← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 70

Sashe 17

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aje tray din zarah tayi tana murmushi tace"
Amatu tunda aka banike nasan hidimarkice yanzu nafara harsai kin haifarmana me kama da Dr dinmu kokuma gwara dai ki haifar Mana me kama da MD dinmu dagani har Dr din saimunfi sonsa sbd MD shine 'dan uwanda Dr yafiso acikin familynsa gaba daya,
As for me nikuma MD shine rayuwata.

Apple amatu tayiwa babbar gutsura tana ci tace"
Anty Dr Yana ina yanzu?

Yar dariya zarah tayi tana zuba Mata Salad Kan dafaffen dankalin da aka dafa matashi da zallar Naman kaza da cabbage tace"
Dr Yana bangarensa Amma nasan tunda matarsa da babynsa na Nan bazamu Kai dare batareda yazoba Dan haka ki kwantarda hankalinki Dr nanan zuwa idanma baizoba zankirasa yazo.

To kawai tace tana cika bakinta da dankali da nama sbd 'dadin da abincin take Mata tace"
Anty idan nagama cin abinci mezanyi Kuma??

Bacci zakiyi ki huta amatu kafin zuwa gobe zanfadawa MD saimu kirawo Dr dina yazo afara dubaki da lafiyar baby.

Sarqewa tayi da qarfi tasaki tari Jin Abinda zaran tace.

Da sauri Zara ta dauki ruwa tana miqa Mata tana Mata sannu tace"
Amatu kodai abincin be Miki bane??

Girgiza Kai tayi da sauri har lokacin tana tari tace"
Ba Dr ne zai ringa dubani ba tunda shine Mijina??

Aje cup zarah tayi tana cewa''
Aa Dr bashi zai ringa dubaki ba munada Dr dinda zai ringa dubaki wato gynecologist Dr likitan Mata Wanda Nima shi nake gani sbd matsalar rashin haihuwarta.

Shiru amatu tayi tana tura abincin kawai sbd tasan ba jimawa asirinta zai tonu duk aka kawo wani likita yadubata zaisan batada ciki
Andi sakawa zaiyi a harbeta da kibiya sbd da gaskia ta fito.

Tana gamawa zarah tasata kwanciya bayan tayi sallah ta rage Mata sanyin AC ta fice bayan tasa hafsatu ta gyara gurin suka ja Mata qofa.

Shiru tayi tsawon mintuna tana tunanin goben idan likita yazo
Miqewa zaune tayi tana cewa''
Dole Naga Dr khalil yau nafada Masa kafin goben Amma dai yanzu inason Fara magana dasu usi.

Jakarta da aka saka cikin wardrobe ta bude ta dauko matacciyar wayarta ta lalulo numbrn USI ta Danna Masa Kira.
##mamuh##
______________
KUNA BU
ATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES
IN BOOKS
IN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon hazi
an marubanku
an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da sa
o ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai bu
atar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntu
ar wa
an nan Numbers 0903
5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks
in kana bu
ata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi.

Idan kuma wasu adadin pages kake bu
ata koda
aya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sau
in gaske
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sau
______________________
#MIN QALB
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/23, 1:35 PM] Zafafa: *_MIN QALB 14_*
_mamuhgee_
ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!!

JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku,
Turarensu qarshene,
Qamshinsu na daban,
Kayansu tabbataccine,
Aikinsu ingantacce ne
shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa?

To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar.

ANNUR PERFUMES donjindadin customers
munkawo muku dadadan turaruka na musamman
masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha
Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari
ina kano gaida layin
massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.

ANNUR PERFUMES
TURAREN WUTA
KHUMRAH.

KULACCAM
MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/B
LACK AND RED MISKI)
DECORATIONS ..

KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)
TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!
**************
Ringin numbern usi din keyi harta katse bai daga ba tasake Danna Kiran tana cewa'
Usi idan muka hadu saina fasa maka baki da kai tunda har zaka iya bacci baka kirani kaji Yaya ta kasancemin ba a wannan zabeerar da kallo daya Andi da Modibbo sukewa mutum sai cikinsa ya mur'da,
Uwa uba arasa gurin ajeni sai anan cikin wannan me bada tsoron da matarsa.

Kira biyar tayi Masa Amma baa daukaba takira wayar iyami cikin sa'a kuwa ta dauka Nan suka jima suna mgn iyamin na maimaita Mata karta taba duk Abinda zata gani na kowa karkuma ta jawowa kanta fitina ko rigima ta jawo musu kafin aka miqawa kawu wayar Shima dai yayi Mata maganar karta taba abun kowa sbd kada 'yan kudin Nan dasuka samu su qare a gun kashe rigima Shima usi sunfada Masa kada ya kuskura ya janyo rigima sbd tanadin kudin Nan zasuyi sbd abinci dakuma qarasa hada takardun komawarsa karatu.

Fadawa lafiyayyan gadon tayi ta kwanta tana lumshe ido bayan tagama wayar
Tai wani juyi tana lulluba da bargon me shegen laushi sbd sanyin AC dake ratsata ta lumshe ido tana cewa'"
Masu kudi wato ko a gurin bacci sunfi talaka samun nutsuwa
Da agidanmu ne da yanxu radion kawu da qarar dakan turmin maman junior da qarar bude tukunyar maman basiru sun Hana mutum bacci,
Rufe idanu tayi tana sake gyara kwanciya take bacci me dadi yayi gaba da ita ga gajiya ga lafiyyan abinci dataci ga lafiyayyan gurin kwanciyar dakuma sanyin AC ga ba hayaniya ai Dole baccinta yau yayi dadi.

