← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct fada ta nufa, da zuwanta taji cewa baban Nata bai shigo ba tukun hakan yasa ta juya ta nufi part dinshi bayi na gaidata amma ko a jikinta burinta bai wuce ta ganta a gun baban taba, Da sallama ta shiga parlour, ganin ba kowa Yasa ta nufi stairs dai dai lokacin suka fito itta Da mamanta suna tafiya suna hira ,a stair Da take ta duka tana kuka ranta kamar ya fice, Da sauri ya karasa gunta yana fadin subhanallah me Ya faru?kara fashewa tai da kuka sosai, hakan Yasa sarkin riko kafadarta suka nufi parlour mama na binsu a baya ittama hankalinta ya tashi,.

Kallan ta yayi fada mun Waya miki wannan abun har ya saki kuka koshi dan gidan uban waye dole IN daukar miki fansa, kallan shi tai sai kuma ta karaa fashe WA da kuka, Dady An ci mutunci na An wulakanta ni duk akan baiwa,da sauri Mama ta tashi tana zaro ido uban waye yai miki wannan abun? Kallan ta Dady yayi fada mun aka miki, Dady me aka mun ba wannan bane kawai dai inasan ka nunawa sultan iyakarshi ka Aura mun shi ta hakane zan dauki fansa, kallan ta yayi shima kanshi yasan bai isa Da sultan ba Amman ina dole yaiwa yarshi abun Da take so, kallan ta yayi shikenan abun Da kike so baiwar haka xa,a barta? Murmushi tai kabarta Dady zanji Da itta wannan Bayan aure, murmushi yayi tare da shafo kanta yayi anythin for you my daughter kije zanyi magana Da momy shi nasan itta zata sashi ,murmushin jin dadi tai sannan ta share hawanyenta ta Mike fice, Da kallo mama ta bita tanajin tausayin yar tata Amman Ya zama dole su dauki fansar wannan abun, zuciya wasai Hindu ta nufi part dinta taji dadin abun Da Ya fada mata,.

Kallan shi sultana tai ganin yadda ranshi ya baci, kallan ta yayi kije ki hada mun breakfast Wanda baida wuya saboda Na kusa makara sannan kije ki shirya kizo tare zamu fita, kallan shi tai wannan Tashi daya yake canzawa kamar bashiba, wucewa tayi ya bita Da ido kafin yabi bayanta,. Kwai kawai ta soya Da dankali sannan ta hada tea ta kai mashi ta wuce bangaren su,.

Da sallama tashiga part dinsu Zulai Ta gani zauna kusa Da Zuwaira tana mata sannu, Da sauri ta karasa gun me Ya sameta? Sultana ta fada Tana taba jikin Zulai Da damuwa ta Kalli sultana bataji dadi ne wlh nig ke Da itta yau kwata kwata banganku ba da na tashi daga bacci, karki wani damu muna lafiya, abu muka fita yi kafin ki tashi karki wani damu, fita tayi kafin wani lokaci sai gata ta dawo Da magani a hannunta dauko ruwa tai ta mika mata Ta Tashi ta sha kallan su Zulai tai Bari zan tafi gun aiki kar suga bana nan, to kawai sultana tace taci gaba Da abun Da take ,saida ta gama abun Da take sannan ta Mike taje tai wanka ta shirya kallan Zuwaira tai wacce take bacci sannan ta ja kofan ta fice,.

Da sallama ta shiga part din nashi, mikewa yayi tare da fadin muje, ba musu tabi bayanshi, kallan shi tai dan bata San inda zata shiga ba gaba KO bayaba, ranka Ya Dade ina zan shiga? Duk inda yai miki ya fada tare da shigewa baya tashi GA ta zauna baice komaiba yaja motan sukai gaba,.

Tuki yake abun shi yana bin karatun dake Tashi a cikin motan, itta dai batasan inda suka nufa sai get da taga abun bude ana fadin barka Da zuwa doctor yau kaso makara inji masu gadin, wlh yau ban tashi Da wuri kallan motan mai gadin yau aa yau Da iyalin ake tafe, kallan shi sultana tai sai kuma ta Kalli sultan Wanda yake abun dake gabashi kallan mai gadin yayi aa kanwa tace, ayyo Mai gadin ya fada shi kuma yaja motan yai gaba, parking yayi Ya juya yana kallanta, fito mu tafi,ranka ya dade anan ake siyar da sim din, bansani ba yace tare da ficewa hakan Yasa itta ta fito tabi bayanshi duk inda sukaje sannu ake mai ana gaidashi yana amsawa, office dinshi suka je, ya bude Da sallama sannan ya ajjiye abun hannunshi, Ya dauki abun Da yake bukata, ki zauna ki jirani ya fada tare da ficewa

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 38*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Kallan office din take sosai yai mata kyau, idonta sauka kan hotan dake office din na momy ne itta Da wannan wacce take mafarkinta,.

