← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 70

Sashe 23

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas Amatu sbd Allah nakesonki tun ranar da kikazo Nan,
Kinmin laifi Amma ban riqeki a raiba sbd sanin ajizanci irin na 'dan Adam,
A da Ina zaune dake amatsayin matar Dr dakuma Amana da aka bani Amma daga yanxu zan zauna dakene amatsayin qanwa da muka fito ciki 'daya.

Zamewa Amatun tayi da sauri tana share hawayenta ta saki qaramar dariya tanason kawar da kukan anty zarah din tace"
Anty da gaske?

'daga Mata Kai tayi tana share hawayenta itama.

Anty zarah karfa wata Rana kice aa alqawari kikamin munzama kamar ciki daya muka fiyo.

Dariya antyn tayi har lokacin hawayenta Basu Gama tsayawaba tace"
Amatu nayi alqawari ba canzawa
Amma kema kinsan kinyi alqawari zakiban babynki idan kin haihu"" tafada cikin tsokanar Amatun.

Da sauri ta kalla Dr dayayi mutuwar zaune da tsananin so,qauna, tausayi tareda ganin girman Amatun
Ta dafe cikinta tana cewa''
Dr kaji anty zarah Wai zamu Bata babyn.

Yana kallonta cikin tsananin shauqi yace"
Idan har kin amince zaki Bata ni Kuma idan har nine dadynsa nayi alqawari da hannuna zanbatashi.

Murmushi yasaki tana shafa cikinta ahankali tace"
Inama inada cikin wlh Dana baki anty zarah.

Qasa yayi da murya daidai kunnenta yace"
Karki damu watanni kadan ne yarage mufita wannan dilemma din zamu bawa antynki da MD baby.

Kallonsa tayi da sauri tana boye dariyarta Dan batasan yajitaba ganin yakasa daina murmushi yasata miqewa da sauri tayi hanyar dining tana cewa''
Anty zarah mijinki yagama ci muzo muyi namu party din a dining Dan wlh har yunwar jiya saina fanshe abuta.

Murmushi sukeyi suna Mamakinta ganin tabbas Bata aje al'amarin duniya a ranta sbd karta wahalar da kanta a banza sbd me gatane ke tsayawa kuka da damuwa Dan a lallashesa suda basuda ko daya sunyi futo na fito da kuka da damuwa tareda abin kunya Sam baya damunsu.
##Mamuh#
ZAFAFA BIYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/26, 7:46 PM] Zafafa: *_MQ 18_*
_Mg_
Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya Mata qwarin gwiwaba amma Dole yace Mata MD yariga yafice tun dazu so karma su jirasa suyi abinsu shima bai tsayaba sbd yau umme tace taredashi zatayi breakfast ya fice ya nufi can tun kafin rashin zuwansa ya shafi Amatu Dan Babu ranarda Bata tsinewa ranar data Fara haduwa da amatun.

Shiru anty zarah din tayi a sanyaye Jin MD baya gidan ya fice.

Dafa hannunta dake zuba chips Amatu tayi tana murmushi tace"
Anty karki damu zai hakura inshallah,
Nice nayi laifin Kuma nice zan gyara
Inshallah Allah saina sa Rabin ranki ya yafe Miki Dan haka ki daina damuwa Amatu zatai Miki handling komai.

Qasa tayi da murya Yana cewa''
Saina Fara sashi yasan dawa yakeyi kafin Nan,
Shine jiya haddasa Dr ya durqusa agabansa Yana wani daddaure fuska Yana Shan qamshi to zaisan yasa Dr da anty zarah damuwa indai nice Amatu saiya sani.

Me kike cewa Amahh.

Cika baki tayi da chips da kwai tana cewa''
Bance komaiba anty zarah
Zauna kici abincinki karki Hana kanki abinci sbd soyayya.

Zama tayi tana murmushi tace"
Amah samun Wanda kakeso yanada Dadi hardai idan shima Yana sinks,
Kinga kamar ke da Dr.

Tea ta kwankwada tana cewa''
Yanxu ni da Dr son juna muke??

Eh Mana gashinan a fili Muna gani musamman Dr bayada damuwa sai Taki,
Farin cikinki da walwalarki sune nasa
Kina gani yanda baya iya dauke Ido a kanki koyaushe kece first priority dinsa.

