← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bakin kofansu sukaji marka Na fadin ga dakin nan, sosai gabansu gaba daya ya Yanke tsabar tsoro ai tuni Zuwaira tai kara shigewa bargo, Da sallama marka Ta tura kofan dakin ,sultana dake tsaye Ta amsa, idonta kan sultan ya sauka Da yake yiwa dakin kallan kurillah, dauke kai tayi ganin hankalin nasan dawowa dakin, kallan ta yayi ya dauke kai, karawa Hafiz yayi ya kalli sultana, ke Amman duk yadda akai baki da gaskiya ace mutun kullun fuska a rufe yau shine hadauwar mu Ta wajen uku kenan Amman ban taba ganin fuskarkiba ya zama dole Inga fuskar wacce take zama daki daya Da wacce nake so, zaro ido sultan yayi yaune yataba jin Hafiz yace GA wadda yake so allahalin ya batata Allah yasa ta wannan haryar ne zai shiryu,.

Gabanshi sultan Ya shiga malam kayi abun Da ya kawo ka ba kasawa wata idoba ina ruwanka Da itta, yana kaiwa nan ya riko hannun sultana, saida yaji shock Amman Ya daure ta fice Da itta,.

Zuwaira kuwa maloo tai bargo ya zatai Da wannan mutunmin kawai guduwa zatai, kallan dakin Hafiz yayi ya Saki tsaki baiga gun zamaaba, ke meke damunki ya fada a dan tsawace, ba komai dama zazzabine kuma ya sauka, tabe baki yayi, gobe ki sameni yana kaiwa nan ya fice ta sauke ajiyar zuciya itta ya zatai dashi ne Ma kawai so yake ya jaza mata masifa Dan tasan mama ba yadda zataiba,.

Suna fita waje sultan ya Saki hannun sultana ya gallah mata harara kinga ki kiyayi kanki Da wannan banzan ba hankaline dashiba banda bata mata ba abun Da ya iya,batace komaiba kawai binshi take, ganin Ya nufi bangaren momy Yasar tabi bayanshi dama nasan fadawa momy Sun dawo ,.
Da sallama ya shiga Tana biye dashi bayin gun suka kwashi gaisuwa Amman momy bata nan itta kwata kwata bata fiya zama a cikin bayiba,haka take, kallan jakadiya yayi jakadiya yaufa kindirmo nake San sha, a aikuwa kazo a saa dan kuwa akwai yau aka siyo yana fridge, kallan sultana yayi jeki debo ki kawomin ki sameni agun momy, an gama ranka ya Dade Ta fada tare da wucewa shi kuma yai sama,.
Da sallama ya shiga taba parlour tana rubuce rubuce, kallan shi tai Tana murmushi welcome son yau ka tashi Da wuri agun aiki, murmushi yayi tare da fadin wlh mom,

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 40*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Zama yayi a kujera, sannu son kunje ka siyawa sultana sim card din dan yau kwata kwata ban gantaba, Da sallama sultana ta shigo, zama tai kusa Da momy ina wuni Momy, shafa kanta tayi tare da fadin kina lafiya? Qlau wlh Mom yama siyamun sim din, OK mom tace sannan ta karbi phone din, matsawa kusa dashi tai ranka ya Dade gashi Ta ajjiye, sannan ta koma kusa Da momy,.

Mika mata wayan momy tai ta karba zata Tashi mom tace ta koma ta zauna tanasan yin magana Da sultan, daukan kindirmom yayi yana sha, son magana zamuyi Mai mahinman ci, OK inaji, son kana Da wacce kake sone?kallan momy yayi sai kuma ya kalli sultana ya bata wata harara a hankali yace aa mom, ajiyar zuciya ta suke, OK naji kana San Hindu ne, Da sauri ya furzar Da Da furar Da yakai bakinshi har saida ya kware, sannu mom tace kallan ta yayi,.

Haba mom meyasa kika mun wannan tambayar wlh badan Allah take sona ba ittama nina Na sani sannan kinfi kowa sanin bana Santa, hmmm aiko hakuri zakayi Dan na yanke shawarar hadaku aure nida mahaifinta nasan wata rana zaka sota ai, Amman kana Da chance a duk sanda kaka wacce kake so zaka iya Aura koda kuwa ranar auren sai mu hada duka Amman wannan auren zumunci zamuyi Wanda babanka yake mafarkin yi ina fatan ba zaka ban kunya ba plz son ,.

Shiru yayi ranshi na soya Amman duk soyan rannan nashi hakan bazaisa yayi mata musuba ittace maman shi kuma bananshi zai iya yin komai wa itta,.

Sultana shiru tai batace komaiba Amman tana hango masifar Da zaai tsakanin hindu Da sultan tunda itta shaidace baya santa,.

Kallan mom yayi bakomai mom Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi yana kaiwa nan ya fice abunshi, Mon ta sauke ajiyar zuciya tasan kawai ya fada ne dan ba yadda ya iya, kallan sultana tai wadda ittama jikinta yayi sanyi, jeki kira mun jakadiya,to tace tare da mikewa ta fice, sai gata ta dawo, .

Dakko takarda da biro hakan akai, sultana karbi ki rubuta abun Da zan fada, karba sultana Tai,.

Bayan sallama ta daura Da sako zuwa fada a sanarwa Da sarki cewa sultan ya amince Da auran hindu zasu iya saka rana a ko wanne lokaci sannan akai sallama, taba jakadiya tace takai sakon, Ta karta tare da ficewa dan cika umarni,.

