Sashe 29
Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda suka fito a hanyarsu ta komawa suka hadu da Nuratu tana ganinsu tahau yada maganganu in marasa Dadi Har Amatu zata tankata anty zarah tayi saurin riqo hannunta tajata
sukabar gurin sunaji tana cewa zarah din munafuka Amma Basu kulataba suka wucewarsu.
Da yamma Salman da kansa yazo ya maidata asibiti tasake ganin Dr Fatima suna baro asibitin kamar a mafarki sai kawai tagansu qofar gidansu yayi parking mota
Da sauri ta juyo ta kallesa bakinta da fuskarta daukeda tsananin mamaki da farin cikin dayasa takasa mgn sai kawai ta bude motar ta fito da gudu tayi ciki.
Da iyami tafara cin karo a tsaye tana kwashe shanya cikin tsananin farin cikin ganinta ta rungumeta tana cewa''
Iyami wlh bansan haka nayi kewarkuba sai yau Dana ganni a qofar gida Ina kawu da usi???
Kawu dake fitowa daga daki Yana jinta dama ya fito Yana ganin yanda Amatunsa ta koma take ya washe baki Yana cewa''
Maza kuzo mu shige daki kada Ido da baki suyi Miki yawa kinsan gidan harda qarin 'yan bani na iya aka samu.
Dariya tayi tana sakin iyami tace"
Yanzu nasan Ina gaban kawuna.
Kallonta iyami takeyi itama cikin Jin Dadi da farin cikin ganin yanda ta sauya tayi kyau kamar 'yar masu kudi har wani qyallin haske fatarta keyi ga suturar alfarma ajikinta sai annushuwa takeyi.
Dakin suka nufa suka zazzauna Nan aka nude sabuwar fira saiga shima usi dake shirye shiryen tafiya jibi yashigo Nan aka Dora firar ga fankasu da iyami tayi aranar dayaji miyar Naman rago da Ganda Nan aka kawo musu suka hau ci suna Santi musamman Salman dan shima yamasa Dadi matuqa.
Suna Nan saiga Kiran Dr khalil yashigo wayar kawu dauka yayi suka gaisa ckin sakewa kamar 'dansa na cikinsa yakejin khalil sbd shiga ransu da yayi iyami ce madai takejin nauyinsa na sirikantaka sbd tuntuni sunsan Amatu yakeso Dan Yama fada musu Kuma sunyi na'am da hakan jira kawai suke tadawo asa ranar aure,
Sabuwar Hira suka Dora da Dr din a waya su Amatu na fada Masa Abinda suke ci Yana cewa''
Umma iyami idan nadawo Nima shi zakibani wandama yafi nasu Dadi.
Murmushi iyamin tayi cikin Jin nauyinsa tace"
Khalilu duk Abinda kakeso idan kadawo Inshallah duk sainamaka su.
Yawwa nagode umma.
Kawu ke tambayarsa ya aikin dayaje yi dafatar akwai nasara??
Eh yace Masa Yana qarawa da alhmdlh Inshallah muna gamawa zan juyoma.
To Allah yakawo ku lfy.
Amin
Basu bar gidanba sai kusan yamma sosai Wanda anty zarah tayi musu Kira yafi a qirga
Itama Saida iyami ta hado Mata fankasu suka je Mata dashi.
Kamar kada su tafi hakanan ta fito suka tafi tana sake dagawa Yan gidan hannu kowa nasakejin kamar kadata koma.
Saida suka biya sahad yayi Mata soyayya sosai har abin na Bata mamaki Amma ganin yanda ya dauketa kamar 'yar uwarsa ya nuna bayason godiyarta da mamakinta itama saita daukesa kamar usi Nan suka sake shiriricewa sai magriba suka kamo hanyar gida.
Suna tafe suna fira harda qyaqyata dariyarsu sukeyi Yana tuqi da gudu gudunsa aikuwa Basu ankaraba wata mota tayo Aron hannu a guje itama me motar yake tahowa,
Cikin wani razanannen firgici yaso kaucewa Amma ganin akwai express dayan gefen sai kawai yayi dayan gefen sukai Kan wata bishiya suka daketa Amatu da tuni ta saki ihun sadaqarwa kanta ya daki qofar motar tsananin tsoro da firgici yasata somewa agurin.
