← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita wasu suka Fara binta a baya, juyowa tayi kartine har uku banda idonsu Wanda ba dugon imani ba abun Da take gani Da sauri ta Fara tafiya, tanaji dayan Na fadin ai kasheki zamuyi wannan umarnine daga sarki duk wadda hafiz Ya kuka kisa ne, zaro ido tai tare da kara sauri,. Tafiya take suma basu fasa binta ba saiji tayi An riko ta, kafin Wanda ya rikota Ya juya Ya Kalli sauran tare da fadin zanji Da itta , jin hakan Yasarm suka juya dan sun ganshi Da irin kayansu .
Tunda ya rikota tasan shine dan taji kanshin turaren shi handala tayi,. Rike hannutq yayi har part dinshi Da gani ranshi a bace yake hakan Yasa sultana ta fara tsorata,yana zuwa Ya hada ta da bango tare da kallon idonta, kafin yace dole yau ki fadan dalilinki Na fitowa Da daddare a wannan masarautar

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 35*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```

Tsuru tsuru tai da ido, saboda yadda ya tasa ta a gaba har tanajin nunfashin shi, dan juyar da kai tayi yai saurin riko habarta, bani amsa inba hakaba wlh saidai mu ta tsayowa a haka muma kwana a haka ba damuna zai yiba, to sakeni sai in fada ma Ta fada Tana kallan shi, harara Ya bata kafin Ya saketa, ajiyar zuciya ta sauke ta na tunanin wacce karya zata shirga mishi kuma, kallan ta yayi ganin Tana tunani Yasa yai murmushi tare da fadin wlh kika sake kika mum karya nida kene, rau rau tai da ido kafin ta sami gu kusa dashi Ta zauna, uhmmmm dama dai wlh kasa bacci nai shine Na fito waje to dana fito shine nake yawo, shine wadancan suka ganni suka biyoni ni ba abun Da nai musu, ganin yadda ya hade rai Yasa tai kara tsorata baice komaiba kawai kallan ta yake ranshi a bace,.
Dan kara dubul bulcewa tayi wlh kadai bari in fada maka gaskiya wlh, dama muna bacci ne naga anzo an dauke Zuwaira shine Na biyo bayansu dan inga inda zasu kaita,hmmm yace tare da dauke kai, ya dauka ba zata fada Mai gaskiya ba,.

Kallan ta yayi, wato so kike a bataki kema KO?dan zaro ido tai Tana kallan shi, eh mana hakane inba haka maye naki Da zaki biyo bayansu inyaso koma Maye a hada dake KO? Ranka Ya Dade Zuwaira fa yar uwatace, tare muke a daki daya taya ina gani zaa dauketa ban biyo baya ba, haba ai ban cika kawaba, murmushi yayi ganin yadda take fada mai kenan zata iya yin komai game da kawarta wowww wannan abun Ya burgeshi friendshi kenan,. Dauke kai yayi Ya dauki system dinshi Da dama can a kunne take Ya ci gaba Da aikin shi,.

Kallan shi tai, kafin ta Fara magana a hankali ranka Ya dade na gode Da taimakon da kake ban na gode dafa tuni Na Dade da, mutuwa baice mata komaiba yaci gaba Da abun Da yake, Amman ranka Ya Dade wai taya kake fitowa a irin wannan lokacin ni abun naban mamaki fa, kallan ta yayi, kafin Ya dauke kai baki San komai game da wannan masarautar ba, MASARAUTAR MUCE baki San komai game da itta ba, tabe baki tai, wai masarautar suce,.

A kullun irin wannan lokacin ina fita ina zaga wannan masarautar saboda Inga ta,asar Da ake aikatawa tun ina yi a boye har yazo nake baiya na kaina har ya kasance nasan Wanda suke Da sa hannu a wannan abun, uhmmm to zaka fada mun dawa dawa ne suke Da hannu a hakan? Kallan ta yayi saboda ke wace? Dauke kai tayi Tare da fadin hmmmm, sai kuma Ya kalleta tare da fadin zonan sultana, kallan shi tai bata gane zonan ba, ganin Ya kafeta Da ido Yasa ta Mike ta Dan matsa kusa da shi, mikon hannunki wancan Ya fada yana nuna mata hannun hagunta, kirjinta ne Ya fadi, ran ka Ya Dade ban ganeba, eh cinye hannun Xanyi Ya fada yana kallan ta, kayi hakuri ranka Ya Dade Amman bazan iya baka hannunaba ai babu kyau Na miji Ya taba hannun Mace kuma ba badan dole ba aibanga abun Da zaisa IN zauna Da kai anan ba niba Matar ka ba, zaro ido yayi ni kike fadawa magana? Aa ranka Ya Dade ba magana nake fada maka ba yi hakuri indai Na bata maka rai, ajiyar zuciya Ya sauke kafin yace to muga hannun naki niba tabawa zanyi ba, kallan shi Tai kafin ta mika mai hannun, kallan hanun yayi sultana wannan zanen nake San karin bayani da gani bada lalle aka Yishiba so nake nasan Dame aka yi kuma kamar zanen masarautar mu,.
Dauke hannu tai ni haka Na taso naga hannun nawa, bansan daga inda yake ba, kallan ta yayi kafin yace zan iya ganin fuskarki sultana yana magana a hankali kamar ba shiba, gabanta ne Ya fadi ina ba zata yadda ba wlh, Dan Allah ranka Ya Dade kayi hakuri ni bazan iya budema fuskata ba tsorata zakai dan fuskata nada matsala, mikewa yayi Ya zauna kasan kusa Da itta, ni a hakan nake San ganin naki, gabanta banda dukan tara tare ba abun Da yake, Dan Allah ranka ya Dade kayi hakuri bana San abunda zaisa hankalinka Ya tashi Amman maye naka Na San dole sai kaga fuskata? Nima kawai Na tsinci kaina Da hakan ne Amman karki fassara dan ba sanki nakeba kkawa jikina yana ban ke kamar kina Da hadi danine saida naga wannan zanen ma, danja baya tai niba wani hadi Da nake dakai ni a jigawa nake Dan Allah kayi hakuri ,kallanta yake kafin ya fara tunani saima ta rainaka Ta dauka santa kake Amman ka tsaya kana wani damun dole sai kaga fuskarta alhalin ka wuce wannan gun, tashi daya yaji haushin kanshi ya mike ya koma kan kujera Ya hade rai karta raina shi

