Sashe 47
Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zanyi tafiya Nanda 5 days but Inshallah I will be back before time din yacika Just do the best you can atare matsalar.
Karka damu Mr zabeera Inshallah zaka dawo kasamu both the mother and the baby lfy.
Thank you"yace tareda miqewa Yana dorawa da cewa''
Stefan zaiyi clearing bills na komai zuwa anjima.
Kamar zaije dakin datake saikuma ya dakata tareda kallon qofar kawai ya wuce daidai isowar su iyami suka gaisa ya fice asibitin gabaki daya.
Da daddare iyami ce kawai ta kwana tareda ita anty salamatu ranar gidansu ta wuce dan dama tanada niyyar zuwa gidan yau yin wani Abu saiga zuwa asibiti ya kamasu.
Umme da Haj maryam ne suka Zo da daddare suka kawo musu abinci
Anty zarah ma tazo takawo wa Amatun furar datake so,
Gaba daya Kwanakin busy take da hidimar gidanta data MAHMOUD da yanzu ta dage sosai take farautar soyayya da kulawar mijinta Wanda Amatun ke sake zugata da Bata qwarin gwiwa Kuma alhmdlh tana samun ci gaba Dan ko last month tare sukaje UK sukaga wani likita Akan matsalar rashin haihuwar ta Wanda itace ta nuna tanason ganin likita cikin sauki kuwa ya amince Mata sukaje UK din daga can Sudan suka wuce Saida sukai kusan wata daya kafin suka dawo wanda tafiyar tasa tafara fuskantar asalin irin rayuwar da mijinta MD ZABEERA takeso wato rayuwar turai shida iyalinsa Wanda duk wayewarta ita Kuma takasa koyawa kanta sbd Sam ita saka qananun Kaya basa gabanta tafi ganin kyan kanta da burge kanta idan ta hade cikin kayanta na yarenta har gwara dogayen rigunan jallabiya taba sakawa sosai saigashi taga yanda yake rayuwa kamar asalin bature idan yabar qasarsa wato wasu irin personalities garesa boyayyu na burgewa ga wasu irin kyawawan manyan 'yan Mata masu aji dasuke huldar business dashi suna jansa da fira sosai Kuma ba laifi Yana 'dan sake musu shiyasa ta Raina kanta suna dawowa tafadawa Amatu damuwarta Wanda hakan ya sanyaya jikin Amatun itama saita Fara zugata akan ta zabure tafara duk Abinda tafara lurada yanaso tunda harta Fara samun Clue.
##Mamuh##*_MQ 36_*
Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada Mata kafin shigowarta akan inda aka tsaya da maganar matsalar,
Ita kanta Amatun a sanyaye take sbd rashin sanin makomar abindake cikinta,
Allah yasani tanason
babynta Kuma tanason samun Abinda Bata fatan tayi wahalar banza shiyasama tunda sunce saita kwantarda hankali babyn zai samu shima lafiyar da akeso tafara iya qoqarin kwantarda hankalin saidai Kuma Sam tsoro da shakkar halinda babynta ke ciki ya Hana hankalin nata kwanciya.
Iyami ce ta miqa mata kofin maganin tsiyayewar zaqi tana cewa''
Karba ki Dan Sha ko kadan ne zai taimaka idan haihuwar ta taso gaba data.
Kallon kofin tayi tareda karba ahankali ta kurba tana rintse ido sbd rashin dadinsa ta ajiye cup din tana girgiza Kai tace"
Iyami bazan iya Sha da yawa ba wannan ya Isa Yana sakani zafin zuciya da yawa.
Fura me sanyi anty zarah ta zuba Mata ta miqa Mata Wanda itace ke cewa tafisonta da sanyi sosai idan ba hakaba Bata iya Sha abin Sha idan baida sanyi Sam.
Karba tayi ta shanye atake tana cewa aqaro Mata saidai aka miqa Mata jug din daya Gama daukan sanyi shima.