Saida garin ya hantse ta tashi tana wata irin miqa me Dadi fuskarta a sake da farin cikin irin baccin data samu tana qoqarin saukowa gadon ne zarah tashigo daukeda sababbin brushes da toothpaste masu kyau tana kallonta tace"
Amatu Yaya? kintashi lfy?

Ya babyn dr?

Qarasa saukowa gadon tayi tana sake yin wata doguwar miqar datasa zarah saurin ajiye kayan hannunta tana riqeta tace"
Amatu zakiwa kanki illa idan kina irin wannan miqar
Idan kinajin gajiya ne za'asa ayi Miki tausa ahankali Amma Dan Allah ki daina kinji??

Kallon sakarai amatu ta Mata Jin hadda miqar ma yanxu wani tsurku zaa kawo sbd ciki...

Amma dai ko yayane bazata Bari banxa ta wucetaba tubda damace tasamu gwara ta dama kafin Takoma inda tafito Dan haka sai ta 'dan yamutsa fuska tana 'dan dafe bayanta tace"
Anty zarah ko Ina jikina ciwo yakeyi na gajiya shiyasa nake 'yar miqar ko zanji jikin ya sake Amma tunda kince za'amin tausa inaga idan anyi zanji jikin ya saki.

Murmushi zaran tasaki tana sakinta Takoma gaban mirror ta dauko toothpastes din different flavors kusan kala biyar tace"
Ga Macleans ki bude kowanne kiji Wanda qamshinsa ya Miki Wanda bazai tayar Miki da zuciyab saiki ringa amfani dashi.

Karba tayi tana washe baki tana duddubasu tace"
Duka ma sunmin abarminsu kowanne
ma qamshinsa zaimin sauran gida zanje dasu idan zantafi.

'yar dariya zarah tayi tana girgiza Kai rashin damuwar amatun na sake burgeta musamman data 'dan Fara lura tun jiya inda amatun tafito tana tareda yunwa gskia Dr be kyautaba barinsu su wahala haka tana matsayin matarsa bayan duk arzikin dayakedashi.

Fita tayi Takoma kicin ita Kuma amatu toilet tashiga tafara yin brush da kusan toothpaste kala hudu kowanne saidata fasa ta 'dan lakata tayi dashi take bakinta suka ringa bada wani qamshi masu Dadi dasuka sakata yin wanka cikin nutsuwa da annashuwa.

Tana fitowa saidatayi sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar jallabiya Mara nauyi Wanda duk zaran ce takawo Mata daga gani duk nata ne Amma suka sabbi ne Babu Wanda ta taba sakawa.

Tana cikin fesa turare tana lumshe ido cikin jin Dadi tace"
wainnan turaren dasu zankoma gida idan zankoma ma komai saina dauka naje dashi bazanga irin wannan Batinba nabariba.

Turarukan ta kwashe duka tabude wardrobe tazubasu cikin Jakarta daga can qasa ta rufe zip din tadawo gaban mudubin tana gyara zaman rigarta a jikinta saiga zarah tashigo tana kallonta Jin dakin yacika da qamshin turaruka yasata Dan 'yin tari tana cewa'"
Amatu wannan turarukan bazasu cutatar dakeba kuwa
Qamshin yayi yawa Zo muje dining muci breakfast idan Kuma akwai Abinda kike buqata ba Wanda akayi ba sai hafsatu ta Dora miki ga Dr khalil ma yazo Yana palon MD suna Magana.

Ba qaramin Jin Dadin zuwan Dr khalil tayi ba sbd sanar dashi Abinda su zarah din ke shirin Yi na Kiran wani Dr shiyasa ta farayin gaba tana cewa''
Ni komaima aka dafa yamin zanci Amma Dr nakeson Fara gani anty zarah Dan Allah kinji.

Biyota tayi tana cewa''
Wannan rashin hkr haka amatu bazaki jira yagama yazo yasameki har dakin ba.

A palon ganin Dr khalil baida lokacin fitowa daga gurin MD yasa ta marairaicewa zarah fuska tana taba cikinta
Take zarah ta tashi da kanta ta hado Mata nata abincin a tray sbd kada yinwa tai Mata illa sbd cikin dake jikinta bazata iya jiransu ba.

Dakinta Takoma acan tayi zaman Yan bori akan carpet tafara cin lafiyayyan breakfast din tana bude plate din farfesun kifin da akayi kawai sbd ita dayaji kayan qamshi da 'dan yaji batasan lokacinda tasaki dariyar farin cikiba tana diba takai bakinta saiga Dr khalil yayi knocking yashigo fuskarsa tayi wani iri na yanayin damuwar dake tattare da ita.

Tsayawa yayi daga bakin qofar ya qura Mata ido yanda take cin abincin sosai cikin Jin dadinsa dakuma bayyanarda baqone agareta sai yaji jikinsa yasake yin sanyi ya rintse ido Yana Jin zafin zuciyarsa na qaruwa sbd baisan ta Ina zaifara da wannan qaqqarfar rigimarba sbd Nan ana Magana ne akan ciki da aure Wanda baa Wasa dasu sbd komai dadewa gskia zata fito idan akwai idan Babu,
Ta Yaya zaifara neman mafita?

Ta Yaya zaifara neman inda mafitar cikin amatu zata fito?
Chapter 17 · 0% Book details