← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 70

Sashe 13

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kawu da iyami tayi Shima kawun kallonta yake yace"
To wannan kudin fa???

Kai tsaye tace kudin albashinane aka bani na watannin Dan daukar nauyin Kai kafin mu fito training din.

Iyami ta kalla tace"
Wlh iyami aiki zanje Yi ba qarya nakeyiba na rantse Miki...

Duk shiru sukayi kafin kawu yace"
Naji kuje zanyi tunani akai.

Miqewa tayi ta fito usi ya biyo bayanta suna fitowa yafara watso Mata tambayoyi tajasa zuwa dakinta da sauri Dan kar kawu yajisu suka zauna tafara yimasa bayani komai Kai tsaye yace wlh bai amince ba.

Hayaniya suka Fara tayi saurin rufe qofa tana cewa"
Idan baka gaji da yawon cell ba ana maka dukan wulaqanci to ni nagaji da ganin hakan,
Rayuwa me kyau nakeson muyi kamar kowa Usman,
Idan har kanason farin cikina danasu kawu wannan maganar mungamata,
Banyi Dan Jin dadinaba sai Dan wainnan bayin Allan dasuka sadaukar da komai saboda mu,
Babu uqubar dabasu shigaba amma suka riqemu da Amana,
Kaima inason ganin kasamu ingantacciyar rayuwar sbd ka tallafesu a gaba Dan ni nasan rayuwata acikiku taqaitacciyace kobanaso nasan Dole wata Rana kawu saiyamin aure..

Usman mubar maganar Nan kawai qwarin gwiwarka nake nema.

Kallonta yayi idanuwansa na cikowa da hawaye yanajin inama ya mutu ya rage Mata 'dawaimiyar datake ganin itace akai,
Maimakon yazama jagora Amma yazama wani irin koma baya itace jagorar.

Ficewa yayi Yana share hawayen fuskarsa dasuka saka jikinta yayi sanyi matuqa Amma batajin zata fasa sbd tariga takai qarshe zasu bar Nan din sbd karatun Usman din.

Kwana biyu ana rigima sosai a tsakaninsu kafin iyami da Usin suka amince akan aikin nata bayan dattijuwar da aka aiko tayi zuwa kusan hudu tukuna.,
Kwana uku masu zuwa zata tafi Amma duk sai jikinsu su hudun hakanan ya mutu sosai suka shiga damuwar tafiyarta duk da dai Basu fadaba sai hakan yataba 'yan gidan Suma sbd su kawun dadu amah sune hayaniyar gidan dake qara Raya gidan shiyasa Suma duk sai sukaji ba Dadi,
Amatun ma hakanan takejin kamar zata rabu dasu kawun ne rabuwar har abada Wanda usi ne ma tadawo Yana qoqarin cire Mata damuwa,
Iyami da kantace ta hada mata duk wani abin buqata a 'yar Jakarta ta goyawa ranarda akazo tafiya da ita iyami duk hakurinta saidatayi hawayen rabuwa da amatun sbd zuciyarta takasa samun nutsuwa da tafiyar,
Kawuma kasa rakiyarta waje yayi saidai Usman ne aka tafi dashi Dan yaje yaga inda take.

Su maman junior hadda rungumeta sukayi sunajin kewarta tun Bata tafiba.
****
Wayarta data gamayi ta kalla tareda kallon haj Maryam dasuke zaune a palon tace"
Su amah ne gasunan a hanya isowa zasukai mintuna ashirin kafin su iso zuwa lokacin an halarta gurin meeting din familyn ZABEERA daza'ayi yau
Yau komai zai qarewa MD ZABEERA.

Murmushi haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye tace"
'yan jaridar Dana gayyatoma suna daga baya suna jiran kirana suzo ya sakarwa duniya wannan labarin da dumi duminsa.

Dariyar farin ciki suka saki atare daidai lokacinda nuratu tashiga cikin kyakkyawar adonta na wata Kuwait jallabiya datayiwa fatarta kyau sai qamshi takeyi tace"
Momy kusan kowa fa ya halarto dan gasu anty bahijja nacan sun iso taredasu anty juwairiyya dasu baba qarami.

