← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 70

Sashe 33

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya sukeyi su biyu Banda salman daya wuce ya nufi motarsa yafita zabeera ahankali kowannensu shiru Babu me mgn dama sun Saba haka suke koyaushe idan suna tare saisun jima shiru kafin su Fara mgn Wanda MD ne me wannan halayyar shikuma Dr khalil Yana girmama kowane irin Hali da MD ya zabawa kansa da rayuwarsa.

Tsayawa yayi ahankali batareda ya juyo ya kalli khalil dinba yace"
Bansan wane mataki ka dauki wannan alamarin ba Amma ya kamata kasan kana saka kanka cikin hadari along with her..

'dan shiru yayi kafin ya juyo ya kalli khalil din cikin wani irin yanayi yace"
Atleast kayi tunanin Hali da Abinda zata fuskanta kafin kasata a irin wannan tight spot din sbd yanxu ku duka Kuna situation dinda only God can help so kafin komai ya fita hannunka kasan Abinda kakeyi ka dawo daidai,the truth doesn't cost anything but a lie could cost you everything.

Kallonsa Khalil yayi tareda sauke ajiyar zuciya cikin damuwa yace"
Bansaniba ko kasan Abinda nake qoqarin boyewa Amma bazaka iya fahimtar dalilina nayin hakan ba sbd komai yazone alokacinda banyi tsammaninsaba Babu mafita bayan wadda na dauka a wancan lokacin da yanzu ma..

Denying the truth doesn't change the fact cewa ka dauki hanya Mara bullewa,
Ka zauna kayi tunani zaka samu wata mafitar wannan batayi ba.

Yana Gama fadar haka ya wuce gaba batareda ya juyoba yayi hanyar sashensa.

Shiru Dr khalil zabeera yayi yana tunanin maganganun MAHMOUD din wainda suka sakashi zurfin tunanin sbd tabbas qaryarsu takusa qarewa wadda idan bai nemo mfitaba asiri ya tonu to daga Ummensa har Amatu dashima suna cikin matsalarne,
Babban burinsa daya dawo dashi shine maganar auren Amatun tukuna sbd duk wasu kayayakin aure na akwati ya siyosu yazo dasu saitin akwatinsa cif ya hado kayan aurensa Wanda ko gidan bai kawosu ba daga airport gidansu kawu suka Fara ajiyesu kafin su qaraso gida.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin shima yabi Bayan MD din zuwa ganin Amatu da tun Yana gurin umme take kiransa yaqi dauka sbd kada farin cikin ummen ya gushe.
##Mamuh#
Kuyi hkr kuyi manage da wannan
hutun weekend naje dakuma mura dake damuna
[4/6, 9:36 PM] Zafafa: *_MQ 26_*
Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi ganin duk tazama so serious Wanda Sam kowa yasan ba halinta bane tafi sabawa da hayaniya shiyasa duk inda take to hayaniya na gurin.,
Ana bude qofar palon atare dukkaninsu suka kalla qofar shigowar kowacce fuskarta daukeda murmushin yiwa Dr khalil din maraba Musamman Amatun da murmushinta na yau ya banbanta Dana kullum sbd yau sauran zuciyar Khalil takeson qarasa sacewa sbd ta zamo Tata ita kadai shiyasa yau komai nasa na musamman ne agareta saidai sabanin ganin fuskar Dr khalil zabeera a cikin idanuwan MAHMOUD ZABEERA idanuwanta suka sauka murmushinta me sanyi da tsada akan fuskarsa yafara sauka gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauya cikeda mamaki da fargaba da sanyin jiki..

