← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 70

Sashe 39

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kashe wayar yayi ya ajiye Yana sake karanta sunan dake rubuce 6aro 6aro akan hoton katin KHALIL DAHEER ZABEERA da AMATULLAH K SALEH.
sake dauke Kai yayi yana lumshe ido tareda sauke ajiyar zuciya ya juya yabar gaban labtop din.
_NIGERIA_
da kanta ta shirya tsaf Babu Wanda yasani ta fito suka fita da salman zuwa zabeera mansion.

A sashen Andi sukai parking tafito ahankali tana kallon koina komai na dawo Mata sabo tana tuno yanda tabar anty zarah dinta cikin kuka da damuwa take taji idanuwanta sun ciko da hawaye Bata damu da tsaidaduba Saida suka gangaro tasaka hannu ta gogesu ta nufi qofar shiga palon Andi din ta tura tashiga da sallama dama Salman ya tabbatar Mata da a irin wannan lokacin Modibbo na gurin Andi.

Modibbo ne yafara gabeta ya zuba Mata idanuwansa masu kwarjini da Khalil da MD suka dauko ta qaraso ahankali ta zube qasa gabansu sai alokacin Andi ya dago ya lura da waye.

Cikin tsananin biyayya da nuna damuwarta a fili tace"
Ina miqo gaisuwata ga Andi da Modibbo tareda neman afuwar babban kuskuren Dana aikata Wanda ya shafi 'da mafi biyayya da gujewa zuciyarku.

Kallon mamakin rashin tsoronta da gwarin gwiwarta suke Mata su duka din ta sauke Kai cikin nutsuwa da girmamawa tace"
Wallahi tallahi Dr khalil zabeera baitaba aikata laifin da kuke tunanin ya aikataba koma wane irine,
Taimako ya hadani da Dr khalil Kuma shine yasa yayita ajiyata acikin zabeera,
Ni marainiya ce kuma Yar bola kamar yanda kowa ke fada Amma Kuma banice nakai kaina bolarba harnayi rayuwa acikinta na tashi acikin
Rayuwa da jarabawar rayuwace takaini wadda itace tabaku girma da matsayi tareda sunan dakuke ganin yafi Dan Adam daraja,
Nayi rayuwar maraici da tozarci irinku masu arziki Baku dubemu ba kuka taimaka Mana saidai maigadin makarantane Wanda yake karban dubu bakwai a wata ya taimakemu,
Nayi rayuwar almajiranci Ina matsayin mace sbd kawai na rayu,
Nayi rayuwar wahala da qasqanci duk Dan sbd na rayu,
Munkwana da yunwa muntashi acikinta,
Lokacinda yaranku da jikokinku suke karatu mu bara mukeyi alokacin sbd muci,
Da kaina na koyi yanda zanyi yaqi da maza na qwaci kaina daga sharrinsu tun inada qananun shekaru
Shin nayi dukkanin wannan ne sbd nazama karuwa a rayuwa????

Nice na zabarwa kaina yin sata amaimakon karuwanci Dan kawai na rayu sbd sata Zan iya rokon me Abu ya yafemun wata Rana Amma Zina fa???

Dr khalil zabeera shine mutum me arziki na farko daya shigo rayuwarmu,
Yakawo Mana walwala da farin ciki a zukatanmu,
Talakawan bangarenmu wainda Dr khalil zabeera yakawo farin ciki akan fuskokinmu da rayuwarmu basa qirguwa,
Meyasa mutum me zuciya irinta Khalil maimakon ayi alfahari dashi za'ayi fushi dashi?

Shin Kuna tunanin ladar aikin Khalil kawai Bata Isa takawo qarin haske da walwala acikin zabeera ba??

'yayan da Allah yabaku dukkaninsu amanace agurinku Allah zaitambayeku alaqarku dasu idan da akwai cutatarwa,
'yayanku ne Amma Kuna gudanar da rayuwarsu kamarta dabbobinku kokuma bayinku,
Wasunsu da dama a tauye suke basa rayuwar farin ciki,
Zaman auren Dole da qunci sukeyi duk sbd bin umarni da qaidojinku,
Shin haramun ne neman farin ciki a wani gurin kokuwa musulunci ne ya hana?

