← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 70

Sashe 68

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon babynta takeyi idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki Dana damuwa taji an zauna gefenta tareda zagayeta da hannunsa har ita har Modibbon Yana kallon Modibbo dake baccinsa cikin nutsuwa ya shafa fuskarsa tareda maido kallonsa Kan fuskarta Yana riqo hannunta cikin kulawa da nutsuwa yace"
Zarah ki daina damuwa akan Abinda ba Allah ne yafadaba,
Banson Baki empty hopes Amma Dan ance bazaki sake haihuwa ba ba lallai bazaki sake haihuwar ba sbd ba fadan Allah bane ki dauki qaddara ki rungumeta Allah nason bayinsa masu yadda da qaddara.

Dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar ruwan hawaye tayi ta kallesa cikin tunani daban daban Wanda ya kunshi irin hope din data hangowa kanta na samun soyayyarsa ta hanyar Tara zuria me albarka dashi sbd gano burinsa da qaunarsa tason Tara Yara.

Kamar yasan Abinda take Tunani ta ganin irin kallon datake Masa ya rungumeta ahankali tareda shafa Bayanta cikin murya me taushi yace"
Zarah yanzu ke ba matata ce kawaiba ke uwar 'yayana ce,
Ayanzu kin riga kinzama wani sashe na rayuwata da zuciyata,
Samun haihuwa a tsakani wani alamarine me girma Dan kuwa kinriga kinzama tamkar jagoran zuriar dazan Tara a gaba ko ba naki yayanba,
A da ke zarah ce matar MAHMOUD yanzu Kuma ke zarah ce matar MAHMOUD uwargidansa Kuma uwar Dan haka ki cire kowane irin tsoro ne kikasa acikin ranki sbd mi MAHMOUD DAHEER ZABEERA Ina baki tabbacin mutuwace kawai zata cireki daga rayuwata.

Wani irin kuka tasaki tana sake qanqamesa zuciyarta na cika da farin ciki da nutsuwar zancensa....

Ahaka ummanta tashigo tagansu Dadi yasake kamata ta karba Modibbon ta fita dashi sbd su iyami dasu maman junior dasukazo ganinsa.

Kwanansu shida a asibitin aka sallamesu suka dawo gida inda kowa keta zuwa barka da farko gida taso komawa MAHMOUD din yace tazauna a gidanta bayason zuwanta ko Ina.

Amatu kullum tana kiransu Jin takeyi kamar tazo Amma Babu dama Dole saidai take ganinsu ta hotuna shikansa MAHMOUD din bataga alamar zai barta tabiyo hanyar zuwaba sbd ko school yanzu ya hanata tuqi da kanta anty salamatu ke kaita wani lokacin Kuma USI idan yanada time kenan sbd akusa da street dinsu yakama apartment yake zaune.

Ranar data Fara Masa maganar tanason zuwa Kai tsaye yace"
No,Babu inda Zan iya Bari kije until you deliver.

Dama tasan haka zai fada Dan haka Bata wani damuba ta bar zancen ta maida hankali Kan rainon cikinta da karatunta ta bangare daya ga MAHMOUD din dayanzu wani soyayya yakeji kodan itama lokacin haihuwarta ya matso ne Amma sam yanzu ko barinta bayayi ta sarara akan Kiran wayarsa.

Bayan sunan Modibbo da sati uku yayi daidai da Gama exams dinsu tana gida kwana biyu Babu inda take fita ga nauyin cikinta ya dameta ma gabaki daya.

Zaune take ita kadaice agidan anty salamatu sunfita da USI siyayyar wasu daga cikin kayansa na lefe dayake siya tun anan sbd Shi da Nuratu sungama daidaicewa tsakaninsu yana dawowa yakeson ayi idan son samunsanema to ahade aurensu danasu anty salamatu sbd dagashi har nuratun kamar zasu cinye juna sbd soyayya shiyasa itama yanzu nuratun kamar ta hadiye Amatu sbd qauna Dan sai yanzu take qara sanin mahimmanci Amatu agurin USI da irin tsananin qaunar junansu dake tsakaninsu.

Kallon wani tv program na likitoci takeyi a CWTv hankalinta rabi nakan waya sbd tun safe take kiran wayarsa Bata shiga Kuma shima tun Daren jiyan raban daya kirata.