Cikin sauri ya juyo Yana qoqarin dagota Yana Kiran sunanta da qarfi cikin damuwa sbd yasan suman tsoroce kawai tayi gashi Babu wani abindama yafaru din sbd bai daki bishiyarba sosai.
Ruwan dayasha ya rage kafin alamarin ya dauka ya shafa Mata saigata tasaki nannauyan ajiyar zuciya a rude tana cewa''
Wlh banason na mutu yanzu saina cikawa Dr khalil burinsa na aurena.
Dariya maganarta ta basa duk da ta daki zuciyarsa Kuma.
Cikin kulawa yace"
Nima banason ki mutu sainaga rabon wace ke a qarshe.
Kallonsa ta juyo tayi cikin rashin fahimta tana qoqarin sake dawowa nutsuwarta.
Murmushi yayi tareda tayarda motar yayi ribas sukabar gurin Yana cewa''
AMATULLAH ki dinga tuna sauran bayin Allah yayin yiwa mijinki na baa dauraba addua.
Sake rudata yayi tasake juyowa gabaki daya tana kallonsa saidai ganin kamar reaction dinta nasake basa damar yadda da hasashensa koma dai yardarsa sai kawai ta basar da zancen tana dariyar tsoron dataji da sumanta tana cewa''
Dan Allah Dr Salman kada anty zarah tasani
Tana sani zata Fara daga hankali ta fadawa Dr banaso ta daga Masa hankali.
Sai alokacin ya Dan juyo ya kalleta zuciyarsa na wani sarawa Yana maida hankalinsa Kan titi cikin sautin nutsuwa yace"
Idan zuciyarki na tsananin kulawa da qaunar Khalil haka
Meyesa zata so MD ZABEERA???
Cak ta tsaya gabanta yayi mummunan faduwa Amma sbd Bata fahimci zancen nasaba saita saki wani yaqen dolen Dole tana kasa juyowa ta kallesa tace"
Meye hadina da Rabin ran Anty zarah kuma?
Ko gaisuwa Bata hadani dashi bama ya cikin mutanen danake qauna gaba daya sbd halayensa na wulaqanta antyna.....
Baya cikin wainda kike qauna sbd shi sonsa kikeyi Amatu.,
Amatu bansan meyasa shedan yake yawo atsakaninmu ba dayake haifar Mana da wani tunanin dabai kamataba bayan sanin cewa ke amatsayin matar khalil kike,
Amatu nafada Miki hakane Dan kije kiyi tunani kada ki auri Wanda farin ciki ya cancanta a rayuwarsa ba dakon son maso wani ba,
Dr Khalil zabeera shine duk duniya cikin maza ayanzu yafi cancanta daya asameki gaba dayanki daga zuciya har ruhi da ganganr jiki
Dan haka kada ki azabtar da rayauwarsa ta basa gangar jiki da qauna kawai
Yana buqatar dukkanki gaba daya har soyayyarki da zuciyarki sbd koba komai shi din Asthmatic patient Wanda yakeda alaqa da zuciya
Dan haka AMATULLAH kije ki zauna ki nutsu kiyi tunani ki Fara koyawa zuciyarki soyayyar khalil ba qaunarsa ba soyayyarki yake buqata.
Kallonsa takeyi sosai kanta na neman bugawa da maganganunsa ta girgiza Kai Yana rintse ido cikin rudewa take cewa''
Mezaisa naso Rabin ran Anty zarah ni Dr nakeso, shikadai nake qauna, shikadai nake tunani shikadai nake gani, shikadai nake.......
Mafarki fa???
Tsit tayi tareda kasa qwaqqwaran motsi sbd Jin tambayarsa,
Idan har ba qarya zatayi Masa ba to tabbas 'daidaikun ranakune Bata kwantawa batayi mafarkin Rabin ran antynta ba.
Cikin firgici ta dago idanuwanta na cikowa da hawaye zatayi Magana yayi parking Yana cewa''
Mun iso gida.
Da sauri ta juya ta kalla waje tagansu qofar part dinsu anty zarah din
Ta sake juyowa gurinsa zatayi Magana cikin rawar murya da sarkewar tunani
Ya katseta da sakar Mata murmushi me sanyi sbd jikinsa da zuciyarsa dasukai sanyi idanuwansa na Dan sauyawa sbd yanayinta ya Gama tabbatar Masa da hasashensa katseta yayi cikin sanyi da cewa''
Kije ki zauna kiyi tunanin Abinda yakamata.
