← Book details Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 70

Sashe 55

Min Qalb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa.[5/29, 10:35 AM] Zafafa: *_MQ 41_*
*_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_*
Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi Amatun dauke wuta tana cewa''
Anty zarah sannu da zuwan bazata.

Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema ta rasa sai kawai ta 'dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace"
Amatu sannu da gida mun sameku lfy?

Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki tana cewa''
Alhamdulillah anty.

Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba'a iya ganewa sai kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana 'dan satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye tray din gabansu tace"
Dady sannu da zuwa.

Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty ko ruwan yayi sanyi ne da yawa.

Batareda ya kalletaba yace"
Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita urgent.

Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace"
Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner.

Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa''
Ina zuwa anty idan akwai Abinda za'a yi Miki ki kirani.

Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah.

Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi tana cewa''
Ya Salam.

Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.

Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage source me
kidney aciki.

Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren 7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta 'dan gaji.

Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci.

Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai tsaye ya nufi
dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa.

Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda tray
Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta shiyasa ya bude matan.

Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye abincin tana cewa''
Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce?

No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha magani.

Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace"
Zansha magani Ina buqatan ruwa.

Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa.

Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa ya miqe yafito hannunsa daukeda magani
Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani
Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace"
Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka..

Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana kallon
tsoron dake bayyane fili akan fuskarta
da bakinta dake Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta
ankare da inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa tace"
Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam.......

Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe tace"
Dan Allah anty zarah nake gudun ta.....

Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi.

Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama.

Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta durqusa tahau kwashe plates din tana cewa''
Anty zarah Yi hkr wallahi.....

Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da danne kukan dake zuwar Mata tace"
Saida safe zanje na kwanta.

Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake Shirin kufce Mata.

Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA.

Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar.

Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school.

Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be tashiba tunda bataji motsinsa ba.

Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi.

Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta ma
anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace"
Good morning.

Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa ta dubo Amatu.

Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita to
Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce makaranta.

Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi ahankali.

Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa noodles da kwai
itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd yafi Mata dadi.

Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa sukuma suna tafiya.

Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta..

Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace"
I love you so very much MAHMOUD ZABEERA..

Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga Abinda tafada din.

Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace"
Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi.

Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri ba.

Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa''
Bari nashiga ko sallah banyiba wlh.

Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan
juya yabi bayanta da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje.

Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba suka fice.
Chapter 55 · 0% Book details