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 36*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Binshi tai da kallo yadda ya wani hade rai kamar ba shine Wanda ya gama make mata murya ba,.

Shiru tayi tana tunanin koya Zuwaira zata kasance may be Ma yanzu Ya gama bata ta Yasa ta fito an kashe ta KO ma meyasa yake sawa ake kashe bayin Allah oho Mai Amman zataso jin dalili kuma Zuwaira ce kawai zata mata wannan taimakon,.bacci take ji Amman shi KO a jikinshi Ya wani bude system kamar ba dareba,hamma tayi Dan ya gani Ya nuna mata inda zata kwanta KO kallan inda take baiyiba, ta sake yin hamma Da karfi har saida yadan tsaya Da abun Da yake kafin yaja tsaki yaci gaba Da abun Da yake tabe baki tai kafin tai murmushi bari tadan tabo masifar shi, karayi tayi Tana salati, a hargitse Ya kalleta waike meke damunki kinzo sai damuna kike, ha,a kallan shi take yana mata masifa, ranka Ya Dade bacci nake ji shi yasa, to rike ki nayi kije kiyi kwanciyar ki mana, kallan shi tai sai kuma ta mike ta nufi kofa taga Ko zaice Ya dawo, ganin har taje kofa baice komaiba yasa ta dan Saki tsaki ta bude kofan, idonta na sauka kan duhun tai maza ta dawo,.

Shi kuwa Kallan ta yake yana Allah dai Yasa yarinyar nan ba ficewa zataiba dan yaga tana fama Da danye kai, kallan shi tai kafin tai sama inda ya nuna mata ranar,.

Washe gari Zuwaira Da wuri ta tashi Dan batai wani bacci bama, tana jin Hafiz Ya fice masallaci, ta Mike Amman sai Da take bari gari Ya danyi haske kafin ta fito ta kama gabanta har gudu take hdawa dashi,..
Sultana bata tashi Da wuriba saboda ba sallah take ba gashi jiya bata Sami wani bacci ba, baccinta take bilhakki abunta gata tajita akan lallausan gado haka abun baa magana,.

Hindu Yau 9:00 nayi ta shirya ta nufi part din sultan Dan itta ta gaji wlh auren shi take San yi, zataje suyi magana tunda 10:00 yake fita aiki,.
Da sallama ta shiga part dinshi ganin baya parlour Yasa tai sama xuwa dakin shi knocking Ta Fara yi tana fadin Yaya sultan,.
Sultana dake bacci taji ana knocking da sauri ta mike ta saka dankwalinta ta fito, dai dai Hindu zata sake knocking kenan sultana ta fito, kallan Hindu tai ta kara murza ido Dan tabbatar wa Da idonta abun Da take gani indai ba karya bane sultana anan ta kwana.

Hade rai Hindu tai Me kike yi anan kardai kice anan kika kwana dan zan iya yin kisa indai naji hakane,? Ta fada tare da nufar sultana, kallan ta sultana tai batace komaiba Tana shirin rabawa ta wuce Hindu tai saurin rikota tare da hada ta jikin bango, wlh ki fada mun KO kuma yanzu inyi kisa ba abune mai wuya a guna ba, ta bayanta taji sultan yana fadin eh anan ta kwana KO kina Da ja ne? Bata kalleshi ba sai kallan sultana Da tai kika kwana a bangaren mijina daga zuwanki zaki bata mun miji, ta fada tare da sake sultana gara wlh in kashe ki IN huta, kokarin kwace kanta sultana take, har kin isa ke Yar uban wace kina baiwa,.

Cikin zafin nama sultan ya jawota tare da dauke Ta da mari , Da sauri ta dafe gun Tana kallanshi, gara suit dinshi yayi yana hararar ta, wlh duk sanda na kara ganinki a kan wannan yarinyar ni da kene bazan iya auren kiba, na fada miki baki cika abun Da nake so ya mace ta cika KO a harkar addini sai na Yar dake balleh aje ga tarbiya, Da gudu Ta fice tana kuka, direct bangaren babanta sarki tayi.

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 37*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Chapter 15 · 0% Book details