To ni anty banajin wainnan abubuwan da Kika fada nadai San acikin maza banida kamar su uku shi da kawu da usi,
Yanda kakejin usi hakan nakejin Dr zan iya komai Dan farin cikinsa da kula dashi.

Bakyajin faduwar gaba duk lokacinda Kika jiyo muryarsa kafin ya iso gareki??

Sake cika bakinta da soyayyan qwai tayi tana cewa''
Banaji Amma Kinga Rabin ranki Dana jiyo ko qamshin turaran Nan Masa me qarfi gabana faduwa yake sbd masifarsa.

Tsit anty zarah tayi tana kallonta kafin tasaki murmushi tana cewa''
Shikenan karki damu zankoya Miki yanda zakiso Dr matuqa kamar yanda yake sonki.

Anty zarah inason nazama wacce zata bawa Dr farin ciki da dukkanin wata soyayya..

Bazaki iya basa farin ciki ba sai kin basa dukkanin zuciyarki da soyayyarki.

Zanbasa sbd shine kadai a duniya cikin maza ya cancanci zuciyata
Koda zuciyata batasan meye so ba zanbada ita saiya koyar da ita da kansa.

Taso bawa maganganun amatu nutsuwa Amma ta watsar sbd Amatun kanta batasan abubuwan datake fadaba Dan haka ba amfanin nazarinsu.

Suna Gama cin abincin Palo suka dawo anty zarah ta zauna tana waya da ummanta ita Kuma Amatu dakinta Takoma Dan watsa ruwa.

Wanka tayi ta sanya riga da skirt na atampa coffee kala ta tsaya gaban madubi Yana duba kanta tana sauke ajiyar zuciya sbd ganin Masha Allah yanxu ita da kanta sha'awar kanta takeyi sbd mulmulewa da jikinta yayi da hutu da kayan gyara jiki da fata.

Akan cikinta dake shafe kamar bashi yake daukar uban kayan Dadi da abincin datake zuba Masa ba ta shafa ahankali tana gyara tsayuwa
Hakanan kawai yanxu tsananin son cikinta ya shigeta duk da tasan ana Magana ne akan Abinda Babu kwata kwata saidai ita zancen yashigeta musamman idan tayi tunanin ganin babyn a hannunta tana Masa Wasa Yana murmushi irin na Dr.

Dankwalin kayan jikinta ta zare tareda nadawa ta saka cikin rigarta daidai cikinta saita saki rigarta cikin yataso ya zauna daidai tareda qarawa tsayinta kyau sai tayi kamar sabuwar amarya me qaramin ciki
Batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana shafa cikin saiga anty zarah tashiga tana cewa''
Amatu baki gama Shirin bane gurin Modibbo zamuje gaisuwa tunda kikazo bakije kin gaishesaba hakama umme sune fa iyayen mijinki....

Tsayawa tayi da maganar lokacinda idonta ya sauka kan 'dan matashin cikin na jikin Amatun take dukkanin farin ciki da Jin Dadinta ya fito fili ta qaraso da sauri tana cewa''
Kinga Amatu yanxu cikinki yafito sbd kinsaka riga da skirt dogayen rigunan Nan boye cikin sukeyi gaba daya..

Kallonta Amatu keyi tana murmushin ganin yanda ganin fitowar cikin kawai yasaka anty zarah wannan farin cikin to ranar da aka haifesa fa ta daukesa a hannunta.

Anty zarah Inshallah kema zaki dauki ciki ki haifi 'yayan kanki Dana Rabin ranki.

Allah yasa Amatu
Sbd babbar adduata a yanxu shine samun haihuwa tareda MD sbd haihuwa ce kawai zanyi na tabbatarda MD ZABEERA yazama nawa,nasamu muhalli acikin zuciyarsa da rayuwarsa.

Gyale coffee ta yafa akanta suka fito zuwa sashen Modibbo,
Kamar Wasa saigasu sun 'dan jima agurinsa sbd yanda Amatun ta zage tana basa labarin qanxon kurege na aurensu da Dr daya sake tambayarta,
Hakanan sai ta 'dan shiga ransa sbd Jin yanda sukayi gwagwarmaya itada mahaifiyata baba Jamila.