MD ZABEERA ma Naga shigowarsa yanxu tareda ZARAH.

Kallon juna sukayi tareda cewa"
Shikenan muje.
_40 min later_
A bakin babban qaton gate din ZABEERA motarsu ta Parker Wanda akayi juyensu da ita zuwa wata matacciyar golf baqa.,
Akaro na farko ta 'dago hoton MAHMOUD ZABEERA da aka Bata bayan anmusu bayani wasu abubuwa akansa ta kalli hoton zuciyarta tayi wata irin bugawa akaro na farko...

Rintse ido tayi zuciyarta na wani irin tsalle tayi saurin rufe hoton tana dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi tace"
Ya Salam..

Meyasa zuciyarta ke bugawa da ganinsa a hoto???

Kallon Babar dasuka Zo tare tayi tana qoqarin Hana zuciyarta bugawa Amma sai qara bugawa tayi tayi saurin miqa Mata hoton tana cewa'"
Ki riqe a hannunki nariga Naga hotonsa zan ganesa da kaina.

Kallonta baba Jamila tayi tana cewa'"
Ki nutsu fa.

Gyada Kai tayi tana yiwa qatoton gate din zabeeran kallon kwadayi da qauyanci.

Shima usi kalle kallen yakeyi baki abude sbd tsananin girma da kyan gate din kafin suka nufo gate din Babu dogon musu sbd babban security in charge yasan da zuwansu yasa aka Bari suka shigo suna kalle kallen baki asake
Amatu tace"
Usi kana ganin Abinda nake gani kuwa????

Kasa magana yayi yafarabin manyan motacindake harabar gidan da kallo Yana cewa'"
Wlh amatu wannan gidan aljannar duniya ce muka shigo.

Itama motacin tahau shafawa tana cewa'"
Aikuwa sa'a takawoni Nan ni amatu.
##mamuh##
______________
KUNA BU
ATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES
IN BOOKS
IN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon hazi
an marubanku
an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da sa
o ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai bu
atar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntu
ar wa
an nan Numbers 0903
5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks
in kana bu
ata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi.

Idan kuma wasu adadin pages kake bu
ata koda
aya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sau
in gaske
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sau
______________________
#MIN QALB
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/15, 10:51 AM] Zafafa: _*MIN QALB 11*_
_mamuhgee_
Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins hudu golden and red sbd girmansa ga kalar dasuka qara qawata palon,
Shine palon da dukkanin familyn ZABEERA ke meeting acikinsa qarshen kowane wata to wannan watan ma hakan ce tafaru dukkanin daukacin zabeeras dake jahar suna cikin palon kusan su sama da arbain kowanne yasamu guri ya zauna ana tsimayin fitowar me kankat wato Modibbo Wanda fitowarsa tayi daidai da tsit da gurin ya dauka sai gaisuwa kawai dake tashi Yana amsawa ta hanyar 'daga Kai batareda ya bude baki ba.

Zama yayi Yana bin kowa da kallon jinjinawa na riqe wannan al'adar dasukayi har idanuwansa suka sauka akan MD ZABEERA wanda ke zaune can bayani iyayensu dukkanin hankalinsa gabaki daya Yana Kan waya dayake karanta email din saqo daya shigosa,
Kallon zamansa Modibbo yayi har zuwa fuskarsa dake daukeda wani irin kwarjini da haiba ya jinjina Kai Yana cewa'
Tabbas Babu wani zabi daya wuce akan mulkin zabeera ayau taron naka ne.

ZARAH kuwa duk da ta shige cikin 'yan uwa da qawayenta 'yan uwanta Amma hankalinta na kansa akai akai take satar kallon gefen dayake sbd ganin yauma dai kamar ko yaushe arayuwarsa ya kebe ne daban duk da yanzu duk Wanda yashigo cikin qanne da tsaransa ma harma da wainda suka girmesa zuwa sukeyi suna gaidashi Wanda Shima yawanci daga Kai ne kawai bai cika bude bakinba Yana amsawa musamman sbd rashin sabo da Yan uwan duk wasu da dama baisansuba.

