← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 70

Sashe 14

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Jamila ce agaba amatu na bayanta fuskarta rufe da doguwar hijab dinda tasaka fuskarta da idanuwanta a kumbure sosai sunyi jajir tsabar aboniki dasuka Sha kamar wadda tayi wata biyu tana kuka.

Tsit sukayi kowa palon na aika musu da kallon mamaki da jiran bayani Amma sai qif qif baba Jamila keyi da idanuwanta tana sunkuyar da Kai.

Alhaji qarami ne ya kalleta tareda kallon amatun dake bayanta kafin ya kalli qafafunsu har zuwa zamansu ya gyara murya yace"
Malama Yaya dai??

Lafiya??

Daga Ina??

Saurin zubewa qasa tayi tareda sauke kanta qasa cikin rawar murya tanason fashewa da kuka tace"
Ranka ya Dade adalci nazo nemarwa 'yata...,
Kowa kallonta yayi wasu Kam Kai tsaye kallon mahaukaciya suke Mata mamakinsuma yanda akayi tashigo zabeera harta iso Nan din.

Cikin mamaki alhaji qarami ya miqe ya qaraso gurinta ya tsaya Yana cewa'"
Malama adalci kike nema ai banan ake zuwaba,
Mu Nan Kinga Muna wani taro ne me mahimmanci kinyi batan hanyane kije security zasu nuna Miki qofar fita......

Girgiza Kai tayi wannan karon tana fashewa da kuka Mai shiga zuciya tana bubbuga kanta.

Yanxu Kam mamakinsu yafara cirewa sai fargaba
Kamar daga sama taji saukar muryar dattijo me ran qarfe,
Muryar data saka 'yan hanjinta kadawa Dan tsoro da firgita da wani irin amo yace"
Idan da kanki a ha
yyacinki kikazo Nan kifadi Abinda yakawoki kokuma ki hadu da hukuncin kutse da datse mahimmin Abu acikin zabeera.

Jan hanci tayi tana shage hawayenta dasukaqi tsayawa murya na rawa tace"
Ranka ya dade 'yatace gatanan cikine a jikinta......

Cikin tsawa me qarfi alhaji qarami ya e"
To Nan asibitine ko gidan aurenta dazaki......

Uban cikin Yana Nan"""ta katsesa cikin rawar murya tana sake bulbulo da ruwan hawaye.

Atake gurin yayi tsit kamar ruwa ya cinyesu musamman Modibbo daya gyara zama Yana kallon matar da kyau kafin ya dago ya kalli amatu dake tsaye har lokacin tana matso hawaye cikin hijab.

Kallon amatu yayi cikin wani irin amo yace"
Ke yarinya bude fuskarki kiyi bayaninda mahaifiyarki keson fada saidai duk Abinda zaki fada kifara tunanin a inda kike.

Qarar wayar Dr khalil ce ta katse maganar Modibbo wadda tasa kowa juyowa ya kallesa da sauri ya Danna wayar tareda miqewa ya fita da sauri Yana magana qasa qasa sbd daga asibitinsane ake Kiran wasu takardune da ake buqata emergency yace suzo su karba Nan gida.

Harabar gidan ya nufa gurin motarsa yana tareda budewa ya dauko takardun cikin Burnet din motar ya nufi bakin gate ya fita Dan miqawa Dr ashir.

Sama sama yayi Masa bayanin takardun sbd hankalinsa dake Kan 'yan jaridar da har lokacin suna gurin take yaji yakasa samun nutsuwa da hakan,
Meke Shirin faruwane?

'yan jarida a qofar zabeera,
Ga Kuma wasu baqi aciki suna maganar anyiwa 'yarta ciki.....

Da matsala yafada Yana sallamar Dr ashir ya juya ciki da sauri Yana tunanin Dole da akwai inda matsala take,
Me zaisa wannan matar su gayyato 'yan jarida??anshirya hakan ne Dan idan baa karbi cikin bane kokuma me??

Something is definitely fishy mezaisa tazo da masu jarida ita Bata damu da mutuncin 'yarta bane idan Yan jaridar suka watsa to kodai tanada wani manufa be???

