake sanyata baqin ciki irin yanda ita ko oho da ciwonta da lafiyarta tunda matarsa taso na taredashi ita Kuma tunda a tausaya Mata a taimaka Mata itada 'danta dasuke marayu shiyasa aka maqalo Masa ita ya aureta gashi tun yanzu ya nuna Mata iyakarta dashi biyan buqata tunda matarsa ta auren so ce agabansa.

Kukan datasha a Daren ranar saidaya sanyata zazzabi me qarfi ga ciwon Mara daya sanyota gaba ga zuciyarta baqin ciki kawai takeji daqyar taga safiyar ranar ta lallaba takai kanta asibiti duk da alamomi da yanda takeji tana tunanin ciki atareda ita zamtowarta gynecology student datake gab da zama likitar.

Lokacinda aka Bata result din she's 2month pregnant wani yanayi na tausayin rayuwarta tasamu kanta har Saida hawaye suka ciko idanuwanta suka sauko Kan kumatunta ta share ta kamo hanyar gida tana sakawa ranta tunanin komawa Nigeria Dan zamanta anan baida amfani gwara takomawarta inda akasan darajarta cikin iyayenta masu qaunarta idan yaso zabeera ta Dade Bata Yi abun kunyar anyi rabuwa acikintaba Amma rabuwa zatayi da MAHMOUD ZABEERA ta huta sbd yagama nuna Mata baisan darajartaba ko daya.

Ta waya tayi booking ticket din komawa Nigeria Amma Babu jirgin zuwa Nigeria a ranar saidai Nanda 4 days ba Bata lokaci tayi booking tayi payment tana isowa gida ta wuce daki ta zube Kan gado wani wahalallen bacci yayi gaba da ita.

Cikin bacci taji doorbell na qara sama sama ta bude idanuwanta dake cikeda baccin wahala takalli agogo taga yamma tayi sosai ta murgina ta tashi ta sauko gadon tashiga toilet ta wanko fuskarta tareda yafo qaramin gyale Kan doguwar rigar dake jikinta Mara hannu ta nufo qofar tana cewa''
Am coming.

Bude qofar tayi bama tareda tafara duba ko wayeba ta camera.

Da MAHMOUD ZABEERA tafaracin karo yayi fresh Abinsa cikin brown Armanis sai Zarah zabeera a gefensa itama tayi fresh haddasu manyan kumatu da Naman wuya sai qananun luggage dinsu ko kallon second daya Bata qarai musu ba ta juyowarta tana zame gyalenta ta nufi hanyar kicin tana receiving call din daya shigo wayarta batareda ta nuna tamaji sannu da zaman gidan da anty zarah ke mata ba tayi banxa da ita.

Bayanta anty zarah tabi da kallo tanajin rashin dadin yanda Amatun ta
kwashesu ta watsar ba musamman MAHMOUD dayake mijinsu ai ya cancanci sannu da zuwa.

Hanyar bedroom dinsa yayi Yana janyeda akwatinsa ita Kuma anty zarah kasa hkr tayi tabi Amatun kicin.

Tana shiga Amatun na qoqarin juyowa daga hada tea da biscuits din dazataci ta kalli fuskarta tana cewa''
Amatu lafiya Naga munshigo ko gaisuwa Kuma MD ma Naga ko sannu baki.....

Wani kallo Amatun tafara aiko Mata dashi kafin tabude Baki tace"
Anty Ina ganin girmanki kabari muje ahakan.

Wucewa tayi tabar anty zarah tanabinta da kallon mamaki da tsoro kafin itama tabar kicin din takama hanyar dakinta.

Sanin sundawo sunajin yunwa gasa anty zarah fitowa tai musu Abinda zasuci taje har dakin Amatu takirata Amma tayi bugun duniya ko cewa waye Amatun taqiyi bare tasa ran zata bude Mata ganin haka MAHMOUD yace tadawowarta tazo taci abinci Tasha maganin taje ta kwanta tana buqatar hutu,
Yasan masifa da rigimar dake cin Amatun shiyasa shima bazai shige mataba duk da yayi matuqar kewarta Amma rigimarta har fargaba take sakashi Sam bayason tashin hankali musamman yanxu da zarah Allah yabata Abinda takeso bayan shekarun jira masu tsayi,
Harga Allah shi baisaka damuwar rashin haihuwa aransa ba kodan yataso cikin kadaicinda har yake sha'awa da son rayuwa shikadai ne?

Sai lokacinda aka haifi Muhammad yaji son 'yaya yashigesa Amma dai still bai saka abin a Rai ba zarah ce ta qwallafa Rai ason haihuwa yanxu gashi Allah zai Bata sanin yanda ta dauki alamarin cikinta yasa yake tayata tattalawa da kulawa sbd taji farin ciki Amma wainnan kwanakin a Santorini shikadai yasan yanda yayi su day tunanin yanda Amatu take anan.
Chapter 59 · 0% Book details