← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 43

Sashe 32

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallan yai kafin yai murmushi Ya ajjiye kayan hannunshi Ya nufi inda take,duk ta tsotara kawai dakewa take ta kasa matsawa daga gun, karbar comb din hannunta yayi kawo in tayaki ,Da sauri taja baya bana so Amman taki yadda su hada idoma, karbar comb yayi Ya Fara taje mata nifa ban ganeba naga sai wani sasanne kai kike KO lafiya, ya fada Tana kallan ta,batace mai komaiba illah juyar Da kai kawai Da tai ,ajjiye comb din yayi sannan ya dauki ribbon ya daure mata kai, An gama anya ba za,a rage wannan gashinba indai yana takurawa Matata, batace komaiba illah wucewa datai tare da fadin thanks sannan ta dauki dankwalinta tasa, daukan kayanshi yayi kafin Ya kalli agogan shi 6:30 Yau da safe zan wuce basai nayi break bama kinji ina Da wani aiki,a dawo lafiyq Allah ya bada Sa,a murmushi yayi Dan yaji dadin maganar na gode Ya fada tare da ficewa,.

Gun motocinshi Ya nufa Ya dauki wacce zai dauka sannan ya fita daga masarautar, abakin hanya Ya hadu Da wani abokinshi hakan yasa ya tsaya Dan su gaisa, suna tsaye yaga wata motar masarautar tazo ta wuce Da wani fuskarshi a rufe kallan motan yayi har ta wuce jikinshi bai kwanta maiba hakan yasa ya yayi sallama Da abokin nashi Ya shiga mota yabi Bayan waccan motan, sunyi tafiya kafin yaga motan tayi parking a wani uncompleted gida,gaba sultan yayi saboda kar a gane shi Yai parking sannan ya dawo Da kafa ,kallan gidan yayi babbane sosai sannan ya shiga,.

Tafiya yake baisan inda yake saka kafarshiba to ina mutumin yaje,.
Sarki kuwa abinci Ya kawo masu Dan yace yanzu shi zai dinga kawowa saboda suyi bankwana .

Sultan dake tafiya jin ana magana yasa yai labe sarki ke fadin ai kasheta zanyi Na aika asan yadda zaai a Sa Ta fito indai hakan yaki faruwa kawai asa mata poison a abinci, zaro ido sultan yayi to wa sarki yasa a kashe, kallan Da wanda yake magana yai idonshi Ya sauka kan abdulsalam, a dan razane yaja baya tare da fadin uncle abdulsalam, Da sauri Ya juya Ya fuce.