Sake Danna kiransa tayi akaro ba adadi still Bata shiga tana qoqarin sake Kira taji ana qoqarin bude qofarsu ta shigowa ta juyo tana kallon qofar da waya a hannunta sukai Ido biyu itada shi ta Dan zaro Ido tana kallonsa tareda miqewa tsaye komai nata na bayyanarda mamakin ganinsa shikuwa kallonta yakeyi cikin kewa da soyayyarta ya tsaida kallonsa Kan cikinta dayayi girma cikin wata free doguwar rigar masu ciki data saka wadda batakai qasa ba sbd kada ta takurata ya ware Mata hannu Yana kallon fuskarta daukeda boyayyan murmushi da gudun dabatasan zata iyaba tayo kansa ta fada jikinsa ya rungumeta Yana Dan dagata sama cikin farin ciki da murna tace"
I love this surprise of urs Husband.

Sauketa yayi tareda Kama hannunta suka qarasa shigowa taso karban luggage dinsa ya hanata suka nufi dakinsa tafara gyarawa Yana tayata suka gyara dakin duk da Babu Abinda yayi 'yar qurace kawai.

Wanka yashiga ta fita zuwa kicin hada Masa abincin dazaici.

Cikin farin ciki tafara dafa Masa pasta da carrots sai beef meat ta hado Masa Kan tray takawo Masa har bedroom dinsa yaci tana zaune tanata tambayarsu Modibbo Wanda kamar ubansu daya da Muhammad sbd suna dibar kamanni.

Yana gamawa ta kwashe kayan ta maida ta dawo ta zauna Kan cinyarsa tana sake tambayarsa meyasa be fada Mata zaizoba.

Fuskarsa ya Dora kan tata Yana sauke ajiyar zuciya a boye yana kallon cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya Dora hannuwansa Kan cinyoyinta Yana shafawa cikin malalacin sauti yace"
Sbd inason ganin farin cikin bazata a kyakkyawan fuskan matana.

Murmushin Jin Dadi tasaki tana sake shigewa jikinsa ahankali tana qara cukuikuyesa qasa qasa da murya tace"
Ko acikin barci MAHMOUD ZABEERA yazomin farin cikina bayyananne ne bare ganinka a zahiri so lovely husband zuwan bazatanka ya tafi da zuciyan AMATULLAH K.
sake matsota yayi cikin jikinsa Yana shaqar qamshin jikinta ya shaqi numfashinta dake sauka Kan fuskarsa sbd matsuwar dasukai da juna ya Dora bakinsa Kan nata Yafara kissing dinta Yana zame hannuwansa zuwa wuyan rigarta.

Koda anty salamatu suka dawo da daddare guraren 9 Bata tareda wata gajiya sosai sbd sun Dan bibbiya guraren hutawa sun shaqata bataga Amatun ba a apalo ta shige da kayan zuwa dakin Amatun inda sauran kayan lefen suke Nan na Bata ganta ba sai tayi tunanin toilet Dan haka dakinta Takoma ta fada toilet itama tayo alwala tazo ta tayarda sallah.

Jin shiru shiru ba motsin Amatu yasata fitowa tana zuwa kicin ta duba ko tana can,
Ganin anyi sabon girki a kicin din yasata bubbudewa tana dubawa tafito Palo ta nufa dining tana ganin plates da kayan da akai amfani dasu ta fahimci oga kwata kwata ya taho kenan ta fito kicin tana kallon hanyar zuwa dakinsa tasake tabbatarda shi dinne yazo ta wucewa daki tana cewa''
Naji dadin zuwanka nasamu yanzu nabi usi next week idan zaije gida.

Washe gari tana kwance cikin jikinsa tana bacci cikin nutsuwa sbd irin kyakkyawar rungumar da yayi Mata suna bacci cikin baccin tafara Jin kamar ciwo ciwon Mara na damunta Wanda yasata bude idanuwanta tana sake saurarawa Abinda takejin saitaji da gaske ciwon yake ta yunqura zata tashi zaune yabude idanuwansa Yana kallonta ta yunqura ta tashi zaune ya tashi shima Yana riqota yace"
Lafiya kuwa?