Khalil ne abokin zamansa akowane meeting tun quruciya Amma yau Khalil din baishigo da wuri ba Abinda baitabayiba ranar meeting wato latti.

Khalil kuwa yanacan ne hanyar gidansu amatu data Hana rayuwarsa da zuciyarsa sukuni,
Tsawon kwanakin Nan bayan haduwarsu da ita bincike yayi me kyau akanta sbd shigo da ita a rayuwarsa Dan sauya musu ingantacciyar rayuwa dakuma tunaninta daya kasa fita ransa da kansa,
Tabbas yasan babban laifine a zabeera neman aure a waje wanda bama ataba yiba asai yanzu dazai Fara shigo da tsarin karya dokar manya sbd bayajin zai iya hkr da maganar amatun a shirye yake daya tallefi yarinyarda zuciyarsa ta riqe a gani na farko Koda hakan na nufin barin zabeera ne barema yasan zai shawo kansu da taimakon MD.

Babban rashin sa'ar dayaci shine bayan isarsa kawu yayi Masa bayanin aiki tasamu ta tafi training Amma dai yabasa numbernta Dana usi din duk da shi Usin Rakata kawai yayi dawowa zaiyi.

Koda ya karba lambar agogo ya duba yaga yayi lattin meeting ga umme Bata gansa ba sai kiransa takeyi
sai bai tsaya Kiran numbrn ba yayi saving tareda dawowa zabeera cikin sauri sbd yasan zuwa yanzu anfara meeting din.

Yana qoqarin shiga gate din zabeera yaga motar 'yan jarida na tsayawa ta gate suna qoqarin gyara cameras dinsu ya Dan tsaya Yana kallonsu cikin mamakin meya kawosu musamman ma da zabeera basa muamala da duk Abinda zai hadasu da 'yan jarida sbd tsira da mutuncinsu da sunans ahalin,
Ganin yayi latti sauri yakeyi yasa bai tsayaba yashigowarsa,
Yanayin parking harabar gidan Kiran nuratu nashigowa wayarsa ya saki siririn tasaki Yana dafe kansa dake Masa ciwo sbd rashin bacci kwana biyun yayi rejecting kiran ko Ina bai tsayaba Kai tsaye ya nufi palonsu na meeting dasuke Kira da zabeera hall.

Yana shiga yaga har anyi nisa yayi saurin yin gefenda ya hango md zaune Ya lumshe fararen idanuwansa ya kwantarda kansa ta baya jikin kujerar dayake Yana sauraron Abinda ake fada cikin nutsuwa.

Qoqarin miqewa alhaji qarami yakeyi zaiyi mgn suka Fara jiyo hayaniya me 'dan qarfi tana tashi daga wajen qofa,
Sharewa sukayi alhaji qaramin yafara bayani Amma sai gaba hayaniyar keyi
Alhaji qarami ya kalli yakub babban 'dan alhaji qaramin yace"
Yakub dubo meke faruwa ne.

Miqewa yayi ya fita Dan dubowar sukuma suka cigaba da meeting din.

Mintuna biyu da fitar yakub sai gashi yadawo da sauri yazo gefen babansa yayi qasa da murya yafada Masa abin dake faruwa da sauri ya kallesa Yana cewa'"
Mene?

Kowa najin haka yayi tsit suna jiran jin abindake faruwa.

Je kashigo dasu""alhaji qarami yace Yana qoqarin cigaba da bayanin dayakeyi.

Sallama sukayi wadda tasa kowa juyawa hadda Shima dazaiyi maganar duk suka kalli qofar wadda ke seti tana kallon center inda Modibbo yake zaune Shima sbd ba'a taba barin wani shigowa ba idan suna taron yasashi dakowa ya kalli qofar.
Chapter 13 · 0% Book details