Shan furar takeyi sunata kawo Mata firarraki kala kala Dan dauke Mata hankali kota cire damuwa da tsoron kwata kwata,
Sai dare dukkaninsu suka watse aka barta daga ita sai iyami sai anty salamatu dasuka Zo taredasu maman junior dasu maman basiru Dan dubata kowanne dauke da kularsa ta kayan gargajiya na marmarin me ciki,
Maman junior sakwara da jar Miya ta kawo Mata wadda taji yaji sai maman basiru data kawo Mata danwake dayaji salad da kwai anty salamatu ma taga soyayyar gyada ahanya da Madara gasassa ta siyo Mata duk saitaji idanuwanta sun cicciko da hawaye har batasan lokacinda tasakesu tana sunkuyar da Kai sbd ayau tasake tabbatarda ba jininka ne kawai Dan uwankaba wani Dan uwanma yafi na jini,
Bata damu da son sanin asalintaba ko jininta wainnan bayin Allahn sune Yan uwanta sune jininta sbd suna qaunarta tamkar jininta Dan haka Bata buqatan sanin inda ta fito Dan kula kawu da iyami tareda usinta sune asalinta hakanma ya Isa rayuwa Alhamdulillah.
Share Mata hawaye anty salamatu tayi tana cewa''
To meyene na kuka Bayan Dr tace ko damuwa ba'a so bare Kuma kuka,
Wannan abin damukeyi duk yiwa Kai ne sbd mu tamkar zuria daya ne idan baki manta ba yawancinmu dake gidan bamuda zuria,bamuda dangi mune Yan uwan junanmu Dan haka meye abin damuwa aciki.
Iyami dai batace komaiba sbd ita wani lokacinma ayanda takejinsu aranta har mantawa takeyi da ba itace ta haifesuba sbd har cikin ranta take qaunarsu a haqiqanin gaskia.
Take suka cika dakin da hayaniyar gida dasuka Saba ana tuttuna baya da irin fadace fadacen dasuka sabayi Wanda haryanxu ba dainawa sukayiba Nan take ta sake saigata ta washe acikinsu tana walwalarta harda dariya da qyaqyatawa
Taci sakwara kadan hakama Dan waken taci sosai shikam kafin ta Dora da masararta tanaji suna firarsu Basu bar asibitin ba sai goma da wani Abu kafin suka tafi anty salamatu ta rakasu kafin tadawo Amatun tayi bacci cikin nutsuwa Wanda ta kwana biyu batayiba.
Washe gari da Dr Fatima ta auna BP dinta taga ya sauka sosai sai abin yabata mamaki takalli iyami cikin Jin Dadi tace"
Tayi bacci ne sosai jiya?
Eh Kam jiya tasamu bacci Dan sallah ma saidai da safen Nan tayita.
Masha Allah gskia idan da zata riqa samun hakan to da Inshallah komai zaizo da sauqi yanda mukeso.
Jin hakan yasa iyami ta aika salamatu tayiwasu maman junior Magana akan su riwa zuwa Dan Allah suna kawowa Amatun firar dare
Ba musu suka amince sbd Suma zasuso tasamu lafiyar.
Aikuwa tuni asibitin Takoma majalisar 'yan gidansu Dan kuwa idan sunayi dariyar Amatun har qofan daki anaji umme ma data ga hakan saita qarawa zuwan nasu armashi ta aiko musu da lafiyayyan abinci da pepper chicken na kaji kullum aikuwa Suma ganin wannan dadin yasa suka sake dagewa da kullum gida suke kwaso abinsu sai sun iso gida araba abawa kowa nasa Kuma kajin ba 'yan kadan ba ga drinks gakuma kudin abin hawa da anty zarah ce itakuma ta Basu Wanda zasu riqa amfani dasu Dan da farko kawu ne duk sukazo yake Basu na komawa sai anty ZARAH ta dauke Masa wannan nauyin.
Kwananta takwas a asibitin ranar na Tara ta tashi da wani mummunan ciwon kai wanda yasanya jini da ruwa 6alle Mata take hankalin dukkanin likitocinta tashi musamman Dr Fatima
Su kansu su umme dasu kawu kowa yashiga tashin hankali musamman ganin yanda take wani wani Abu kamar jijjiga haka aka kwasheta akai labour room da ita aka barsu tsaitsaye suna Kai kawon jira cikin rashin hankali.