Kallonsa tayi da sauri tana dafe qasan cikinta a Dan tsorace tace''
Ina ganin labour ne..... kasa qarasawa tayi cikin tsananin azaba da firgici tace"
Hospital hospital hospital take me" duk arude take maganar a jujjuye batareda tasaniba
Ganin hakan ya sauko gadon ya nufi wardrobe ya dauko shirt da wando yasaka cikin sauri tareda dawowa ya dauko Mata riga kamata ya sanya Mata suka fito tana sake dafe cikinta cikin azaba tana Kiran sunan Allah Dana MAHMOUD din cikin ciwo.

Jin dogon salati da qarfi yasa anty salamatu fitowa daidai qarasowarsu tsakiyar palon a Dan rude ta kallesu tana maida kallonta Kan Amatun daketa faman salati ba qaqqautawa cikin mamaki tace"
Subhanallah haihuwar ce ko me?

Lafiya kuwa?

Muje asibiti"kawai ya iya furtawa anty salamatun Yana nufar qofa da matarsa.

A gigice suka Isa asibiti musamman da ciwon ya taso Mata gabaki daya suna Isa ruwan haihuwa na fashewa akai labor room da ita.

Zama yayi Kan kujerun jira Yana kashe wayarsa sbd baya buqatan ko hayaniyar ringing waya.

Suna zaune saiga USI shima ya iso Nan suka Fara zaman jigum jigum cikin zullumi da fargaba,
Wannan zaman jiran dayakeyi yau yana daya daga cikin ranakun tsananinsa na rayuwa sbd gabaki daya Jin yake kamar nutsuwarsa zata bar jikinsa Amma haka dai yake zaune shiru kamar ba Wanda ke cikin tension ba.

USI da anty salamatu ne ke samun damar waya da Yan gida sunajin yaya kota haihune?

Zaman awa uku sukayi cikin ta hudu kafin Allah yabata ikon haihuwar baby girl lafiyayya da ita saidai ba qatuwa bace sosai sai kuka takeyi aka shiryata aka miqowa familynta ita ya karbeta Yana kallonta cikin wata irin nutsatsiyar sonta da qaunarta ya shafa Dan qaramin kumatunta Yana Mata adduoi da murmushi akan fuskarsa yace"
De symbol of my love FADIMATU ZARAH MAHMOUD ZABEERA.

Aikuwa cikin farin ciki anty salamatu itama ta karbi babyn tana kallon fuskarta cikeda murna tace"
MAHMOUD wannan 'ya da yayunta take Kama.

Murmushi kawai yasaki zuciyarsa na sake wanzuwa da farin ciki sai alokacin ya bude wayarsa da atake Kira suka Fara shigowa ya fice Yana amsawa.

Yana dawowa ya tararda anfito da Amatun ankaita dakin hutawa ya shigo Yana aika Mata da wani irin kallon samun nutsuwa ya qarasa bakin gadonta ya zauna tareda Dan rungumota yabata kiss agoshi yace"
Thank you.

Murmushi tasaki tana Dan harararsa tace"
Bazan qaraba daga wannan.

Dariya maganar tabawa anty salamatu takuwa ringa qyaqyata dariyarta shikuma wani guntun murmushi ya sake Yana sake kissing hannunta dake cikin nasa batareda yace komaiba.

Acan Nigeria kuwa cikin both families din haihuwar ta Isa kunnen kowa akaita Sanya alkhairi da yiwa FADIMATU ZARAH adduar Allah ya raya Akan sunna,
Zarah da akaiwa takwara kuwa rasa abin cewa tayi sbd farin ciki shiyasa ma tace zatazo taga takwara da kanta.

Kwananta daya a asibitin suka sallamota suka dawo gida Nan anty salamatu tayita hidima dasu ganin suna hutu Kuma gashi umme da zarah hadda Nuratu since zasuzo yasa ya yanke shawarar su dawo gida bayan ko 30days ne saita dawo.

Kwana biyar da haihuwar suka dawo Nigeria Nan aka kacame da sabuwar murnar zuwansu 'yan barka suka Fara sintiti musamman aminanta su maman junior da kullum saisun Zo iyami ma kwana biyu ta jera tana zuwa Saida akai suna tukuna suka samu sauqin baqi sai alokacin tafara samun kanta.
Chapter 68 · 0% Book details