By hajara Mami natty girl
[9/14, 8:59 AM] Hajaramami: 👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 76*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

```INDICATED TO MAMAN SHUKRAH AUNTY UMMI```

Mota ya koma zauna duk Ya shiga rudani wai dama uncle yana raye ku kuma aljanune suka bude Mai ido KO fatalwarshi Ya gani, no Amman gashi naga daddy agun har yana Mai magana wannan real ne to taya akai dama bai mutuba daddy Ya buyeshi kenan,gudun kar daddy Ya fito Ya ganshi yasa ya tada motan Ya tafi, haka yaje asibitin kowa kuwa yazo Dan meeting zasuyi, karasawa gunshi habib yai Ya bashi hannu suka gaisa, ya amarya, Hakan yasa sultan yin murmushi, aboki you look same how kodai amarya ta bata maka raine? No aboki wlh ba haka bane, aboki dama mutun yana iya mutuwa sannan ya dawo KO kuma wai Da gaske dama akwai fatalwa, zaro ido habib yayi subhanallah ba wani fatalwa a duniyar nan sai IN mutun Ya mutu kadinga mafarki dashi Amman there no something like ghost, ka gane batun mutun Ya mutu kuma dawo babau saidai indai dama can bai mutunba,ammma kai kuwa maye namun wadannan tambayoyin, hmmmm aboki Wanda nake tunanin Ya mutune yau na ganshi kuma a raye har yana magana da baban Hindu abun yaban mamaki fa aboki since wajen 19years kaga yadda ya koma Annman a hakan Kana iya ganin kamannin shi I am so shock aboki, to Allah mai iko, bari in mun fito zamuyi magana a kai,, Da haakan suka shiga meeting din KO was wajen meeting din Ma hankalinshi kwata kwata baya jikinshi kawai yana zaunene,.

Sultana kuwa Bayan Ta gama abun Da take ne ta fito parlour zataje bangaren momy, anan taga sabuwar baiwa, abayinta nada wata ta duka ta fara mata bayani, wannam daga wajen sarki take shiya kawota amatsayin baiwar Da zata dinga tayaki wasu aiyukan, kallan ta sultana tai waye Ya kawota baku fada inda bayiba kumama bana San da yawa zan iyayin komai Da kaina, Matar ce tai saurin karba, ranki ya Dade aiba ta haka bane dolene ake ba KO wannne bangare baiwa kuma dole suke karba saboda daga masarauta ne koda kina Da wani sakon Da kike San akai masarauta shine aikin mu, kallan ta sultana tai kwata kwata batasan bayi Da yawa gashi Matar Ma bata mataba, ganin irin kallan Da sultana ke mata yasa tai kasa Da kai tare da fadin innayi laifi tuba nake ranki Ya dade sunana marka, ganin matar tayi giving up ( sarrander )yasa sultana sakin fuska na gode marka Allah ya bamu zaman lafiya, Tana kaiwa nan Ta Fara tafiya Dan ficewa,baiwa daya ta biyu bayanta dan rakata bangaren momy din haka har suka isa,.

Da sallama ta shiga wannan lokacin momy na parlour farko,da murmushi ta karasa ta durkusa ta dauki gaisuwa sannan ta zauna kusa Da kafar momy din haka sukai ta hira daga karshe sultana ta shiga kitchen dan tace yau itta zatai mata girkin safe, Da taimakon bayin bangaren ta gama ta saka Tray sannan tai saman parlour dan lokacin momy ta koma sama,.

Ajjiye abincin a dining sultana tai sannan ta shiga ta fadawa mom Ta gama hakan yasa suka fito tare, zama momy tai Tana cin abinci sannan sultana take sanar Da itta zuwan Zulai, shikenan in tazo za muyi magana,.

Bayan sun fito daga meeting ne shi sultan duk Hankalinshi yayi gida, hakan yasa habib bai tsayar dashiba yaka Kama hanyar zuwa masarautar, yana parking bangaren momy ya nufa yai sama, ganin bata parlour yasa yai dakinta Da sallama Ya shiga, sultana na kwance akan duguwar kujeran dake dakin tana danne danne a phone dinta, zama yayi kusa Da momy, momy sannu Da gida,yauwa son Yau ban ganka Da safe ba, wlh mom meeting ne damu shi yasa banshigoba wlh har yanzu ban wani yi karyawar kirkiba, eyyya ga matar ka can saita maka girki, kallan sultana yai wacce ta juya mai baya bata San su hada ido murmushi yai, mom wai dama mutun yana mutuwa Ya dawo kuma ne? Ko kuma fatalwa gaskiyane, murmushi tai saidai indai dama bai mutunba kuma ba wata fatalwa,me Yasa kkake wannan tunanin, idonshi NE Ya kada mom uncle abdulsalam fa na gani kenan bai mutuba kenan? Mikewa mom tai son ban gane me kake nufi bafa wlh mom uncle abdulsalam naga ni shiya buyeshi kenan,.jijjiga kai Mon tai anya kuwa ba gamo kaiba sultan

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 77*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

```INDICATED TO MAMAN SHUKRAH AUNTY UMMI```
Zauna kawai yayi baice komaiba, sultana ta mike ta kawo Mai abinci duk sai taje jin ba dadi Da taga baya walwala,haka yaci abincin sannan ya Tashi ya tafi bangaren su Dan akwai abun Da yake San zai duba, kallan sultana yai itta yake San yaiwa magana so yake tazo suje tare kuma baiga alamar tana San tashiba, kallan mom yayi kafin Ya kalli sultana kizo muje inasan zan nuna miki wani abune, kallan mom tai momy ma hankalinta baya kansu, mikewa tai tabi bayan shi suka wuce,.

