← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 70

Sashe 67

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gidansu ta yini Daren ranarda zata koma canma Saida tayiwa su iyami kukan barin gida kafin yazo da daddare ya dauketa suka koma gida.

Washe gari Saida tayiwa kusan kowa dake cikin zabeera bankwana kafin suka wuce USI ne dakansa yakaisu airport suka wuce yadawo.

Sbd son cire Mata damuwar data sanyawa ranta yasa Basu koma Greece ba direct suka nufa US.

Wata irin rayuwar Jin Dadi da sakewa sukai a US tamkar turawan qasar Dan sai alokacin tasake sanin asalin waye MAHMOUD ZABEERA sbd wani bangarensa data gani na dabam wato Dan rayuwa.

Duk yanda zatai rayuwa bazata manta wainnan kwanakin dasukai a US ba sbd ya shayar da ita soyayyarda har abada bazata barta ba,
Ya sanyawa zuciyarta wani sabon maganadisun sonsa da qaunarsa.

Kwanansu takwas suka tattara suka nufi gida saidai Kuma kamar karsu dawo tunda suka dawo tafara zuwa school kwana biyu shikenan ciwon zazzabin dare ya sanyota gaba sunyi yawon asibitin hardai aka tabbatar musu da ciki ne Dan haka ba wani magani haka suketa fama duk wani aikinsa ya ajiyesu jinyar matarsa yake cikeda kulawa da tsananin qauna.

Ganin harya share kusan wata daya da rabi yasa ta daure ta bawa kanta qwarin ta nuna Masa ta warke sarai kafin yafara maganar komawa sbd tarin ayyuka da Kiran dayaketa faman Sha dazai tafi ita dakanta takaisa airport suka fito motar ya kamo hannunta ya matso da ita cikinsa Yana kallonta da fararen idanuwansa dake bayyana newarta tun kafin ya tafi ya bude baki ahankali Yana shafo cikinta cikin laushin murya yace"
I will miss you wife.

Dan dago qafarta tayi sbd yafita tsayi takai bakinta Kan nasa ta Dora ahankali ta zura Harshenta tabashi wani irin kiss tana kallon cikin idanuwansa tace"
I will miss you More.

Rungumeta yayi tareda sauke ajiyar zuciya Yana shafa Bayanta yace"
I love you.

Qanqamesa tayi kalmarsa na sake kashe jikinta.

Sun jima ahakan kafin lokacin tafiyarsu yayi yabata kiss a goshi ya wuce tana kallonsa harya shige ta juya jiki amace ta shiga mota tabar airport din tana Jin kewarsa kamar tabisa.
##Mamuh#*_MQ 50_*
https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg
Please subscribe to our YouTube channel
Tana komawa gida kwantawa tayi tun anan Palo tana waya da anty salamatu akan maganar zuwan datakeson tayi suna gamawa anan palon bacci ya dauketa.

Bacci me nauyi tayi sai kusan yamma ta farka ta tashi zaune tana Dan dafe kanta dayayi Mata nauyi sbd baccin datai dakuma Dan ciwon dayake Mata.

Miqewa tayi ta nufi daki Kai tsaye toilet ta wuce tayo wanka dan jikinta yasaki tayo alwala tafito ta sanya riga da wando me Fadi ta sanya dogon hijab tahau dadduma ta tayarda sallah.

Bayan tagama sallar kicin taje ta hado tea da biscuits tazo ta zauna Tasha tana kallon agogo tasan zuwa yanzu ya Isa sauka Amma bazata kiraba zata Bari idan yahuta yasamu lokaci zai kirata.

Washe gari da wuri ta wuce school sbd akwai asibitin dazasuje daga school din,
Tunda safe shine ya tayarda ita daga bacci suketa waya Saida zata Shiga wanka suka aje tana Shirin fitowa yasake kiranta harta Isa school suna waya har Anty zarah yabata suka gaisa tayi Mata ya jiki daga Nan daqyar tasamu yayi hanging wayar ta maida hankali Kan Abinda yakawota,
Sai yamma likis ta dawo gida amatuqar gajiye Dan haka ko abinci Bata tsaya Ci ba wanka tayi ta kwanta baccin gajiya da daddare data tashi bayan tayi komai tasake komawa ta kwanta suna waya ta rikice Masa akan sai anturo Mata anty salamatu wlh bazata iya rayuwa ita kadaiba.

