← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 70

Sashe 63

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon inda yake kalla tayi numfashinta nason sauya fita ta hanyar qara sauri tana dannewa ta kalli gurin tagansa zaune Kan kujerun harabar gidan tareda kawu
Kawu sai zuba yake Masa Amma shi idanuwansa na kanta ya zuba Mata su cikin yanayi da kasalar da ganinta ya sakar Masa idanuwansa na bayyanarwa sbd wani lumshewa dasukeson Yi Amma Basu lumshe din ba.

Bugawa ZUCIYARTA ke Naman Yi sbd wani irin kyau da sheqi tareda qwarjinin da Allah ya horewa wannan bawa nasa MAHMOUD DAHEER ZABEERA ta dauke idonta ahankali tareda juyawa ta shige ciki batareda tabari kawu ya gansu ba Dan yanzu zai Fara kawo Mata zantukan tazo ga mijinta.

Suna shiga daki tashige ta tube saidatai wanka kafin tayi sallar magrib da yanzu aka gama ta sanya doguwar riga mara nauyi me kamar boubou ta fito tana tambayar abinci ta nufi kicin ta dauko zobon da iyami keyi tana sawa a fridge sbd baqi dakuma kawu dakeson ruwa me kala ta fito tana Shan zobon saiga USI yashigo yace taje palon kawu yana namanta.

Can ya wuce Kai tsaye sbd ta daina Jin hayaniyar Muhammad tasan sun tafi ne tunda dare yafara Yi takumasan babansa bai Bari ana fitar dare dashi.

Tana shiga da Muhammad din tafara cin karo kwance yayi bacci jikin kawu
tana ganin hakan saita daure fuskarta taqi kallon dayan gefen Dan taji ajikinta MD ne agurin.

Kallon kawu tayi muryarta na daidaituwa cikin nutsuwa tace"
Kawu likita yace kana kirana.

Eh mijinki ne gashinan zaune yazo tun dazu bakwanan yanata zaman jira.

Miqewa kawun yayi daukeda Muhammad ya fice yakaiwa iyami dakinta ya fita zuwa gurin abokanan hirarsu ta dare a qofar masallaci.

Kawun na fita ta nufi qofar fita itama batareda ta kalli inda yake ba ko qofar Bata qarasa isaba taji yariqo hannunta tareda dawo da ita baya har bayanta na gugar qirjinsa ya bude baki da muryarsa me taushi yace"
Why?

Meyasa Zaki taho a irin yanayin da kike ciki Kuma ki dauki fushi Bayan nine yakamata na dauki fushin tunda kin baro batareda sanina ba.

Juyowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta zame hannuwansa cikin nata daya riqe ta wuce tabarshi tsaye Yana kallonta.

Qofar data fice yabi da kallo Yana Dan rintse idonsa ya sauke numfashi Yana komawa zaune dama yasan Amatu bazata sauko acikin sauqi ba.

Hakanan ya fito ya wuce batareda kowama yasaniba Yana Isa gida ko abincin dare daqyar yaci sbd kada Zarah daya lura kamar itama tafara iya Magana akan Abu tayi Magana bazai iya daukar wani stress Bayan Wanda yake daukaba yanzu aikin dayayi a Sudan duk tsawon kwanakin baiwani bada hankali yayi Abinda yakaisa ba sbd har lokacin komai Kiran dazaiyiwa Amatu baya samunta,
Wanka yayi ya kwanta kawai dama akwai gajiya a taredashi sbd yau din ya dawo.

Washe gari ma taso fita Amma iyami ta hanata sbd cewar mijinta na gari ba Maganar yawo yanzu Dan haka Dole ta zauna gida tana kallo su Anty salamatu hadda iyamin suka tafi gurin sunan qanwar maman basiru suka barta.

Tana zaune Palo tana kallo sama sama bayan la'asar har bacci ya Dan Fara daukarta taji qamshin imperial majesty na shiga hancinta kobata juyoba tasan shine zai shigo palon ta tashi zata shige daki tun bai qarasa shigowaba tana kaiwa tsakiyar palon Yana shigowa da sallamar cikin sauti me taushi ya tsaya gabanta Yana kallon fuskarta dake daure tam sai yaji jikinsa yayi sanyi ya rasa kalmar furtawa ya riqo hannunta cikin nasa idanuwansa na kanta a gajiye da wannan fitinar yace"
Wannan shirun naki is killing me
Kiyi mgn Koda zakiyi fada ne I'm ready Zan dauka infact I won't say a word indai har Zaki sauko.