Shi mutunci da girma Allah ne yake badawa Kuma shiya Baku
Idan Allah yabaku suna duk Abinda wani Dan Adam zaiyi bazai Bata hakanba Koda kuwa me zaiyi.,
Nazo zabeera ne sbd son kudina dakuma rashin sanin ciwon kaina Amma sbd tseratar da mutuncinku yasa ya karbi laifi da bacin sunan da baisan lokacinda aka hadosaba,
Wallahi niba karuwa bace,
Bantaba aikata zinaba,
Bansan ta Yaya ake aikataba,
Aikin gidajen abinci danayi nayine Dan neman halak Dina Wanda haryanxu Ina alfahari da hakan sbd Allah bai bani matacciyar zuciya ba.

Dagowa tayi da idanuwanta dasukai jajir ta ajiye katin Daurin aurensu cikin sanyin jiki tace"
Babban burinsa shine aurena yakawoni gabanku Dan neman yafiyarku da gafararku nikuma babban burin danakeson cika masa shine bashi kaina amatsayin mata dakuma sasantawarsa daku iyayensa,
Hawaye masu tsananin zafi suka gangaro Mata cikin daci da damuwa tace"
Dan Allah Ina roqan gafarar ku yafe Masa kodan kasancewarsa 'da me biyayya da gudun zuciyarku a baya,
Ku basa farin cikin dabai taba samu daga garekuba tun haihuwarsa....

Umme dake bayanta tuntuni a tsaye batasan lokacinda tafashe da kukaba tana sake Jin qaunar Amatu ta qaraso gabansu Modibbon ta zube itama cikin kuka tace"
Andi Dan Allah ku yafewa khalil kubarsa ya aureta wlh dukkaninsu ba laifinsu bane nice me laifin sbd nice na kawo Amatu zabeera da wata manufarda rashin wadataccen ilimina yabani.

Zayyane musu komai tayi sukai tsit Babu me motsi musamman Andi dashi maganganunsa Amatu ne sukafi shigarsa,
Shin dukkanin yawancin 'yayansu rayuwar kunci sukeyi sbd gudun zuciyarsu???

Tabbas tunda yake tsawon rayuwarsa Babu Wanda yataba kallonsa yafada Masa haqiqanin gaskia sai yau yaringa qanqanuwa daya Isa haihuwar ubanta koma kakanta ta kallesa tafada Masa quncin dayake saka 'yaya da jikokinsa shekaru wa shekaru.

Modibbo Kam dama tuni Amatu ta Dade dashiga ransa bazai iya nunawa bane sbd bacin ran Andi Amma tuni yajima da sanin yarinyace me fadar gskia batareda tsoro ko shakkaba.

Miqewa tayi ahankali ta juya ta fice tana share hawayenta daketa fita da gudu ta fada mota suka bar zabeera.

Kwance yake yau kwana biyu kenan ciwonsa nacinsa harya Fara cin qarfinsa ko fita daqyar yakeyi sai dare cikin duhu yake zuwa gidansu kawu sbd kada agano halinda yake ciki magungunsa yasiyo dasu inhaler Amma Sam kamar basa Masa aiki sbd kullum sanyi sake shigarsa yakeyi a gidan.

Yau laraba saura kwana daya Daurin aurensu Amma abin yaci qarfinsa tuni aka gano baida lafiya sosai sbd Koda Ibrahim yaje gidan tuni ya Dade da fita hayyacinsa hankali tashe ya kwashesa sai asibiti.

A asibiti Koda aka karbesa numfashinsa yayi nisa sosai cikin gaggawa akai emergency dashi ana qoqarin saka Masa oxygen.

Su kawu Ibrahim din yafara fadawa kafin yakira salman yafada Masa cikin qanqanin lokaci duk suka halarto asibitin hankalinsu duk atashe.

Kallo daya Amatu tayi Masa hankalinta yayi mummunan tashi sbd lokaci daya sanyi ya kumburasa
Numfashinsa Sam kwata kwata Babu saidai oxygen dinne ke janyo Masa ahankali idanuwansa a rufe fuskarsa tayi haske hakama bakinsa yayi haske sosai ya bushe.

Hawaye ne suka kufce Mata ta saki siririn kuka ahankali tana cewa''
Meyasa zaka boye bakada lafiya harsaida abin yayi tsanani haka?

Zaman rashin hankalin kurame sukeyi a asibitin daga ita har kawu da iyami duk suna asibitin da salman sai ummensa dasu Nuratu dasuka iso kowa cikin tashin hankali bama kamar umme datasha kuka idanuwanta sukai jajir.