Dole ya amince wa buqatarta yaje yasamu kawu da kansa yayi Masa roqon zuwan anty salamatun wannan karon hadda iyami ya roqa taje tadubota tunda batada lafiya zataji dadin ganinta sosai.

Kawun bedai cemasa ya amince da zuwan iyaminba tukuna Amma dai ita salamatun zataje itama bazata jimaba sbd maganar neman aurenta da Andi ya nemawa alhaji qarami Wanda yake autansu Modibbo basason doguwar bidia kamar a taqaice suke son ayi auren.

Da kansa yasa akawa anty salamatun shirye shiryen tafiya sbd kusan shima a matse yake dataje din yasamu me kula Masa da Amatun Dan gabaki daya hankalinsa ba'a natse yakeba Jin yake kamar yaje da kansa yayi jinyar abarsa Amma Kuma ayanzu zarah dake kusan haihuwa tafi buqatarsa shiyasa ma duk wasu tafiye tafiyensa ya rage saita haihu sbd Bata kulawar datake buqata.

Duk yanda yaso anty salamatu ta Isa cikin kwanaki qalilan bai yiyuba sai bayan sati biyu da maganar ta tafi tareda USI dazaiyi 6month program acan aikuwa Nan suka dasa sabuwar rayuwa a Greece hakan kuwa ba qaramin nutsuwa yabawa MD din ba Dan dama shineya tsayawa USI akan zuwa Greece din yin program dinsa acan infact ma shine yadauki nauyin komai sbd kawai Amatun tasamu Yan uwanta atareda ita hakan ne kawai zai bashi cikakkiyar nutsuwa sbd yanayin datake ciki.

Zaman USI agarin tareda zuwan anty salamatu ya kawarda duk wata damuwarta da rage Mata kewarsa sosai Dan haka saita kwantarda hankalinta take karatunta cikin kwanciyar hankali da bada himma musamman yanzu da cikinta yafara girma Dan kusan wata hudu cikin na biyar kenan ita Kuma zarah ayanzu tana gab da shiga cikin watan haihuwarta shiyasa Koda yazo gurinsu bai wani dadeba yakoma yasake barinta cikin sabuwar kewarsa Dan har wata qaramar tafiya sukai dayazo din.

Zaune suke apalo tana duba wasu textbook na school anty salamatu Kuma tana yanka Mata gwaibar data siyo daga wani superstore ahanayarta ta dawowa school suna Dan fira sama sama sbd Rabin hankalinta nakan books din wayarta tayi ringing tun daga Kan kalar ringtone din tasan waye me Kiran ta Kai hannu ta dauki wayar tana sake wata qaramar ajiyar zuciyar son mijin nata t
a daga cikin kasalalliyar murya tace"
AMATULLAH's husband..

Duk da Yana cikin wani yanayi na damuwa Saida yadan murmusa hartaji sautin murmushin ta cikin wayar ahankali tace"
Barka da yamma.

Barka wife,
Hw are you and my baby?

Ya anty salamatu hope duk Kuna lafiya?

Yes lafiyanmu kalau it's just that we're missing you badly.

Numfashi ya sauke Wanda yasata Dan gyara zama tana ajiye books din jikinta cikin sauti me nutsuwa tace"
Lafiya kuwa?

You sound worried.

Dafe goshinsa yayi cikin yanayi na damuwa yace"
Zarah na asibiti tun safe she can't deliver by her self itama aiki za'a yi Mata.

Faduwa gabanta yayi cikin tsoro da damuwar itama zatazo wajen ga tausayin anty zarah din sai jikinta yayi sanyi da rawar murya tace"
Yanxu tun cikin dare anty zarah take cikin wannan halin Amma baka fadaminba dady sai yanxu?

Wlh na tausaya Mata yanxu kenan suna ZABEERA specialist?

Yes yau sukeson ayi aikin sbd qarfinta harya qare nagaji da ganinta cikin wannan halin.

Kwantar da murya tayi cikin tausayawa anty zarah din da tausayinsa shi kansa sbd tana iya Jin irin damuwar dayake ciki a muryarsa tafara qoqarin kwantar Masa da hankali tana sake bashi qwarin gwiwa akan Allah yasa ayi aikin lafiya akuma dace.