Bata kallesaba ta kwace hannunta a hankali kafin tace"
Zan kwanta Kuma bakowa a gidan nikadai ce.

Tunda yadawo gida zarah ta rasa gane kansa abun duniya ya isheta ga cikinta nada damuwa an hanata sakawa Rai damuwa Amma wlh bazata iya rashin damuwarba sbd Abinda take gani shi ake Kira da asalin damuwar,
Yau satinsa guda cif da dawowa Amma yarasa gane Kan Amatun tun abin na iya tsakaninsu har gidansu Amatun dai kowa yasan Abinda yake faruwa kawu dayaji hadda 6arin ciki tayi sai baiji dadin yanda MAHMOUD din yabari tadawo ba ita kadai cikin yanayi irin wannan Amma zamansa uba saiya ringa bin Amatun da rarrashi har gwara iyami na Dan Mata zafi wani lokacin Amma duk da hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar tarewa idan yayi mgn da Amatu.

Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar.

Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa
Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan wayar Yana wani gurin..

Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya.

Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace"
Thank you and you look great.

Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan juyowa ya kalleta Yakuma cewa''
Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news.

Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake taredashi tana iya hango damuwa ataredashi.

Numfashi takuma saukewa akaro na biyu kafin ta Kai hannunta ta Dora Kan nasa ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasukai laushi sbd rashin isashen bacci ta bude baki ahankali tace"
I'm really sorry MD sbd tun farko daban Bari ta tahoba da duk haka bai faruba,
Laifina ne na yarda Kuma Inshallah idan munhadu Zan fahimtar da ita hakan but for now idan akwai ta inda Zan taimakawa alamarin let me know please..

Shiru yayi idanuwansa a rufe na mintuna kafin ya budesu ahankali ya juyo ya kalleta na mintuna Yana NAZARIN yanayinta ya bude baki yace"
She respects you fiyeda komai sbd tanajin nauyinki fiyeda komai because of the old relationship that you two shared Wanda deep down haryanxu tana Miki kallon yayarta.

Kallonsa take da dukkanin girman idanuwanta bugun zuciyarta na sauyawa sbd Fara tammahar inda zancensa keson dosa muryarta na rawa tace"
To ta Yaya hakan zai.....

Ki tayani fahimtar da ita Abinda nakeson tagane please.

Saura qiris zuciyarta ta buga daga cikin qirjinta ta da Abinda ya fada din,
Wani dishi dishi take neman Fara gani sbd bugawar da zuciyarta keyi da sauri,
Wani irin zafi yafara taso Mata tun daga cikin qasan zuciyarta Yana mamaye zuciyar Tata take taji tsanarsa nason darsuwa a zuciyarta akaro na farko a rayuwarta Amma ta yakice hakan tareda kallonsa cikin Ido ta bude baki Kai tsaye tace"
For the first time yau MAHMOUD ZABEERA ka farkar Dani daga wani babban kuskuren danake ciki,
Miqewa tsaye tayi ta kallesa cikin muryar dake bayyanarda jarumtarta tace"
Zuciya ce a kirqina ba dutse ba dan haka inaga ko dan Abinda yake cikina na cancanci wata karramawar Amma duk da hakan tunda ka buqata Zanyi mgn da ita Amma bisaga sharadin idan Bata dawoba Nima nagama zaman gadin gangar jikinka sbd inason ayau kasan sonka zuciyata ya Kama bawai zuciyar ya cinye ba.

Zaiyi mgn tabar gurin batareda ta tsaya sauraronsa ba ta nufi dakinta ta shige tareda rufowa ta Isa bakin gado ta zauna tana son fashewa da kuka Amma Abinda takeji yafi qarfin kukan
sai kawai ta miqe ta zari doguwar hijab da keys din motarta ta fice tanajin idan Bata bar gidanba komai zai iya faruwa.

Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo.

Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana kallonta tace"
Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda cikin baida qwari.

Tashi zaune tayi tana share hawayenta ta zare hijabin jikinta ta dago ta kalli umman dake Mata kallon jiran jin dalilin wannan kukan.
Chapter 63 · 0% Book details