Da sallama sarki two shiga bangaren momy yace Da bayinshi su tsaya a bakin kofa su jirashi, haka kuwa akai, yana zuwa duk bayin suka zube suna kwasar gaisuwa, sannan jakadiya tai ciki dan kiran momy, momy tayi mamaki sosai kuma ta tabbatar koma maye abune babba, hijab tasa ta fito parlour kuwa ya basu gu zama tayi suka gaisa,..
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Fara nasan dai kin hadina Da marigayi Yaya Mubarak kuma nasan inda yana raye ba abun Da zan nema a gunshi IN rasa,kallan shi tai Abdullahi baka Da wata matsala ka fada mun maye indai zan iya yi ba komai ni Mai makace,hmmm yai ajiyar zuciya, yauwa Na gode Da wannan magana Da naji, ina fatan kina sane da cewa sultan bai daukeni tamkar Mubarak ba ni nasan kinsan Da haka shiyasa dana tashi neman alfarma banje gunshi ba nasan abun Da babba zan gano yaro bazai iya ganowa ba, haka yake Abdullahi ka fadi koma Maye ina jinka,yauwa dama zumunci ne nake San mu hada mai zai hana tunda wadannan yara nasan junansu mu hada su aure ina nufin sultan da Hindu, kallan shi tai nadan second tabbas kafin Mubarak ya mutu yana fada kamata yayi adinga auren dangi a wannan masarautar mai zai hana indai Maman sultana ta haihu a hada su aure indai macece (lokacin Maman sultana nada ciki kenan, )Amman GA abun Da Allah yayi ME Yasa back zatabi wannan hanyar ba ta cikawa mijinta burinshi tasan wataran sultan zaiso hindu kuma Hindu zata shiryo, Amman matsalan ba anan take ba sultan dinne taya zata Mai wannan maganar,?

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli sarki ba matsala Allah Yasa Hakan shi yafi alkairi indai sultan yazo za muyi magana IN sayo sai kaji yadda akai, wani murmushin jin dadi yayi kafin Ya mike tare da cewa Allah ya taimake Ameena ta fada sannan Ya fice,.

Da sallama sultan ya shiga office din nashi, banda tsaki ba abunda sultana take dan duk ta gaji, kallan ta yayi tashi mu tafi, ranka ya Dade harka gama aikim ne? Baice komaiba ya fice hakan Yasa tabi bayanshi, mota suka shiga Ya mika mata sim a gidan shi sannan yaja motan, sosai taji dadi ashe Yasa a siyo basai tasha wuya ba,.

Na gode ta fada sannan ta kara kallan shi Zuwaira bata jin dadi ranka ya Dade inasan IN naje zan wuce part dinmu, OK kawai yace,...
Tana parking Ta kama hanya,.
Bagaren shi yaje ya ajjiye abun dake hannunshi KO hutawa baiyiba ya nufi part din Hafiz,

Da sallama ya shiga, Hafiz Ya juyo yana kallan shi Da kwalban wine a hannun shi, murmushi yayi Ashe babban bako nayi ya fada tare da zama akan kujeran daya dake parlour, kallan bayin parlour sultan yayi yace su basu guri, zaro ido Hafiz yayi yace kace abun babbane,.

Ya dauki wine zai kai bakinshi kenan sultan ya dauke yana bashi harara, zaro ido Hafiz yayi tare da fadin easy men Me ke damunka part dinafa kazo, zama sultan Ta yayi wai me Yasa baka Da tunanine mai Yasa kake San batawa yaran mutane rayuwar su,? Yanzu fisa billahi ka batawa yarinya rayuwa sannan bakaje kaga Lafiyarta ba? Gyara zama Hafiz yayi men ban ganeba go on straight to the point mana, Zuwaira Da kaiwa fade jiya bata jin dadi, a dan razane Hafiz Ya tashi baice komaiba Ya raba Ta gefen sultan ya fice hakan yasa sultan mikewa yabi bayanshi,.

By hajara Mami natty girl

👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 39*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```

Bin bayanshi yayi yaga inda zai nufa yana fita ya kira bayinshi kan cewa Sumai jagora zuwa dakin bayi na mata tunda bai saniba, angama ranka ya Dade sukayi gaba sannan aka Fara binshi a baya,

Tsaki sultan yayi KO Mai zaije yace oho Mai Amman gara ya bishi kar yaje ya cutar Da Yar matane tunda shine sanadi shiya fada mai,.

Cire Dan kwalin kanta sultana tai ta zauna kusa Da Zuwaira Da yanzu taji karfin jikin nata sai zufa take alamar zazzabin sauka zaiyi,. Sannu, murmushi tai nama samu sauki ina San zuwa in sanarwa Da Mama kartaga banjeba, da wanne karfin zakije daga tashi sai ki Fara yawo ai itta yakamata ta aiko taji KO lafiya bakeba kiyi zamanki zanje IN mata bayani,. To kawai Zuwaira tace, kallan ta sultana tai Zuwaira jiya Da daddere ina kikaje? Gabanta ya fadi ya zatai gaskiya zata fadawa sultana koya,tsareta Da ido sultana tai tana San taji me zatace,ta bude baki kenan zata fara magana sukaji ana fadin ga yayan sarki nan zasu shigo, hakan yasa KO wacce baiwa ficewa suka zube suna kwasar gaisuwa banda sultana dake kokarin daura Dan kwalinta Zuwaira kuwa jan bargo tai ace bata Da lafiya,.
Chapter 16 · 0% Book details