Shiru tayi tana kallonsa kamar bazata fito motarba saigashi kuwa motar MD ZABEERA ta iso gurin yayi parking Dan da kansa yayo tuqin yadawo gida.
Motarsa ta qurawa ido zuciyarta na bugawa da sauri da sauri kamar zata bullo qirjinta ta fito,
Saida yadauki mintuna biyu zuwa uku kafin yafito motar Yana amsa waya fuskarsa a 'dan sake Wanda yasata kusan suman zaune da sauri ta rintse idanuwanta tanaji kamar yanzu ne da Salman yayi maganar ya zuba Mata son MD din me tsanani cikin ranta ta girgiza Kai da qarfi Yana cewa''
Bazan taba son Rabin ran Anty zarah ba.
Bude motar tayi da sauri ta fito batareda ta sake waiwayo Salman ba Wanda tunda motar MD tashigo fuskarta ya tsurawa ido
Jan motarsa yayi yabar gurin Yana sauke numfashi me zafi ya nufi gurin mum dinsa da tun rana take kiransa duk tabi ta hargitse ta daga hankalinta akan alaqarsa da Amatu Wanda yakejin da akwai matsala Dan kuwa kome zatayi bazai iya rabuwa dasu Amatu da familyntaba.
A sukwane tashigo ba cikin hayyacintaba tayi nisa cikin tunani da fargaba tareda tsoro taji andafa ta tayi saurin dagowa sukai Ido biyu da anty zarah tana sakar Mata murmushi tace"
Amatu Yaya dai?
Sai yanzu kuke dawowa tundazu nakira Usman yace kunbaro.
Qaqalo murmushi tayi tana qarasa shigowa palon tace"
Wani guri mukaje Salman yayi min siyayyar kayan babies da kayan dadi" ta qarasa fada tana qaqalo dariya sbd kawar da banzan tunanin dayake yawo cikin kanta.
Siyayyar ta miqawa anty zarah tareda fankasu din dasuka Zo Mata dashi
Cikin farin ciki ta karba tabawa hafsatu tace ta zubo Mata a plate
Ita Kuma dakinta ta nufa Dan yin wanka ta gyara jikinta Amma cewa anty zaran tayi zatayi sallah ne.
Wankanta tayo tareda shiryowa cikin riga da wandon bacci masu Dan kauri ta sanyo qatuwar rigar sanyi akai sbd ana Dan sanyi gashi gidan Sam komai sanyi sunsaba da rayuwar AC ta sanyo hula tareda slippers ta fito tana waya da Dr khalil Wanda yanzu take tsananin Jin kunya da tausayinsa.
Cikin annashuwarta ta fito suna wayar harda 'yar dariyarta sosai sbd labarin abincin dasuka ce na 'yan Chinese yake Bata kamar zaiyi kuka da amai
Ganin yanda labarin ke sakata nishadi yasa yaketa Jan labarin Yana sake fada Mata yanda kalar abincin yake da yanda ake cinsa sbd walwalarta na basa farin ciki da nutsuwa.
Dining ta nufa tana sake qyaqyata dariyarta datasashi tsayawa cak daga cin abincin dayakeyi akan dining din tareda zarah wadda yau duk farin cikinta a bayyane yake sbd gata ga Rabin ranta suna cin abinci tare.
Qoqarin zamata takeyi a dining din idanuwanta suka sauka cikin nasa daidai dagowarsa ya kalleta da idanuwansa dasuka narketa gaba dayanta saita samu kanta da kasa dauke idonta daga kansa zuciyarta na harbawa ahankali.
Sarqewa yayi sbd wani dalili daya kasa sani yafara tari ahankali Yana Kare bakinsa da tissue
Anty zarah dake Shirin Magana tayi saurin daukar ruwan sanyi zata miqa Masa daidain Amatun ita Kuma ta miqa Masa juice cikin cup.
Kallon juna sukayi itada anty zarah din tayi saurin dire cup din tana barin gurin da sauri ya 'dan bi bayanta da kallo qasa qasa ahankali kafin ya karbi ruwan hannun zarah din yakai bakinsa ya kurba kadan ya ajiye yakai hannunsa ya dauki cup din juice din yakai bakinsa yasha kadan sai kawai ya miqe Yana cewa''
Alhmdlh I'm full.