← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 70

Sashe 22

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri zarah ta zube qasa itama zatai Magana ya daga Mata hannu batareda ya kalletaba yace"
For first time ayau naji nayi takaicin amincewa da aurenki,
Hw cud you zarah,
Bakisan mutuncin kanki da Wanda ya ajiyeki bane dazaki fita in the first place batareda izini ba
Ever this stupid being came here nasan zaayi haka wata Rana sbd wannan ba mace bane she is just a shame,
Sata rayuwarta ne
Shi aka reneta dashi sbd Abinda tasani shine kawai sata da yawo cikin maza with no shame,
A hausance banma san sunan dazan kirataba sbd idanma ankirata da abin kunya an Bata sunan mutunci
Amma ke this is the last thing I expected from you...

Banason hayaniya I prefer rayuwata ni kadai yafi nutsuwa da kwanciyan hankali so please ku duka just park ur things kubar Nan
Ni kadai nakeson zama anan just I think kowannenmu need a break.......

Wani irin kuka Mai taba zuciya anty zarah tasaki tana qoqarin basa hkr ya juyawarsa zai haye sama Amatu ta miqe da saurin Tasha gabansa tareda sake zubewa tana tsiyayo hawaye masu tsananin 'dacin kalaman daya furta akanta saidai komai 'dacinsu zata hade bazata Bari laifinta ya lalata auren anty zarah ba kodan yanda tasan shine rayuwar anty zarah din.

Akaro na farko a rayuwarta datake qwallan cin zarafi da akai Mata sabanin da ko ajikinta Dan ko damuwa batayi barema ada Babu Wanda ya Isa ya tsareta ya iya fada Mata haka Bata saka an Masa zanen yorbawa a fuskar ba.

Sabbin hawaye suka gangaro Kan fuskarta ta bude baki muryarta a matuqar sanyaye tace"
Dan Allah kayi hakuri anty zarah batada lai...

Ko kallon inda take baiyiba ya wuce tayi saurin rarrafawa zatasha gabansa cikin tsananin 6acin Rai ya daga qafa zai wuce da ita aka saka hannuwa biyu aka tare qafar
Ya tsaya cak kallon Dr daya riqe qafar tasa cikin tsananin mamaki da sabon takaici.

Dr daya jima tsaye Yana sauraran duk Abinda MD din ya fada suna dukan zuciyarsa duka me tsananin daya karya gwarin gwiwarsa.

Baice komaiba sai kawai ya sauke gwiwoyinsa qasa gaban MD din tareda sunkuyar da Kai cikin tsananin rauni da damuwa me nauyi murya a sanyaye yace"
MAHMOUD karka hukunta zarah akan laifin amatu na roqeka da sunan Allah,
Itama Amatu Ina roqonka daka yafe Mata Koda hakan zai zama alfarmar qarshe dazakamin arayuwata to Dan Allah ka yafe Mata ba laifinta bane laifina ne Dana kasa bar Mata duk Abinda yakamata nabar Mata......

What???Khalil Kama San waye wannan yarinyar kuwa?

Tun farko bansan me kagani na hankali atareda wannan yarinyarba harka iya sabawa iyayenka ka aureta,
And now kana durqushe a gabana duk sbd ita
Khalil Kama ganin daidaine hakan?

Rintse idanu Dr yayi a sanyaye Yace"
Abinda nasani yanxu arayuwata shine indai sbd itane zanyi har Abinda yafi durqusawa sbd tsirar Mata da mutuncinta,
Kai Dan uwanane mafi kusanci agareni Wanda kalmomin batanci mafi Muni suka fito daga bakinka kan macen danafi so da qaunar Kare martabarta shiyasa na durqusa gaban nake neman afuwarka sbd ita,
Cikin sake kunnasa da Khalil din yayi da maganganunsa hakanan kawai yaji mugun zafinsu
Yau Khalil ne ke fadar kariya da martabarta
Rintse ido yayi suna qara rinewa ya kalleta
Sautin kukanta na fita ahankali sbd maganganun Dr sungama sanyata cikin nadama me tsanani
Take zafin zuciyarsa yafara loosing control ya juya zai wuce Khalil ya miqe tareda Shan gabansa yace"
MD matuqar haryanxu matsayina na Nan a zuciyarka da rayuwarka inason ka tabashi biyu kabani nida Amatu sbd wlh ni itace tawa rayuwar,
Zakaimin alqawarin yafe Mata tareda Bata mutunci amatsayinta tawa,
Idan bakayi Dan ni ba kayi kodan jinina dayake jikinta Wanda yake shima naka jinin,
MD Ina fatan zakamin wannan alfarma ko bayan idona.