Daganan sashen umme suka nufa Kai tsaye Amatu nata sake bude idanuwanta da zabeera din koina kallo takeyi cikin burgewa tana sake tantance asalin girma da wadatar Zabeera din.

Kwankwasa qatuwar qofar shiga palon umme sukayi
Tsawon mintuna hudu kafin me aikinta tazo ta bude musu suka shigo Amatu na santin kallon qayataccen palon da qamshi tareda sanyin AC suka cikasa.

Zama zukayi jiran saukowarta saidai shiru shiru Bata saukoba Nan Zarah da aka Kira tayi baquwa ta tafi tabar Amatu na zaman jira.

Saidata shafe awa kusan biyu a zaune kafin ummen ta fito cikin shigar alfarma tana waya Kuma dagaji da Dr take wayar sbd yanda take amsawa da Dan sauran haushinsa dabai Gama sakinta ba
Saidata shigo tsakiyar palon ta lurada Amatu dake zaune tana kallo tana Kira ruwan lemu da aka kawo Mata hankalinta kwance Dan wuce guri da volume bai ishetaba ta dauko remote taqara tana shigaba da kallonta remote din a hannunta sai murmushin Abinda take kalla takeyi.

Ko sallama da Khalil din batayi ba a wayar ta kashe tana cewa"
Uban waye zaune har cikin palona?

Juyowa Amatu tayi tana aje cup din hannunta da murmushi Kan fuskarta tace"
Haj Mama nice Amatu matar khalil nasan zuwa yanzu kinmantani.

Cikin quluwa ta daka Mata tsawa tana cewa"
Uwar matar khalil din ce ba matarsa ba
Zoki fice kafin nasa kiyi nadamar zuwa Nan.

Matsowa Amatu tayi da sauri gabanta tana cewa''
Umme Dan Allah kiyi hkr da Abinda yafaru ba laifina bane bakuma laifin Dr bane qaddarane Kuma nidai na karba qaddarar nan da hannu biyu ta zama matar Dr wlh inaso.....

Ganin tafara loosing patience dinta batason tayiwa Amatun komai yanzu sbd tanadin datai Mata tukuna shiyasata fixgota a wulaqance ta jeho ta waje daidai isowar Nuratu wajen ta tareta daga faduwar dazatai saidata dago taga Amatu ce aikuwa ta saketa amatun tayi muguwar faduwa akan hannunta na dama take ta samu kurdewar qashi tasaki wani razanannen ihu tana qoqarin tashi Amma takasa dafawa sbd azaba take wani zufa ya karyo Mata ta kalli Nuratu a masife tace"
Ita waccan data jeho ni nasan dalilinta kekuwa da kikaimin haka meye naki dalilin??

Dalilina shine cikin jikinki""tafada cikin tsananin tsana da takaicin ganin cikin jikin Amatun.

Miqewa tayi da qyar tana dafe hannun cikin azaba tace"
To ke meye ruwanki da cikina kokuwa kema cikin 'yan koren uwar Mijina ce sbd dai bakida alama da 'yan zabeera daga Ina malama???

Baqin ciki maganar Amatun tai Mata tana sake quluwa tace"
Ni ba matsiyaciya bace kamar ki wadda Babu Wanda yakeda tabbacin ba karuwa bace Khalil ya fada tarkonta ta auresa sbd kudi
Wama yakeda tabbacin wannan cikin nasane Kona wani qa........

Wani gigitaccen Mari ya sauka akan fuskar Nuratun dayasa gefen bakinta 'dan fashewa
Ta dago da sauri tace"
Ni Kika Mara???

Zuciya data gama ciyota kukan kura tayi tai Kan Amatun zata mareta aka riqe hannunta ta bayanta ta fizge zata Kuma Yi Kan Amatun ya sake riqe hannunta tareda zagayo gabanta kyakkyawar fuskarsa ta jinin zabeera tana fidda sheqi
Tace"
SALMAN????

Sakeni,
wlh saina koyawa wannan mummunar karuwar hankali..

Saukar wani Marin ne a fuskarta yasata qarasa zaucewa tana qwacewa tace"
Wlh yau sainaga ubanda ya tsaya wannan tinkiyar...
Chapter 23 · 0% Book details