Oh no.." yafada da sauri tareda yin ciki da sauri haryana hadawa da gudu gudu...

Karo yayi da mutum Wanda yasashi yin baya zai Fadi USI yayi saurin rikosa Yana cewa'"
Da sauri Dr khalil din ya dago Ya kalli Usin mamakinsa a bayyane Dan komai nasa ya nuna mamakin cikin sauri yace"
Usman?

Kaine anan?

Me kakeyi anan??

Kallonsa Usman yayi Yace"
Aiki amatu tasamu anan......

Saurin gintse bakinsa yayi sbd shaf ya manta Abinda ya kawosun.,
Ya shafo kansa Yana waskewa yace"
Dr kaima me kakeyi anan din???

Kafa Masa Ido Dr khalil yayi ba Wasa a fuskarsa yace"
Wane aiki ne amatu tasamu anan din??

Ina amatun take????

Shiru yayi Yana shafa Kai Yana qoqarin hado qarya Dr khalil ya katsesa da cewa"
Ina amatun?

Rasa yanda zaiyi yayi yace"
Tana ciki tashiga da wata Mata.....

Wattt???

Yafada da qarfi cikin firgici da tashin hankali yace"
Meke faruwa?

Me sukaje yi?

Infact meya kawoku Nan din nakeson ji""zuwa lokacin yafara hasala yace"
Kuma wlh karka kuskura kamin qarya.

Kame kame usi yafara Yana neman yanda zaiyi saidai gskia zai fadawa Dr khalil idan yaso qila shi zai taimakesa ya shawo Masa Kan amatun kar tayi Abinda zatayin
Kallonsa yayi tareda jansa gefe yace"
Dr Dan Allah kayi alqawarin zaka taimaki amatu bazakayi Abinda zai jefata hadariba Dan Allah kayi wannan alqawarin.

Cikin zaquwa Dr khalil din yace"
Koba Dan alqawarinka ba bazan taba Bari amatu tashiga hadariba zan tsaya Mata ako Inane just tell me.

Cikin fargaba Usin yafada Masa yanda amatun tayi da hajiya aisha saidai ya boye Masa da yardar amatun nuna masa yayi kamar tursasata hajiyar tayi sbd amatun ta daukar Mata kudi.

Tsit yayi kamar ruwa ya cinyesa
Har wani duhu duhu idanuwansa ke gani sbd tsananin tsoro da firgicin zancen,
Ita umme ko tunanin hadarinda zata jefa 'yar mutane batayi da kantama tunda komai jimawa dai wataran gaskia zata fito,
Idan ita amatu hankalinta bai Kai ba ita meyasa zatayi hakan??

Qarin tashin hankalinsa MAHMOUD za'ayiwa wannan mummunar 6ata sunan
Haqqinsa bazai bar umme ba hattasu yayanta sai haqqin MAHMOUD ya shafesu Dan haka bazai Bari tadau wannan alhakinba dazai ja Mata azaba gaban Allah hakama bazai Bari rayuwar 'dan uwansa ta lalace ba hakama amatu rayuwarta nacikin mugun hadari.....

Da sauri ya kalli usi yace"
Usman Yi sauri kabar Nan katafi gida namaka alqawarin dawo da amatu Babu Abinda zai sameta maza katafi karka fadawa kawu komai..

Da gudu ya nufi ciki yayi hanyar palon Yana adduar Allah yasa amatun Bata bude fuskartaba Yana Isa ya fada palon da qarfi daidai lokacinda amatun tariga ta bayyana fuskarta akace ta fada cikin waye ajikinta,meye alaqarsu dame cikin?

Bude baki tayi hannuwanta da qafafunta na rawa zuciyarta na harbawa da qarfi zatayi magana tana kallon inda MAHMOUD ke zaune har lokacin idanuwansa lumshe Kuma duk yana jin abindake faruwa kawai dai ba huruminsa bane shiyasa ko hankali bai badaba,
cikin wani irin sauri Dr khalil ya dako tsalle ya fado tsakiyar palon tareda cewa"
Allah ya taimaki Modibbo nine.