Kasa kallon Khalil din yayi sbd baqin ciki da takaicin duk akan mace ya zare haka macen ma ba kamar matan mutunci ba haryana kirarin idan yana qaunarsa saiya qaunaceta
Ra'besa kawai yayi ya haye sama tun kafin shida Khalil din ta 6aci akan yarinyar.

Bayansa Khalil yabi da kallon harya shige kafin ya saki numfashi a sanyaye tareda juyowa ahankali ya zauna gefen amatu dake kuka qasa qasa takasa ko motsi.

Kallon zarah dake nata kukan yayi zaiyi mgn ta miqe tabar gurin tayi dakinta ta rufo sbd itama kukan takeso tayi sosai ko nauyin zuciyarta zai ragu.

Cikin sanyin jiki ya maido da kallonsa Kan amatu yafara lallashinta Yana Mata nasiha hartayi shiru da kansa ya dauko ruwa a fridge yabata Tasha ya rakata har dakinta kafin ya wuce zuwa nasa part din jiki da zuciyarsa amatuqar sanyaye.

Sallolinta tayi ta zame ta kwanta Kan dadduma a inda tayi sallar yau ba Maganar cin Dadi
Amma datayi awanni a kwance taga bacci ba zuwa zaiyiba sbd yunwa hakanan ta miqe ta fito taje kicin taci fruits dinta da yoghurts ta qoshi tazo ta kwanta tunanin Dr na dawo Mata bangare daya Kuma damuwar da anty zarah take ciki.

Washe gari tunda safe Dr khalil yazo sbd yasan shikenan MD zai Fara rashin 'dan zaman dayakeyi a gidan fita tinda safe dawowa sai dare qarshema yasan zai iya tafiya yabar qasar yakoma wata qasa sai yaga dama ya dawo.

MD na ganinsa ya kallesa Yana watsar da tunanin abubuwan jiya din sbd shi ba mutum ne me aje hargitsi cikin kansa ba Sam ko maganar batason a tayar sbd kar asashi cuwon Kai.

Kallonsa Dr khalil yayi Yana qaqalo murmushi yace"
Good morning MD ZABEERA.

'dan kallonsa MD din yayi Yana maida kallonsa Kan agogon hannunsa cikin miskilanci yace"
Morning Dr khalil zabeera.

Murmushi Khalil din yayi Yana cewa''
Sorry MD.

Kallonsa ya 'danyi kafin yaci gaba da duba wayarsa.

Bai kamata nama Magana irin yanda nayi maka a jiyan kayi hkr.

Karka damu I can't even recall Abinda yafaru a jiyan.

Numfashi Khalil ya sauke Yana gyara tsayuwa kafin yace"
Amma akan Amatu inakan duk Abinda nafada Dan haka Ina riqon alfarmarka sbd abin dake cikinta please kabata damar dazan gyarata kodan 'yayana su samu uwa ta gari.

Gaba daya MD din ya dago ya kallesa wannan karon tareda 'dan lumshe fararen idanuwansa yasaki wani sahirtaccen numfashi kafin yace"
I hope you know wat u're doing.

Motarsa ya fada tareda cewa''
Mu yini lfy Dr.

Murmushi Khalil yayi Yana cewa''
Zan dauki wannan amatsayin amincewa da roqona thank you.

Ciki ya qarasa gurinsu sbd Suma yanason mgn dasu musamman zarah bayason tasamu matsala da Amatu akan wannan alamarin sbd ita kadaice yasan Amatu is safe a gurinta.

Cikin sa'a kuwa Zarah din na dining tana qoqarin jera breakfast tayi 'dan adonta duk da ba walwala sosai a fuskarta duk sbd taqara bawa MD hakuri.

Cikin sakin fuska yakira sunanta
Ta juyo tana yaqen Dole suka gaisa
Suna cikin mgn saiga Amatu ta fito jiyo muryarsa
A sidade ta qaraso tana kallon fuskar zarah a raunane.