Tsayawa yayi kallonsu fuskar na bayyanarda mamakinsa daba'a cika ganewaba ganin yanda dukkansu suka waiwayo suka zuba Masa Ido kowacce fuskarta daukeda murmushin daya mugun daukar hankalinsa da sakashi wasi wasin mamakinsu musamman Amatu datafi bayyanarda murmushinta da dukkanin farin cikinta dabai taba ganiba,
Ganin Ahankali Amatu ta dauke idanuwanta dake cikin nasa tana kallon bayansa murmushinta da farin cikinta fiyeda na farko Yana dawowa yasashi dawowa MD dinsa ya sauke boyayyan numfashinda Babu Wanda yaji ya Fara takowa ahankali idanuwansa na sauyawa cikin wani boyayyan yanayin dayake ciki sbd sai alokacin ya fahimci Khalil ne keda wannan murmushi da farin cikin,
Zama yayi Kan couch din dakinsa Yana rintse idanuwansa tareda yamutsa kansa yanajin wani irin zafi na ratsa dukkanin jikinsa
Take kuwa zufa ya kakkaryo Masa Tako ina bayan ga kukan AC Nan yanaji yasan a kunne yake....

Zarah ya tuno da itama taketa washe baki tana murmushi to idan ita waccar tayi Dan Yana sunan mijinta to itafa???

Jin kansa ya dauki zafi Yana neman saukewa zarah laifin sai kawai ya miqe ya fada toilet yayo wanka yayi clearing mind dinsa ya shirya cikin kayan bacci ya dauki laptop yafara wani aiki Yana basar da tunanin komai da kowama.

Dr khalil kuwa duk yanda yake tunanin Amatu takai cikin ransa sai yanzu yake gane ta wuce Nan sbd wannan murmushin datake jifarsa dashi yagama hargitsa Masa Kai da tunani.,
Zama yayi bayan sungama gaisawa da zarah ta wuce tabasu guri ya juyo suna fuskantar juna Yana kallonta cikin kulawa yace"
Hw are you AMATULLAH???

Zuba Masa idanuwanta tayi har lokacin murmushinta bai daina fitaba tace"
Nayi fushi ka koma na barwa Nuratu.

Wani irin Dadi yaji ya kamasa me sanyi cikin nutsuwarsa yace"
Kishi kikeyi ita tafara tarbona???

Harara ta sakar Masa tana cewa''
Zanyi maka kuka idan kasakemin maganarta.

Kallonta yayi Yana cewa''
Ok tom yanzu duk wannan adon sbd zandawo akayisa?

To Meyesa baki shafamin Dan lipstick dinnan naku danaga ana sakawaba Nuratu tasaka ita......

Miqewa tayi a fusace tayi dakinta Yana kiranta ko waiwayosa batayiba tana shiga gaban mudubi ta wuce Kai tsaye
Ta dauki janbaki hot red tashafa a bakinta tana kallon madubin saikuma taga tayi kyau saita dauki turare taqara fesawa tadawo palon tana kallon yanayin dayake kallonta fuskarsa na bayyanarda farin ciki sosai sai taji farin ciki yakamata sbd ganin ta kyautata Masa shiyasama take nuna kishin Nuratu sbd ganin hakan na sanyasa farin ciki.

Cake din datayi da fruit drink dominsa taje ta dauko takawo Masa Nan suka Fara fira cikin nutsuwarsa yake cin cake din duk da a qoshe yake Amma sbd itace tayi da kanta yakeci cikin alfahari.

Sai guraren qarfe goma yabar part din ta rakosa har waje kafin tadawo ciki ta wuce dakinta tanajin farin ciki kamar bazata iya bacci ba yau din.

Washe gari ataredasu Dr khalil din yayi breakfast kafin suka fita tare harda Dr Salman daya Fara aiki asibitin Dr khalil kafin ya kammala shirye shiryen sa danshi ba anan qasar yakeson aikiba.

Gidansu kawu suka Fara zuwa tunda ta Isa gidan kowa ke Mata wani irin kallon burgewa suna tayata murna Wanda yasata sakin baki tana kallonsu cikin mamaki.
bakin dakin iyami tagan akwatina a jere tsaf su maman junior sai washe baki sukeyi suna budewa iyami ma yau bakin Nan har kunne sai annashuwarta takeyi tana sake bubbudewa su maman junior kayan suna gani suna shewa.
tsayawa tayi tana kallonsu cikeda mamaki kafin ta juyo ta kalli su Dr khalil dasuka tsaya qofar shigowa suna Magana da kawu Wanda shima yau harda saka babbar rigar farar shadda wadda itama Dr khalil ne ya dinko mishi su kusan kala bakwai.