Kallan sultana momy taii dauki furar nan ki kaiwa sultan, sannan a matsayinki ka kanwarshi kisan yadda zaki kwantar Mai Da hankali, daukan furar sultana tai ta fice ta nufi bangarshi,.

Da sallama ta shiga yana parlor ya jingina Da kujera

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 41*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

Da sallama ta shiga Part din nashi, yana xaune a kan kujera ran a bace yake, wai taya zaai ace ya auri Hindu yarinyar Da bata Da tarbiya bata san abun dake mata ciwo ba dadin dawa bama ya Santa,.

Karasawa parlour tayi tana kallan shi taya zata fara tunkarar shi gaskiya momy Ta hada ta da aiki ,Jiyar zuciya ta sauke ta karasa gunshi ta ajjiye Mai, kallan ta yayi Maye wannan kije dashi bana so, murmushi tayi kayi hakuri ranka ya Dade bai kamata wai dan akan hakan kana fushiba ai abun alkhairine Ma ace kana Da aure kamarka ranka ya Dade ace baka Da mata, juyawa yayi yana kallan ta it like yasan wannan muryar, tsaki yaja ya koma ya zauna ki dauke abunki ki wuce dashi banaso nace, OK Ta fada tare da ajjiyewa amma ranka ya Dade aduk halin daka tsinci kanka kana salati hakan zai sanyaya maka zuciya, baice komaiba kawai yayi shiru Amman zuciyarshi tafar fasa take, daga waje yaji ana shelar cewa gobe ana taron kowa Da kowa zuwa gun Sa ranar yarima sultan da yar sarki Hindu, Wanda zaa yi gasar harbin kwari Da baka a bisa Al, adar wannan Masarauta indai abun farin ciki ya samu suna wannan gasar sannan ansa babbar kyauta GA Wanda yaci wannan gasa , kallan sultan sultana tayi ya wani Kara hade rai kamar hadari,.

Juyawa sultana tayi zata fice dai dai lokacin Hindu ta shigo Da sallama, kallan sultana tayi, ittama kallan ta sultana tayi kafin tai kasa Tana kwasar gaisuwa, murmushi Hindu tai kiyi mikewar ki yau ai ranar farin cikine saboda haka karki wani damu so nake muyi magana dake, kallan ta sultana tai sai kuma Ta Saki murmushi Ta Mike tabi bayanta, zama Hindu tai a kusa Da sultan, Ta tabe baki dole dai a so ni wlh, yana jinta baice komaibq kuma bai dagoba,

Kallan sultana tai plz zuba min wannan furar yau kinsan yadda nakejina kuwa a sama nake jina, murmushi sultana tai ta mike taje kusa Da furar Ta zuba mata Ta mika mata, thanks ta fada Tana murmushi,plz zauna akan kujera yanZune lokacin ki Da ya wuce bazaki sami wannan damar ba kinsan yaushe zai wuce? Aa sultana ta fada tare da zama daura kafa kan daya tana jijjagawa tare da fadin Bari inyi anfani Da damata,, murmushi kawai Hindu tai, daga ranar dana shigo wannan bangaren a matsayin matar uban gidanki kashinkine zai bushe,, zaro ido sultana tai kice inyi anfani Da wannan damar karta wuce, amma dole insa wannan ranar a tarihi, murmushi Hindu tai hakama sultana,.

Hindu taci gaba kinsan me yasa gasar harbi? Gyara zama sultana tai fada mun insha plz, saboda ke nasan ba abun Da kika iya nasan ba zaki iya ciba shiyasama nace harda mata, wani kayataccen murmushi sultana tai inkuma naci fa mai zai kasance? Motace haddadiya nasa kinaci shikenan ittace kyautar ki, gyara zama sultana tai ai kuma baki tsanmanim zan ci ai kamata yayi kiban dama IN dama KO?ok fadi ina jinki koma Maye zan iya miki ,koma maye kin dauki alkawari? Daga kai Hindu tai batare Da wani tunani ba, koma Maye Dan nasan ba iya ci zakiyo ba, mikewa sultana tai Tana murmushi zan wuce sai mun hadu gobe, ta juya tana kallan sultan dake dauke Da murmushi KO Na maye oho Mai, ta kalli Hindu tai tare da daga mata hannu, da harara Hindu ta rakata ai nasan ba zaki iya ciba koma Ma ye ina dauke dake banza kawai, haka taitaiwa sultan surutu shidai baice komaiba dan kanta Ta gaji Ta fice,.

Suna zaune a daki duk su ukun, Zulai take fada musu zancen kasar, tsaki Zuwaira taja wannan ai shashanci ne sai kace a littafin yaki wannan ai aikin banzane, mtswwww taja tsaki, murmushi sultana tai kinga kuwa nima zan shiga wannan gasar kawai saboda sultan da momy duk basa San auren saboda zan shiga, duk kallan ta sukai To dan basa so taya kika ganin zaki cecesu a matsayin ki Na baiwa? Murmushi tai sannan ta fada musu abun Da take shirin yi, zaro ido Zuwaira tai kafin Ta taba wuyan sultana anya kuwa ba zazzabi kike ba, dariya Zulai tasa kaji bama wannan ba a ina Ta isa harbi sai kace yar gidan maharba, murmushi kawai sultana take,.
Riko kafadar Ta Zuwaira tai Dan Allah ki tashi daga wannan baccin kinsan Hindu ba zata taba amincewa Da wannan kudurin nakiba,.

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 42*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com
Ture hannunta sultana tai banisan Iskanci Na fada miki saboda abun Da zanyi babu ruwanki, tabe baki Zuwaira tai kawai,.
Chapter 17 · 0% Book details