Ganin yanda tayi din sai anty zarah din taji rashin Dadi ta saki 'dan guntun murmushi tana cewa''
Amatu Zo
Kinci abinci jiya da daddare kuwa?da maganinki ma kinsha??

Wani sabon girma da qaunar anty zarah dinne suka rufeta batasan lokacinda ta qarasa gurinta da sauri ba ta rungumeta tareda sakin wani siririn kuka tana cewa''
Anty zarah Dan Allah ki yafemun wlh nayi nadama me tsanani akan Abinda na ja miki.

Karki damu Amatu qaddarane Kuma yariga ya wuce tunda kince bazaki sake ba.

Zama tayi gefen anty zarah din ta share hawayenta tana sunkuyar da Kai tace"
Anty zarah kunyarki nakeji haryanxu sbd tun yanxu nafara saka Miki da Abu Mara kyau akan alkairi da qaunar da kike mini,
Ayau naji gida nakeson komawa inda nafito,
Cikin mutanenda nafito,
Cikin rayuwar damuka saba da qanqancin da muka Saba dauka sbd nafara gane ban cancanci zama cikin mutane masu mutunci da daraja kamarku ba,
Anty zarah daukar abin wani yazama tamkar qaddaratace sbd saimun dauki abin wani muke iya ciyar da cikinmu abinci wata Rana,
Rayuwa da mutanen cikintane suke tilastamu ga aikata wasu laifukan wata Rana,
Nida usi muntaso cikin bola muka rayu acikinta mukayi wayo,
Acikin bola muka Fara sanin yanda zamuyi fafutuka mu gudanar da rayuwarmu,
Bayan Tasha shine gurin kwananmu
Shine muhallinmu a lokacin,
Tun munada shekarun da bamu Gama sanin bambamcin jinsuba aka lalatawa usi rayuwa ta hanyar Masa fyade,
Fyaden da shine sanadin farko na qarin tabarbarewar rayuwarmu,
Alokacin mukasan ba tausayi atareda mutanen cikin duniya,
Munkoyi data Danmu ci mu tsira mu rayu,
Anty zarah bamu qara fuskantar qasqancin halin rayuwa da mutanen cikintaba sai alokacin da nida USI aka kamamu a gaban idonsa aka yaga tsumman sutura dake jikina za'ayi mini fyade Wanda yayi sanadin haduwarmu da mutum na farko daya Fara yima kallon muma 'yayane Kuma mutane 'yan Adam,
Kawu ya gabatar Mana da sabuwar rayuwar almajiranci wadda nayita acikin maza da siffar maza ta hanyar rayuwa usman namin aski,
Munyi almajiranci na wahala Wanda yasamu baqin jini acikin almajirai Yan uwanmu,
Munyi kukan sarari munyi na fili saidai bamuda tudun dafawa har Saida rayuwar wahala da garari ta aure mu kafin kawu yasake kallonmu da idanuwansa na rahama da jin qai ya zamo uba garemu,
Ya bamu uwa me qaunarmu tamkar 'yayanta iyami,
Mezamu ce arayuwar Nan bayan wahala da rayuwar garari a jininmu take shiyasa ko a gidan kawu tsanani da Matsin rayuwa be qare Mana,
Muna kwana da yunwa mutashi da ita Kuma muyi rayuwarmu,
Munshiga masifu iri iri da rayuwa ta jefamu aciki saidai Babu wani mahaluki 'daya daya taba kallonmu da zuciya me kyau
Kowa nada buri Mara kyau akanmu Wanda ya dangantamu da irin wannan rayuwar da ake qyamarmu sbd ita,
Rayuwa ta zabar Mana gwagwarmayar samun Abinda zamucu kota halin Yaya alokacinda 'yaya kamarmu suke makaranta suna karatu shin anty zarah bawa shi yake zabarwa kansa qaddarane??

A tsawon shekarun ban bantaba Jin nadamar daukar abin waniba sai a jiya Dana jawa macen data Soni tsakaninta da Allah batareda ta hada komai daniba,
Anty zarah a shirye nake Dana bar Nan sbd zamana anan masifa zai janyo Miki ba alhe.......

Rungumeta anty zarah tayi da sauri Yana sakin sheshekar kukan datakeyi na tausayin Amatun da usman tareda su kawu dasuka taimakesu bayan Suma taimakon suke nema.
Chapter 22 · 0% Book details