Bayan sungama waya tana fadawa anty salamatu tana lalubo numbern umman zarah din ta Danna kiranta,
Tana dauka ta gaidata cikin ladabi ta Dora da cewa''
Umma Ashe anty zarah haihuwar tazo wlh bansaniba sai yanzu dady yake fadamin tun safe Kuna asibiti.

Amatu antynki Kam tanajin jiki kitayata da addua Allah yarabasu da bbyn lafiya.

Inshallah Allah lafiya kalau zasu rabu
Allah yasa ayi aikin cikin sa'a
Nasan bazata iya mgn yanzu ba Ina Mata sannu zuwa anjima zansake Kira naji Inshallah.

Shikenan Amatu angode Allah yayi albarka.

Amin umma ngd sai anjima.

Aje wayar tayi tana kasa cigaba da karatun ta shiga damuwa da tunani tasake Kiran MD din takuma kwantar Masa da hankali.

Haka Takoma sukuku tunda sukai Magana takasa sukuni sbd hadda tsoro tsoron zuwan tata haihuwar yake sake shigarta takasa zama sai kiransu takeyi akai akai tana tambaya har lokacinda aka shiga aikin da zarah Amatun kiransa takeyi tana Kiran umman zarah din harsaida umman tace Mata"
Amatu ki kwantarda hankalinki tunda kema bake kadaiceba kada ki daga hankalinki wata matsalar ta taso Kuma ku rabawa mijinku hankali Kashi biyu.

Ana fitowa sallar magriba aka fito da lafiyayyan jaririn zarah cikin qoshin lfy sai kuka yakeyi cikin qoshin lfy aka wuce dashi sukai duk aune unen dasuke buqata kafin aka shiryasa cikin fararen overall masu kauri nurse ta fito dashi fuskarta daukeda murmushi ta nufo inda MAHMOUD yake tareda mahaifinsa Modibbo daya iso asibitin alokacin tareda umme da Haj maryam.

Modibbo aka miqawashi ya karbesa cikin farin cikin ganin jikinsa 'da na farko ga MAHMOUD dinsa.

Addua yayiwa jaririn kafin ya miqawa MAHMOUD da idanuwansa suke Kan fuskar yaron Wanda tunda nurse tafito dashi kafin yashigo hannunsa zuciyarsa tagama cika da soyayyar 'dansa.

Zarah tabasa farin cikin rayuwarsa,
Ada baidamu da samun 'dan kansaba Amma tun Bayan haihuwar Muhammad zuciyarsa ta cika dason Tara zuriar me yawa kodan ya Gina tashi zuriar sbd fita rayuwar kadaici.

Addua yayiwa yaron tareda Masa huduba yakirasa da sunan Muhammad DAHEER Modibbo.

Godiya Modibbon yayi cikin Jin dadin takwaran da akai Masa.

Nan kowa yafara karban yaron ana Yaba kyawunsa da kamannin babansa daya Dan dauko.

Saida aka gama murnan samun Modibbo aka koma murnar samun nasarar aikin da akayi umman zarah kuwa farin cikinta a bayyane yake ganin yanda kowa ke murnar haihuwar 'yarta.

Babban tashin hankalin dasuka shiga na samun mugun labari daga bakin likitoci shine ba lallai zarah din tasake haihuwa ba sbd rashin qwarin mahaifarta data fashe kafin Cs din.

Hankalin ummanta yatashi sosai hakama da duk Wanda yake gurin Saida jikinsu yayi sanyi Amma ganin MAHMOUD dakansa ya dauki qaddarar ya dauki juriya yasa kowa ya hkr suka buge da tarairayar zarah wadda tayi kukan wannan mugun labarin MAHMOUD na aikin lallashinta cikin nuna Mata tsananin damuwarsa Dole qarshe ta dangana tabarwa Allah akan hakan shine qila mafi alkhairi.

Amatu data sake Kira kusan karo na biyar kenan bayan haihuwar sai yanzu tasamu damar Magana da anty zarah din Tai Mata barka tana sake Mata sannu daga Nan suka Dan gaggaisa da jamaar dake asibitin ta kashe wayarta.
Chapter 67 · 0% Book details