Suna zuwa Da sallama marka dake tsaye bakin kofar kitchen ta karaso ta zube tana kwasar gaisuwa agun sultan, kallan sultana sultan yayi wace wannan kuma? Wai sabuwar baiwace daga masarauta aka aikota, ko ina aka kai KO iya nan ne Ya fada yana kallan marka din aa ai dama sudin suna dasu nan dinne dai babu, tsaki yaja kije masarautar kice bama bukatar wata baiwa indai ina San zan aika sako Da kaina zanje, afuwa nake nema ranka Ya dade Amman yace kar in sake inbar bangarennnan, hade rai yayi tare da fadin get out plz, ganin Yadda fuskarshi ta koma yasa ta Tashi ta tafice,. Sama yai sultana tabi bayanshi, kowa Ya shiga dakinshi,.

Sultan kuwa kwantawa yayi yana tunani kowa sarki yasa a kashe, sultana ta fado mai kodai su sultana ta gani a dakin ajiya, no basu bane wannan aljanune,.

Haka yaita ta tunani har wajen sallahn mariba sannan ya tashi Ya wuce masallaci,.

Sultana kuwa hakan yafi mata kowa yai zamanshi a nashi banganren haka itta taita tunani KO ina su abbah suke yanzu Allah masani,.

Bayan sallar isha sultan yana tafiya yaji muryar Dady na kiranshi hakan yasa ya juya yana kallan daddy din gabanshi Ya fadi, bayi yace subasu gu hakan yasa suka bar gun,kalllan sultan yayi Nice akawo baiwa ka kureta bansan daliliba? Gyara tsayuwa sultan yayi saboda tsaro ban yarda Da itta bane saboda inaji akwai abun Da ake kullawa, kallan shi daddy yai kardai yasan me yake aikatawa, ban gane me kake nufibafa sultan, karka damu daddy ina binciken masu San kawo karshenmune ba wani abun daga hankali bane, sai safe Ya fada tare dayin gaba, Da kallo daddy Ya bishi kafin Ya gaba,.

Da sallama sultan ya shiga parlour lokacin bayin Sun tafi sultana ke zaune a parlour tana kallo, amsawa tai Tana kallan shi Ya zauna kusa Da itta tare da fadin washhhh na gaji sosai, mikewa tai ta nufi dining ta debo mashi abinci a tray ta kawo Mai ta ajjiye sannan ta zuba Mai, murmushi yai tare da fadin thanks, tai murmushi kawai hakan Ya gama cin abinci sannan ya zauna ayi kallan dashi.

Film din India ne na soyayya mata Da mijine ke soyewa hakan yasa sultana kasa nutsuwa duk tabi ta takura bata San kallan film din soyayya a gaban wasu duk kunya take ji, kallanta yayi ganin kamar ba a nutse take ba ,mutsawa kusa Da itta yai wannan film din Da ake kallo soyayyar Da zaa mun ake koya, abun saiya bata kunya yanzu zaice mata yar iska mikewa tai zata bar gun yai saurin riko hannunta Ya dawo Da itta, yaya sultan bacci nake ji, OK kije inasan ganin ki inkin gama akwai abun Da zan nuna miki, OK Ta fada tare da Tashi tai sama shima kashe wutan yayi yai sama,.
Wanka yayi Ya shirya Ya zauna yan jiranta,.
Chapter 32 · 0% Book details