Sake juyowa tayi gurinsu iyami da suke Mata barka da zuwa Maman junior kuwa rawa tahau Yi tana janyota tana waqarsu ta yarbawa tana cewa''
Amatunmu tasamu mijinda zai Bata farin ciki da suna me girma na mutunci.

Kallon rashin fahimta tayi Mata gabanta na mummunan faduwa ta qwace da sauri zatayi Magana iyami datasan Abinda zata iya fada tayi saurin cewa''
Kayan Dr khalil ne jiya da daddare aka kawo.

Kallon iyamin tayi da sauri tareda juyawa ta kalli inda suke Magana da kawu Yana Dan sato kallon inda suke Dan yaga reaction dinta..

Wani irin farin ciki Mara misaltuwa ya shigeta da sauri ta rungume maman junior tana cewa''
Alhamdulillah ya Allah.

Dariyar farin ciki iyami ta sake tana sake sakawa Khalil din albarka sbd duk iya bincike kawu yayi akansa Kuma sun Dade da yaba nutsuwarsa da halayensa sbd a wannan zamanin basu taba haduwa da yaro me nutsuwa ba kamar Khalil din,
Shiyasa Babu wani dogon janye janye na al'adu kawu yabasa auren Amatun kawai waliyan Khalil din yake jira idan sun daidaice da khalil din sbd Khalil ya sanar dashi akwai Yar hayaniya a zuriar tasu idan ta lafa zasu zo idan Kuma akasin hakan ne ya amince asamu waliyai a daura musu aure.

Zama tayi gefen iyami ta bude kayan tsaf taga abinta tana sake Jin inama gobene ranar auren ayi kowama ya huta.

Ciki su Dr khalil din suka qaraso suka gaida iyami tareda gaisawa da sauran mutanen gidan suka koma waje suna jiran Amatun tagama ganin kayan su fito.

Kusan awa biyu ta Bata kafin ta fito suka wuce asibiti inda ya ajiyeta a office dinsa suka Shiga meeting tayi zamanta tareda miqewa a kujerarsa tana game a wayarsa daya barmata wadda kyakkyawan hotonta yake shimfide lock screen dinsa na ummensa Kuma a main screen dinsa sai hakan yasaka jikinta yin sanyi sbd a rayuwar Khalil yanzu duk Wanda yasansa yasan itada ummensa sune sanyin zuciyarsa da idaniyarsa Amma Kuma gashi Sam ko inuwa daya basa zama a taqaicema ummen Babu Wanda ta tsana a rayuwa kamarta ita Kuma Babu wadda take ganin ta rainawa wayo kamarta
sai kawai taji Bata girmama soyayyar Dr khalil dinba.

Sai qarfe uku suka baro asibiti sai kawai suka wuce gurin cin abinci a 5star daganan ma gurin shopping suka wuce sai gab da magrib suka shigo zabeera
Kai tsaye sashen ummensa ya nufa tana ganin sunyi parking bakin flat din tayi saurin kallonsa shima ita ya kalla Yana cewa''
Inason ganin Mata biyu masu mahimmanci gareni sun zama daya wannan shine babban fatana,
Amatu please kiyi hkr da duk Abinda umme ke Miki ki Bata dama kigani tanada zuciya me kyau,
Abinda nasani shine duk Abinda nakeso ummina na sonshi bare ke datasan Ina Miki tsaftatacciyar so Wanda bazan iya dainawaba
Dan haka nasan zata soki wata Rana ko Ina Raye ko bana Raye nasan wata Rana saita soki kamar yanda takesona,so please AMATULLAH ki qaunaceta ki kulamin da ita I promise you wata Rana zata daina tsangwamanki zata qaunaceki kamar yanda take qaunata.

Wani irin sanyi jikinta yayi sosai saitaji kunyarsa ta kamata ta dago a sanyaye ta kallesa ya da yayi saitaji kamar Bata girmama soyayyarsa ba tunda takasa girmama mahaifiyarsa.,
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin sanyi tace"
Inshallah Zan kiyaye zancenka daga yanxu zanyi iya qoqarina gurin kyautata Mata.

Numfashi ya sauke ahankali yace"
Thank you AMATULLAH.
Chapter 33 · 0% Book details