Wattttt????umme tafada da sauri tareda miqewa tsaye tareda haj Maryam
Nuratu ma da antynsa juwairiyya duk miqewa sukayi cikin tsananin firgici
Take palon yadauki hayaniya cikin rasa abin fada alhaji qarami yace kowa yatafi antashi meeting.

Hayaniya aka Fara saidai yanayin Modibbo yasa kowa yin tsit suka Fara sulalewa suna ficewa.

Kaf kowa ya fice Banda uwayensu maza da 'yannansu maza sai iyaye mata hatta MAHMOUD na gurin bai fitaba lokacinda yaji muryar khalil amatsayin me cikin yasashi bude Ido ahankali ya sauke Kan amatu dake gefen Khalil din tana kallonsa cikeda mamakin daga Inda ya fado.

Kallonsa takeyi tanason Kiran sunansa Amma ganin yanayinsa ta tana hango tsananin 6acin Rai da takaicinda yake ciki,
Idan har da khalil da MAHMOUD yayan hajiya mama ne kamar yanda tafada mata to acikinsu duk Wanda tace shine me cikin ta cecesa daga hawa mulkinda zaa salwantar da rayuwarsa to kenan duk dayane koba komai zatafi farin cikin kubutarda Dr khalil sbd kurkinsa akansu.

Da hanzari umme ta qaraso gabansa ta kalli cikin idanuwansa cikin 6acin Rai tace"
Me kake fada?

Maza maza fice wannan ba Abinda ya shafeka bane...ba magana nake maka ba""ta fada cikin tsawa da firgici.

Gyaran murya Modibbo yayi akaron farko bayan shock din daya samu na daqiqu ya kalli khalil tareda kallon amatu dake kallon Khalil din cikin rashin Jin Dadi qunci da bacin ran datake hangowa cikin idonsa.

Khalilu ta Yaya kazama uban cikin jikin yarinyar na???

Hadiye wani yawu me mugun daci yayi sbd dai gskia bazata faduba Dan idan yafada gski umminsa da amatu duk suna cikin hadari Dan umminsa har zamanta cikin zabeera saiya ware.

Rintse ido yayi ya budesu suna kadawa jajir take jijiyoyin kansa suka firfito sbd qarya ba halinsa bane bare wannan qaryar datafi kowace muni.

Muna sauraronka Khalil kafin fushinmu ya sauka akanka kayi bayani"cewar alhaji qarami.

Sauke Kai yayi daga kallonda Modibbo ya tsaresa dashi me girgiza jarumtarsa yace"
Mun jima muna qaunar juna tsawon shekaru uku
Nasan bazaa Bari na aurotaba shine mukaje wani guri aka daura Mana aure.....tassssssss
Umme tasakar Masa wani gigitaccen Marinda Saida ya zube Kan gwiwoyinsa tareda sauke Kai.

Cakumo amatu tayi cikin tsananin 6acin Rai tace"
Modibbo ba gskia yake fadaba Khalil bazai taba aikata wannan qazamin aikinba wannan ita zata fada ubanda ya Mata ciki Amma badai Khalil ba....hannu ta daga zata kaiwa amatun Modibbo ya daka Mata tsawa da cewa"
Aishatu ki dawo hankalinki ciki ne ajikinta kada hannunki ya sauka jikinta..

Ke matso fili ki fada Mana Abinda yafada gskia ne kokuwa??

Fitowa tayi daga bayan Khalil din tana kallon idanuwan umme dake fitowa da ruwa tace"
Eh gskia ya fada.

A Ina kuka hadu??

A asibitinsa.

Shekara nawa yanxu da auren??

Rawar murya tafara tana neman dufewa tace"
Daya.

Aikuwa take kowa yaqarin tsit cikin tashin hankali.
##mamuh#
______________
KUNA BU
ATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES
IN BOOKS
IN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon hazi
an marubanku
an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da sa
o ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai bu
atar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntu
ar wa
an nan Numbers 0903
5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks
in kana bu
ata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi.
Chapter 14 · 0% Book details