Sunanan zaune har magriba saiga anty zarah da MD ZABEERA sun iso tana ganin anty zarah suka tsaya kallon juna cikin tsananin kewa da qaunar juna tazo da gudu tafada jikinta tana fashewa da sabon kukan datake ta riqewa tuntuni na ganin har lokacin sai Abinda yayi gaba ajikin nasa.

MD ne dakansa yaje yayi mgn da likitocin suka sake yimasa bayanin sanyine yayi mugun shigarsa Wanda yasa gaba daya jijiyoyin huhun Jan numfashinsa sun daskare ya tayarda ciwonsa gaba daya harya basa attack Sam numfashinsa yaqi dawowa ta oxygen dinma alamarin sai ahankali.

Tsorone yashigesa akaro na farko rayuwarsa
Dawowa yayi dakinda Khalil din yake ya tsaya akansa Yana kallonsa yaji zuciyarsa na neman karyewa da sauri ya juya fice.

Anan ta kwana asibitin itada ummensa da iyami har gari ya waye be farkaba zuwa lokacin Kam ko mgn basa iyayi da junansu sbd damuwa zazzaune kawai suke suna rarraba idanuwansu dasuka kode sukai zuru zuru.

Da yamma tayo alwalar magriba tazo gefensa ta tayarda sallah tayi tagama tana cikin addua taga kamar ya motsa hannunsa kadan ko shafa adduar batayiba ta zabura ta miqe sai taga idanuwansa a bude sunyi fari tas dasu cikin tsananin farin ciki ta fada kansa ta rungumesa tana sakin hawayen farin ciki.

Umme data fito toilet din dakin tana ganin haka tayo kansu da gudu har sanyin ruwan qafarta na zameta itama fadawa tayi kansa ta rungumesa
Ya lumshe ido ganinsu su biyun ba qaramin farin ciki yasashi ba yasake lumshe ido cikin azabar ciwo yanason motsawa Amma sun dannesa
MD daya shigo yayi gyaran murya itace tafara juyowa sukai Ido biyu tayi saurin dauke Kai tana maido da kallonta Kan Khalil cikin tsananin farin ciki tace"
Dr Dan Allah karka sake rufe idonka.

Qarasowa yayi ahankali Yana kallon fuskar Khalil din yau farin cikinsa dai Kam ya bayyana
Shima Khalil din shi yake kallo fuskarsa nason bayyana farin cikin ganinsa Amma azabar ciwo ya hana.

Cikin sautin murya me taushi yace"
Kun sakar Masa nauyi da yawa inaga.

Da sauri dukkaninsu suka dagasa kafin suyi wata Magana saiga Andi da Modibbo tareda alhaji qarami sun shigo salman yakawosu take umme da amatun suka saki hawayen farin ciki suna kallon fuskar Khalil din da idanuwansa suka nuna zallar farin ciki ganinsa hawaye masu dumi suka gangaro ta gefen idonsa
Andi da kansa ya matso gefen gadon ya dafa kansa yasaka tissue ya share Masa Yana jinjina Masa Kai.

Salman da MD ne suka tayar dashi zaune amatu ta hado ruwan zafi da towel suka gyara Masa jikinsa tareda Sanya masa shirt Mara nauyi aka basa tea yasha kadan har lokacin da oxygen a hancinsa Kuma har lokacin bai iya mgn sbd bai iya jan dogon numfashi.

Kafin dare yadan warware ba laifi sbd Yana Dan magana ahankali tareda zuwa toilet idan ankamasa.

Da kawu yaso daga Daurin auren a gobe Amma Andi yace abarshi kada a daga tunda anriga anyi sanarwa.

Da daddaren ranar duk yanda ta nace hanata kwana asibitin akayi akace Takoma gida Salman zai kwana dashi tunda washe garine Daurin auren Dole ta koma bayan tayi Masa bankwana yabiya da Ido cikin kewarta tun Bata wuce dinba.

A gida duk wani hidimar al'ada sunyi abinsu hatta lalle anyi Mata a blue fox anty zarah takaita akayo Mata tareda gyaran Kai dana jiki Daurin auren kawai suke jira a goben akaita zabeera.

Tunda ta kwanta mafarkin Dr kawai takeyi sai kawai ta tashi tayo alwala tazo ta tayarda sallar nafila.
Chapter 39 · 0% Book details