Kafin qarfe hudu na yamma dukkanin 'yan uwanta da wasu daga cikin familyn ZABEERA suna asibitin Babu me wata walwala acikinsu sbd har lokacin Babu wani labari daga likitoci sai yawo ake ana fita ana shiga.
Dr Fatima ce ta fito Bayan tayi waya da Modibbo ta sanar Dasu komai na halinda ake ciki ta kalli kawu da umme da iyami dake gabanta cikin office dinta dake cikin labour room cikin tsananin damuwa da sanyin jiki tace"
Wato Abinda ake ciki shine Amatu bazata iya haihuwa da kanta ba sbd lokacin haihuwar baiyiba gabanta ko kadan bai Fara budewaba gashi baza'a iya jiraba sbd qarfinta zai qare hakama babyn ruwan dayake ciki kowane lokaci zasu iya tsiyayewa Wanda hakan na faruwa hadari ne Mai matuqar girma Kuma barazana ce ga rayuwarsu su duka,
Dan haka bazamu Bata lokaci ba na sanarwa su Modibbo zamuyi Mata aiki saidai Abinda zata Haifa din zamu sakasa a kwalba sbd rashin isarsa haihuwa idan Allah yasa andace...
Tsit sukayi kamar wainda sukaji mugun labari,
Koda yake kusan hakan ne Dan umme tuni tafara hawaye sbd tasan rasa babyn zatayi kamar yanda ta rasa Khalil dinta.
Numfashi kawu ya sauke cikin jarumata yace"
To shikenan likita ba damuwa ayi aikin Allah yasa hakan shine mafi alkhairi yasa Kuma ayi cikin sa'a.
Amin tace tana qoqarin amsa wayarta da Kiran MAHMOUD ZABEERA ke shigowa Dan takirasa dazun bai dagaba.
Itace tafara Magana sbd tadan fahimci bai cika maganaba yafi saurare Dan haka Bayan ta Masa ya aiki saita Fara koro Masa bayanin halinda ake ciki ta Dora da cewa''
Modibbo yace Kaine zaka saka hannu a file din gashi Kuma bakanan and bazamu iya wuce Nanda 20min ba bamu Shiga da itaba ba sbd.......
Kai tsaye cikin wata murya me sanyi ya katseta da cewa''
I will be there in 10min yanzu nake baro airport.
Kafin tayi Magana ya datse wayar ya ajiye gefensa ya sauke sanyayyan numfashi tareda rufe Ido ya bude ya kalli Mal Umar yace"
Mal Umar Yi parking.
Ba musu yayi parking din saiyaga ya fito daga Bayan motar ya zagayo gurin sit din driver ya bude yace"
Fito ka koma baya zanyi tuqin.
Fitwo Mal Umar yayi da sauri batareda yace komaiba duk da Yana cikin mamaki Amma dai sanin ba Abinda yafi tsana wani lokacin kamar tambaya yasa baice qalaba ya zagaya ya Shiga dayan gefen ya zauna.
Batareda ya kalli gefen mal Umar dinba Bayan ya shiga ya tayarda motar yace"
Saka seat belt dinka.
Da sauri ya janyo ya saka.
Wani lafiyyan speed yabawa motar Wanda yasa Mal Umar saurin hade qafafunsa Yana hadiye yawu tareda damqe qofa Yana zazzare idanuwa dan ba halin Magana bare ya nuna tsoronsa,
Allah ya kaimu inda zamu lafiya yafada cikin ransa Yana satar kallon MD din dake sake bawa motar wani mugun speed din Wanda yamanta rabonsa da irin wannan tuqin qila tun Yana cikin samartakarsa idan Khalil ya matsa Masa Akan suyi tseren mota a Sudan idan yaje gurinsa.
Fitowa Dr Fatima tayi daga labour room sanyeda kayan CS tana duba agogon wayarta datakeson kashewa kafin Shiga CS din taga minti Tara kenen da wayarsu da MD Amma haryanxu shiru ga kowa jigum jigum shi ake jira yazo yasa hannun ga Modibbo ma ya iso asibitin Amma baisaka hannunba yace ajira MAHMOUD din tunda yace abasa mintuna kadan...