← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 70

Sashe 27

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare tana qoqarin zama bayan futowarta daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci masu Dan akuri ta saka wularsu sai qamshin turaren Dr khalil takeyi Wanda yabata datace tanason qamshinsa saiga kiransa yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira da numbernsa tacan tayi saving.

Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba sbd gaban anty zarah ne tace"
Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai.

Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a natse yace"
Baga zarah Nan ba.

Shiru tayi kafin ahankali tace"
A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin tsaro da kulawa idan har bakanan,
Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa.

Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun nutsuwa yace Mata"
Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda zanbari yasameki sai qaddara.

Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita baqar wahala idan zatayi period,
Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima ana Yan dubaru har tagama period din tukuna.

Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data daina cin zaqi.

Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya takeba.

Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah.

Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa ya
kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa.

Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku,
Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri.

Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan azaba.

A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace"
Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata
takira Mata Dr Fatima.

Umme Kuma"""
Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta.

Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu.

Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri.

Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci.

Umme zarah ce
Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai.

Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa''
Uban Dr Fatima zankira muku,
Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki wlh.

Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a jikin dogon wandon Amatu din.

Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace"
Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace.....

Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin rudewa tana kasa Magana.

Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be
Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya sauko zarah din na bayansa.

Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu
Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin dake jikinta
Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito Yana cewa''
Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe.
##mamuh#
ZAFAFA BIYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/30, 10:39 AM] Zafafa: *_MQ 21_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wad
da ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata koma
a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*
**********
Seat din gaba yasakata ciki tareda 'dan kwantar da seat din ya rufe ya zagaya yashiga motar ya tayar yabar gurin cikin gudu sosai,
Cikin mamaki securities suka firfito Amma suna ganinsa sukai saurin bude Masa gate din suna Masa adawo lfy kota kansu baibiba ya fice.

Anty zarah sai alokacin ta tsaya sake da idanuwa tana cewa"
To Ina zai iya da ita shi kadai daya Bari nabiyosu,
Kiran khalil ne yashigo wayarta cikin sauri ta dauka tana fada Masa MD ne yatafi Kai Amatun asibiti.....

What????""""yafada da sauri cikin firgici Yana cewa'"
Me umme tace?

Yaushe suka tafi??

Umme Bata daga wayarba gashi jini yafara balle Mata shine yatafi kaita da kansa,
Dr Ina fatan kada wani Abu yasamu cikin Nan Dan Allah ka Kira asibiti tun kafin su Isa kafada musu suyi duk iya qoqarinsu Dan Allah karsu Bari cikin Nan yasamu matsala.
kasa Magana yayi ya kashe wayar tareda Kiran Dr Fatima dayasan asibitin na hannunta yanzu tunda bayanan cikin tsananin damuwa da tashin hankali yayi Mata bayanin abindake faruwa.

Cikin sauke numfashi tace"
Karka damu Bari su iso Ina asibitin yau zanyi call(night) ne Inshallah za'ayi yanda aka Saba Mata duk wata,
Problem din dai shine sunriga sunga cewa tafara bleeding ya zamuyi da wannan?

Just handle everything please Dr Fatima
Nabar Miki komai ki kula dashi nidai kawai please Dr Fatima Amatu azaban datake ciki nakeson kifara bi takai
Inaji ajikina tana cikin azaba sosai Dan Allah Dr Fatima ki kularmin da ita gobe zan biyo jirgin Rana nadawo bazan iya daukaba
Tafiyan kwana daya harta Fara shiga abubuwa iri iri.....

Calm down please Dr khalil komai zai zama daidai Inshallah Babu Abinda zai samu Amatun zanyi iya dukkanin qoqarina gurin ganin Babu Abinda zai sameta.

Thank you Dr""yace Yana kashe wayar sbd Jin ana buga office din datake.

Tun kafin ta aje wayar nurse Abida tashigo tana cewa''
Dr Fatima ga MD ZABEERA nan matar Dr Khalil ya kawo it's emergency mun karbeta ke ake jira.

Medical glass dinta kawai ta dauka ta miqe suka fito sister Abida nasake Mata bayanin taimakon gaggawar dasuka Bata.

Tana zuwa taga halinda Amatun take ciki take tasaki wani guntun murmushi sbd ganin yanda Dr khalil ya daga hankalinsa akan alamarin ba haka bane menstrual pains ne kawai.

Nan tahau dubata tareda Bata allurai Dan samu 'dan relief tareda qarin ruwa sai paracetamol data Bata.

Tana fitowa daga cikin emergency din sister Abida ta biyota tana cewa''
Dr Fatima zamuyi shifting nata ne zuwa Amenity ko kuwa?

Yes u can shift her Amma kafin Nan kufara taimaka Mata ta gyara so that kar jinin ya qarasa Bata Mata jiki,
Ok zamu Bata pad ne kokuwa abata cotton tayi amfani dashi,
And dose na injection dinta after 2 hours ne zamu sake Bata parainject din??

Yes after 2 hours ko Kuma 3 hours tunda menstrual pains ne kawai.

Sister Abida na barin gurin Kiran Dr khalil ne yashigo wayarta saidata saki numfashi kafin ta dauka tana cewa''
Kafin kace komai Dr khalil please listen to me
Maganar gskia Dr yarinyar Nan tunda har kasan kowane wata irin wannan matsalar ta al'ada na damunta Kaine kawai zaka iya magance Mata matsalar sbd kada wata Rana abin ya zarce ya zamar Mata matsala babba,
Mu'amalar aure ne kawai zai kawo Mata qarshen wannan monthly pains din.

Zata sake Magana ya katseta da cewa"
Dr Fatima lafiyanta kalau yanzu dai ko??

Eh komai ya daidaita zuwa asuba zasu iya tafiya gida..

Ok thank you Fatima
Sauran maganar please mubarta idan nadawo zamuyita.

To kawai tace tareda kashe wayar ta wuce tabar gurin batareda ta juya taga MD dake zaune a bayantaba idanuwansa ne kawai ba'a kanta ba Amma hankalinsa gabaki daya akan zancen datayine tunda nurse Abida har Khalil dasuka Gama Magana yanzu,
Shiru yayi Yana qoqarin nazarin fahimtar zancen sbd idan har yayi amfani da iliminsa na 'dan Adam Koda baitaba haihuwaba ko samun ciki da amatarsa yasan dai Mai ciki Bata period,
Hakama Mai aure harda ciki baza'a ce Yana buqatar rayuwar auratayyaba kafin yasamu saukin cramps,
Bude idanuwansa dake lumshe yayi ahankali Yana tunanin Khalil na boye wani Abu gameda yarinyar Nan wanda yake da matuqar mahimmanci ko hadari,
Koma dai menene ba huruminsa bane Abu dayane zai fadawa Khalil yasan Abinda yakeyi.

Dakin da aka maidata ya qarasa yashiga lokacin ta bude idanuwanta daidai shigowar tasa sai idanuwansu suka shiga cikin na juna
Ita tayi saurin yin qasa da idanuwanta sai kawai idon nata ya sauka kan farar jallabiyarsa da jini ya Bata daga gaba gurin cikinsa take tayi saurin rintse ido akaro na farko wata irin kunya me tsanani ta kamata saita samu kanta da kasa bude Ido ta kallesa.
Chapter 27 · 0% Book details